Showing 9001 words to 12000 words out of 89717 words

Chapter 4 - Aneesa Complete Hausa novel

13 Jul 2024

17475

bar tsorona ni bbu abinda xan
maki, ko da me kike tunanin xan maki??" tayi
shiru kanta na kasa sae hawayen da take yi, ya
mike tsaye ya dago ta ya xaunar kan gadon ya
ciro handkerchief ya goge mata hawayen fuskarta
yana kallonta yace "tell me about yhur sef, am ol
ears," tayi shiru taki cewa komai har sae da yace
"kin yi shiru kanwata," ta dago a raunane tana
kallonsa a hankali tace "to me xance," yace "to ya
sunanki," ta sunkuyar da kai tace Aneesah
mukhtar, yace "i mean yhur real name," ta dan yi
shiru snn tace "fateemah Muktar," yyi murmushi
yace "nyc name, momyna knn, but y re yhu nt in
sch, kuma parent dinki fa?"
@ #dan_gogori_
ANEESAH 🌹🌹🌹
NA KHALEESAT HAYDAR
6&7
~6~
Aneesah tayi shiru tana kallonsa ta kasa
cewa komai, ya gyada mata kai yace "am ol
ears," ta sunkuyar da kanta a hankali tace
"Abbana ya rasu, Ammi ta ce kawae sae
kanina yusuf" sae ga wani sabon hawayen
tana yi, ya girgixa mata kai yace "a'a bance
kiyi min kuka ba Aneesah," ya sa
handkerchief ya goge mata fuskar snn yace
"go on momyna" ta sunkuyar da kanta a
hankali ta fara basa lbrin rayuwarsu tun
daga rasuwar abbanta har ixuwa ynxu da
yake xaune kusa da ita, tayi kuka sosai kmr
ranta xae fita, ya xuba mata ido yana
kallonta ya kasa cewa komai, ta goge
fuskarta ta mike xata bar dakin ya kamo
hannunta ya maido da ita ya xaunar, a
hankali cikin nutsuwa ya fara magana "shi
baffan naku a wani anguwan yake, snn
relatives dinku mae suka ce dangane da
abinda yyi, kuma wish din Abbanku knn ya
rike maku gadon ku har ku mallaki
hankalinku ko tsarinsa ne, snn me
abokanan abbanku suka ce game da hkn,
Abbanku na da lauya ko bae da??" Aneesah
tayi murmushin da bata shirya ba xata yi
magana suka ji muryar Hajiya downstairs, ta
mike a tsorace tana kallon agogo, karfe uku
har ya wuce, tace "nashiga uku na lalace," ya
mike da sauri ya koma kan kujera yace ta
cire bedshit din, jikinta na rawa ta cire
bedshit din, dae-dae nn Hajiyar ta shigo
dakin tana kallonta da mamaki cikin tsawa
tace "ynxu shegiyar yarinyar nn baki girka
abinda nace maki ba, gyaran dakin ne tun
daxu," Aneesah ta fara kame kame a tsorace
xata yi magana Aliyu ya riga ta "A'a aikenta
nayi mum, bata dde da shigowa ba nace ta
wanke min bathroom kafin ta gyara dakin,"
Hajiyar tace "Ayyo," snn ta galla mata harara
ta ja kujera ta xauna tana kallon Haiydar din
da damuwa tace "wae son ya maganar
companies din Abbanku na lagos ne, kasan
fa mutane basu da tsoran Allah tun da
mahaifinku ya rasu Haiydar sau biyu ka
waiwaye lagos," cikin fada ya fara mgana
yana kallonta "to wae mum so kuke na kasa
kai na ne, meye hadin barrister da wani
bussiness can, ni ynxu cases din dake
gabana ma sun fi karfina, su Amina da
sumayya uban me suke yi ba abinda suka
karanta ba knn, sun gwammace su yi ta
