Showing 60001 words to 63000 words out of 70370 words

Chapter 21 - FANSAR FATALWA complete hausa novel

26 Oct 2025

104

buWe baki da niyyar yin magana sai dai yin arba da mutumin da yake mishi maganar ta sanya ta shi maganar ma?alewa inda ya kafe mutumin da ido cikin wani irin yanayi mai wuyar ganewa.

Kallon da mutumi ya ga Justice Kabir Win yana bin shi da shine ya sanya shi cika da mamaki kafin kuma ya jijjiga kai ya koma cikin motar shi yana ganin cewar kamar Justice Kabir ba mai lafiya ba.

Saurin jan motar shi Justice Kabir ya yi tare da komawa gefe sannan ya sanya hannu ya Wakko hoton Malam Kabiru ya duba nan fa ya buWe motar da sauri ya shiga duban inda ya ga wannan mutumin ya nufa sai dai ya tarar har mutumin ya shiga motar shi ya tayar yana ?o?arin barin wajen , da sauri shima Justice Kabir ya koma cikin motar shi tare da bin bayan motar mutumin amma kuma sai dai sama ko ?asa ya nemi motar ya rasa ta Sace mishi.

Hankali tashe Justice Kabir ya shiga bin bayan motoci da gudu amma ko mai kalar motar mutumin bai gani ba.

Hankali tashe Justice Kabir ya koma cikin motar shi sannan ya tayar tare da barin wajen ya na nufar gidan Rediyo Win,shi kam duk da a hoto ya ga fuskar Malam Kabiru ko shakka ba ya yi wanna mutumin shine mahaifin Amrah. To amma ta ya hakan ta kasance tun da ya san a labarin da Amira ta bayar na Amrah ta sanar da su cewar iyayen Amrah talakawa ne to amma ya akayi yanzu kuma ya ga Malam Kabiru cikin shiga ta alfarma?.

Amsar da Justice Kabir ya kasa samarwa kan shi Kennan har ya isa gidan rediyon zuciyar shi cike da tunani iri-iri.

Yana isa gidan Rediyon ya sanar da su abin da yake tafe da su sannan ya basu hoton Malam Kabiru Win tare da cewar duk wanda ya gano inda Malam Kabiru da iyalan shi su ke ya masa al?awarin kyautar kuWi har Naira Miliyan guda.

Bayan ya gama komai ne ya fito daga cikin gidan rediyon sannan ya nufi motar shi da niyyar shiga sai dai kuma ?iran da ya shigo wayar shine ya sanya shi dakatawa tare da Waukar number Win.

"Hello ya ake ciki ?".

"Ranka ya daWe na samo labarin inda mutumin yake yanzu haka yana Jahar Yobe a cikin garin Potiskum,a wata unguwa da ake cewa Tsohuwar kasuwa,dan haka duk sanda ka shirya sai ka mun magana na raka ka".

Shine bayanin da aka yiwa Justice Kabir a cikin wayar aikuwa cikin zumuWi da murna ya ce gobe za su wuce garin.

Sai dai abin bada ya bashi mamaki to shi kuma wancan da ya gani Wazu fa waye?.

Tambayar da ya kasa bawa kanshi amsa kennan.


*****

Anwar tafe yake a cikin motar shi baka jin sautin komai a cikin motar face karatun Alkur'ani da yake tashi cikin zazza?ar Muryar Sheikh Sudes cikin ?ira'ar sa mai sanyaya zuciya.

Tun daga nesa yake zabga horn sakamakon kallon mace da yayi a tsakiyar titin tana tafiya cikin ?wanciyar hankali kamar ta samu cikin Wakin ta. Wani abin ?arin haushi da takaici shine bai wuce yadda Anwar yaga ta manna mishi ba duk irin Horn Win da yake zabgawa Win ta ?i barin kan titin ko a jikin ta balle ta nuna mishi ta san ma da wanzuwar hallitar shi a wajen.

Sai da Anwar ya iso daf da ita kafin ya ja wani mahaukacin burki ko kashe motar bai yi ba ya buWe murfin motar ya fito a fusace ya fara magana.

