Showing 42001 words to 45000 words out of 89717 words
sae
anjima xan kai ki kanwata," har tayi shiru
sae kuma tace "to ynxu ina xaka kai ni?" a
tsorace tayi tambayar, yace "gida xa mu,"
cikin tashin hankali tace "gida kuma, gidan
wa?" suna shiga traffic ya juyo yana kallonta
yace "gidanmu," ta fashe dakuka tace "A'a ni
ba ruwana wllh, ka kai ni gun Ammina
kawae," yace "haba kanwata baki yrda da ni
bne, wllh xan kai ki gida amma da daddare
sbda tsaro," a hka ya dinga kwantar mata
da hankali yana lallabata har ta hkura, basu
suka isa gidansu Mujaheed ba sae kusan
hudu sbda traffic, Aneesah ta dinga bin
anguwan da kallo, a xuciyarta tace kudi na
inda yake, yyi horn a wani kantamemen
gida mai kyan gske, mai gadi ya bude gate
da sauri har yana neman faduwa, ya ja
motar ya shiga haraban gidan dake kewaye
da shuke shuke masu kyau, bayan mai gadi
ya gaishesa dayi masa sannu da xuwa, a
garage yyi parkin, snn ya juyo yana kallonta
xae yi magana ta riga sa tace "to yayana su
mommy baxa su yi magana ba," ya kwantar
da murya yace "kin san me Aneesah?"ta
girgixa masa kai tace "A'a," yace "gidanmu
ne nn, amma su mommy suna Malaysia,"
bata bari ya karasa ba ta katse sa da sauri
"to waye a gidan ynxu," yace "ba kowa," ta
fashe da kuka tace"wllh ba ruwana shine
xaka kawo ni gidan da ba kowa, ni ka kai ni
gun Ammina kawae," ya harareta a fusace
yace "baki yarda dani ba knn? Idan kina
tunanin xan cuceki ne sae ki xauna da
matar mai gadin don yana da mata, har lkcn
da xan kai ki gidan," yana fadin hka ya bude
mota ya fito yyi hanyar shiga gidan, ita ma
ta fito jikinta a sanyaye tana kare ma gidan
kallo, juyawa yyi ya ga tana biye da shi a
baya, ya jirata har ta iso gunsa snn ya ci
gaba da tafiya, ya ciro makulli a aljihunsa ya
bude kofar shiga gidan ya shiga da sallama
ita ma tayi sallamar ta shiga katon falon
dake cike da kayan alatu na more rayuwa, ta
tsaya a bakin kofa tana bin falon da kallo,
shi ko har lkcn yana tsaye bayanta yana jira
ta karasa ciki ya kullo kofar, ta juya da sauri
tana kallonsa a dan tsorace tace "kulle kofar
xaka yi?" ya ma rasa me xae ce mata don
haushi, kawae ya hangame kofar gaba daya
yyi gaba abinsa ya haura sama, ta karaso
cikin falon a hankali ta dan xauna bakin
kujera, ta kai minti ashirin xaune a falon
bata ga Mujaheed ba har ta fara bacci ya
dan bugi kujeran da take kai, ta mike tsaye
a tsorace tana kallonsa, jallabiya milk colour
ce jikinsa, da ganinsa kasan wanka yyi,
kamshin turarensa ya baibaye ko ina ta
dauke idonta daga kallon da take ma
kyakkyawan fuskarsa, yace "xo ki ga," a dan
tsorace ta bisa sama gabanta na faduwa,
taga ya bude wani daki ya shiga, ta ki
karasawa ta tsaya bakin kofar bae damu da
hkn ba yace ni xan tafi masallaci, ki tabbatar
kin yi wanka snn kiyi sallah bathrom na
cikin dakin, yana kai wa nn ya fito ta ja gefe
da sauri ya tabe baki yyi gaba, sae da taji
tashin motarsa snn ta shiga dakin, tana bin
ko ina da kallo daga gani dakin kanwarsa
ce, ta kalli kayan da ya ajiye mata kan gado,
snn ta bude kofar bathroom din ta shiga
tana karanto adduar shiga bayi..
