Showing 57001 words to 60000 words out of 70370 words

Chapter 20 - FANSAR FATALWA complete hausa novel

26 Oct 2025

116

ya tsari Gatari da saran shuka.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine kawai abun da na iya faWa domin kuwa a lokacin in da wani ne yace mun Anwar zai aikata haka a Amrah wallahi ?arya tawa zan yi amma da idona da kunne na ji, ya Subhannallah.

A ranar na yi kuka sosai irin kukan da rabon da na yi shi tun bayan mutuwar Amrah,na ji na tsani ?awance fiye da tunanin mutum,na tsani Afrah fiye da yadda na tsani Azrah da Anisa domin kuwa Afrah ita ce silar komai.

A kwana a tashi har magana ta yi nisa tsakanin Anwar da Afrah inda cikin lokaci ?an?ani aka tsaida ranar biki, sai dai a ranar da za'a Waura mu su aure komai ya lalace domin kuwa a ranar Amrah ta kashe Afrah.


Follow my Whattpad account @shamsiyamanga Arewa books @Shamsiyyamanga
Whatsapp number
07060943991
Phone number
09065779330.
Comment
Share fisabillillahi.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ =؀? &?).

*Tsarawa/Rubutawa*

? *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

-----------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*029*
____________________________

Shiru Amira ta yi tare da Sunkuyar da kan ta ?asa wasu hawaye masu Wumi ne suka shiga zubo mata tana jin zuciyarta kamar zata faso ?irjin ta ta fito,ji take kamar a yanzu komai yake faruwa bada labarin da ta yi ya fame mata ciwon da bai gama warkewa ba a cikin zuciyarta,da ?yar ta Wago fuska sannan ta dubi mutanen cikin police station Win wanda sun kasa furta komai.

"Wannan shine a ta?aice abin da ya faru da rayuwar Amrah domin kuwa akwai abubuwa da yawa waWanda bayyana su ma bashi da amfani,rashin faWar su shi yafi alkhairi, idan har nace zan farke komai to zan jawa su Azrah ba?in cikin da kaf ahalin su sai ya shafa,duk da cewa a yanzun ma nasan zuciyoyin mutanen wajen nan sun cika da tsanar su. Tabbas! Amrah ta lashi takwabin Waukar Fansa tare da ?udurin hakan a ranta,kuma gashi kamar yadda ta ?udurta sai da ta aikata Win shi daman idan zaka gina ramin mugunta to ka gina shi gajere wata?ila baka sani ba ko kai zaka afka cikin sa. Su Azrah sun yi tunanin zasu tarwatsa rayuwar Amrah su zauna lafiya basu san cewa kwanakin mutuwar su suka janyo ba, Allah Ubangijin ya ji ?an ki Amrah ya sa kin huta ya kyautata makwancin ki,ya miki sakayya tsakanin ki da azzaluman da suka ruguza rayuwar ki".

Amira ta faWa tana fashewa da wani irin kuka mai sauti.

Tun da Amira ta dasa aya baka jin sautin komai a cikin police station Win sai sau?ar ajiyar zuciyoyin mutane,kowa ka kalla a cikin wajen idanun shi ya sanja launi daga fari zuwa ja, Inspector Rasheed ne yayi ?arfin halin fara magana.

"Tabbas idan nace an zalunci wannan yarinyar ban yi ?arya ba,Tabbas waWannan yaran sun zalunce ta zalunta mafi muni,kuma ban ga laifin Amrah da ta Wauki Fansa da kan ta ba domin kuwa yau idan da bata Wauki Fansa ba da ba wanda zai tsaya mata a cikin ?asar nan wajen bi mata ha??in ta duba da yadda ?asar ta mu ta lalace ta zama komai sai Wan wane da wane,kuma wanann hukuncin da ta musu shine dai-dai da su duk da ma ni hukuncin ya mun kaWan amma ba komai Ubangiji Allah zai bi mata ha??in ta kuma zai saka mata,dan haka wannan ya zama izinah ga masu mummunar zuciya irin ta su Azrah masu kuma sha'awar aikata irin abin da waWannan ?anmata suka aikata suma zasu shiga hankalin su,sai dai abin da na kasa fahimta shine ya aka yi Anwar ya warke har ya zo ya fara soyayya da Afrah duk irin wannan soyayyar da yake nunawa Amrah Win".

