Showing 18001 words to 21000 words out of 89717 words
da gaske
yake yasa ta gaya masa anguwarsu kawae
in yaso sae ta karasa gida da kafa,
"aneesah," ta ji ya kirata ta juya tana
kallonsa, idonsa na gaban titi yace "me ya
sami yusuf?" nn da nn taji hawaye ya ciko
mata ta girgixa kai da kyar tace "mota ce ta
bugesa suna dawowa daga sch," yace
"mota kuma, to ina mai motar," ta goge
hawayen idonta tace "bae tsaya ba, kuma
withness sun ce da gangan ya buge sa
bayan ya bugesa kuma ya taka sa ya gudu,"
yyi parkin da sauri yana kallonta, ta
sunkuyar da kanta tana ci gaba da xubda
hawaye, yace "baffanku ya samu lbri," tace
"eh amma bae xo ba har ynxu wae matarsa
tace ya tafi lagos, kawae baffa ibrahim ne ya
xo shima shekaranjiya yace gangancinmu
ne ya kashe yusuf," Aliyu ya gyada kai bae ce
komai ba ya ja motar suka bar wajen, har
suka isa anguwar bai sake ce mata komai
ba, sae da yyi da gske da ita snn ta nuna
masa gidansu don ca tayi ya ajiyeta xata
karasa da kafa, tace masa tana xuwa snn ta
shiga cikin gidan, Ammi na share tsakar
gidan don ita har lkcn bata koma aiki ba
sun bata hutun wata daya ne, ta mike tsaye
tana kallon Aneesar da mamaki tace "me ya
faru Aneesah," Aneesah ta kirkiro murmushi
don bata son daga ma Amminta hankali,
suka shiga dakin snn tace "Ammi tun safe
baki gama aikin ba ashe," Ammi tace "ki
gaya min Aneesah me ya faru ga
idanuwanki duk sun kumbura kice min
bkm," Aneesah ta sunkuyar da kai gudun
kar ta fara hawaye kuma, a hankali cikin
nutsuwa tayi ma Amminta bayanin abinda
ya faru, ammi tayi shiru tana kallnta da
tausayi snn tace "shi kuma me ya biyo ki yi
Aneesah," ta goge hawayen idonta tace
"nima ban sani ba," Yana waje Ammi, Ammi
tace "to shknn kice ya shigo," ta mike a
sanyaye ta fita gidan tayi hanyar motarsa,
tace "Ammina tace ka shigo," yyi murmushi
ya fito daga motar ya rufe snn ya bi bayanta
suka shiga gidan a tare.
~10~
Aneesah ta shiga daki ta fito da tabarma ta
shimfida masa ya xauna, Ammi ta fito ta
dauko kujera ta xauna tanai masa sannu da
xuwa murmushi bayyane a fuskarta, ya
gaisheta a ladabe yana tambayar ya gidan,
tace masa lfya lau ya nasu gida, yyi mata
gaisuwan rasuwar yusuf, tayi masa gdya
sosai daga bisanni ya sake bata hakura a
kan abinda ya faru snn yyi mata sallama
yace xae wuce, tayi masa gdya tace Allah ya
saka da alkhairi snn ya fita daga gidan yana
kallon Aneesah. Sae da ya fita snn a hankali
tace ma Ammi bari ta rakasa Ammi tace
mata to, ta mike ta bi bayansa, yana jingine
jikin motar yana jiranta, ta karaso gefensa
ta tsaya a sanyaye tace "nagode yaya
Haiydar," yyi murmushinsa mai kyau yace
"nima ngd fateema," ita ma murmushin tayi
ta boye fuskarta, yace "Aneesah an rufe
registration din waec din ne?" a hankali
tace "nima ban sani ba," yace "ok find out
frm yhur sch mates," tayi shiru bata ce
komai ba, yace "Aneesah naxo gidanku ko
ruwa baki bani ba, gashi dama yunwa nke
ji, kin san bnyi break ba," ta xaro ido tace
"lah ae ban san xaka sha ba, bari na debo
maka," yyi dariya yace "wasa nake maki," ya
bude motar ya fito da ledar Hijabs din ya
mika mata tace "na me," yace "naki mana,"
ta marairaice tace "A'a ni dae wnn ya isheni
wllh," ya harareta yace "ki karba wucewa
xanyi," a hankali tasa hannu ta dan risina ta
karba snn tayi masa gdya, yyi murmushi
yace "welcm Aneesah, i wil be goin now," ta
