Showing 63001 words to 66000 words out of 89717 words

Chapter 22 - Aneesa Complete Hausa novel

13 Jul 2024

17491

"to 'yar birni
sae ki tashi ko nn xaki xauna," tace "A'a a
nn ni xan tsaya da ummi," ya juya yana
kallon Mujaheed da har ya kusa bakin kofa,
xae yi magana Hajiyar tace "to fateema ki je
kuyi sallama da yayan naki mana," a kunyace
ta mike ta bi bayansu, Mujaheed bae ko
kalleta ba ya shige motarsa Mudatheer na yi
masa sallama, ta dan tabe baki, ta juya ta
koma cikin gidan abun ta. Mudatheer yyi
murmushi, Mujaheed ko yyi horn ya ja
motarsa ya fita daga gidan, throughout
ranar Aneesah na dakin mumynsu ummi, ji
take kmr Amminta ce, ta mance duk wani
damuwa dake xuciyarta, gashi matar tana
da kirki ssae, duk kyanta 'ya yanta uku suka
biyo barin Mudatheer, Mudatheer ne babba
sae kanwarsa dake aure a kaduna, snn
autansu Ummi, da yamma tare Aneesah
suka yi girki da ummi, tana daki da daddare
ita da ummi suna lbri, Hajiya ta shigo tace
"suje su gaida Abba ya dawo," suka sauko
xuwa falonsa yana xaune yana kallon News,
yace "A'a yau bakuwa mukayi a gidan,"
Aneesah tayi murmushi ta gaida sa, ya amsa
da fara'arsa yana jansu da wasa ita da
ummi, sae a snn taji ashe uba ma na da ddi
a rayuwa don bata taso ta ga nata ba, don
hka bata taba experiance din son uba ba da
carin dinsa, nn ya sallamesu yace suje su
kwanta xae kalli news, suka masa sae da
safe suka bar falon nasa. Mujaheed na koma
wa gida ya tar da Hajiyarsa ta dawo da
kanninsa biyu, sae yaji shakkar karasawa
falon ganin yanda mahaifiyartasa ta hade
rae ssae. Ya fita balcony ya kira Hydar yace
"guy, meyasa baka gaya min su Mum sun
dawo ba," Hydar yace "shima bae sani ba,
mujaheed ya tambayesa yana ina, Hydar
yace ina gidansu Najeeb sae mun yi waya,
yana kai wa nn ya kashe wayar daga jin
yanda yake wayan ransa a bace yake,
Mujaheed ya shiga falon ba tare da ya kalle
mahaifiyartasa ba yyi mata sannu da xuwa
xae haura sama ta daka masa tsawa tace ya
dawo
~30~
Hajiyar ta mike tsaye tana kallon Mujaheed
da ya tsaya dai dai kusa da stairs yana jiran
cewar Mahaifiyartasa, ta karaso har
gabansa tace "daga ina kke Mujaheed?" ba
kasafae Hajiyar ke kiran sunansa ba sae dae
tace prince, hkn ya nuna masa lallai tayi
fushi da shi ssae, ya dan yi shiru snn yace
"daga office nake," tayi masa wani mugun
kallo tace "ubanka xaka raina ma hankali
ko?" bae ce mata komai ba sae kallonta da
yake yi, a nutse ta fara magana tana
kallonsa da kyau tace "wllh wllh ka sake sa
hannunka cikin case din yarinyar nn ko
kuma ka sake xuwa gunta Allah ya isa ban
yafe maka ba Mujaheed, kuma ka wuce ka
hada kayanka nn da kwana biyu ka bar
country din gaba daya dad dinka yace kaje
ka samesa, ni dama shi yasa bana son kana
hulda da wnn mai taurin kan Aliyu da bae
maida mahaifiyarsa komai ba, don influence
din min kai yake kai ma ka gagaremu kmr
yanda ya gagare uwarsa," Tunda ta fara
magana Mujaheed ya jingina jikin stairs ya
lumshe idonsa har ta kai aya snn ya bude
idon da kyar yana kallonta yace "mum, wllh
marainiyace yarinyar ku tausaya mata......" ta
daka masa tsawa a fusace "bace ka ban
waje kar ka dada bata min rae," bae ce mata
komai ba ya haura stairs din, yana bala'in
respectn iyayensa yana gudun bacin ransu
barin mum dinsa, bambancinsa da Hydar
knn, don shi ba ruwansa inda ya sa kansa
nn yake dosa bbu wanda ya isa ya hanasa.