"Ke wace irin ?ar gadara ce kina tafiya a kan titi kamar kin samu titin gidan ku,ko an gayamiki cewar titi wajen shashanci ne iyee?, Ko ke kurma ce bansani ba".

Sai a sannan wannan matashiyar budurwa ta juyo itama cikin masifa ta fara magana.

"Shin kai makaho ne!?, Ko an gayama an yi titi ne saboda shashashun mutane irin ku masu tsula gudu a kan titi ba bisa hankali ba!, Da zaka dinga gudu a titi sarai na jika kaka mun horn kawai ban yi niyyar kaucewa bane domin ina so na tabbar ko da sauran hankalin ka".

Tun daga juyowar da tayi Anwar ya kafe ta ido ko runtsawa ba yayi har zuwa yanzu da ta dasa aya a maganar da take Win,tsananin mamaki da ruWani ya shiga a lokaci guda kafin ya furta.

"Amrah!".

Ya furta a hankali kafin kuma ya ji idanun shi sun fara mishi dishi-dishi ga kan shi da ya sara mishi a lokaci guda sakamakon tozali da fuskar budurwar da yayi fuskar da har ya koma ga mahaliccin shi ba zai manta da mamalakiyyar fuskar ba, cikin rawar murya da hannu ya shiga nuna ta yaba furta.

"Amrah da......ma...n ki.....nna a....Ra...ye..., Amr...ah..da...m..a .n ba ...ki.....mu....tun.....ba?".

Anwar ya ?arashe maganar yana mai kai hannun shi tare da shafa fuskar wannan budurwar da yake ikirarin Amrah ce.

Wani ihu wannan budurwar ta sake sannan ta make hannun Anwar da yake kan fuskar ta kafin ta zura da gudu tana furta.

"Allah ya isa na wallahi wuta balbal,haka kawai daga ganina zaka hau taSa mun fuska kana wani ?iran wata Amrah mugu kawai,wallahi ban yafe taSa mun fuska da ka yi ba".

Ai shima Anwar da gudu ya bita yana ?wala mata ?ira yana cewa ta tsaya dan Allah.

Ai ina! ita kuwa ganin ya biyota da gudu ya sanya tsoro ya ?ara rufe ta nan fa ta ?ara kaimin gudun ta haba wa zo ku ga gudu ?afa mai naci ban baki ba.

_Ku yi ha?uri ba zan dinga dogon typing ba saboda_ _idona_ .

Follow my Whattpad account @shansiyyamanga, Arewa books@shamsiyamanga.
Whatsapp number
07060943991
Phone call
09965779330
Don't forget to share and comment pls.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_=؀? &? ).

_Tsarawa/Rubutawa_

? *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

-------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*31-35*
_______________________________

Haka Anwar da wannan matashiyar budurwar suka cigaba da gudu a kan titi kasancewar titin ba irin public titi bane ba sannan gashi unguwar ba mutane shiru. Sai da suka kusa ?ure titin kafin ya ga ta sha wata kwana inda tana sha ta nufi wani gida wanda shine na uku a cikin layin sannan ta shiga buga gate Win gidan kamar zata Salla shi.

Da sauri mai gadin gidan ya buWe gate Win ko jira bata yi ya gama buWewa ba ta hankaWe shi ta shige cikin gidan da mugun gudu, mamaki ne ya cika mai gadin ganin halin da ta shigo cikin.

Le?awa waje yayi ya ga ko lafiya kuwa inda kuma a dai-dai sannan Anwar ya ?ara so bakin gate Win gidan yana ?o?arin danna kan shi cikin gidan .

Da sauri mai gadin ya tare shi yana cewa.

"Malam lafiya kuwa?, Ya zaka zo ina bakin aiki na ba magana kawai zaka fara ?o?arin ture ni ka shiga gidan mutane".

Sai a sannan Anwar ya dawo hayyacin sa ya lura da abin da yake shirin aikatawa Win, kan shi ya shiga sosawa sannan ya fara bawa mai gadin ha?uri.

"Dan Allah kayi ha?uri bawan Allah, Amrah na biyo kuma ta san da zuwa na".

Kallon shi mai gadin ya yi she?e?e sannan yace

"Wacece haka kuma?, Wacece Amrah?".