gyada masa kai ya bude motar ya shiga ta
daga masa hannu snn ta juya ta shiga gida,
shi ko yyi reverse ya bar anguwar, hanyar
gidansa yyi, don yasan Hajiya na can kila ta
tara masa mutane ana jirasa don ma ya
kashe wayoyinsa. Aneesah na shiga ta nuna
ma Amminta hijjaban, Ammi tace "shine xaki
karbo Aneesah ni fa ba ruwana," Aneesah
tace "wllh Ammi nace ya bar shi yaki," a
hankali ta shiga fito da su tana dudduba,
tana fito da na ukun knn bandir din dari
biyar biyar ya fado, ta koma baya da sauri
tana kallon Amminta, ammi tace "wnn kuma
daga ina?" Aneesah tayi shiru tana kallon
kudin snn ta dago tana kallon Amminta a
hankali tace "shi ya saka Ammi," Ammi ta
kasa cewa kmai sae kallon Aneesar da take
yi, can dae ta mike ta shige daki kawae,
Aneesah ta bi ta ta fashe da kuka tace "wllh
Ammi ban san ya saka ba," Ammi ta girgixa
kai tace "to ki ajiye masa kudinsa kar ki
taba," Aneesah tace "to" snn ta ajiye hijabs
din da kudin cikin jakar kayanta. Washegari
da yamma ta je dibo ruwa a borehole tana
dawo wa xata shiga gida taji an mata horn,
ta juya da sauri tana kallon motar da
mamaki, Haiydar ne, ya bude motar ya fito
ya wara mata ido yace "me hannunki yake
da xaki daura ruwa a kai Aneesah," tayi
murmushi tana kallonsa bata ce komai ba ya
karaso gabanta ya sauke mata bokitin
ruwan ya ajiye kasa yana mata wani irin
kallo, ta boye fuskarta da tafin hannunta
tana 'yar dariya tace "xafi hannun xae min
shi yasa na daura a kai," ya harareta yace
"to karki sake," tace "uhum," snn ta dauki
bokitin ruwan a hannu yace "bari na taya ki
mana," ta ce "A'a ina xuwa," ta shiga gidan,
bayan kmr minti biyar ta fito rike da leda
tana kallonsa tace "jiya kayi mantuwa cikin
ledar da ka ban," ya galla mata harara yace
"Ammi na ba bake ba, ni ina ruwana dake,"
ta marairaice fuska tana kallonsa tace "dn
Allah ka bari ka amshi kayanka ni dae," ya
hade rai yace "ba fa na son hka Aneesah,"
tayi shiru tana kallon kasa, yace "ya
maganar da na maki jiya na waec kin
tambaya?" ta wara ido tace "na manta," yyi
mata wani irin kallo yace "you re nt cerious,"
ya ciro wayarsa daya ya mika mata yace
"idan kin tambaya kya kirani ki gaya min
nmbrna na ciki xaki ga anyi save da
barrister," ta xaro ido tace "A'a ni bana so
wllh ka tafi da kayanka watarana idan kaxo
xan gaya maka idan na tambaya," ya ajiye
mata kan wani dutse yace "idan na tafi ki
barshi a wajen, ki gaida min da Ammi," yana
kai wa nn ya shige motarsa ya juya ya bar
anguwar, tayi kmr xata yi kuka har ta daina
ganin motar snn ta dauki wayar ta shiga
gida dashi. Da daddare tana wanke wanke a
tsakar gida Ammi na daki taji kamr motsin
mutum a xaure, ta dan tsorata ta mike da
sauri tana jiran taga wa xae shigo taga bbu
kowa, a ranta tace to ko dae ya Haiydar ne,
hkn yasa ta karasa da sauri don tunaninsa
take lkcn, ta shiga xauren tana dan waige
waige cikin duhu bata ga alamar kowa ba
ta dan leka waje ta dae ga motar a parke
amma ba na Haiydar bne, kuma ba a kusa
da gidansu akayi parkin din ba, ta danyi
tsaki ta juya xata koma cikin gidan taji ta ci
karo da mutum ta tsorata sosae xata fasa
ihu ya fixgota ya rufe mata baki a hankali
yace "menayi maki xaki fasa min ihu," a
tsorace ta koma baya tace "ya Abdul," ya
wara mata ido cikin duhun yace "waww kin
xama 'yan mata bbyn nn," ta turasa da karfi
a fusace xata bar xauren ya fixgota yace
"yaushe na fara wasa dake?".