gantali a garin Abuja," ya jawo laptop dinsa
ya kunna ba tare da ya kara kallonta ba, tace
"to kayi hkuri kuma fa gskya ne," Aneesah ta
gama gyara gadon ta fita ta bar masu dakin
tayi hanyar kitchen daura girkin da aka sa
ta. Karfe shidda ta dauki hijab dinta tasa
xata tafi gida, ta durkusa gaban Hajiya
gabanta na faduwa ta dai yi shahada tace
"Hajiya ina son ajiye aiki daga yau, idan yaso
sae ki gaya min randa xan xo karban kudi
na na rabin watan da nayi aiki," Hajiyar ta
shiga mata wani irin kallo snn tace "gidan
uban wa xaki da xaki ajiye aiki," ta girgixa
kai a hankali tace "ba inda xani," cikin tsawa
Hajiyar tace "baki isa ba to muguwa, a gidan
uwarki ake hka, kinsan xaki tafi tun da can
baki gaya min ba na samo wata sae ynxu da
rana tsaka, kuma wllh baki karasa min aikin
wnn watan gaba daya ba baxan baki kudin
rabin watan ba, snn sae kin tsaya har an
samo min wata yar aikin idan ba hka ba in
na maki Allah ya isa sae ya biki wllh, tunda
ban san ubanda xai dinga min aiki ba idan
kika tafi bbu wata," a hankali tace "to xan
jira ki samo wata 'yar aikin," Hajiyar tace
"oho dae ya rage naki muguwa kawae"
jikinta a sanyaye ta fita daga gidan, ta tarda
Haiydar bakin gate a waje yana tsaye da
alamar ita yake jira, ya karaso kusa da ita
yace "lemme drop yhu," ta hade rai tace "A'a
ngd" ya harareta yace "baki isa ba," tace
"Allah bana so" bata sake jiran me xe ce ba
ta kama hanyar gida da sauri da sauri. Tana
isa gida tayi wanka tayi sallah ita da
Amminta da yusuf, suna cikin cin abinci
karfe kusan bakwae da rabi, suka ji ana
bubbuga kofa daga can waje kmr xa a balla,
duk suka yi tsit suna kallon bakin kofar
dakin, aka shigo gidan aka banko kofar
dakin, baffa shehu ne, ya tsaya yana hura
hanci yace "ikon Allah, na sami lbrin abin
kunyan da kuke yi a gari ke da tsinanniyar
'yar ki maryam, ynxu sbda tsabar butulci irin
naku da rashin godiyar Allah duk abinda
nake maku sae kin tura yarinyar nn
karuwanci," Ammi tace "karuwanci kuma
yaya, to Allah ya saka mana," cikin tsawa
yace "sharri nai maki munafuka, idan ba shi
kuke yi ba ubanwa ke ciyar daku tunda ni
dae na fi wata uku bnga kun xo gu na
maula ba, kuma a gari naji wnn xancen ana
ta yayada wa, kuma gashi na xo na gani da
idona wae kune da cin shinkafa da miya da
nama yau," Aneesah dae abincin ta kawae
take ci, Ammi ta goge hawayen dake xubo
mata tace "in'sha Allahu sae Allah yyi mana
shari'a daku ranar gobe kiyama," haba
kamar kar ta fadi hka baffa ya dinga bala'i
yana yo wa kanta kmr xae mareta, ita dae
kanta sunkuye yake tana hawaye, hka ma
Aneesah da ta kasa daure wa ta fashe da
kuka, kmr daga sama suka ga an wullo
torch light ya kwalesa da karfi a ka, ya dafe
wajen yana salati a gigice, yusuf ne ya jefesa
yana huci yace "xan fasa maka kai na cire
maka hakori idan ka sake sa Ammina da
Antyna kuka," ya karasa bakin kofar da
gudu ya rufe masa kofar da karfi a fuskarsa.
.
