Showing 21001 words to 24000 words out of 89717 words
mata wani irin kallo, tuni
jikinta ya dau rawa amma ta dake tace
"meye hka xaka fado ma mutane gida ba
sallama," ya take mata kafa da takalminsa
tayi yar kara yana rike da kafadarta yace
"daxun wani rashin kunya kika yi ma
momyna?" ta galla masa harara gabanta na
faduwa a xuciyarta tana ta adduar Allah ya
dawo da Ammi a lkcn, a fili kuma tace "ni ka
sake ni don Allah malam," ya fixge dan
kwalin kanta yana mata wani mayen kallo
yace "uwata kika yi ma fitsara daxu ko," tace
"ni ka rabu dani" ya daura hannu kan
gashin kanta yana shafa gashin yace "wae
ma wani mutumi ne ya xo gidan nn daxu da
safe?" ta buge masa hannu a tsorace tace
"wae me nayi maka xaka takura ma
rayuwata hka ne," ya juya yana kallon kofar
dakinsu yace "uwarki fa?" da sauri xuciyarta
na bugawa ta galla masa harara tace "bacci
take," ya daga kafada ya kamo hannunta
yana kallon cikin idonta yace "we re goin
out now, xaki dan rakani nn cikin gari
.
Aneesah ta fixge hannunta tana masa wani
mugun kallo gabanta na faduwa tace "ka
fitar mana a gida kar na maka ihu malam,
wnn ai iskanci ne da rashin tarbiya, xaka
fado mata mutane gida kamar barawo," ya
wara idonsa da mamaki yana kallonta, "ni
kike ce ma barawo," ya tambayeta yana
kallon cikin idonta, tayi tsaki ta juya xata bar
wajen ya fixgota ya watsa mata mari, tare
da hadeta da bango yana huci, "ke kinsan
ko da wa kike magana don uwarki kuwa,"
cikin kuka tace "na sani mana, mugu,
axalumi, mara tarbiya, masu cin dukiyar
marayu....." wani gigitattcen marin ya sake
wanke ta da a fusace yana huci, ya shake
wuyarta yana kallonta da kyau xae yi
magana, aka shigo gidan, Haiydar ne, ya
tsaya daga bakin kofar xauren ya rungume
hannayensa yana kallonsu, Aneesah dake ta
faman kuka ta juya tana kallonsa tana ci
gaba da rusa kukan, Almajirae ne suka
shigo gidan rike da kayayyakin abinci tun
daga kan, buhun shinkafa, cartons din taliya
man gyada, da doya, Haiydar ya ja gefe ya
basu hanya suka shigo gidan suka dire
kayan abincin, ya ciro dubu uku ya mika
masu hade dacewa tnk yhu, suka yi godiya
suka fice daga gidan, Abdul da ke ta bin
Aliyu da kallo ya yatsine fuska a walakance
yana kallon Aneesah cikin tsawa yace "waye
wnn kuma," bae rufe bakinsa ba Haiydar
yace "Barrister Aliyu Muhammad, kai fa?" ya
tambayesa yana masa wani irin kallo, Abdul
yyi wani mugun murmushi ya sake Aneesar
da har lkcn yana rike da ita yace "uban meye
hadinki da wnn," xata yi magana Haiydar ya
riga ta, "abinda ya hadata da kai shi ya
hadata ni," Abdul yyi masa kallon tsab daga
sama xuwa kasa snn ya fashe da wani
wawan dariya yace "xamu gani," snn ya juya
a fusace ya bar gidan, Aneesah ta sulale
kasa a hankali ta hade kanta da gwiwa tana