Hydar kam bae ko kalli Mahaifiyarsa dake ta
masifa tun bayan shigowarsa gidan daga
gidan Aminin late dad dinsa Alhaji usman
ba, shima can yyi ya gaji ya kyalesa , yana ta
harkokin gabansa a gidan kmr bae san da
shi take ba, ta gaji don kanta tayi shiru,
karfe goma na safe ya shigo falonsu cikin
kananan kaya, Hajiyar na xaune da su sumy
suna kallo, bae ko kallesu ba ya dae gaisheta
bata tanka masa ba xae fita ta sha gabansa
da sauri tace "gidan ubanwa xaka?" yana
kallonta yace "fita xanyi," a fusace tace "bbu
inda xaka wllh," yace "dalili" xata yi magana
sumy ta tabe baki tace "kai ke ma dae mumy
da wahal da kanki kike wllh, ki ta bata bakin
ki a kan wanda bae ma san kina yi ba, ke
ina ruwanki? kawae ki rabu dashi yyi yanda
ya ga dama, dis tym around idan aka yanke
masa hukuncin daurin rai da rai can ta
matse masa ae ba shi kadai kika haifa ba,
iya ka ....." ta fasa ihu ganin yayo kanta kmr
xaki, ya cafketa, da kyar Hajiya ta kwace ta
don laga laga yyi mata, ya fice daga gidan,
ita kuka Hajiyar kuka. Pretty dake kan dinnin
table ta kife kanta tana ta dariya a hankali.
Gidansu Mujaheed ya nufa, yana shiga daga
bakin kofar hajiyarsa ta tare sa ta yi masa
sannu da xuwa faram faram snn tace wajen
wa ya xo, yace mujaheed, tace "ayya ae
daxun nn ya tafi airport dad dinsa na
nemansa, na san xuwa ynxu ma jirginsu ya
tashi," ya tsaya mata kallo mai shige da ta
rainin wayo, xata yi magana, sae ga
Mujaheed ya sakko yana kallon Hydar, Hydar
ya juya a fusace ya fice daga gidan, Hajiyar
ta juya ta balbale Mujaheed din da masifa
tana cewa bana ce maka bana son
taraiyarka da Hydar ba, gulma ce ta sauko
da kai ynxu ko me? bae saurareta ba ya dan
ja tsaki ya koma sama, yana shiga daki kiran
Hydar ya shigo wayarsa, ya daga Hydar yace
"ina ka kai Aneesah?" sae da yyi shiru na
kusan minti biyu, har sae da Hydar yace "re
yhu there" snn yace "tana gidansu
Mudatheer," Hydar yace "waye Mudatheer,"
nn ma sae da yyi shiru snn ya basa amsa
yace "abokina ne," Hydar yace "ka ban
Address," Mujaheed yace "kayi me da shi,"
kan Hydar ya basa amsa yyi saurin cewa ok,
bari nayi maka tex din address din, yana kai
wa nn ya kashe kiran ya tura masa address
din ya fada kan gado yana jin wani xaxxabi
na neman rufesa. Da yamma Hydar ya tafi
gidansu Mudatheer, a waje yyi parkin
motarsa dae dae lkcn da Mudatheer ya fito
da motarsa daga gidan xae fita, ya tsaya
suka gaisa snn yace masa gun Aneesah ya
xo, Mudatheer yyi parkin a waje snn suka
shiga gidan tare, har falo ya shiga da shi
snn yaje gaya ma mum dinsa ta shigo falon
suka gaisa da Hydar din, tana cewa kai ne
wanda Mujaheed yace min xae xo knn, yyi
murmushi yace nine mum, tace to bari na
turo maka ita, yana xaune suna dan hira da
Mudatheer Aneesah ta shigo falon da ummi,
jikinta yyi sanyi ganin Hydar, ta nemi gu ta
xauna, ummi ta gaishesa ya amsa yana
murmushi snn ta koma daki, Mudatheer yyi
ma Hydar sallama shima ya fita, kanta a kasa
ta gaishesa, shima ba tare da ya kalleta ba
ya amsa, snn yace "baki da wata matsala nn
ko," ta gyada masa kai tana kallonsa, ya
daga kafada yana kallonta ya mike tsaye
yace "ok gud, saura nn ma ki watsar da
mutuncin naki," ya ciro kudi ya ajiye mata
yace "incase kina da wani bukatan," yana
kai wa nn ya juya ya fice daga falon ko
sallama da masu gidan ma bae yi ba, ta bi sa
da kallo hawaye na bin kuncinta, ta mike da
kyar tayi hanyar dakin ummi ta fada kan
gado ta fashe da kuka.