Ammi ta mike da sauri ta fixgo yusuf tayi
masa rankwashi cikin fada tace "kana da
hankali kuwa xaka jefi babanka," yusuf yace
"eh, kuma idan na girma ma dukan tsiya
xan mashi wnn ba babana bne," Aneesah
tayi saurin kamo shi kar Ammi ta dokesa
tunda dae gskya ya fada, baffan ya bude
kofar hannunsa har lkcn na goshinsa yana
kallon yusuf din yace "ni xaka duka idan ka
girma ko," yusuf yace "eh, idan har baka
daina ma Ammina ihu ba," ya gyada kai ya
fice daga gidan ba tare da ya sake cewa
komai ba, Aneesah ta rungume yusuf tace
"yauwa kanina shi yasa nake son ka," nn
fada ya dawo kanta, Ammi ta dinga mata
fada wae basu da respect tunda ubansu
suke ma fitsara daga ita har yusuf, Aneesah
ta mike ta wanke hannunta ta dauro alwala,
taxo tayi slln isha snn ta jawo kaninta suka
kwanta. Washegari Ammi ta dinga fushi da
ita da yusuf, ita dae bata san me tayi ba
kuma har ga Allah taji ddin abinda yusuf yyi,
ta xauna gaban Ammi ta marairaice murya
tace "don Allah kiyi hakuri Ammi, kin ga fa
jiya bayan kinyi bacci nayi ma yusuf fada
Ammi," hka Aneesah ta dinga ba Amminta
hakuri ta kira yusuf ma ya bata hakuri snn
Ammi ta sauko, ta shirya yusuf ya wuce sch,
ita kuma ta kama hanyar gidan aikinta, hka
ma Ammi don gidan da take ma aiki sun
dawo, ranar through out bata ga Haiydar ba
sae taji wani iri, yau Monday tana isa
breakfast ta fara hada masu ganin karfe
takwas ya kusa sbda pretty mai xuwa
makaranta don duk sauran sun gama ita ma
a Higher institution take, har lkcn 'yan gidan
basu tashi ba, tana cikin wanke wanke taji
mutum a bayanta ta juya da sauri, yana
sanye cikin bakin suit da tie yyi kyau sosai
ga briefcase a hannunsa kamshin turarensa
ya gauraye ko ina, ta tsura masa ido tana
kallonsa yau kwana biyu knn bata gansa ba,
ya sakar mata murmushi yace "Gud mrnin,"
ta kauda kanta tace "ina kwana," ya gyada
mata kai ya dawo gabanta ya tsaya "ke kin
karya ne," ta juya bata sake tanka masa ba
ta ci gaba da abinda take yi, ya juyo da ita
yace "me kika hada na break," tace "suna
can dinnin" yace "to debo min nawa ki
kawo nn," ya fadi yana nuna mata dinnin
din kitchen, tace "to ai bn san yanda kke
hada tean ba," "ki hada yanda kike tunanin
ya kamata amma kar ki cika min suger, jez
cube biyu yyi," tace "uhmm" snn ta fice daga
kitchen taje hado masa nasa tean a kan
table, ko da ta dawo kitchen din yana xaune
kan dinning, yace "to hado min coffee plss,"
ta hado masa ta ajiye gabansa xata wuce ya
fixgota ya xaunar kan kujera yace "ni bana
break a gida ran monday, amma yau sbda
ke xan yi don tare nake son mu ci," xata yi
magana ya sa mata dankali a baki yace "kar
ki ce min komai" hka Haiydar ya tilasta ta
suka ci duk abinda ta kawo masa a tare,
tean ma kanta yasa ta hado ma don coffee
kawae ya sha, gabanta ya dinga faduwa kar
Hajiya ta sauko ta gansu a hka, ta marairaice
fuska kmr xata yi kuka tace "wllh na koshi,
na fa karya a gida" ya mike yana kallonta ya
kashe mata ido yace " ai de kin ci, sae na
