Showing 27001 words to 30000 words out of 89717 words
mutuwa, Ammi
tana kuka tace ta bi shi amma Aneesah tace
bbu inda xata ita kam, da kyar Ammi ta
lallabata ta hada ta da kayanta da take
hadawa tace ta bishi, kuka Aneesah take
kmr ranta xae fita hka baffa ya ja ta, yana
rike da jakan kayan nata dayan hannunsa,
ya wurga ta cikin mota da jakar tata, yace
driver ya kula da ita kar ta fita snn ya koma
cikin gidan yana huci, ya ciro dubu biyu ya
jefa ma Ammi yace "ke ma maxa maxa gobe
ki kama hanyar gombe da asuba don baxan
tsaya da ku a garin nn ba ana nuna ni da
dan yatsa, maxa ki tattara komatsan ki kiyi
kauyenku kar naxo na tarar dake nn gobe,"
yana kai wa nn ya fice daga gidan ya shiga
mota, driver na ta kokuwa da Aneesah dake
neman ficewa daga motar ta karfin tsiya,
baffa ya koma da sauri ya dauko iccen daxu
ya dawo motar, Aneesah na ganin iccen ta
fasa ihu "don Allah baffa kayi hkuri wllh na
tsaya, wllh nayi shiru, ya kwale mata a ka
yace "don ubanki da ke kabari ma kiyi
mana," tsit tayi tana ajiyar xuciya a motar, ya
shiga gaban mota driver ya ja suka bar
anguwar suna hawa titi yace da driver ya
shiga gidan mai xa su cika tanki, hka ko
drivern yyi aka cika tankin motar snn baffa
ya biya suka hau titi kuma, a ladabe drivern
yace "to ina muka dosa mai gida," baffa
yace "samu waje kayi parkin ka bani motar
kawae baxa ka yi irin tukun da nake so ba,
driver yyi parkin motar baffa ya dawo driver
tsit shi kuma ya koma daya bangaren, snn
baffa ya ja motar ya dinga sharara gudu
kmr xasu ta shi sama, Aneesah kam duk ta
tsorata kuka kawae take tana kiran Allah a
xuciyarta, tun tana gane hanye har ta daina,
taga sun soma fita daga Abuja, ta fara ganin
daji da duhu, baffa ko tuki kawae yake kme
xae tashi sama da motar, har baccin tashin
hankali ya dauke Aneesh.
.
A tsorace Aneesah ta farka ta dalilin buga
kujeran bayan motar da Driver ya dinga yi
da nufin tada ta, ta fara waige waigen cikin
motar xuciyarta na bugawa, xata tambaye
Drivern ina ne nn suka kawota, baffa ya
xagayo bayan motar a fusace yana cewa
"kin fitowa tayi don ubanta," da sauri ta fito
daga motar gabanta na faduwa daga ita sae
dankwali tana kare ma inda suke kallo, ko
ina tsit sae ciyawa dake ta bow down wa
iskan dake ta kada su, ga uban duhu, crow
din cock da ta dinga ji ne yasa ta gane
Asuba tayi, cikin tasin hankali ta shiga
tambayar kanta ina ne nn kuma baffa ya
kawo ta, tsawarsa ta tsinta a tsakiyar kanta
yana cewa "duk inda na bi ki bi, idan ba hka
ba xan wurga ki cikin dajin can na bae ma
macixae sadakar ki, kae kuma saleh ka jirani
daga nn, ba jima wa xanyi ba," yana fadin
hka ya bi ta dan wani hanya duk ciyawa,
Aneesah ta bi sa a baya tana hawaye, da
taimakn hasken wayar sa suka dinga ratsa
grasses din wajajen ga hanyar duk cabi da
ruwa, har suka bullo wata hanyar daban da
karamar abun hawa xata iya bi, tafiya yake
kmr xae tashi sama yana yi yana waiga
bayansa ya tabbatar tana biye dashi, ita ko
binsa kawae take tana hawayen tsoro, sun
kusa minti talatin suna tafiya har daga
karshe taga sun shigo wani dan karamin
gari, abinda Aneesah ta fara cin karo da
shine bukkokin mutane, abun yyi mugun
daure mata kai ko ba a fada mata ba tasan
kauye ne nn, hka Aneesah ta dinga binsa a
baya har daga karshe taga sunyi fullstop a
dai-dai wani katon bishiya duk bawon rake