"Amrah dai ta gidan nan mana wadda ta shiga yanzu".

Anwar ya faWa yana cigaba da le?a cikin gidan.

"Kaga Malam gidan nan ba wata Amrah ina ganin ka yi Satan kai ne".

Mai gadin ya faWa yana ?o?arin juyawa zai mayar da gate Win ya rufe.

Da sauri Anwar ya sanya hannu ya ri?e gate Win tare da cewa.

"A'a dan Allah bawan Allah ka tsaya na maka bayani, Amrah fa ta cikin gidan nan wadda ta shiga yanzu,da idona na ganta ta shida cikin gidan kuma kace mun ba Amrah a gidan nan".

"Oh wai Farida ka ke nufi!, to ai wannan sunan ta ba Amrah ba sunan ta Farida".

"Kamar ya wace Farida kaga nifa Amrah nagani ba wata Farida, dan Allah ka ?yale ni na shiga mu yi magana".

"Kai Malam wallahi ba inda zaka shiga ya ina faWa ma magana kana mun musu ni da nake aiki a gidan nasan kowa a gidan ba wata Amrah a cikin gidan nan, dan haka kauce ka cire mun hannun ka a jikin ?ofar nan zan rufe ?ofa".

Ai Anwar yana jin abun da wannan mai gadin ya faWa ya yi saurin zube gwaiwowin shi a ?asa tare da ri?e ?afar shi yana mishi magiya akan ya taimaka ya bar shi ya shiga.

Shi kam mai gadin mamakin wannan lamari ya shiga yi,inda ya shiga kiciniyar ?wace ?afar shi daga hannun Anwar Win, a dai-dai sannan kuma wata mota ta ?araso ?ofar gidan tare da yin horn a mai gadin.

Da gudu mai gadin ya ?wace ?afar shi a hannun Anwar sannan ya buWe gate Win gaba Waya inda mai motar ya kunna hancin motar shi zuwa cikin gidan.

Ai Anwar yana ganin haka da gudu shima ya mi?e tare da rufawa motar baya shigar Anwar cikin gidan yayi dai-dai da tsayawar motar inda matu?in motar ya ziro ?afafuwan shi waje tare da fitowa.

?aga ?afar shi Anwar yake ?o?arin yi amma ya kasa sakamakon tozali da fuskar mutumin da yayi.

Wani matsanancin bugawa ?irjin shi ya shiga yi a lokaci guda kuma wata zuffa ta shiga karyo mishi.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun wannan ai mahaifin Amrah ne to amma ya aka yi hakan ta faru?, yaushe ya zama mai kuWi? Sannan ya tabbata Kennan Amrah ba mutuwa ta yi ba ko mai hakan yake nufi?, Ko dai gizo suka fara mishi domin kuwa a labarin da mahaifiyar shi ta ba shi ta sanar dashi cewar a gaban idon ta aka kawo gawar Amrah sannan a gaban idon ta aka Wauke ta aka sallace ta a ta?aice ma ?anin shi Nazir a gaban idon shi aka sanya gawar Amrah a cikin ?abari. Sannan shi dai ya san tun da aka kafa duniya Allah ya hallici mutanen cikin ta ba'a taSa mutuwa an dawo ba.

*****

Yau Justice Kabir suka kama hanyar garin Yobe domin zuwa ya haWu da iyayen Amrah kamar yadda ya ?uduri niyya.

Kasancewar garin Yobe da Zaria akwai tafiya sosai domin kuwa a ?alla zai Wauki mutum tsawon awanni shida kafin ya isa jahar Yobe Win.

Lokacin da suka isa garin Potiskum Win basu wani sha wahala ba wajen neman unguwar da aka ce musu Malam Kabiru Win yake, Kasancewar Tsohuwar kasuwa tana Waya daga cikin manyan unguwanni kuma daWaWdu a cikin garin.

Da tambaya da komai aka kawo su har ?ofar gidan Malam Kabiru Win inda suka tarar da shi zaune da wasu mutane manya guda huWu yana ?ara musu karatu.