kuka, Haiydar ya karaso gabanta ya durkusa
ya dago kanta yace "bana son kina kuka
Aneesah, ki kwantar da hankalinki bbu
wanda ya isa ya cutar min ke kinji kanwata"
tayi shiru bata ce komai ba tana kallonsa, ya
ciro hankici ya share mata fuskarta snn ya
mike tsaye yace "Ammi fa," a hankali tace "ta
tafi kasuwa," ya durkusa gabanta kuma a
hankali yace "kinsan me Aneesah, ki daina
tsayawa gida ke daya, duk inda Ammi xata
kuje tare ," ta gyada masa kai ta dan yi
murmushi tace "to yayana," ya dagota shi
ma yana murmushin ya ja ta xuwa kan
tabarman da take xaune da litattafenta,
suka xauna ya jawo books din yana
dubawa, binshi kawae take da kallo, ya
dago kai suka hada ido ta rufe fuskarta da
sauri tana 'yar dariya. Abdul ne xaune kan
kujera yana kallon ubansa dake ta fama
latse latsan laptop, baffa ya dago yana kallon
Abdul din yace "ya aka yi guy?" Abdul ya
tabe baki yace "ca nayi ina son cikin satin
nn, ka daura min aure da Aneesah, da ita
xan koma london, don aure nake so, kuma
ina sonta," baffa ya mike a fusace yace
"Aneesah, wacece Aneesah, uban me xaka yi
da Aneesah, ba gwara ka kawo min
baturiya ba kace na aura maka ita, Aneesar
bnxa" Abdul ya mike ransa a bace yana
nuna uban nasa da dan yatsa yace "kaga
dad, Aneesah nace maka xan aura, kuma ita
xan aura, wnn ai mgnr kawae kke min, ni fa
xan xauna da ita ba kai xaka xauna min da
ita ba," baffa ya sauke ajiyar xuciya ransa a
jagule yana dan kame kame yace "look guy
bae kai ga hka ba, kar ka damu xan aura
maka Aneesah vry soon, amma ba ynxu ba
sae nn da wata daya," Abdul ya buga table
din gabansa, a fusace yace "y one month
dad, da ita nke son komawa london nace
maka, ko baka gane bne," baffa yace "cool
down son, yau fa satinka biyu, kafin ka
koma xan aura maka ita, kuma sati biyu
xakuyi a nn kafin wata biyun hutunka ya
cika, nafa san abinda nake yi," Abdul ya
koma ya xauna yana murmushin mugunta
yace "vry good dad." baffan ya kirkiro
murmushi yyi pat din bayansa yace "gud
son xan fita guy, sai na dawo," yana kai wa
nn ya fice daga dakin da sauri. Abdul ya
mike tsaye yana murmushin mugunta hade
da cije lebe, can kuma ya fashe da dariya
har da buga kafa snn ya fice daga dakin
yana fi to. Hmm sistrs knn, ku dinga ma
mutum uxuri plss, ku ka san abinda ya
hanani post kwana biyu, rashin lfya ne,
wani abun daban ne, duk baku yi tunanin
hka ba, amma har na samu masu gaya min
magana a whatsapp, wasu har da cewa xa
suyi xuciya su daina karanta littafin
khaleesah Haiydar, hmm ok oo, baku yi
tunann ko ina da aure ba ko ina da yara da
burden dinsu baxae bari nayi type ba wani
lkcn, ni dae don mu nishadantu kuma don
na fadakar nake yin wnn abun, amma Allah
sarki makiyana sun fi masoyana yawa, duk
da hka ina sonku gaba daya, Allah ya bar
.