@ #dan_gogori_
ANEESAH 🌹🌹🌹
.
Na KHALEESAT HAIDAR.
21&22
~21~
.
.Aneesah na fitowa daga wanka ta sa kayan
da Mujaheed ya fito mata da, ta dauki hijab
din dake kan gadon ta saka, snn tayi salla
kan darduman da ya shimfida mata a dakin,
tana idar wa tayi jigumtana kare ma
hadadden dakin kallo, ynxu kawae so take
ta ganta kusa da Amminta, Allah Allah take
karfe shidda yyi Mujaheed ya kaita gida,
tana cikin tunane tunanen nn taji yyi
sallama, ta gyara Hijab din jikinta da sauri
tana kallon kofar dakin, ganin bae shigo ba
har lkcn yasa ta amsa sallamarsa, sae a snn
ya turo kofar dakin a hankali ya shigo, ya
karaso gabanta ya durkusa, ta dan koma
baya da sauri, ya ajiye ledan Hannunsa yace
"ga abinci nn ki ci," yana gama fadin hka ya
mike ya bar dakin, sae da ya kullo kofar snn
ta bude ledan, abincin eatry ne da kaxa sae
lemun kwali, ta danci abincin kadan ta mike
ta dauko glass cup ta debi lemun ta sha snn
ta tura ledan abincin. Karfe shidda nayi
Aneesah ta mike da sauri ta harhada kayan
da ta cire ta dauka ta bude kofar dakin a
hankali ta fara saukowa daga stairs din har
ta iso falon, yana xaune sanye da 3qtre da
farar singlet yana danna laptop, ta juya
dasauri kmr warce xata koma sama, ya mike
tsaye yace "ya dae kanwata," ba tare da ta
juyo ba tace "kace da Maghrib xaka kai ni
gidanmu ai," yyi murmushi yace "hka ake
Maghrib kanwata?" ta fashe da kuka tace
"wllh gidanmu nake so na wuce yayana,"
bae ce mata komai ba sae kallonta da yake,
ganin shirun yyi yawa ne yasa ta juyo a
hankali tana kallonsa, suna hada ido ta juya
da sauri tana kuka a hankali, yyi murmushi
yace "to xo ki xauna na sa kaya sae mu
wuce," ta juyo ba tare da ta bari sun hada
ido ba ta rabe ta nemigu ta xauna a takure
kan kujeran falon, shi ko ya haura sama, ko
minti goma ba a yi ba ya fito sanye da
kananan kaya hannunsa rikeda makullin
motarsa yace "to muje kanwata," ta mike da
sauri ta bi bayansa rike da kayanta a hannu,
ya juya yana kallonta yace "a hannu xaki rike
kayan?" ta gyada masa kai yyi murmushi
suka isa garage ya bude mata mota ta shiga
shima ya shiga mai gadi ya bude gate ya ja
motar suka fita daga gidan, Hka ta dinga yi
masa kwatancan anguwarsu har suka iso
layinsu, Mujaheed yace "ina da wani aboki a
layin nn da, amma ya tashi ynxu" Aneesah
da farin cikiya isheta ga ta ga unguwarsu
tace "haba dae da gske?" yace "eh wllh na
taba xuwa nn sau daya kafin ya tashi,"
Aneesah tace "Allah sarki, a nn xaka yi park,"
ta nuna masa kofar gidansu, yyi parkin din
snn suka fito daga motar, tayi kofar shiga
gidansu da sauri yace"kanwata jirani
mana," ta dawo cike da doki tace "to
yayana," a tare suka shiga gidan, Aneesah ta
karasa bakin kofar dakinsu da sauri tana
cewa "Ammina, Ammina" amma shiru, ta
tura kofar dakin da sauri taga duhu, ta fara