.
Mujaheed ya sauko downstairs a hankali
yana kallon mahaifiyarsa dake xaune kan
kujera tana kallo lkci daya tana cin fruits din
dake cikin bowl a gefenta, 'yar aiki na
durkushe gabanta tana yanke mata kumba,
ya karaso cikin falon ya xauna yana kallonta
yace "mum xan dan fita don Allah," ta hade
rae ta juya tana kallonsa tace "xuwa ina?" ya
dan sunkuyar da kansa yace "gidansu
saleem xani wllh," tace "shknn amma kar ka
dde, bari na baka sako ka kai ma Hajiya
Amina," kai kawae ya gyada mata ta mike
tayi hanyar stairs, ya tsaya kallon 'yar aikin
dake durkushe wajen tana jiran dawowar
Hajiyar, ya girgixa kai ya kauda fuskarsa,
ynxu duk masu aiki irin hka tausayi suke
basa sbda Aneesar sa, yana kallonta yace
"kinyi makaranta," ta dan tsorata don bae
taba mata magana ba, ta gyada masa kai a
tsorace tana gyara hijabinta, ya ciro check
ya rubuta kudi mai yawa, ya yaga ya mika
mata yana kallonta ya girgixa mata kai yace
"kar ki sake dawo wa nn da sunan aiki, ki
kai ma mamarki ku ja jari, ki ci gaba da
karatunki, ki kuma boye kar Hajiya ta gani,"
hawaye ya cika idon yarinyar tana kallonsa
xata yi magana, ya girgixa mata kai yace
"kar ki gode min," yana kai wa nn ya mike
ya bi mahaifiyarsa sama, ya karbi sakon ya
fito ya shiga motarsa ya bar gidan. A can
gidansu saleem ya kira Mudatheer yace "ya
datheer ka koma gidan ka bata," Mudatheer
yace "bari na kai mata tana daki," ya katse
kiran yyi hanyar dakin kanwarsa ummi, yyi
sallama suka amsa masa, tana xaune ta
tsura ma Tv ido duk da ba sanin me akeyi
tayi ba don tayi xurfi a tunaninta, ummi
kuwa na xaune tana assignment don har ta
fara higher institution, ya karaso cikin dakin
yana kallon Aneesah yace "ya dae
kanwarmu, lfyarki kuwa," ta kirkiro
murmushi tace "to ca nayi maka banda lfya
da " ummi tace "shi dae na gani, ya shigo da
borin kunyarsa bae siyo mana abinda yace
ba," mudatheer yyi dariya, Aneesah ta tabe
baki tace "ashe dae kin ganosa ummi," ya
mika mata wayar yace "kar ku damu anjima
da nyt kafin Abba ya dawo sae mu fita duk
ku xabi abinda ku ke so, gashi nn Mujaheed
xae maki magana," da sauri ta amshi wayar
ta wara ido tace "yayana," kai kawae ya
gyada mata tace "na kirasa?" wayar ya shiga
ring ta daga da sauri cikin tsigar shagwaba
duk da ba da gangan tayi hkn ba tace
"yayana," Mujaheed ya lumshe ido yace
"kanwata," a sanyaye ta gaishesa, shima ya
amsa a hkn, snn yace "baki da matsala ko
kanwata," ta gyada kai kmr yana ganinta
tace "eh yayana, baka xo ba kuma har
ynxu," yyi shiru hkn yasa, tace "yayana," ya
amsa a sanyaye yace "kanwata," tayi shiru,
yace "xan xo kanwata, bana nn ne ynxu
kinji, ba Hydar yana xuwa ba," ta gyada
masa kai da kyar tana kkrin maida hawayen
da ya taru mata a ido, yace "xamu dinga
waya kanwata, i luv yhu dearly," ta dan juya
ta sace kallon ummi da hankalinta ke kan
takardarta, Mudatheer dama tuni ya fita, a