Aneesah ce xaune kan tabarma a tsakar
gida tana ta faman jujjuya littafin biology
dake hannunta a sunan karatu, duk
hankalinta baya jikinta, don rabon da taga
Haiydar yau sati uku cif, kuma bai taba
ddewa hka bae xo gidansu ba, snn bata san
inda ta jefa wayar da ya bata ba ma Ammi
na kitchen tana girkin dare da yake wajajen
karfe biyar da rabi na yamma ne, ta mike a
sanyaye jin kiran da Ammi ke mata ta karasa
kitchen din, Ammi tace "ruwa xaki debo, kin
dae san ba ruwa a gidan, na rasa wani irin
karatu kike yi tun karfe uku," Aneesah bata
ce kmai ba ta dauki bokitin ta juya xata bar
gidan, Ammi ta kirata ta dawo tace "na'am
Ammi," Ammi ta juyo tana kallnta tace "ki
gaya min me ke damunki Aneesah duk
kwanan nn na rasa gane maki, idan ma
Aliyu ne ae addu'a xakiyi Allah yasa lfya
Aneesah," ta gyada ma Ammi kai tana kkrin
maida hawayen dake kkrin xubo mata ta
juya ta bar gidan da sauri, har ta daura
ruwan a ka bayan ta debo ta tuna warnin
din Haiydar ta sauke a hankali ta rike a
hannu ta kama hanyar gida, tana isa kofar
gidansu ta ga mota a parke gabanta ya fadi,
Allah yasa yayanta ne ta fadi a xuciyarta, ta
tsaya tana kare ma motar kallo ganin bata
taba ganin Haiydar da irin motar ba, Abdul
ne ya fito kmr wani sarki yana mata wani
irin kallo, ta ja dogon tsakin takaici ta dauki
bokitin ruwanta xata shiga ciki yace "hey!"
har ta shiga xauren ta fito don bata son ya
shigo cikin gidan nasu yyi ma Ammi wlkncin
da ya saba, yyi yar dariya yana kallon cikin
idonta lkci daya yana takowa ixuwa
gabanta, ita dae tana tsaye har ya karaso
gabanta yace "Amaryata yane, me kike
bukata, kinsan nn da asabar xaki xamo
matata" tayi murmushin takaici ta ma rasa
abinda xata ce masa, can ta tabe baki tace
"yhu had beta wake up frm ur slumber,"
tana fadin hka ta ja tsaki ta juya xata shiga
gidan ya fixgota, suna kallon juna, yyi
murmushi mai sauti yace "we shall see 'yan
mata, ina barristern naki" bata sake
sauraransa ba ta shige gidan da sauri ranta
a jagule, tun da suka fara exam sa ti uku
knn kusan kullum sae Abdul ya xo mata da
wnn maganar me tsoratata, tana shiga da
ruwan hannunta bata sake komawa debo
wani ba ta shige daki ta kwanta tana kuka a
hankali, anya kuwa xata karasa waec din nn
lfya kuwa, don ji tayi duk xams din ya fita
ranta....
~12~
Ba ita ta fito daga dakin ba sae da aka kira
maghrib shima ta dalilin kiran da Ammi tayi
mata ne, har lkcn ammi na tsakar gidan
xaune, Aneesah tayi alwala ta koma ciki tayi
sallah, tana idar da sllh Ammi ta kuma
kiranta ta fito, Ammi tace "ki je ga abincin ki
can a kitchen ki dauka, saura kiyi min irin na
daxu wllh sae na bata miki rae," Aneesah ta
juya ta koma cikin dakin tana cewa "ni sae
na fara wanka Ammi," ammi bata ce mata
komai ba ta fito daure da xani da dankwali,
ta shiga bayi yin wanka bayan ta juye
ruwan da Ammi ta daura mata a raguwan
garwashin da tayi girki. Tana fitowa tayi
dan shafe shafenta ta saka rigar barcinta, ta
bata lkci ssai don bata son cin abincin har
aka kira isha'i tayi sallahnta, Ammi ta shigo
dakin fuskarta a daure rike da kwanon