a watse a kar kashinta, ya juya fuskarsa
daure yana kallonta yace "ki jira ni a nn," kai
ta gyada masa taga yyi wata 'yar hanya, ta
fashe da kuka abun tausayi, to ita ynxu ya
xata yi ita ba wae tasan guri bane bare ta
gudu ga ko ina duhu, ta fara waige waige
tana nema ma kanta solution kafin baffan
ya dawo sae ko gashi da wani mutum sun
dawo gabanta yyi mugun faduwa har suka
karaso, mutumin yace "to ku shigo daga ciki
mana Alhaji, ashe xaka tuna dani Alhaji
gaskiya naji ddi sosae," baffa ya kalli
Aneesar yace "maxa ki biyo mu a baya," hka
ta dinga binsu a baya har suka shigo wani
dan gida da bukka guda uku, cikin tsawa
baffa yace ta tsaya daga bakin kofa snn
suka karasa cikin gidan da tsohon mutumin,
baffa yace "ina mai dakin naka mati,"
mutumin da xa su xo sa'anni da baffa yace
"bari na tado ta Alhaji tana ciki ai," da sauri
ya shiga sae gashi sun fito tare tana mitsika
ido tace "wanga ai walakanci ne malam, me
ya faru xaka tado ni cikin sanyin nn," yana
wage baki yace "ke shatu Alhaji shehu ne a
kauyan namu yau," ta bude ido da sauri
tana kallon baffa tace "lah Alhajin Allah ashe
baka manta mu ba, sae ta fashe da dariya
tana cewa ikon Allah, sannu da xuwa Alhaji
amma da asuban nn me ke tafe da kai hka,"
baffa dake dan murmushi yana sosa keya
yace "A'a wnn yarinyar na kawo ku taimaka
min ku riketa amma ba amana ba, don 'yar
iskar kanta ce, karuwanci take a birni wllh,
mun rasa yanda xamuyi da ita 'yar wata
abokina na kut da kut ne, ga ta nn nasan
shatu ke ce maganinta, idan Allah yasa ta
samu mijin da xae jajuban ma kansa wahala
ku aurar da ita kawae ko sadaka ce, nasan
baxa ta taba gane hanyar fita daga kauyen
nn ba bare ta gane hanyar komawa gida,
kar ku sake tayi kawaye ni dae ynxu tamkar
na kawo maku baiwa ne, dan tallan nn da
aikace aikace duk ta iya xata maku, kuma nn
ba da ddewa ba nke son ku bada sadakarta
ga duk mai so," yana kai wa nn ya ciro duba
daddaya har ashirin ya mika ma mati da ya
xube har kasa yana gdya "an gama Alhaji
in'sha Allahu duk yanda kace hka xa ayi,"
shatu tayi wani shegen dariya irin tasu ta
'yan kauye tace "ka xo inda xa a share maka
kukan ka Alhajin Allah, ka manta mu su
waye ne, ka kwantar da hankalinka kawae
Alhaji kar ka samu damuwa," baffa yyi
dariya sosae yace "ae na yarda daku, ni
ynxu xan koma driver na can bakin hanya
yana jirana don ma kar ta gane hanyar fita
yasa ban bari muka shigo ciki da motar ba,
na dinga ratsawa da ita ta daji, cikin ikon
Allah kuwa muka iso nn," suka yi dariya
suka rakasa har bakin kofa suna masa Allah
ya kiyaye hade da gdya, har lkcn Aneesah na
bakin kofar shigowa gidan tunda baffa bae
ce ta shigo ba, tana ganin su ta ja gefe
gabanta na faduwa, cikin tsawa shatu tace
"kya tsaya kina rabe rabe bakin kofa kmr
warce bata san duniya ba shegiya, da'alla
shiga daga ciki ki tsaya," jikinta na bari ta
shiga gidan tana kallon baffa, kar dae tafiya
xae yi ya barta, nn suka yi ma baffa dake ta
washe baki ganin har shatu ta fara aikinta
sallama, yyi masu sallama cike da farin ciki
ya bi hanyar da xae sada sa da bakin hanya
xuciyarsa fari kal. Mati shaidanin mutum ne
da yyi ma baffa aiki a birni da ddewa,
aikinsa kuma baya wuce kashe wancan
binne wancan kamo wancan, nemansa da
ake ruwa a jalo a Abujan ne dalilin da yasa
ya dawo kauye da xama da karuwar
matarsa da 'ya yansu biyu zano da xulai.