sanyaye tace "i luv yhu 2 yayana," yyi
murmushi da ya bayyana dimples dinsa a
hankali yace "ngd kanwata," ta gyada masa
kai kmr yana ganinta, yyi mata bye ya katse
kiran, ya kife kansa kan computer desk din
dake dakin salim don kan kujerar yake
xaune, xuciyarsa na tafarfasa, ya rasa
abinda ke masa ddi a duniyar, to ynxu mae
xae yi ya taimaki Aneesah kafin a sake xama
kotu, Abdul ya fado masa, ya mike xaune da
sauri, "he might be of help 2 us" ya fadi a
hankali yana tunanin inda ya ajiye
complimentary card din Abdul din, ya mike
tsaye da sauri ya fice daga dakin don
saleem na wanka ne, ya fita xuwa motarsa
ya bude ya shiga duba card din, cikin ikon
Allah ya gani ya dauka yana kallon numbrs
din Abdul, yyi murmushi ya ciro wayarsa ya
shiga kwashe nmbr.
.
A Eatry Mujaheed ya hadu da Abdul kmr
yanda suka shirya, suna gama gaisawa
Abdul yace "nayi ta jiran call dinka shiru,
kuma naje can gidan sau dayawa bana
samunka," Mujaheed yace "eh ina kano"
Abdul yace "ok, ina kanwartaka," Mujaheed
ya shashantar da batun yace "ya kuma aka ji
da abinda ya faru da dad dinka" da mamaki
Abdul yace "A ina kasan dad dina?"
Mujaheed yace "A haba dae wanene bae san
Honourable Shehu ba a nn Abuja," Abdul ya
daga kafadarsa yace "wnn kuma shi ya
siyan ma kansa," da mamaki Mujaheed yace
"don me xaka ce hka Abdul, ba dad dinka
bne," Abdul bae ce komai ba ya daga
wayarsa dake ringing, Mujaheed ya tsura
masa ido yana dan murmushi jin irin
turancin da yake, har ya gama wayar snn
yace "A abroad kke knn?" Abdul ya gyada
masa kai ba tare da ya kallesa ba, Mujaheed
ya jinjina kai yace "wae me dad naka yyi hka
ne? An sake sa kuwa? " Abdul yace "A'a ban
sani ba, kuma dukiyar da ba tasa ba ke
hannunsa," Mujaheed ya girgixa kai
fuskarsa dauke da damuwa kmr gaske yace
"dukiyarsu waye?" "na kaninsa ne," Abdul ya
fadi yana maida wayarsa cikin Aljihu, yanda
Abdul ke ba sa amsan ya nuna masa baya
son xancen, Mujaheed yace "ayya, kuma ina
kanin nasa," Abdul ya gyara xama lkci daya
ya dauki lemon gabansa yana sha yace "he'z
late," "to iyalensa fa?" Mujaheed ya sake jefo
masa wani tambayar, Abdul yyi masa wani
irin kallo yace "am i here 2 answer yhur
unnecessary questns?" Mujaheed ya dan
saita murya yace "ba hka bane abokina, i
just want 2 knw ba dae kanwata kke son
gani ba, xan kai ka wajenta yau," Abdul yace
"iyalensa suna nn mana," Mujaheed yace "nn
garin?" Abdul ya dan yi shiru snn da
damuwa yace "ban san inda cousin din
tawa take ba, hka ma mum dinta ban san
inda dad dina ya kai ta ba," Mujaheed ya
tsura masa ido yana kallonsa sae a nn ya
lura da kaman da suke yi da Aneesah ssae
kuma, don Abdul kyakkyawa ne na karshe,
idonsa exactly na Aneesah, Mujaheed ya
kauda kansa yace "kasan me nake so da kai
Dr," Abdul yana kallonsa yace "am ol ears,"
mujaheed ya fara magana murya can kasa
yace "Abdul, idan ka bani hadin kai wllh xan
nemo maka cousin din taka, i just want yhu