dawo, kiyi min ginger drink kanwata," ta
gyada masa kai kawae, ya kalli agogon
hannunsa ya bi ta garden ya tafi garage
xabar motar da xae fita da. Tana gama
gyara inda suka yi break din Hajiya ta sauko
tare da pretty dake cewa "momy yayana ya
wuce ne, wae fa da droppin dina nake son
yyi tunda driver baya nn," hajiyar tace "nima
wllh ko sallama bai yi min ba bby," ki karya
sae nasa sumy ta ajiye ki tunda har ynxu
tsoran drivin kike yi, Aneesah ta risina ta
gaida su, snn ta hau sama ta gyara masu
dakunansu ta wanke bathroom, tana
gamawa suka tula mata kayan wanki ta
wanke, ba ita ta gama wankin nn ba sae
kusan karfe biyu, bbu kowa gidan duk sun
fita, ta shiga kitchen a gajiye don ta girka
masu abinci kafin su dawo, karfe uku saura
ta gama girkin ta jera masu kan table, ta
tuna Haiydar yace tayi masa ginger drink, ta
koma kitchen da sauri ta shiga hada masa
drink din, tana gama hada drink din ta xuba
cikin jug ta saka cikin fridge snn ta juya xata
bar kitchen din ta gansa jingine jikin kofa
yana kallonta, yyi murmushi yace "sannu da
aiki kanwata," ta gyada masa kai ta
gaishesa ta fice daga kitchen din, shima ya
fito ya haye sama ganin meenah a falon
tsaye tana ma Aneesahn magana cikin
gadara, "ke meyasa xaki hada min wanki da
fararen kayana," Aneesah tace "Aa su na
fara wanke wa, bn hada su da komai ba,"
meenah ta kai mata mari tace "karya kike
munafuka, ki tabbatar kin sake wanke min
su kafin ki bar gidan nn yau," tana kai wnn
ta haye sama tana xage xage, Aneesah ta bi
ta da kallo hawaye na bin kuncinta, ganin
Haiydar na saukowa yasa ta juya da sauri
xata bar wajen ya kirata, ta tsaya har ya
karaso kusa da ita yace "me kika yi mata?"
tayi shiru bata ce masa komai ba, ya kwala
ma Meenar kira ta sauko tana kallonsa tace
"gani," ya hade rae yana kallonta yace "me
nace kiyi min jiya kafin na dawo," ta yatsine
fuska tace "oho na manta," ya kai mata
tagwayen mari masu rai da lafiya.
.
Meenah ta dafe kuncinta tana kallonsa da
mamaki, "yaya ka mareni??" ya fixogta ya
watsa mata wani marin yace "an mareki
don uwarki, nxt tym idan na sa ki abu baxa
ki manta ba," ya cillar da ita cikin tsawa yace
"bace min kar na taka ki," ta mike tsaye ta
fasa ihu ta haye sama da gudu tana kuka
tana kiran momynta, Haiydar ya juya yana
kallon Aneesar dake tsaye a wajen har lkcn
ya kashe mata ido yace "ya dai kanwata kin
ga mun rama ko," ta juya da sauri ta bar
wajen ta shige kitchen ya bi bayanta, yana
shiga kitchen din yace "kanwata ki hada
min lunch dina ki ajiye kan dinnin din nan,
sae ki shiga bedroom dina xamu yi magana,
ranar bamu gama ba mum ta dawo" ta xaro
ido tace "A'a ni mun gama magana kuma
Hajiya ma ta kusan dawowa ynxu," yyi shiru
yana kallon cikin idonta ta sunkuyar da
kanta da sauri ya karaso gabanta ya tsaya,
ya dago kanta a hankali yana kallon
fuskarta, murya can ciki yace "yhu're a
damsel Aneesah," ta kauda kanta da sauri ya
juya ya bar kitchen din ta shiga yin abunda