.
Aneesah ta rintse idonta cikin tashin hankali
ta kara budesu tana kare ma gidan kallo
cikin duhun daren, hawaye ya dinga sintiri
bisa kuncinta ynxu baffa wucewa yyi ya
barta a inda bata da kowa kuma bata san
kowa ba, muryar shatu taji tana cewa "kina
ji na ki tsaya nn kar ki shigo min bukka da
kudin cizo, ki jira nn har gari ya soma
wayewa snn ga tulu can kije rafi ki debo
mana ruwa don ko wanda malam xae yi
alwala anjima bbu," tana gama fadin hka ta
shige cikin bukkarta ta jingino kofa ta rage
fitilar dakin. Tun Aneesah na tsaye har ta
gaji ta dauko wata yar kujerar tsugunno da
ta gani tsakar gidan ta xauna tana ci gaba
da xubda hawayen takaici, ita dae tasan ta
kusan awa uku xaune wajen gari bae waye
ba, hkn yasa ta gane cewar kila karfe biyu
suka iso kauyen ashe take tunanin asubace,
mari taji an wanka mata ta mike tsaye a
tsorace tana waige waige ashe har bacci ya
dauketa gurin bata sani ba, ta dago kai tana
kallon shatu dake gabanta tana huci, ba
karamin tsoro taji ba ganin shatu cikin
haske tunda gari ya waye har rana ta fito,
shatu mummunan gske ce ga baki kmr coal,
ta koma baya jikinta na bari murya na rawa
tace "kiyi hkuri don Allah bn san gari ya
waye ba," cikin tsawa shatu tace "don
ubanki ina ruwan da nace kije rafi ki debo
mana," Aneesah da ta gama rikicewa tace
"ki kiyi hkuri bn san lkcn da bacci ya...." mari
ta kai mata tare da fixgota ta rankwashi
kanta hade da turata da karfi tace "maxa
dauki tulu kije debo min ruwa shegiya
kawae," Aneesah na kuka ta dauki tulun da
ta nuna mata ta yi hanyar fita sae kuma ta
juyo tana kallon shatun da har lkcin ke
hararata tace "ban san rafin ba ai," "ehh kije
can bakin hanya ki jira duk wanda kika ga
alamar ruwa xae je debowa sae ki bisa,"
tana gama fadin hka ta shige bukkarta tana
cewa "ae ni irin hka nake so," Aneesah ta
fita daga gidan tana goge hawayen da yaki
tsaya mata ta dinga tafiya ba tare da tasan
inda xa ta ba, duk inda tabi indae da
mutane sae sun bita da kallo har ta kure
masu, ta rasa dalilin kallon hkn yasa ta kalli
kanta daga sama xuwa kasa, riga da skirt
na atamfa ne jikinta sae dankwali da
takalmin dake kafarta, tana kaiwa dai dai
wani hanya dake da hagu da dama ta rasa
inda xata bi, hkn yasa ta tsaya rike da tulin
tana kalle kalle kmr munafuka, wata yarinya
da baxa ta wuce ta ba ce taxo wucewa rike
da tulu ita ma, riga daban xani daban sae
dan sanda dake hannunta tana tafe tana
dan wake wakensu ta kauye, tana wucewa
Aneesah ta bi ta a baya, yarinyar ta juya tana