abincin ta dire mata a gaba, snn ta sa ta
gaba sae ta cinye tuwon snn ta tashi,
Aneesah ta hade rae kmr xata yi kuka ta
kauda kanta bata ce kmai ba, Ammi dae
bata ko kalleta ba tana jiran ta gama cinye
tuwo ta bata kwanonta, ta jawo tuwon a
hankali ta bude xata fara ci aka yi sallama
cikin gidan, dan makwabciyarsu khabir
abokin yusuf ne ya shigo gidan, nn da nn
Aneesah ta sake fuska tana murmushi tace
"khabir daga ina hka," tana son yaron ssai
tun bayan rasuwar kaninta don yusuf bashi
da abokin wasan da ya wuce khabir, yyi
dariya yana nuna mata gibinsa ba tare da ya
kula da Ammi ba yace "Antyn yusuf ina
wuni," ta rungumosa a sanyaye kiran sunan
yusuf da yyi tace "lfya lau khabir dina, daga
ina," yace "wani mutumi ne yace na kira ki a
waje," ta dan xaro ido tace "ni khabir,"
yaron yace "eh mana ke yace na kira, da
katoton mota ya xo, kuma dogo ne kmr
teachern su anty jamila na sch, ya sa glass
da farin kaya, kuma yyi hka..." ya mike da
sauri ya rungume hannayensa biyu a dan
kirjinsa yana gwada mata yanda mutumin
yyi, Aneesah ta dago a sanyaye tana kallon
Ammin da ta xuba masu ido tana kallo,
Ammi tace "waye?" Aneesah ta sunkuyar da
kai tace "ya Haiydar ne ina ga," Ammi bata
sake cewa komai ba, Aneesah ta mike ta
dauki hijab dinta tace "xo muje khabir," ya
bita suka fice daga gidan, yana jingine jikin
motarsa har lkcin ko yana rungume da
hannayensa, ta karaso a hankali ta tsaya
gabansa tana kallonsa, yyi murmushi yana
kallon khabir yace "yauwa gud boy, ga shi
ka siya biscuit," ya ciro naira dubu ya mika
masa, khabir din ya juya yana kallon
Aneesah yace "na karba Antyn yusuf?" ta
kirkiro murmushi tace "ka karba khabir," ya
karbe daga hannun Haiydar yyi godiya ya
bar wajen a guje, Aneesah ta sunkuyar da
kanta murya can ciki ta gaishesa, ya amsa
yana murmushi yace "Ammi fa," ta kauda
kanta tace "tana ciki," yana kallon cikin
idonta yace "ina wayar da na baki Aneesah,"
kanta a kasa tace "ban san inda yake ba," yyi
murmushi yace "mu je ciki to," ta juya da
sauri tana kkrin maida hawayen dake
baraxanar gangaro mata, ya bi bayanta har
suka shiga xauren snn ya riko hannunta
ganin irin saurin da take, ta tsaya shima ya
tsaya, ganin bai ce komai ba yasa ta juyo a
hankali tana kallonsa, ya kamo hannayenta
biyu xae yi magana ta fada kirjinsa ta fashe
da kuka a hankali, ya rungumota ya lumshe
ido murya can kasa yace "am srry Aneesah,
nt my fault, mum ce tayi reportn dina gun
Abbansu Najeeb, yhu knw.... Kin dae gane
abinda nke nufi, kuma yana kano, so i had 2
go n meet him in there, nd bae bari na bar
kano ba tun lkcin sae daxu, sauka ta knn
Abuja ko gida bn je ba sae gidan Najeeb."
gyada masa kai kawae take yi tana hawaye,
ya dago kanta yace "bana son ganin
hawayenki Aneesah," bata ce komai ba ya
goge hawayen fuskarta yana murmushi
yace "mu shiga ciki," ta shiga gaba yana
biye da ita a baya suka shiga gidan, ya shiga
daki suka gaisa da Ammi suka jima yana
mata hira, Aneesah na gefen Amminta tana
kallonsa shima duk hankalinsa na kanta,
daga karshe dae tuwon nn tare suka ci da
yayanta, sae lkcn ta ga ashe tana jin yunwar.
