Showing 36001 words to 39000 words out of 70370 words

Chapter 13 - FANSAR FATALWA complete hausa novel

26 Oct 2025

100

Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_

*Free book*

---------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*019*
_____________________________

Takowa Amrah tayi cikin sauri har ta ?araso in da nake tsaye Win,sannan ta sanya hannu ta juyo da fuska ta muka kalli juna cikin matsanancin mamaki Amrah ta furta.

"Amira kuka!, Amira kuka kike mai ya sameki?".

Duk yadda na so na daidaita kaina amma abun ya gagara inda a maimakon na bawa Amrah amsar tambayar da ta mun Win,kawai sai gani tayi na rungumeta tare da fashewa da wani irin kuka mai taSa zuciya.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun, Amira wai meye haka dan Allah?, Amira ko wanine ya mutu ban sani ba?, Dan Allah ki sanar dani".

Amrah ta faWa cikin matsanancin tashin hankali a lokacin itama har idanun ta sun fara cikowa da hawaye saboda yadda nake rubzar kukan duk rashin tausayin mutum sai ya ji tausayi na domin kuwa zaku yi tunanin cewar ko uwata ce ko ubana wani ya mutu.

?ofar Wakin namu muka ga an buWe inda muka ga su Azra sun fito daga cikin Wakin alamar kukan da nake Win ne ya sanya su fitowa.

"Subhannallah Amira lafiya kuwa? Amrah mai yasameta haka?".

Azra ta faWa tana ?o?arin kai hannun ta jikina dan ta taSa ni.

Ai da sauri na Wago da fuskata da niyyar balbale ta da bala'i, sai dai mai kallon da naga tana jifana dashi ne ya dakatar dani daga abin da nayi niyyar yi Win, domin kuwa wani irin kallo mai cike da alamar gargaWi Azra Win ta shiga aika mun,idanun ta kaWai na kalli na fahimci inda ta dosa da kuma abun da take nufi,watau Amira kar ki fara wannan gangancin domin kuwa zaki yi dana sani.

Wannan kallon da naga Azra tana mun ba ?aramin tayar mun da hankali yayi ba,take jikina yayi sanyi inda na janye jikina daga na Amrah sannan na shige cikin Wakin ina tafiya kamar wadda ?wai ya fashewa a ciki,na bar su Amrah tsaye baki sake.

Sai dai ina shiga cikin Wakin Amrah ta biyo bayana da sauri tana cigaba da jaifamun tambayoyin da tamun Wazun amma shiru nikam ba amsa.

Sai dai a raina na ?uduri niyyar in sha Allah duk yadda zan yi sai nayi domin na tarwatsa shirin su Afrah Win,sannan zan samu Azra ko gobe ne mu keSe da ita na mata nasiha ko Allah zai sa taji.

Sai dai washegari tun da asubar fari aka ?irani a gida inda ake mun neman gaggawa sakamakon jikin mahaifina da ya tsananta har an kaishi asibiti.

Cikin tashin hankali na tashi na shirya sannan na sanar da su Amrah abin da yake faruwa,sai dai sun bu?aci na bari su shirya mu tafi tare,ban so su Afrah suka bini ba,amma ba yadda zan yi domin kuwa ina yin wani abu ?alilan Amrah zata iya fahimtar wani abu shiyasa na ?yale su muka tafi tare, inda bayan sun duba shi suka dawo makaranta nikuma suka barni a can.

Allah sarki Amrah ashe wannan dawowar da suka yi ita ce mafarin komai.

Bayan tafiya ta da kwana biyu abubuwa sun faru waWanda ban san wasu ba,wasu kuma na samu labarin su daga wajen wasu abokanan karatun mu.

Yau ta kama Friday da wuri su Amrah suka tashi a lecture tafe suke su huWu a harabar makarantar,idan ka kalle su sai sun baka sha'awa domin kuwa zaka iya rantsewa zuciya Waya suke zaune da juna sai da ta ciki na ciki.

A dai-dai wajen roundabout Win da zaka nufi hanyar hostel suka ci karo da wata ?ar class Win mu in da tana hango su ta fara musu kirari tun daga nesa.