kallon Aneesar da ta tsaya ganin ita ma ta
tsaya, can yarinya tayi gaba Aneesah tabi
bayanta, ta sake juyowa tana kallon
Aneesah, hkn yasa Aneesah ma ta tsaya,
yarinyar ta sake yin gaba sae da Aneesah ta
bari ta dan yi nisa kadan snn ta shiga binta
da dan saurinta, yarinyar ta juya tace "ke
wae ni kike ta bi ne koko, kiyi hkuri babata
ce ta aikeni debo ruwa" Aneesah ta kirkiro
murmushi don a xatonta da yarinyar bata
jin Hausa ganin maka makan billen dake
fuskarta, Aneesah tace "ruwa xan debo
kuma ban san hanyar rafin ba," yarinyar ta
fasa dariya tace "ayya ni ae tsoro kika bn ina
ta tunanin ko ma Aljana ce....." Aneesah tayi
murmushi tana kallon yarinyar tace "sbda
me kike tunanin ni aljana ce ko garin nn
mutane da aljanai ne a hade?" yarinyar tayi
dariya ssai tace "A'a naga kina da kyau da
yawa kuma ke fara ce, duk kauyen nn bbu
mai irin kyan nn da haske shiyasa na tsorata
amma daga ina kike....." Aneesah tace "uhum
ni bakuwa ce bn san ko ina ba," yarinyar
tace "amma nn kauyen kika xo?" Aneesah ta
gyada mata kai kawae, yarinyar tace "to ya
sunanki kuma gidansu wa kika xo a nn?"
Aneesah tace "sunana Aneesah" yarinyar ta
saki dariya tace "tab kaji wani suna kmr
sugar wae Adeesam," Aneesah tayi dariya
tace "Aneesah nace, ke ya sunanki?"
yarinyar na washe baki tace "amma fa
sunanki da ddi, ni sunana karime," Aneesah
tace "ke ma naki ae da ddi, ynxu ki rakani
naga rafi na debo ruwa ana jirana a gida,"
karime tace "to wae gidansu wa kika xo nn,
don su ladiyo kadae ke da dangi a birni,"
Aneesah tace "nima dae ban san ko gidan
waye ba jiya da daddare na xo, amma
sunan matar gidan kmr Shatu," karime ta
xare ido tace "shatun mati, babarsu zulai,"
aneesah tace "kila ita ce," karime tace "tab,
shaidanun kauyen nn knn, bbu wande bai
san su a kauyen nn ba wajen mugun hali, ke
kyakkyawa ko meye hadinku, gasu munana
kmr gwaggwon alade," Aneesah tayi
murmushin takaici tce muje de mu debo
ruwa karime lkci na wucewa, yarinyar tace
"to," snn suka kama hanyar rafi tana ma
Aneesah firar dandalin garinsu. Haiydar ne
ke driving cikin nutsuwa xa shi gidansu
Aneesah, amma duk he is nt himself ya rasa
abinda ke damunsa, dai dai kwanan da xae
sha ya shiga layinsu wata mota tayi parkin
gabansa mutane hudu suka fito ya bisu da
kallon suprise duk kananun kaya ne jikinsu,
ganin gunsa suka nufo yasa ya bude
motarsa a hankali ya fito yana kallonsu, daya
daga cikinsu yace "Aliyu Muhammad ryt?" ya
tsaya kmr mai naxari snn yace masa "yea
any problem?"