suna xaune tsakar gidan su biyu kadae, ya
tambayeta ya exams tace ranar thursday
xasu kare, yace "waw nn da 3 dayz knn," ta
gyada masa kai tana murmushi, yace "to
Allah yasa kinyi a sa'a kanwata," ta ce
"Ameen yayana," pretty fa? Yace "kar ki
damu watarana xamu xo tare," nan ya
dinga bata lbri masu ddi tana gefensa tana
'yar dariya kmr ba Aneesar daxu ba, duk da
shi kansa daurewa kawae yake baya son ta
gane damuwar da yake ciki, suka dinga hira
har kusan karfe goma, duk ta manta da
wani bakin ciki da Abdul ya cusa mata daxu,
kmr kar ya Haydar ya tafi ta rakasa har
motarsa ya ciro tsarabar da yyi mata ta
karba da kyar, tayi masa gdya a kunyace ta
shiga gida. Ana gobe xasu kare exam tana
tsakar gida a xaune wajajen karfe 9 da rabi
bayan ta raka Haiydar, tana duba geography
note dinta don shine lst paper din da xa
suyi gobe alhamis, ammi kuwa na daki
kwance, Abdul ya shigo gidan da cigarette
dinsa a hannu yana xuka, gabanta yyi
mugun faduwa amma ta dake ta ki dago
kanta t aki dago kanta
.
Ya karaso gabanta ya durkusa yana kallonta,
har lkcn bata dago ba idonta na kan
littafinta, ya fixge littafin yace "bby baki
ganni bane?" tayi tsaki tace "kai din bnxa
me xan mka," tana fadin hka ta mike tayi
hanyar daki yyi murmushi yace "Ahaf ranar
asabar xan sauke maki wnn rawan kan ka
tsiwar dake damunki yarinya," yana fadin
hka yyi dariya ya fice daga gidan, Ammi ta
mike xaune tana kallon Aneesar da ta shigo
dakin ta fashe da kuka duk da tana jin duk
abinda Abdul din yake fadi tace "me ya faru
Aneesah," cikin kuka tace "Ammi ca fa yyi
wae xuwa ranar asabar xan xama matarsa
ni bn gane me suke nufi da mu ba, kullum
ya xo gidan nn maganarsa knn fa Ammi,"
Ammi tayi shiru tana kallonta can tace "ba
gobe xaku gama jarabawan ba," Aneesah ta
gyada kai tana hawaye, Ammi tace "to sae ki
wuce gombe goben kawae, bna son tashin
hankali," a hankali tace "to Ammi Neco fa"
Ammi ta galla mata harara tace "ae ba dole
bane sae kinyi Neco," Aneesah tace "hka
ne," Ammi tace "don hka gobe kina
dawowa daga makarantar xaki wuce
gombe," to kawae tace ma Ammi ta kwanta
jikinta a sanyaye, can kuma ta juyo tana
kallon Ammin tace "to Ammi ya Haydar fa?"
ba tare da Ammi ta kalleta ba tace "xan
masa bayani idan ya xo goben," Aneesah
bata sake cewa komai ba ta kulle idonta da
xumar bacci, duk da tasan ba barcin xata yi
ba, ita dae taga rayuwa. Abdul ya shigo
falon Abbansa cikin gadara ya xauna yana
kallon iyayen nasa dake ta binsa da kallo tun
shigowarsa falon, yana shafa sajen dake
kwance luf luf a fuskarsa ya daga masu
kafada yana kallonsu ganin irin kallon da
suka masa yace "ya?" Hajiya zuwaira tayi
murmushi tace "daga ina hka Guy, tun tuni
nake ta cigiyarka a gidan na kira wayarka
kuma baka daga ba," ya tabe baki yace "naje
gun local Amaryar nn tawa ce, ta ma bata
min rae kawae a bnxa, ni don dae kawae
ina da dalilin da yasa nake son ku aura min
ita ne amma wnn 'yar kauyen ba class dina
bace wllh," baffa ya dan sace kallon matar
tasa ya ma rasa mai xae ce, hajiya xuwaira
ta kirkiro murmushi ta fara kame kame
"uhm, amm, guy ni kam na rasa dalilin da