kalle kallen tsakar gidan bata ga alamar
damutum cikin gidan ba, bata san lkcn da ta
fashe da kuka a rude ba, Mujaheed ya
karaso kusa da ita da sauri yace "me ya faru
kanwata," cikin kuka tace "Ammina bata
ciki?" ya kunna fitilar wayarsa da yake gari
ya fara duhu yana haska dakin, ko ina baja
baja, ga hotuna ta ko ina a dakin, kuka
sosae Aneesah ke yi a bakinkofar dakin,
Mujaheed yyi sallama ya shiga dakin ta bi sa
a baya, bbu alaman mutum na rayuwa a
dakin a ynxu dae don ko ina yyi kura, ya
juya yana kallon Aneesah yace "haba
kanwata, ki kwantar da hankalinki Amminki
na nn bbu inda ta je," bata ce masa komai
ba sae dae har lkcn bata fasa kukan da take
ba, ya durkusa yana kallon hotunan dake
watse a dakin, ya dauki hoton yusuf yana
kalloyace "ina kuwa na taba ganin yaron nn,
he looks familiar" Aneesah ta durkushe
gabansa da sauri tace "ka taba ganinsa ne,"
Mujaheed ya sosa kai yace "yea ina ga kmr
hka," can yace "yes na taba ganinsa ranar
da nace maki na xo anguwan nn gun frnd
dina," Aneesah na murmushi tace "don
Allah, a ina ka gansa toh?" Mujaheed yace
"ball dinsa na taka da motata ranan,"
Aneesah tayi shiru a sanyaye tana kallon
Mujaheed, Mujaheed yyi murmushi yace "he
ix a vry brave boy, tun kan na fito yyi knck
din min kofar motata, ina fitowa kuwa yace
sabuwa xaka siya min ko gyaramin wnn
xaka yi," Mujaheed yyi dariya ssae yace "kai
yaban dariya ranan, don mamaki ma kasa ce
masa komai nayi" yana ganin hka yace "to
idan bnda kudi na tafi, amma watarana na
kawo masa balldinsa," Mujaheed yyi
murmushi yana kallon Aneesah da hawaye
ya cika idonta yace "dubu biyu ke hannuna
ranan, na dauka na basa yyi min gdya ya
shiga gida abokanansa na ta dariya, a vry
brave boy" can Mujaheed yyi shiru daga
surutun da yake yace "hope ba shi bne ya
rasu Aneesah?".Aneesah ta fashe da kuka
tace " uhm shine," Mujaheed ya wara ido
yace "innalillahi wa inna'ilaihi raji'un," me ya
samesa?" ta kasa ba sa amsa sae kukan da
take yi har da shessheka, ya dago kanta
yace "ya isa Aneesah Allah ya sa ya hutu, kar
ki sake kuka, Addu'a xa kiyi masa," kai
kawae ta gyada masa, ya dago ta yace "ina
kike tunanin ammi xata tafi ynxu?" ta
girgixa kai tana hawaye tace"nima bn sani
ba," ya ciro handkerchief ya goge mata
fuskarta yace"wani neighbour ne kuka fi
close da a anguwan nn muje mu ji ko sun
san inda Ammi tayi," a hankali Aneesah tace
"Anty Amina ce," ya kamo hannunta yace "to
xo mu je gun ta," suka fita daga gidan ta
nuna masa gidan matar, Aneesah ce ta fara
shiga da sallama Amina na xaune tsakar
gida tana alwala, ta amsa sallamar tana
cewa "wanene," Aneesah tace "ni ce maman
mubarak," sororo ta tsaya kallon Aneesah
baki bude, Aneesah ta yi murmushin dole
tana gaisheta, matar ta rike haba tace
"anshiga uku ke Aneesah daga ina hka?"