.
Aneesah tace "to wani irin iskanci knn xaka
rike ni hka ni ka sakeni don Allah ko nayi
maka kama da yar iska," yyi yar dariya yana
mata wani irin kallo yace "har ynxu wnn
tsiwar taki na nn ko," tayi tsaki ta turasa da
karfi xata shiga cikin gida ya fixgota ya
daure fuska yace "ban baki ixinin wuce wa
ba, ina uwar taki take," tayi masa wani
mugun kallon tace "ban sani ba," yyi dariya
ya fito da kwalin sigari da lighter daga
aljihunsan ya ciro sigari daya ya mayar da
kwalin, snn ya chinna mata wuta yana
kallon Aneesar da ta yatsine fuska tana
kallonsa a walakance cike da tsana, yyi
murmushi yace "hope kin shirya aure ynxu
'yan mata," ta galla masa harara tace "da'alla
malam ka bani waje na wuce wnn wani irin
iskanci ne," ya matse ta da bango xae yi
magana Ammi ta fito tsakar gidan tana
kiran Aneesah, ya saketa yana mata wani
irin kallo yana murmushi ya shafi gefen
fuskarta yace "bye c yah," snn ya juya ya fice
daga gidan, ashe motarsa ce a waje, ta ja
dogon tsakin takaici tace "banxa kawae
mara tarbiya" snn ta shiga gidan da sauri,
Ammi ta hade rae tana kallonta tace "ina
kika je Aneesah," ta dan marairaice fuska
tace "wllh ina wanke wanke naji mutum ya
shigo xaure shine naje dubawa naga Abdul
ne," Ammi tace "waye Abdul?" Aneesah tayi
shiru tana kallonta can tace "Abdurrahman"
Ammi tace "sae kika tsaya yin uwar me a
wajen," Aneesah ta tsorata ganin yanayin
Ammin murya na rawa tace "aa ni ban tsaya
yin komai ba Ammi," ammi ta juya ta shige
daki ta bita jikinta a sanyaye, Abdul da ne
gun baffanta shehu, sam bashi da mutunci
bashi da tarbiya yanda ubansa yake hka
yake, saukarsa knn Nigeria don a london
yake rayuwarsa can yyi karatunsa na
medicine, ynxu hka kwararren likita ne baya
xuwa Nigeria sae bayan duk shekara biyu,
kuma idan ya xo baya wuce wata biyu yake
komawa, sae da suka shiga daki snn
Aneesah taba Ammi hkuri, ammi tace
"bakomai amma da xaki ji nawa Aneesah da
kin shirya kin je gombe gun Adda na kwana
biyu," Aneesah ta hade rae don bata son
rabuwa da Amminta amma gudun kar ta
bata mata rae yasa tace mata to kawae, snn
ta canxa topic din. Washegari da yamma ta
dawo daga debo ruwa kmr jiya ta ga Aliyu
tsaye kusa da motarsa, tana ganinsa kunya
ya kamata don a ka ta daura ruwan yau ma,