"Kaga taurari guda biyar a ganku a barku tun daga nesa kuke haskawa,amma kuma gaskiya yau akwai abu Waya da babu a cikin ku".

"?ayar tauraruwar ce babu, watau Amira".

Anisa ta faWa da sauri.

"Tabbas!, Amma ina kuka baro ta".

"Hmmm wallahi Fiddausi mahaifin ta ne ba lafiya tana gida an kwantar dashi a asibiti".

Amrah ta faWa fuskarta da alamun damuwa.

"Eyya Ubangiji Allah ya bashi lafiya".

Fiddausi ta faWa cikin jimami sannan ta mana sallama ta wuce.

Da Ameen suka amsa mata sannan suka wuce suka nufi Hostel.

*****

A Sangaren na kuwa a can asibiti yau mun tashi da matsanancin tashin hankali domin kuwa yau jikin mahaifina ya tsananta likitoci ne kawai suke kaiwa da komowa a kan shi.

Sai dai abin da Allah ya nufa ba makawa sai ya faru,ashe jinyar mahaifina bata tashi bace,inda ba'a Wauki tsawon lokaci ba rai yayi halin shi, Allah ya yiwa mahaifina rasuwa.

Wannan rasuwar ba ?aramin girgiza ni tayi ba dani da sauran ?an gidan mu musamman ma ni domin kuwa har aka kai mahaifina ma?abarta aka dawo dashi ban san inda kaina yake ba.

Bansan yadda aka yi su Amrah suka samu labarin rasuwar mahaifin nawa ba,sai ganin su nayi gaba Wayan su a daren ranar har a lokacin ma ban farfaWo ba, sai da na kwana ban san a wace duniyar nake ba kafin bayan gari ya waye na farfaWo inda na tarar da su Amrah da Afrah a kaina suna mun firfita.

Sannu suka mun gaba Wayan su,amma ban samu damar amasawa ba sai ido da na bisu dashi.

Kwanan su Amrah biyu a gidan mu kafin a ranar na uku suka kama hanya suka koma makaranta bayan sun raka mahaifina da addu'ar samun rahamar Allah.

Tun daga bakin gate Win makarantar mu Amrah ta fara ganin wani ba?on al'amari yana faruwa domin kuwa duk inda suka wuce sai taga Walibai ana binta da kallo wasu kuwa har nunata suke wanda ta rasa gane dalilin hakan.

A haka dai suka cigaba da tafiya har suka doshi hanyar Hostel, sai dai abun mamaki shine suna isowa daf da wata dabar wasu ?an mata da samari,kunnuwan Amrah suka jiyo mata wata kalma da tayi matu?ar bata mamaki.

"Kun ganta waccan ta tsakiyar ita ce ai,ku ganta kamar ta Allah ashe munafuka ce kullum cikin hijab ashe na ?arya ne".

Wani saurayi ya faWa yana nuna saitin inda Amrah Win take.

"To kai daman Hamza ai kawai ka kalli masu sanya hijab Win nan ka ?yale su,domin kuwa duk munafukai ne,cikin su fal yake da iskanci".

Da sauri Amrah ta kai duban ta wajen samarin sannan ta dubi su Azra a tunanin ta ba da ita suke maganar ba, sai dai tana kallon su taga ita suke nunawa.

"Azra kun ji abun da waWan can suke faWa kuwa?".

"Wallahi na jisu amma share su neman maganane kawai".

Azra ta faWa cikin son ta kawar da zancen.

Haka dai suka ?arasa Hostel inda suna shiga suka ci karo da Fiddausi ta nufo su hankali tashe, tare da kama hannun Amrah tace.

"Amrah Dan girman Allah idan kin ?arasa shiga cikin Hostel duk wanda kika ji ya miki wata maganar banza karki saurari kowa".

"Fiddausi lafiya kuwa mai yake faruwa?".

Amrah ta faWa fuska cike da mamaki.

"Bakomai kede kawai kiyi abun da nace".

Fiddausi tana kaiwa nan a zancen nata ta wuce su Amrah da sauri ta bar wajen.

Shiru Amrah tayi cike da mamakin waWannan abubuwan.