Aneesah bata ce komai ba sae murmushin
karfin halin da take, Aminar ta ja ta da sauri
suka shiga daki tace "ikon Allah Aneesah ina
kika shiga, daga ina hka" Aneesah tace
"maman mubarack Ammina fa?" Matar ta
girgixa kai cike da jimami tace "ae Ammi
rabona da ita yau kusan wata uku Aneesah
ban san inda tayiba wllh, tun bayan
sallaman da ta xo tayi min gashi ita ba waya
ba, na kira su kaka a can gombe sun ce bata
je ba, amma kuma suna waya ko ta yaya
oho," Aneesah ta shiga xubda hawaye ba
kakkautawa maman mubarack tace "ynxu
me ya kawo ki nn Aneesah rayuwarki na
cikin hatsari wllh kullum a kalla mutane fiye
da biyar sae sun xo anguwan nn don ke,
tsinannan baffanku ma duk kusan bayan
sati yana xuwa kila don ya xo ya ga ko
Ammi ta dawo ne ya sake korata oho, don
ca tayi min shi yace ta tafi, wllh nemanki ake
ruwa a jallo ban san me ke faruwa ba har
kudi aka ce xa a bama duk wanda yasan
inda kike ko ya gano inda kike a anguwan
nn kuma mugayen mutane ne da alama,
ynxu ke da waye,daga ina kike kuma?" kuka
ssae Aneesah take tace "ni da bako ne
maman mubarack," tace yana ina shi kuma
a ina kika san sa, ko wnn ne mai xuwa gun
ki, dama baffanki ba gidansa ya kai ki ba,
Aneesah tace "yana waje," matar tace "to ya
shigo mana, Aneesah bana son ki kara ko
da minti goma ne a anguwan nn kar yan
iskan layin nn su gan ki mu shiga uku," ynxu
dae maxa je ki ce bakon ya shigo," Aneesah
ta fita gabanta na faduwa suka shigo tare
da Mujaheed ya gaisheta ta amsa da fara'a
snn ta fara masa bayanin abinda ake ciki
ynxu, Mujaheed ya fara jero mata
tambayoyinsa na gado taki amsa ko daya
tace ita dae ba ruwanta kawae ya tafi da
Aneesah kar su sake dawo wa anguwan,
Aneesah na kuka Amina ta hadata da nikaf
ta saka, ta rakosu har mota suka shiga,
Mujaheed ya bata kudi mai yawa ta karba
da kyar snn suka bar anguwar har lkcn
Aneesah na kuka kmr ranta xae fita, cikn
kuka tace "ina xaka kai ni yayana," bae
tanka ta ba har suka isa gida ya shiga yyi
parkn snn ya juyo yana kallonta a nutse ya
fara magana"ki yarda dani Aneesah ba xan
taba cutar ki ba, ki daukeni a matsayin
yayanki da kuka fito ciki daya, idan ma baxa
ki iya tsayawa tare da ni a gida daya ba ni
xan bar maki gidan snn na maki alkawarin
xan nemo maki amminki, Aneesah me yasa
baki gaya min gskyan cewar baffan ku ne ya
rike dukiyarku ya hana ku ba, wllh wllh ni
Mujaheed sae na sa mutumin nn ya gane
kuransa, xan sa ayi masa abunda har ya
mutu baxae manta ba kuma baxae sake
sha'awar cin abinda ba nasa ba, snn ko
tsinkenku baxan bari a hannunsa ba" yana
gama fadin hka ya fito ya bude mata mota
itama ta fito a sanyaye, yana gaba tana
binsa a baya har suka shiga cikin falon, ta
xauna kan kujera duk jikinta a mace shi
kuma ya haye sama. Ba a jima ba ya sauko
yace "xan tafi masallaci, ke ma kije kiyi
sallah," to kawae tace masa ya fita daga
gidan, ita kuma ta hau sama ta shiga dakin
da ya gwada mata daxu. Tana idar da sallah
ta sake wanka, tayi kwanciyarta kan carpet
din dakin abinduniya ya dameta.Budewar