~15~
.Daya daga cikinsu ya fito da I.D card daga
aljihunsa ya nuna ma Haiydar yace "yhu re
under Arrest," da mamaki Haiydar yace "4
wat reason?" suka ce idan muka je station
ka ji, any more word wil b said against yhu
in d court..... Yace "ok" snn ya mika makullin
motarsa ya bi bayansu suka shiga tasu
motar, wani daga cikinsu kuma ya taho da
motar haiydar. Ba karamin abun mamaki da
al-ajabi Haiydar ya tarar a station ba, wae
ana tuhumarsa da sace yarinya daxu da
safe, ya ma rasa ta cewa sae ido da ya xuba
ma 'yan sandan, suka mika masa hoton
Aneesah da kuma wani hoton shi da
Aneesar ya tsura ma hotan ido da mamaki,
cikin motarsa aka daukesu hoton, ya girgixa
kai yace "ni ban san me xan ce maku ba,
amma ni nayi maku kama da kidnapper,"
yana fadin hka ya ciro Identity c. Dinsa ya
nuna masu, inspectorn dake gabansa ya
karba yana kallon I.d din, snn ya tabe baki
yace "to barrister meye hadinka da wnn
yarinya, kuma ina xa ku a wnn hoton cikin
motar gashi da alama ma cikin tashin
hankali take a lkcn, tunda kuka take?" xae yi
magana Abdul ya shigo station din a
hargitse kmr mahaukaci, kan Haiydar ya yo
ya cakumosa yace "wllh wllh ka fito da
Aneesah idan ba hka ba sae na kashe ka,"
'yan sandan suka rirrike Abdul din, cikin
fushi inspector yake cewa "wnn kuma waye
xae shigo mana kamar mahaukaci, halan
bae san inda yake bne" da sauri wani
sergeant ya sara masa yace "dan wajen
honorable Shehu ne sir," inspector ya mike
tsaye yace "ohh kar ka damu yallabai muna
nn muna bincike ne ka kwantar da
hankalinka, kaje gida xuwa anjima ka
dawo," Abdul yyi ma Haiydar dake kallonsu
da mamaki wani mugun kallo snn ya fice
daga station din yana huci, duk yanda aka yi
da Haiydar a kan cewa shi ya sace Aneesah
sae dae ya girgixa masu kai yyi murmushi
yace "bani ne na sace ta ba, ku dae yi
bincike da kyau," hkn ya harxuka 'yan
sandan chief inspector yace a wuce da shi
cell kawae, suka karbe duk wayoyinsa da
agogan hannunsa, yace "amma ku yi min
alfarma daya na kira mum dita," wani
sergeant yyi masa mugun kallo yace "an ki
maka," Haiydar yyi masa wani mugun kallo
yace "kasan ko ni wanene," inspector ya sa
aka dauko wayar station din aka basa ya
kira mum din tasa, ba karamin rudewa
Hajiya tayi ba bayan Aliyu yace mata yana
station snn ya bata address din, tace "Aliyu
statiion kuma, me kke yi a station mai ya
faru?" yace "ki kwantar da hankalinki mum,
sae kin xo," yana kai wa nn suka amshe
wayar snn suka wuce cell da shi. Baffa ne ya
shigo station din yana xaxxare ido yace "ya
fadi gaskiyan inda ya kai min 'ya ta?" wani
sergeant yace "A'a bae fadi komai ba har
ynxu, sae ma mahaukata da ya mayar da
mu," cikin tsawa baffa yace "ina dpo yake,
uban me xae hana ku lallasa shi, tsayawa ku
kayi kallonsa kawae,?" wani sergeant ya
taho da sauri yace "honourable sir, dpo yace
ka shiga office dinsa," a fusace baffa yyi
hanyar office din dpo yana cewa "ae wnn
maganar bnxa ce, kunsan halin da muke ciki
ne na rashin yarinyar nn, xaku dinga binsa