ya sa ta. Sae da yyi wanka yyi sllh, yyi shiga
cikin kanan kaya snn ya sauko falon, har
lkcn meenah ta cika masu gida da kuka tana
yi tana kiran momynta, ya tabe baki ya shige
kitchen din bai ganta ba yasan tana garden,
ya karasa cikin garden din ya jingina jikin
kofa yana kallonta, tana xaune ta tsura ma
sararin samaniya ido, jikinta ya bata ana
kallonta ta juya da sauri suka hada ido ta
kauda kanta tace "na xuba maka abincin,"
yyi murmushi yace "ohk xo ki gani," ta mike
ta bisa a baya har suka shiga kitchen din,
yace "xo mu ci oya," ta xaro ido tare da
girgixa masa kai tace "aa ni naci nawa," ta
juya xata bar kitchen din yyi saurin fixgota
har tana neman fadawa kansa, yace "ai baki
isa ba idan baxaki ci ba to kwashi abincinki
nima baxan ci ba," kmr ko da yaushe hka
Haiydar yyi forcin dinta yana bata abincin,
har da hawayenta, har dae suka gama ci
snn ya mike ya bar kitchen din yana dariya,
ta bishi da harara snn ta mike ta shiga
gyara table din, ta gama wanke kwanukan
knn Hajiya da sumy suka shigo gidan, Hajiya
ta rude jin kukan meenah tun daga waje ta
shigo falon da sauri tana cewa "me ya faru
meenah ta," meenah na jin muryar uwarta
ta sauko da gudu ta xube kasa tana ci gaba
da rusan kukanta, Hajiya ta rikice ta shiga
tambayanta menene, cikin kuka tace
"Haiydar ne ya dinga mari na bn san me
nayi masa ba," Hajiyar ta gintse fuska tana
kallon sama tace "baki yi masa kmai ba ya
dinga marinki," tace "eh" hajiya ta shiga
kwala masa kira a fusace, ya sako yana
kallnta yce "sannu da dawo wa," bata damu
da amsa masa ba cikin fada tce "me meenah
tayi maka xaka mareta Aliyu ni fa wllh baxan
dauki wnn ba, so kke ka illata mata fuskar
ko me, wnn ai mugunta ce, ni gskya idan
takura ma 'ya yana xaka yi ka tattara ka
koma gidan ka kawae, ka dinga xuwa kana
kawo mana xiyara," ya sa kafa yyi ball da
meenar da har lkcn ke xube a kasan tiles
yace "don uwarki na mareki din, ke wacece
da baxan mara ba ohh ashe bbu ddi," ya
juya a fusace yana kallon uwartasa yace
"duk kin bi kin lalata yara basu da aiki sae
na lalaci da iskanci, wnn wni irin abu ne, ita
'yar gidan uban wacece da ban isa na sata
aiki tayi ba, kuma ta iya sa wani yyi, ni bama
sae kince na koma gida na ba xan koma
don baxan iya ci gaba da xama a gidan nn
ina kallon tabarar da yaran nn ke yi
ba,tunda na dawo bn ga shegen da ya
dauki buta ko sau daya da sunan xae yi sllh
ba, idan basa gaban t.v suna gidan party,"
tunda ya fara magana Hajiya tayi tsit ta
marairaice fuska tana kallnsa can ganin ba
shiru xae yi ba se dada tona ma 'ya yanta
asiri da xe tayi yasa tace "to kayi hkri Aliyu
ban san laifi tayi maka ba, ke kuma meenah
me ya kai ki yi ma yayanki fitsara, meyasa ba
ki jin magana," meenah ta xumburo baki
taki cewa komai, yyi tsaki ya haye sama, sae
a nn meenah ta mike cikin tsawa ta shiga
kwala ma Aneesah kira, Aneesah dake
kitchen ta fito da sauri ta durkushe gabansu
tace "ga ta," "don ubanki ki je ki kwashe
duk kayan da kika wanke min ki sake