*****

A can gidan mu kuwa,cike gidan yake da mutane har a sannan gidan kamar yau aka yi mutuwar. Kun san yadda gidan mutuwa yake a wannan zamanin wanda ya mutu shine dai ya mutu sai kuma ?an uwan shi na jiki wanda mutuwar ta shafe su. To haka take a gidan namu ma inda wasu cin abinci ne ya kai su, wasu kuwa gulma ce ta kai su,kowa dai da abin da ya kai shi.

"Ke ?awata kinga wani video da akayi posting Wazu a TikTok".

Wata mata ta faWa tana nunawa ta gefen ta wayar tata.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun ?awata wannan ai yarinyar da suka kwana a gidan nan ne jiya,?awar Amira".

Matar ta faWa tana ?asa-?asa da murya wai gudun kar na jita,sai dai bata san ta makaro ba domin kuwa caraf naji dirar maganar tata a kunnuwan na.

Haka kawai naji gaba ya shiga bugawa,inda naji a raina ina son naji akan abun da suke maganar.

A hankali na tashi sannan na nufi inda suke zaune Win na zauna a gefen su.

Su kuwa ganin na dawo kusa da su sai suka fara ?o?arin sauya zancen da suke Win, ni kuwa hannu na sanya na Wauki wayar da take kan cinyar matar sannan na cemata cikin dasasshiyar murya ta wacce kana ji kasan ta gaji da kuka.

"Nuna mun videon da kuke magana a kai".

Haka kawai matar taji na mata wani irin ?warjini take ta karSi wayar ta shiga TikTok Win sannan ta kunna videon.

Fuskar Amrah ce ta bayyana a jikin videon,inda ta shiga toilet sanye da towel sannan ta cire shi ta ajiye a gefe sai gata tsirara haihuwar uwar ta tana wanka.

Wata irin sarawa kaina yayi take kuma wayar ta suSuce mun a hannu inda na fara ganin dishi-dishi sai kuma cak numfashi na ya datse inda na zube a wajen a sume.

Nan fa mutane aka yo caaaaa a kaina inda kowa ya shiga faWin albarkacin bakin shi, mahaifiya ta ce ta nufo ni cikin tsananin tashin hankali tana kuka.

WaWanda basu san dalilin sumewar tawa ba,cewa suka fara yi na zama marar tawakkali domin kuwa i zuwa yanzu ya kamata ace na karSi wannan ?addarar da ta same mu nayi ha?uri tun da shikam mamaci ya riga da ya mutu. Haka dai kowa ya shiga faWin ta bakin sa.

Bayan wani lokaci aka yayyafa mun ruwa na farfaWo, ina farfaWowa da sunan Amrah na farfaWo a baki na,inda na kai dubana wajen waWannan matan sai dai wayam inda suke zaune Win babu su ba alamar su ashe wai tun lokacin da suka ga na sume Win suka cika wandon su da iska.

"Ina wayata Umma".

Shine abun da na faWa ina kallon inda Umma na take tsaye.

Kallo na Umman nawa ta shiga yi cikin tsananin mamakin abun da taji nace Win.

Ni kuwa ganin irin kallon da Umman take mun sannan na lura bata da niyyar bani wayar tawa ya sanya na tashi da gudu na tsallake duk tarin mutanen da suke zaune a wajen sannan na shige cikin Wakina inda na tarar da wayar tawa a yashe a kan gado. Da sauri na Wakko ta sannan na shiga dialing number Win Amrah sai dai no answer, na mata ?ira ya kai goma a jere amma ba'a Wagawa, nan fa hankalin na ya ?ara dugunzuma, wayar Azra na shiga ?ira inda ina mata bugu Waya ta Waga.

"Shegiya munafuka,makira algunguma ina Amrah?".

Duk da bana gaban ta amma sai da na fahimci cewa taji zafin zagin da na mata Win. Ban damu ba inda na cigaba da magana.

"Wallahi Azra ban taSa sanin cewa ke azzaluma bace sai a yau,tabbas kin cika shaiWaniya amma sai dai ki sani wallahi baki yi nasara a kan Amrah ba, domin kuwa sai na tona miki asiri ki jira dawowa ta makaranta ki gani tsinnanniya kawai".