Waje suka nema suka zauna a gefe suka jira har Malam Kabiru Win suka dasa aya sannan ya juyo ya dube su cikin sakin fuska yana musu maraba.

Suku wa waWannan mutanen tashi suka yi tare da yiwa Malam Kabiru sallama suka Wauki littafan su suka tafi.

Bayan tafiyar mutanen ne Malam Kabiru suka shiga gaisawa sannan ya tashi wani yaro da yake zaune a gefe yace ya shiga cikin gidan yace a bashi ruwa yayi ba?i.

?ofi mai tsafta aka zubo musu ruwan a ciki,ruwa mai sanyi kamar na fridge.

Sai da suka sha ruwan sannan Malam Kabiru ya dube su yace.

"Maraba sannun ku da zuwa hala ba?i muka yi?".

Murmushi Justice Kabir Win ya yi sannan yace.

"Eh alah gafarta Malam fatan mun same ku lafiya?".

"Lafiya lao Alhamdulillahi amma sai dai ban gane ku ba?".

Malam Kabiru ya faWa yana mai tattara gaba Waya hankalin shi zuwa kan su.

Mukhtar ne wanda suka zo tare da Justice Kabir ya dubi Malam Kabiru yace.

"Eh Malam daman balalle ka gane mu ba domin kuwa baka san mu ba, ba?i ne mu daga Zaria mu ke".

Tun da kalmar Zaria ta dira a kunnen Malam Kabiru gaba Waya yanayin fuskar shi ya sanja daga fara'a zuwa haWe fuska, su kan su su Justice Kabir Win sai da jikin su yayi sanyi.

"Bayin Allah to mai ya kawo ku waje na?, Ku yi ku faWa domin inada abun yi".

Malam Kabiru Win ya faWa yana kawar da kan shi gefe domin tun bayan barin su garin Zaria ya ji ba ya sha'awar ko sake waiwaiyar abin da ya shafi Yamma ma balle kuma wata Zaria,har zuwa yanzu yana jin abin da mutanen garin suka mu su a ?asan zuciayar shi sannan ba zai taSa mantawa da wannan abin ba har ya koma ga mahaliccin sa.

"Malam daman mun je garin Giwa ne neman ka sai kuma mu ka bugi gurbi muka samu labarin cewar kun bar garin, shine na sanya aka bincika mun sai ake sanar dani cewa kana Jahar Yobe. Malam idan ba damuwa wata alfarma na zo nema a wajen ka dan Allah ka yi ha?uri ka saurare ni ka kuma duba girman Allah ka mun wannan alfarmar".

Justice Kabir ya faWa yana Sunkuyar da kan shi ?asa,shi kam Malam Kabiru shiru yayi bai tanka ba sai dai zuciyar shi kuma da yaji tana buga mishi da sauri da sauri kamar zata fito waje.

Jin Malam Kabiru Win yayi shiru ne ya sanya Justice Kabir ya cigaba da magana inda ya bu?aci a mishi iso cikin gidan domin maganar da zai faWa Win yana bu?atar ace duk wani makusancin Amrah yana wajen.

Da farko Malam Kabiru bai amince ba amma kuma jin sunan da Justice Kabir Win ya ambata na Amrah ya sanya ya musu iso cikin gidan.

A tsakar gida suka zauna inda Gwaggo Sa'adatu ta shimfiWa musu tabarma sannan ta sake kawo musu ruwa a ?aton kofi da abinci a kwano.

Sosai Justice Kabir ya ji daWin irin karamcin mutanen duk da sun kasance basu da wani arziki amma akwai wadatar zuci,gashi dai basu san su ba amma kalla yadda suka karramma su.

Usman ne suka shigo cikin gidan dashi da Umar da matayen su da alama Malam Kabiru ne ya ?ira su,waje suka nema suka zauna sannan suka gaishe da su Justice Kabir Win.

Sai da suka gama gaisawa sannan Malam Kabiru ya dubi su Justice Kabir yace.

"Bayin Allah muna jin ku mai yake tafe da ku?".

Shi kam Justice Kabir tun da ya ga yadda ?an uwan Amrah Win suka taru sai gaba Waya yaji wani tsoro haWe da fargaba sun rufe shi har yaji ya rasa ?warin gwaiwar da zai fara sanar da su abin da yake tafe dasu Win.