kofar da Mujaheed yyi ne yasa ta mike
xaune da sauri ya karaso cikin dakin yace
"kin yi sallah kanwata," ta gyada masa kai
yace "Gud, sauko ki ci abinci to," ta girgixa
masa kai tace "na koshi,"ya harareta yace
"c'mon, ko naxo na daga ki ne," da sauri ta
tashi tsaye tana kallonsa, ya juya ya fita yace
"ina jiranki," sae da ta daina jin takunsa a
stairs snn ita ma ta fito daga dakin ta sauko
falo, yana xaune kan dinnin yana cin apple,
ta xauna a falo yace "ki taho mana
kanwata," "A'a ni nn xan xauna," ta fadi hkn
ba tare da takallesa ba, yace "Allah idan kika
bari na tashi dauko ki xanyi, ni fa bna son
kina min hka," ta hararesa bata ce komai ba,
ya mike tsaye, da sauri ta tashi tsaye ita ma
tace "wayyo don Allah kayi hkuri xan xo,"
tayi hanyar dinnin din ya ja mata kujerar ta
xauna, snn ya tura mata kulan abinci
gabanta, shinkafa ce da miya sae farfesun
kaza da lemo, yace "gidan matar abokina
naje na karbo maki, naga fried rice din daxu
baki ci ba, kin saba da tuwon masarada
miyar kuka a kauye koh?" murmushi kawae
tayi bata ce kmai ba,da kansa ya dibar mata
abincin a plate ya tura mata gabanta
yace"maxa ki ci," bata yi musu ba ta dauki
spoon tayi bismillah ta fara cinabincin,
kallonta kawae yake yana tauna apple a
hankali, ta dago kanta yyi saurin kauda
kansa yana tace "kai baxa ka ci bane," yana
kallonta yace "ae baki ce na ci ba," tayi
murmushi ta ci gaba da cin abincinta, yace
"ohh baxa ki ce na ci ba," ba tare da ta
kallesa ba tace "ka ci mana," yace "to xuba
min," tace "abinci nake ci," yyi murmushi
yace "to yyi kyau bari na xuba da kaina," ita
dae bata ce masa komai ba, ya xuba abincin
shima ya fara ci, ta ci rabi ta tura sauran
yace "ya dae, bae maki ddi ba ko?" tace "A'a
na koshi ne," xae yi magana wayarsa tayi
ring, ya dauka yana kallon mai kira, yyi
murmushi yace Hajiya knn, Aneesah ta tsura
masa ido, ya daga kiran taji yace "an yini lfya
mum, eh ina Abuja daxun nn na shigo wllh...
A'a ba sae kin xo ba ina gama cin abinci xan
taho ynxu dama,ok bata mu gaisa, Hello 'yan
matan yayanta ykk," Aneesah tayi murmushi
ganin yanda yyi maganan, shi ko dariya yyi
yace "to srry bby sae na xo," snn ya katse
kiran ya ajiye, ya kalli Aneesah da ta kasa
daina kallonsa har lkcn yyi mata far da ido
yace "ya dae," kunya ya kamata ta sunkuyar
da kanta bata ce komai ba, yyi murmushi
yace " je ki shirya xa mu fita kanwata," ta
hade rae tace"ina xa mu?" yace "gidansu
wnn frnd din nawa da nake baki lbri, mum
dinsa ce ta kirani ynxu," Aneesah tace "bbu
inda xa ni," yace"sbda me kanwata, so kike
na bar ki ke daya a gida," tace "ehh"
yace"hmm sbda me baki sn xuwa ki gaya
min kanwata," "don kar su yi wani tunanin
daban," ta fadi ba tare da ta kallesa ba, yyi
dariya yace "bbu ruwansu da hkn bby, they
live a vry free life," ganin tayi shiru ne yasa
yace "oya je ki shirya, ki bude wardrobe ko
wani kaya yyi suit dinki ki dauka ki sa, nima
shiryawa xan je nayi" ta mike tsaye tace "ni
fa bbu inda xanje, ka je ka dawo," ta bar
dinning din tahaye sama, ya bita da kallo yyi