"Sanin hakan da nayi Amira shiyasa na miki babban tanadi,ki sani cewa kin makaro domin kuwa ni Azra murucin kan dutse ce ban fito ba sai da na shirya, Amira ina nan ina jiran ki dan Allah ki tona mun asiri kinji".

Azra tana kaiwa nan a zancen ta ta datse wayar ta bar ni da baki a sake.

Kan kuce kwabo gidan mutuwa ya zama dandalin zancen Amrah domin kuwa cikin ?an?anin lokaci aka bi duk wata kafa ta sada zumunta aka yaWa wannan videon,kafin wani lokaci video ya samu viewers sama da mutum dubu Wari biyar a TikTok ban da facebook da sauran kafafen soshiyal media Win.

Wani abun da zai baku mamaki da kuma zai Waure muku kai shine duk videon da aka sanya Win a lokaci guda aka sake su,sannan gaba Waya sunan Amrah ne akan duk account Win da aka Wora videon wannan ya tabbatarwa da mutane cewar Amrah Win ce da kanta tayi posting videon tsaraicin nata.

Lokacin da labarin wannan videon ya riski Amrah ?aryatawa tayi sai da ta ganshi ido da ido kafin fa hankalin ta ya tashi inda ta shiga suma tana farfaWowa,domin kuwa ta suma ya kai sau biyar,ga wasu irin zantuka da ta dinga yi marrassa kan gado kana jin su zaka ce ta zauce.

Duk wanda yake wajen Amrah a wannan lokacin sai da ta bashi tausayi hatta ita kanta Afrah sai da taji tausayin Amrah Win take wani irin dana sani ya rufe ta,inda ta shiga rusa kuka itama kamar an aiko mata da sa?on mutuwa.

Wani abin mamaki shine sune Azra sun fi uban kowa shiga damuwa domin kuwa idan ka kalli Afra ta kalli Azra ka kalli Anisa sai ka kasa tantance wacce tafi wani shiga damuwa.

Kafin wayewar gari video ya samu sama da one million viewers likers kuwa ba zasu ?irgu ba, haka cikin makarantar su Amrah duk inda ka wuce ba zancen da ake wanda ya wuce na videon tsaraicin Amrah Win.


*MANGA*
'?.
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ =؀? &?).

_Tsarawa/Rubutawa_

*? SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillah_.

*Free book*

---------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*020*
______________________________

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun na shiga uku na jama'a ku sanar dani cewa mafarki nake, Amira dan Allah ku cemin mafarki nake ba gaskiya bane abun da na kalla, Wayyo Allah na hasbunnallahu wa ni'imal wakil, Ubangiji Allah kayi gaggawar Waukar rayuwata tun kafin na gano cewa ba mafarki nake ba".

Amrah ta faWa wadda farfaWowar ta kennan daga suma na shida da tayi Kennan.

Saurin ri?o ta Afra tayi sannan ta sanya hannu ta toshe mata baki,tare da fara magana cikin kuka.

"Amrah dan Allah kiyi ha?uri ki daina kuka, wadannan maganganun duk ba su kamace ki ba a wannan halin da kike ciki, Amrah addu'a ita ya kamata kiyi".

Da sauri Amrah ta Wago idanuwanta da suka kumbura suka sanja kalla saboda tsabar kuka sannan tace.

"Afra ha?uri!, Ha?uri fa kike ambatar nayi, Afrah da gaske ne videon tsaraicina ne yake trending a social media?", Dan Allah kuyi gaggawar sanar dani".

Anisa ce ta kamo hannun ta wadda itama hawayen take amma na munafurci sannan tace.

"Amrah ki Wauki hakan a matsayin ?addarar rayuwar ki, Amrah ki sani kowane bawa da kalan tashi ?addarar kuma ita ?addara ba a iya kauce mata,kiyi addu'a kawai Allah ya baki ikon cinye wannan jarrabawar".

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun Kennan ya tabbata da gaske ni ce nake yawo tsirara a social media, idan kuwa har haka ne to wallahi banga amfanin rayuwa ta a doron ?asa ba,gwanda na mutu kowa ya huta".