Da ?yar dai ganin duk sun zuba mishi ido ya sanya shi buWe baki sannan ya fara magana inda ya shiga sanar da su abin da yake tafe da su.


*****

Daga Farida har iyayen ta kuka su ke sharSa sakamakon labarin da Anwar Win ya sanar da su na Amrah duk da daman sun riga sun san labarin a gidan Rediyo.

Daman tuntuni mahaifin Farida ya yiwa Anwar iso har cikin gidan saboda tun lokacin da Anwar ya ?ira shi da wani suna jikin shi ya bashi cewar lokacin daina kukan shi ya iso.

Kallon Anwar mahaifin Farida ya yi da idanun shi da suka yi jawur sannan yace.

"Yanzu a ina kake ganin zan haWu da mahaifin Amrah?".

Shiru Anwar yayi na Wan lokaci kafin daga bisani ya ce.

"Eh to a gaskiya yanzu sun bar garin Giwa sai dai na samu labarin cewar suna jahar Yobe a wani gari wai Potiskum, sannan na samu labarin hakan ne ta wajen abokina Umar wanda har gobe muna tare sannan duk wani hali da su ke ciki ina samun labarin hakan ta wajen shi".

"Idan ba damuwa ina son gobe ku shirya zamu tafi Yobe, idan har kai Anwar kana da wani uzuri to zaka iya tafiya amma mu dai gobe zamu tafi zamu yi sammako".

Cewar mahaifin Farida Win yana kawar da kan shi gefe sakamakon yadda yake jin zuciyar shi tana mishi zafi.

"Ai ba wani uzuri Dad in sha Allah gobe dani za'a yi wannan tafiyar Ubangiji Allah ya kaimu kawai da rai da lafiya"

Da Ameen suka amsa gaba Waya kafin Anwar ya mi?e tare da mu su sallama zai tafi.

A hankali ya saci kallon gefen da Farida take inda take suka haWa ido ita ma shi take kallo.


Follow my Whattpad account @shamsiyyamanga,
Arewa books @ shamsiyyamanga
Whatsapp number
07060943991
Phone number
09065779330.
Don't forget to share and comment pls.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_=؀? &?).

_Tsarawa/Rubutawa_

*? SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._

*Free book*

------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*36-37*
_______________________________

Tiryan-tiryan Justice Kabir ya shiga bawa su Malam Kabiru labarin duk wani abu da ya faru da Amrah kamar yadda Amira ta sanar da su ba bu wani abu da ya Soye musu,sai dai bisa mamakin shi a maimakon yaga tashin hankali ko Sacin rai a tattare da ahalin Amrah Win sai ya ga saSanin haka domin kuwa kaf Win su ba wanda ya nuna alamar damuwa a tatare dashi sai yaga alamar ma kamar labarin bai zama sabo a gare su ba.

Wani murmushi irin na dattako Malam Kabiru ya sake kafin kuma ya Waga hannu sama tare da furta.

"Alhamdulillahi Ubangiji Allah na gode daka nuna mun zuwan wannan ranar dana daWe ina tsunamayi Allah na gode ma daka bani ikon ganin wannan ranar ba tare da na koma gareka ba, dukkan godiya ta tabbata ga Ubangiji da ya tsamo gaskiya ya bayyana ta a idon duniya a lokacin da idon mutane ya rufe da ganin gaskiya!, A lokacin da mutane suka sanya ?afa suna ganin gaskiya suka take ta. Amrah ina ma kina duniya kiga wannan ranar!, Amrah Ubangiji Allah ya miki Rahama duk da cewar jikina yana bani kina cikin rahamar Ubangiji".

Magana Malam Kabiru ya kasa cigaba da yi sakamakon zuciyar shi da ya ji tana mishi zafi,wasu hawaye ne masu zafi suka shiga ?o?arin zubo mishi sai dai tunin ya sanya hannu yayi saurin goge wa.

Ita kuwa Gwaggo Sa'adatu duk yadda ta daure sai da abin ya gagare ta bata san sanda ta fashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login