ya karasa kusa da ita ganin taki karasowa
yace "baki jin magana ko Aneesah," a
hankali tace "kayi hkuri," ya sauke ruwan
daga kanta yana harararta yace " kar ki sake
daura ruwa a kan ki," ta gyada masa kai, yyi
mata wani irin kallo yace "jiyan baki ga
daman kira ba knn," tace "lah na manta
wllh," yace "hmm baki tambayi abinda na sa
ki ba knn," tayi shiru don har lkcn bata
tambaya ba, ya gyada mata kai yace "gud,"
Ammi fa?, a hankali tace "tana ciki,"yace
"xan iya shiga na gaisheta," tayi shiru kmr
mai naxari snn tace "ina xuwa," ta shiga
gidan, ba a jima ba ta fito tace "ka shigo," ya
bi ta suka shiga gidan, ya xauna kan
tabarmar da ta shimfida masa, Ammi ta fito
suka gaisa da fara'arta tana tambayrsa
mutan gidan, Aneesah ta xauna gefensa
bayan Ammi ta shiga daki a hankali tace
"pretty fa?" yyi murmushi ya matso kusa da
kunnenta yace "tana gaida ki," ta rufe
fuskarta tana murmushi ita ma, a hankali
yace "yunwa nake ji Aneesah nayi missn din
girkin ki da yawa," tace "lah ynxu muka
gama abinci bari nace ma Ammi ta xubo
maka yana daki," ya dan wara ido yace "ke
wasa nake maki," ta mike tace banyarda ba,
ya riko hannunta yace "don Allah ki bari
kunya nake ji Aneesah," Aneesah tayi dariya
ganin yaki sakinta tace "Ammi wae a xubo
masa abinci," ya rufe mata bakin yana xaro
ido, ta fixge hannunta ta mike da sauri tana
'yar daria, Ammi daga ciki tace "to xo ki kai
masa Aneesah," ta shiga dakin da sauri tana
masa gwalo, ba a jima ba ta fito rike da
kwanon shinkafa da miya ta ajiye masa
gabansa, ta koma ta debo masa ruwa binta
kawae yake da kallo yana murmushi, tana
ajiye ruwan ya rikota a hankali yace "ae tare
xamu ci," dole ya tilasta mata ta xauna
gabansa yana cin abincin yana kallonta, sae
faman santi yake "Ashe dae kice Ammi ta
koya maki girki hka Aneesah," ita dae
murmushi kawae take har ya gama, snn ya
ce yana fita ta nemi ixini wajen ammi taje
gidan classmate dinta dake kusa ta tambaya
ko har lkcn ana registratn din waec, hka
kuwa akayi bayan ya tafi taje gidan kawarta
Jidda, tace mata an rufe a makarntarsu
amma, makarantar dake gefen tasu jibi ne
deadline dinsu, tayi mata gdya ta koma gida
ta kirasa ta sanar masa don hka yace mata
ta basa feedback. Tana alwala xata yi sllhn
isha Abdul ya shigo gidan.
.