Amrah ta ?arashe maganar tana gwara kanta da jikin gadon da suke zaune Win take kuwa kan nata ya fashe sai ga jini ya fara SulSulowa daga goshin ta, amma duk da haka Amrah ko a jikin ?o?ari take kawai taga ta ?ara fasa kanta.

Cikin hanzari Azrah ta mi?e tare da ciro bandage a cikin side drawer Win su,kasancewar suna da first Aid Box a Wakin inda suke ajiye ?an abubuwan da ba za'a rasa ba,irin su allurai da wasu magungunan haka saboda gudun abun emergency ya faru.

?o?arin rike Amrah ta fara domin ta samu damar tsayar da jinin da yake zubomata Win,amma ina Amrah gaba Waya ta fice daga hayyacin ta, lokaci guda ta fara wasu irin buge-buge kamar mai wasu aljanu,kanta kuwa bata daina bugashi a jikin gadon ba,da ?yar su Afrah suka haWu suka danne ta sannan Azra ta samu ta naWe mata kan nata da bandage Win tare da yi mata allurar kashe zogi.

BuWe baki Afrah tayi zata mata magana sai dai cikin sauri Amrah Win ta katse ta sannan ta cigaba da magana.

"Karki cemun komai Afrah, shin maina aikata a duniya wanda na cancanci irin wannan mummunan hukuncin?, Shin waye yake son ganin bayana a doron ?asa?, Maina aikata musu?, Tabbas duk wanda ya mun wannan cutarwar wallahi wallahi ba zan taSa yafe mishi ba domin kuwa bai cancanci yafiyata ba".

Jikin Afrah ne ya ?ara yin sanyi jin kalaman da Amrah Win take yi,Tabbas sai a yanzu ta fara nadamar abun da suka aikata mata Win, innalillahi wa'innailaihi rajiun meyasa na bari shaiWan yayi galaba a kaina?, Maiyasa na bari soyayya ta rufe mun ido har na manta da muhimmanci ?awance da kuma zaman tare?, Maiyasa na yadda aka haWa kai dani aka cutar da baiwar Allahn nan?, Yanzu da wana ido zan kalle ta har na nemi yafiyar ta?".

Kallon ta Azra tayi sannan ta mata wata alama da ido wadda na kasa fahimtar ta mainene.

Turo ?ofar Wakin namu aka yi aka shigo, inda muka ga wasu ?anmata ne guda biyar suka shigo tare da neman waje su zauna sannan Waya daga cikin su ta dubi Amrah ta ce.

"Subhannallah Amrah ashe abun da ya faru kennan! Ashaaa! Gaskiya abu bai yi kyau ba,bai kuma yi daWi ba,kamar ke yadda kike da ilimin addinin nan amma a wayi gari kin yaWa tsaraicin ki a duniya,gaskiya ilimi bai yi rana ba".

Ta ?arashe maganar tare da sakin wata shewa ita da abokan nata.

Ai Afrah bata yi wata-wata ba ta tsinke wadda take maganar da wasu irin tagwayen maruka sannan ta nuna ta da yatsa.

"Kefa daman Khadijah baki da mutunci inda mutunci yake ma baki dosa ba,ke a rayuwar ki baki da wani buri kullum wanda ya wuce kiga kin tozarta mu, to kiyi gaggawar fice mana daga cikin Waki tun kafin mu sauya miki kammanni".

Afrah ta ?arashe maganar tana sakin wani irin huci.

"Kan bala'i ni zaki mara Afrah to wallahi yau sai dai ko mu ko ku a cikin Wakin nan, dan wallahi yau sai dai ayi kare jini biri jini".

Khadija ta faWa tana mai yin kukan kura tare da kaiwa Afrah wata irin wawar sha?a.

Ai fa nan suma sauran ?anmatan da suka shigo tare da Khadijah suka mara mata baya tare da rufe Afrah da duka.

Ganin haka ya sanya su Azra ma suka shigarwa Afrah inda take faWa ya kacame a tsakanin su, duka suke kaiwa junan su ta ko ina ba ?a?autawa burin kowa shine yayi galaba akan Wan uwan shi.

Allah sarki Amrah kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login