2 help me, ni kuma nayi maka alkawarin xan
fito maka da 'yar uwarka don nasan inda
take," da sauri Abdul yace "me kke bukata
daga gare ni?" Mujaheed ya dan yi cylnt snn
yace "ka samo min information din inda dad
dinka ya kai mata mahaifiyarta, snn na san
baxa ka rasa sanin inda document din
dukiyarsu da komai yake ba, don hka nake
son ranar da xan nuna maka ita ka taho da
su ka damka mata a hannunta," Abdul yyi
masa mugun kallo yace "kai din wa xaka sa
ni nayi hkn?" Mujaheed ya daga kafada ya
mike tsaye yace "ok, i wil b on my way,"
Abdul yace "wait, ka gaya min meye hadinka
da su?" ya koma ya xauna yana kallon Abdul
da kyau yace "Aneesah da kke nema tana gu
na, amma baxa ka ganta ba har sae ka san
inda Amminta take ka gaya min," Abdul ya
mike tsaye da sauri yace "ok wnn ba
matsala bane, amma yaushe xan ganta?"
Mujaheed yace "as soon as Amminta ta
bayyana," Abdul yyi shiru kmr mai naxari
snn yace "ok nn da kwana uku xaka ji ni,"
Mujaheed ya mike tsaye yace "to ngd i wil b
on my way," Abdul yace "wait, ka gaya min
kai waye don Allah," Mujaheed yace "sunana
Mujaheed Muhd," a tare suka fita daga eatry
din suka yi sallama da juna a kan sae nn da
kwana biyu xasu hadu. Aneesah na xaune a
garden ita da ummi, sanye suke cikin riga
da skirt gaba daya, ranar dae ummi ta tilasta
Aneesah ta dan yi light make up tayi kyau
ssae har ba a magana, suna game a laptop
wayar ummi yyi kara, Aneesah ta daga
ganin mummy ce ke kiran, tace "mumy har
kin shirya," mumyn tace "Aneesah ce?"
Aneesah tace "eh nice mumy," Hajiyar tace
"maxa ki shigo gida ana nemanki," Aneesah
tace "to gani nn xuwa mumy," ta mike tana
kallon ummi tace "ummi xo ki rakani wae
ana nemana kila yayana ne," ummi tace "je
ki ina xuwa don baxan tashi ba sae na
gama abinda nake," Aneesah bata sake
saurarata ba ta shiga falo da sallamarta,
xaune ta gansa yana danna wayarsa,
gabanta yyi mugun faduwa don a tunaninta
Mujaheed ne ya xo, ta karaso falon a
sanyaye jiki ba kwari, ta dan xauna kan
kujera tana kallonsa tace "ina yini," ba tare
da ya dago kai ba yace "lfya lau," ta
sunkuyar da kanta bata sake cewa kmai ba
shi ma hka, can ta dago a hnkli tana kallnsa
taga kallnta yke, suna hada ido ya sauke
idonsa da sauri itama hka, a hkn Hajiya ta
sauko ta samesu tace "lah ke dae Aneesah
shirmammiya ce wllh, ko ruwa baki kawo
masa ba ashe," Aneesar ta mike tsaye tana
murmushi, hajiyar ta koma sama, ita ko tayi
hanyar fridge ta dauko lemo da ruwa ta
daura kan faranti da cup ta shigo falon ta
durkusa gabansa ta ajiye masa, har xata
mike sae ta fasa ta bude lemon ta xuba
masa a cup ta daga tana mika masa a
sanyaye tace "gashi ya Hydar," ya tsura mata
ido bae ce komai ba, hkn yasa xata ajiye
kofin, ya mika mata hannu ta dago dara
daran idonta tana kallonsa ta mika masa
lemon, hmm tarihi ya maimaita kansa, don
kasa rike cup din yyi, ya fada kan farin
kayansa.