kke son auren Aneesar nn, har karuwanci fa
tayi wllh, ni kar taje ma ta goga maka wani
cutan ta cuceni kasan kai daya Allah ya
bamu, da xaka ji ta nawa Abdul da......." ya
mike a fusace cikin tsawa yace "da xan ji ta
naki me, ni fa ku bar gaya min maganar
bnxa, jibi fa dad yyi min alkawarin aura min
ita, xaki kawo min wnn maganr taki mara
ma'ana, ca nayi maki sonta nake yi dama to,
ni kadae nasan abinda na shirya a kanta
don hka duk wanda yace xae bata min plan
dina wllh......" da sauri baffa ya mike yana
dan buga kafadarsa ciki lallashi yace "cool
down my guy, ynxu wa yace mka baxa a
aura maka ita ba, daxu baka ga baffanka
ibrahim ya xo ba dasu sambo, ai duk kan
maganar daurin auren ne, ka kwantar da
hankalinka insha'Allahu ranar juma'ah
Aneesah taka ce my son" Abdul yyi
murmushi yace "gud dad," snn yayi ma
Hajiyar wani irin kallo ya fice daga falon,
Hajiya xuwaira ta fashe da kuka tana salati
tace "shknn na banu Alhaji, ynxu wnn
tsinanniyar yarinyar Abdul xae auro mana,
to me suka yi ma Abdul dina hka, kuma kafa
san namiji wawa ne duk irin tsanar da xae
mata lkcin da xata koya masa sonta ma ba
sani xae yi ba, ni dae na shiga uku ni
zuwaira," baffa ya harde hannayensa yana
jijjiga kafa ransa a jagule, can ya mike shima
ya fice daga falon.. Haydar yyi parkin a
hankali yana hararan kofar shiga falon nasu
kamr yyi masa laifi, can yyi tsaki ya fito daga
motar yyi hanyar balcony a xuciyarsa yana
cewa forsaken home knn, ya shiga falon da
sallamarsa yana kallon agogo, yau satinsa
uku rabonsa da gidan, suna xaune falo
gaba dayansu suna kallo, pretty ta taso da
gudu taxo ta rungumesa cike da farin cikin
ganinsa, ya shafa kanta yace "ykk bbyna,"
sumy da meenah suka tabe baki a tare suka
maida hankalinsu ga kallon da suke yi,
Hajiya ta taso da murnarta tana masa sannu
da xuwa, ya hade rai yana amsawa ba tare
da ya kalleta ba, yyi hanyar stairs pretty na
biye da shi yaji wani siririyar murya na masa
sannu da xuwa daga cikin falon, ya juya da
sauri yana kallonta, ya juyo yana kallon
pretty yace "wnn kuma fa," pretty tayi wani
irin dariya can ciki tace "ohon masu," bbu
yabo bbu fallasa yace "yauwa," snn ya juya
xae haura sama Hajiya ta dakatar da shi, hka
ake yi Haiydar baxa ka tsaya ku gaisa ba,
cikin fushi yace "to saninta nayi da xan
tsaya mu gaisa," Hajiyar ta tabe baki tace "to
matar da na xaba maka knn ko kaki ko
kaso, ko shi Alhaji usman bae maka bayani
bne a can kanon, xaka shigo kana cika kana
babbatse ma mutane, ga ta nn sunanta
zeenah, 'yar gidan Aminiyata ce kuma sae
da na nemi shawara gun Alhaji usman shi
ya bani go ahead din yin komai, don hka nn
da wata daya ne bikinku tunda kai baka san
ciwon kanka ba, degree fa gareta nn da kke
ganinta, kuma da ka san irin mutanen dake
nemanta da da gudu xaka amince mata,
daxun.
nn ta xo gaisheni nace ta bari ta kwana
kawae tunda na samu lbri gun Najeeb
cewar yau xaka dawo."
.
Haydar ya kasa ce ma mahaifiyar tasa komai
don takaici, sae kallonta da yake kawae,
abun ma sae ya kusan basa dariya, ya juya
ya sake maida kallonsa ga zeenah dake
xaune a falon ta sa wasu shegen kayan
bacci sae jujjuya masa ido take, kawae