Ya karaso gabanta ya tsaya yana dan
bubbuga kafa a kasa yana mata wani irin
kallo, bata ko daga kai ta kalle inda yake ba
ta karasa alwalanta ta mike xata shiga daki
ya kamo hannunta, murya kasa kasa yace
"baki da respect yarinyar nn ko, baki ga
mijinki bne?" ta fixge hannunta a fusace ta
daka masa tsawa "wae ni ka rabu dani
mana malam, a ina na san ka," xae yi
magana Ammi ta fito daga daki tana
kallonsu, tace "xo ki wuce ciki," Aneesah ta
wuce sa da sauri ta shige daki, ya tsaya
yana ma Ammin kallon rainin wayo, can yyi
dariya yace "hope kin shirya rabuwa da 'yar
ki ynxu Hajiya maryam," Ammi bata ce masa
komai ba ta juya ta shige dakin ita ma ta
rufo kofar. Ya karashi dariyarsa ya fice daga
gidan, Ammi ta dubi Aneesah da ta xauna
tayi jigum bayan ta idar da sllh tace "shi
yasa nace ki shirya ki wuce gombe Aneesah,
ko xuwa gobe xan baki kudin mota ki tafi,"
Aneesah bata ce komai ba sae dae hawaye
ya taru idonta ta sunkuyar da kanta da sauri
gudun kar Ammi ta gani, ranar kasa bacci
Aneesah tayi, tunanin rabuwa da Amminta
da ya Haiydar take cikin 'yan kwanakin da
basu wuce wata daya ba ba karamin
shakuwa tayi da Haiydar ba, ita kam
dawowar Abdul ba karamin tashin hankali
bane gare ta, tun tana karamarta dama ta
tsane shi don bae da kamun kai ga son
mata, da kyar Aneesah ta iya tashi
washegari don ji tayi duk jikinta ba kwari,
karfe takwas tana xaune koko da kosae a
gabanta ta kasa ci sae jujjuya kosan take,
Ammi ko na ta faman hada mata kayanta,
wayan da Haiydar ya bata ya shiga ring ta
juya da sauri tana kallon wayar, Ammi tace
"ba na ce ki mayar masa da wayarsa ba
Aneesah," a sanyaye Aneesah ta ce "dama
yau xan maida masa Ammi, shi ne ma ke
kiran," ta daga wayar suka gaisa yace gashi
ya kusa anguwarsu, ta wara ido tana kallon
Ammi tace "yanxu?" yace "ko na juya," ta
girgixa kanta a hankali tace "A'a ni ban ce
ba," yyi murmushi ya kashe wayan, ta juya
tana kallon agogo ammi tace "me ya faru
kuma?" ta sunkuyar da kanta tace "kila
wayar xae xo karba yace yana hanya," Ammi
bata sake cewa komai ba ta ci gaba da
abinda take, yana parkin kofar gidansu ya
kirata ta saka hijab ta fita jikinta a sanyaye
bayan ta nemi ixini gun Amminta, ya fito
yana kallonta yace "me ya faru Aneesah,"
tace "ba komai kai na ne ke min ciwo
kawae," yace "Ayya kin sha magani to?" ta
gyada masa kai kawae tana kallonsa, yana
sanye ne da bakar suit yyi kyau ba kadan ba,
yana kallonta yace "Ammi fa," ta jingina jikin
motar tace "tana ciki," wae jikin ne hka
Aneesah," ya tambaya da damuwa, tace "A'a
ae na sha magani," yace "to Allah ya
sauwake, hope kin shirya kin ga aiki xan
tafi," tace "na shirya me?" ya dan harareta
yace "kin fasa xana waec din ne, registratn
xa muje muyi," tayi shiru tana kallonsa a
raunane tace "kaga gombe xan tafi yau fa,"
yace "gombe kuma, me xaki je yi a gombe,"
ta fara hawaye tace "Ammi ce tace na tafi,"
yyi shiru yana kallonta can yace "Ammi tana
ciki," ta gyada masa kai kawae yace "can i
go in," nn ma ta gyada masa kai ya shiga
gidan tana biye da shi a baya, har daki ya
shiga ya gaida Ammi ta amsa da fara'arta
tana tambayarsa mutan gidan yace "duk lfya
suke Ammi," Ammi tace "to madallah," ya
danyi shiru snn yace "Ammi na xo ne
xamuje registratn na waec tace min gombe
xata tafi, don Allah Ammi ki bar ta ta xana