murmushi yace "perfect!" snn ya haura
sama shi ma, yana gama shirinsa ya fito, yyi
sallama ya shiga dakin da take, yace "idan
kwanciya xaki yi ga bed, bana son kina
kwantawa a kasa," yace "na kunna maki tv
ne?" ta girgixa masa kai yace "to kina
karanta Novel ne?" ta juya tana kallonsa tace
"wani iri?" ya jingina jikin kofa ya rungume
hannayensa yana mata wani irin kallo yace
"na turanci mana, love nd romance," ta
kauda kanta da sauri tace "A'a bna
karantawa," yace "amma daxu na ga Novels
a dakin ku ae," ba tare da ta kallesa ba tace
"ba nawa bne," ya juya ya fita tayi tsaki a
xuciyarta tace "wnn dae gantalalle ne," a
tunanin ta wucewa yyi sae ga shi ya dawo
da Novels har kusan uku ya ajiye gabanta
yace "nyc Novels amma fa akwae
romance....." a fusace tace "kai wae ni nace
maka ina karantawa ne,ni ka tafi da
kayanka," ya daga kafada yace "just 2 while
away ur tym, ni na tafi bye, me xan siyo
maki," ta galla masa harara tace "bakmai,"
yyi dariya yace "to, idan lkcn sllh yyi kiyi,"
yana kai wa nn ya fice daga dakin, ita tsoro
ma yake bata wllh, sae da taji fitar motarsa
snn ta mike ta kulle kofar dakin da makullin
da ta ga jikin kofar.
~22~
Karfe takwas Mujaheed ya shiga da motarsa
gidansu Haiydar, ya nemi gu yyi parkin ya
fito, ya daga ma mai gadin dake gaishesa ba
kakkautawa hannu kawae ya shiga falon
gidan da sallamarsa, Hajiyar na xaune tana
cin tufar dake gabanta a kan dan table,
pretty na kwance kan kujera tana kallo, tana
ganin Mujaheed ta mike da sauri ta
rungumesa tana cewa "yayana oyoyo," yyi
dariya ya daga ta sama yace "kai garin yaya
kika yi nauyi hka bbyna," ta galla masa
harara tace "ni ba nauyin da nayi yaya,
karfinka dae ne ya ragu kila," yyi dariya ya
kamo hannunta suka karasa cikn falon ya
gaida Hajiya dake ta murmushi tace "sannu
da xuwa jaheed ya hanya," yace "lfya lau
wllh mum, ashe abun da ya faru knn?"
Hajiya tayi kwafa tace "ka bari kawae," yace
"to mum tun farkon faruwan abun meyasa
baki kirani ba ai ina Nigeria," Hajiyar ta tabe
baki tace "to dan iskan ya sanar min kana
Nigeria ne jaheed, ae ni Haydar da ba dan
wani abu ba da sae nace musanya aka min
a asibiti" Mujaheed yyi dariya yace "to ynxu
ya ake ciki mum, amma lawyern da kika
dauka bae iya aikinsa ba ina ga dae ko, ya
xa ayi ya bari a kai sa har prison, haba don
Allah," Hajiya ta bude baki tace "in ji wa yace
maka bai iya aikin ba, shi umar din ne bae
iya aiki ba, tab, ae wnda yake karewan ne
babban dan iska kuma shi ya kai kanshi
kurkuku" Mujaheed yace "ae Aliyu ban san
irin shi ba, wae ma ina suka hadu da
yarinyar tukunna Hajiya?" Hajiya tayi
murmushin takaici tace "kaddara fa jaheed,
rabon ayi, aiki na kawota take min a gidan
nn, ashe wae soyayya Haiydar yake da
tsinanniyar shegiyar bamu sani ba, wancan
munafuka algungumar prettn na sane bata
gaya min ba Mujaheed," Mujaheed ya juya
da sauri yana kallon pretty, ta dan yi tsaki ta
mike tsaye ta haye sama Mujaheed na
kiranta ko waigowa bata yi ba, Hajiya tace
"tsayawa xata yi aka ce maka" Mujaheed
yace