cikin ruwan sanyi, shine fa karshen wanda
yaje wajenta jiya mahaifiyarta ta ce min
kafin tayi disappear, ba kuyi amfani da
statement din da na baku bne" yana shiga
office din dpo ya mike yana masa sannu da
xuwa, baffa ya xauna yana kallonsa yace
"kai ya aka yi ne sule, ca nake xan xo na
tarar ana jibgar shege," dpo ya girgixa kai
yace "ka ga har fa ynxu honourable bbu
kwakkwaran abinda xa mu fake da a kan
cewar shi ya dauke wnn yarinya, snn fa dat
aside, babban barrister ne, to ta ina kke ga
xamu fara ynxu," baffa yyi tsaki yace "ka ji
ka sule sae kace ba tsohon dan duniya ba,
kudina ne fa ke magana a nn, kuma ba ga
hotuna nn na kawo ba ko wnn bai isa a
fake da ba" sule yace "to shiknn, amma fa
sae ka kara kudi honourable, da alamar ina
ga xamu yi nasarar jefa sa prison idan mun
shiga court, tunda ynxu kam bae da mafita
ga hotunansu nn da yawa a tare, kawae dae
a tabbatar har a gama shari'ar nn, yarinyar
nn baxata bayyana ba," baffa yyi dariya yace
"ka kwantar da hankalinka ni ina da yakinin
baxata taba fitowa daga inda na kai ta ba
sae dae in fito da ita aka yi, ae matata tayi
maganin wnn, daxun nn ita ma ta dawo
daga kauye taje aiki." dpo yyi dariya ssae
yace "to sae naji alert honourable," baffa ma
ya mike yana dariya yace "wnn ai ba matsala
bace, ku dae kuyi aikinku da kyau," yana fita
daga office din yyi hanyar cell din da Haiydar
yake yana nuna sa da dan yatsa kmr xae yi
kuka yace "mugu munafuki sae ka fito min
da 'ya ta," Haiydar ya mike tsaye da sauri ya
cakumosa ta karfen cell din ya makure masa
wuya da karfi, baffa ya dinga tsala ihu da
kyar 'yan sandan suka kwace sa, a tsorace
baffa yace "kun ga ya kashe min 'ya nima
yana neman kashe ni ko," ku tabbatar kun
hukunta min shi wllh, baffa ya fice daga
station din kmr munafuki. Yana fita Hajiya ta
shigo a rikice tana cewa "ina dpo..." 'yan
sandan suka ce baxa ta samu ganinsa ba, a
rude ta bukaci sanin abinda dan nata yyi,
tana jin hka kuwa ta xaro ido da mamaki
tana kallon hoton Aneesah da suka mika
mata.
.
Duk yanda Hajiya ta so ganin Dpo hkn bae
yiwu ba don 'yan sandan ca suka yi baxa ta
sami ganinsa ba, tace to tana son magana
da dan nata, nn ma suka ce sae dae ta dawo
xuwa anjima, nn da nn tashin hankalin dake
fuskarta ya bace ranta yyi mugun baci,
amma bata ce masu komai ba, ta tsura ma
hotan Aneesah dake hannunta ido tana
huci, ynxu duk hankalinta na ga son sanin
'yar gidan uban wacece Aneesah, meye
hadinta da Aliyunta har xa a daure mata son
a kanta, tayi murmushin mugunta tace
"muddin na tabbatr ke wacece kwananki ya
kare yarinya" ta fice daga station din kmr
xata tashi sama a xuciyarta tace ynxu gun
su barau da lado xa ni, Allah ya kai mu
anjiman, amma yarinya kin jawo ma kanki
don sae na sa an kashe min ke an kashe
banxa snn duk wani naki ma sae ya bakunci
lahira, kai har matar da ta kawo min ke ma
sae na sa an nemo min ita yau, "wato
Ammi," duk sae na ga bayanku ni Fateema,.
A bangaren Ammi kuwa baffa bae sauka
gidansa ba yana isa