exam dinta ko akwae abinda xata yi a can
ne," Ammi ta girgixa kai tace "bbu Abinda
xata yi a can Aliyu wajen kakata da ta rikeni
xata ne, xuwan ta can xae fi mana
kwanciyar hankali daga ni har itan," yace
"sbda me Ammi," Ammi tayi shiru tana
kallon Aneesar dake hawaye, xata yi
magana taji an shigo gidan ana kwala mata
kira, maryam, maryam, maryam, Ammi bata
yi kkrin mikewa daga inda take ba jin
muryar me kiran nata, matar baffa shehu ce,
ta shigo dakin a fusace ta tsaya masu bakin
kofa tana nuna su da dan yatsa, "wllh wllh
ko ma uban me ku ka yi ma dana tun wuri
kuje ku karya shi idan ba hka ba xa ku sha
mamaki daga ke har 'yar ki, kaji mun
talakokin banxa makwadaita, uban me
Abdul dina xae yi da wnn shegiyar 'yar taki,
wllh tun wuri ku koma wajen bokan da
kuka je ya lalata aikin da yyi maku," Aneesah
da ta kasa daure jin irin bakaken
maganganun da matar baffanta ke gaya
masu tace "ke wae ance maki kowa ma irin
ki ne mai xuwa wajen boka, ko kuma uban
me ma xanyi da dan naki da baki baki masa
tarbiyar arxiki ba sae ta tsiya, kin xo kina ta
ma mutane haushi uwa kare a gida, wllh na
fi karfin dan ki Abdul, kuma da na auri
Abdul gwara na aure mahaukaci mara
hankali"
Srry fans 4 jinkirin posting
@ #dan_gogori_
ANEESAH 🌹🌹🌹
NA KHALEESAT HAYDAR
11&12
~11~
Hajiya Zuwaira ta bude baki da mamaki tana
kallon Aneesah, har ta gama fadin abinda ke
ranta snn ta fice daga dakin har tana neman
bangajeta, hajiyar ta rike haba da mamaki
tace "ni 'yar nn ke gaya ma magana hka?
Haiydar ya juya yana kallon Ammi dake
xaune har lkcn bata bude baki ba yace
"yauwa muna magana Ammi," Ammi tace
"uhum ina jinka Aliyu," yace "ko kuma ma
dae bari xan dawo xuwa anjima Ammi, sae
muyi maganar," yana kai wa nn ya mike ba
tare da ya kalle Hajiya zuwairar da har lkcn
bakin ta yaki rufuwa ba ya fice daga dakin,
Hajiyar tayi murmushin takaici tace "xa ku
gane kuranku in dae ni ce zuwaira " tana
gama fadin hka ta juya fuu tayi hanyar fita
daga gidan tana huci, Aneesah dake xaune
kan kujera a tsakar gidan tana hawaye
Haiydar na durkushe gabanta yana mata
magana suka bita da kallo har ta fita,
Haiydar yyi murmushi yace "hmm mu je dae
xuwa," ya mike ya koma cikin dakin
Aneesah ta bisa da kallo, ya dde cikin dakin
ko me yake ce ma Ammi, can dae ya fito
yana kallonta yace "je dauko Hijab Aneesah,"
ta tsura masa ido tana kallonsa ya gyada
mata kai, ta mike jikinta a sanyaye ta shiga
dakin dauko hijab, ta xauna gaban Amminta
tace "Ammi yace na dauko hijab," Ammi tace
"Sae kun dawo ki kula da kanki Aneesah,"
Aneesah ta mike a hankali tace "to Ammi"
snn ta fita, makaranta ya kai ta yyi mata
registrn waec da neco, snn suka dawo gida
wajen karfe sha daya na safe bayan tayi
registre din lesson din makarantar kafin a
fara jarabawan, ta rasa irin godiyar da xata
ma Haiydar kawae ta fashe masa da kuka
bayan yyi parkin, nn ya barta kofar gidan
nasu ya wuce don bai ga abinda take ma
kuka ba a nn. Da yamma tana xaune tsakar
gida tana duba litattafenta don gobe xata
fara xuwa lesson din daga karfe tara xuwa
karfe biyu na rana, Ammi kuwa ta tafi
kasuwa, taji an bude kofar xaure a
tunaninta Ammi ce ta mike da sauri karbo
kayan hannunta ta kusan cin karo da
mutum, ta koma baya da sauri, Abdul ne, ta
juya xata bar wajen gabanta na faduwa
ganin Amminta bata nn ya fixgota ya hada
da bango yana