END OF BOOK TWO
@ #dan_gogori_
ANEESAH 🌹🌹🌹
NA KHALEESAT HAYDAR
31&32
~31~
.Aneesah ta koma baya a tsorace tana
kallonsa gabanta na faduwa, don gani take
kmr xata ji an rufeta da duka kmr wancan
ranar, duk ta rude ta rasa abinda xata yi, ta
cire mayafin jikinta da sauri ta shiga goge
masa muryarta na rawa tace "kayi hkuri ban
sani ba," ya sauko kasa a hankali yana
kallonta ya karbi mayafin daga hannunta, ta
sunkuyar da kai ta koma baya da sauri, duk
ta takura da irin kallon da yake mata, hkn
yasa ta fara kkrin mikewa daga wajen, taji
ya kirata, ta dago kai tana kallonsa, a hankali
taji yace "i love yhu," ta yi still a wajen kmr
an dasa ta ta tsura masa ido tana kallonsa, a
raunane taji ya fara magana yace "ina sonki
Aneesah, ina sonki ssai, tun ranar da na fara
daura idona a kanki naji sonki, ban san
wani irin so nake maki ba Aneesah,
Aneesah ki fada min tsakanin ki da Allah
meye tsakaninki da Aminina Mujaheed, ni
nasan waye Mujaheed just lyk dat baxae
sake maki har hka ba, miskili ne shi dan
girman kai, bae dauke mace a bakin komai
ba, ki gaya min mene ya janyo hkn kar ki
min karya Aneesah" yyi shiru yana kallonta
ganin irin hawayen da take tana girgixa kai
kmr ana xubo su, ya kauda kansa da sauri
ya rumtse idonsa, da kyar ya iya mike wa
bae ce mata komai ba ya fice daga gida,
Aneesah ta jingina jikin kujera tana hawaye
ba kakkautawa ji take kmr numfashinta xae
dauke, maganganunsa suka shiga yawo
mata a kai, ta kasa gaskata abubuwan da
taji daga bakinsa, a hka ummi ta shigo ta tar
da ta, ta karaso cikin falon da sauri ta
durkushe gabanta tace "me ya faru Aneesah
kukan me kike," Aneesah ta girgixa mata kai
ta fashe da kuka, a fusace ummi tace "wae
wnn waye da kullum in ya xo sae ya sa ki
kuka," Aneesah bata ce mata komai ba, hkn
yasa ummi ta mike tayi hanyar daki Aneesah
ta rikota da sauri sanin mumy xata je ta kira
mata, da kyar tace "wllh bbu komai ummi
yayana ne," ummi ta galla mata harara tace
"bbu komai kike kuka hka," Aneesah ta
girgixa mata kai tana share fuskarta tace
"sbda ya tafi ne shi yasa nake kuka," ummi
ta durkusa tana kallonta da tausayi tace "to
kiyi hkuri, kuma ai naga yana xuwa a kai a
kai ko," Aneesah ta gyada mata kai ummi ta
kamo hannunta suka bar falon suka yi
hanyar daki. Hydar na kwance dakinsa
idonsa a lumshe, pretty na gefensa a xaune
tana kallonsa 4 d sixth tym knn tana masa
magana tun bayan shigowarta dakin amma
yaki kulata, tace "shkkn yaya tunda baxa ka
kulani ba ni xan fita amma shawarar da xan
baka a matsayina na kanwarka da baxae
cutar da kai ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login