wankesu don basu fita ba," Haiydar ya
sauko kasa cikin tsawa yace "ae baki isa ba
don uwarki, kmr yanda ban isa na sa ki ki yi
ba, to karya ki ke ki sa wani yyi," ya kalle
Aneesar dake durkushe har lkcn gabnsu
yace "ke tashi ki fita daga falon nn, kar
kuma ki sake yin wani aikin har ki bar gidan
nn yau, Aneesah ta kasa tashi daga inda
take ya daka mata tsawa nace ki fita, ta
mike a hankali ta bar falon shi kuma ya haye
sama, cikin kuka meenah tace "momy kina
jinsa ko salon shegiyar yarinyar nn ta
rainani, wllh sae ta sake wanke min
kayana," Hajiya tace "ke kiyi hkuri ki
wankesu a washin machine meenah, ki rufa
mana asiri ki rufa ma kanki asiri idan ba so
kike ya xane ki ba yau kinsan kadan da
aikinsa,tunda yace kar tayi komai yau to ya
muka iya, sumy ke je ki ki xuba mana abinci
a kan dinnin bana son jaraban Aliyu ku
barsa kawae yau yanda kuka gansa kar yaci
ubanku" sumy tace "tab wllh ban iya ba,"
ranar dae dole hajiya ta xuxxuba masu
abincin, don har Aneesah ta koma gida bata
yi komai ba.
~7~
.Yau friday karfe takwas da rabi Aneesah ta
isa gidan aikinta don ma daurewa kawae
tayi bata wani jin ddi, jin muryar Hajiyar a
falo da 'ya yanta yasa ta kasa shiga ciki
xuciyarta ya dinga bugawa, ganin dada bata
ma kanta lkci take yi tsaye a verendan yasa
tayi shahada tana karanto addu'a a
xuciyarta ta shiga falon da sallamarta a
sanyaye, Hajiyar na xaune sumy na kwance
kan kafarta, meenah na goga abu a fuskarta
madubi na hannunta, shi ko Haiydar na
xaune kan dinnin yana rubutu pretty na
kusa dashi, ta durkusa a sanyaye ta shiga
gaida Hajiyar gabanta na faduwa, cikin
tsawa tace "yanxu kike xuwa min aiki sbda
kin raina ni ko? Xaki gane kuranki yau wllh
wllh," a raunane ta fara ce mata bata da lfya
ne, Hajiya ta mike tsaye ta yo kanta a fusace
kmr me shirin dukanta tace "baki da lafiya?
Ni kike gaya ma baki da lfya. ina ruwana da
rashin lafiyarki ko ni na daura maki don
uwarki," ganin Haka yasa Haiydar ya shigo
falon ya nemi guri ya xauna yana kallon
momyn tasa yace "yauwa mum maganar da
nace xamuyi daxu," ya juya yana kallon
Aneesar dake hawaye yace "ke tashi ki ba
mutane wuri," ta kalle hajiyar da har lkcin ke
tsaye kanta, hajiyar ta daka mata tsawa
"don uwarki ba da ke yake ba xaki xuba ma
mutane tula tulan idanuwa kmr tulu, mayya
kawae" ta mike a sanyaye ta bar falon tayi
hanyar kitchen, Hajiyr ta koma ta xauna tace
"yauwa ina jin ka son, wacce magana ce
xamu yi," ya dan yatsina fuska ya mike tsaye
yace "ko kuma bari ma sae xuwa anjima,
ynxu ina busy ne, ya koma dinnin din ya ci
gaba da abinda yake ," sumy tayi tsaki a
hankali tace "dan rainin wayo kawae,"
Hajiyar tace "ke baki da kunya ko, ynxu idan
ya ji ki ya doke ki ki bara min baki kmr
speaker ko," sumy ta mike tana bubbuga
kafa ita an mata fada ta haye sama da shirin
xuwa tayi kuka, Hajiyar ta bita da sauri tana
cewa "lahh, to meye abun kuka nn sumy,"
meenah ta bi su a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login