"Wallahi Inspector Rasheed wannan tambayar sai dai shi Anwar Win ya bamu amsar ta da kan shi domin kuwa ni kaina ban san ta yadda aka yi wannan lamarin ya faru ba,Anwar sai ka sanar da mu yadda abu ya faru".

Amira ta faWa tana kai duban ta inda Anwar yake zaune wanda tun da ta gama bada labarin har zuwa yanzu ya kasa Wago ido ya kalle ta.

?ago kan shi yayi a hankali sannan ya dubi mutanen da suke wajen kafin kuma yayi saurin kawar da kan shi gefe sannan ya fara magana.

"Amira wallahi nasan duk wani bayani da zan muku ba lalle ku fuskance ni ba duk da ni nasan cewar ban ci amanar Amrah ba kamar yadda ki ke mun kallo. Watau abin da ya faru shine bayan na tashi daga doguwar jinyar da na shafe watanni ina yin ta,domin kuwa lokacin da naji labarin mutuwar Amrah ba wanda ya sa ran zan sake ?ara kwana guda a doron ?asa saboda yadda na birkice ikon Allah ne kawai ya tashi kafaWuna,amma an sha jinya jinya mai suna jinya. Wata rana muna zaune da Mahaifiyata falon mu sai muka ji Sallamar wasu ?an mata har suka shigo cikin falon suka zauna ban kalle su ba,waje Mahaifiyata ta nuna musu suka zauna abin da na lura shine kamar mahaifiyar tawa ta san su domin kuwa cikin sakin fuska suka shiga gaisawa har naji tana tambayar su ya karatu, sannan naga ta tashi ta nufi kitchen ta kawo musu abinci da abin sha haka dai ta shiga nan da nan da su har a wannan lokacin idona a rufe yake ban buWe ba balle nasan su waye, domin ni haka kawai tun bayan mutuwar Amrah na ji duk wata mace ta fice mun a rai idan ka cire mahaifiyata,kamar a cikin bacci na ji sau?ar Muryar Afrah a dodon kunnena tana gaishe ni.

"Anwar Barka da gida ina yini,ya kuma ?arfin jiki?".

Ban buWe idona ba na amsa ciki-ciki sannan su ma sauran ?awayen nata suka shiga gaishe ni,ni dai ban san adadin lokacin da suka Wauka ba a gidan suka tafi domin kuwa tashi na yi na shige cikin Waki na bar su a wajen.

Bayan kwana biyu da zuwan su Afrah gidan mu kawai sai ga Mahaifiyata ta same ni da wani zance wanda yayi matu?ar tayar mun da hankali shine wai tana so na auri Afrah,da farko dariya na yi wadda rabona da yin ta tun bayan mutuwar Amrah sannan na dube ta nace.

"Haba dai mama amma dai wasa ki ke ko?".

Kallo na ta yi sannan ta ce.

"Ba wasa nake ba Anwar idan kuma kana tsammanin wasa nake to ka kalli cikin idanuna zaka faskara gaskiyar abin da nake nufi Win".

Nan fa na zaro ido waje sannan na fara ?o?arin son naga na fuskantar da Mahaifiyata illar abin da take son sani na aikata Win,amma fir Mahaifiyata ta rufe ido ta shafawa idon ta toka tace ta ci alwashin tare da rantsuwa a kan sai na auri Afrah idan kuma har naga ban auri Afrah ba to Wayan biyu ne ko dai bani da rai ko kuma ita Afrah Win bata da rai wannan shine kaWai abin da zai hana a aura mun ita tun da gawa bata auren gawa. Jin wannan kalaman na mahaifiyata ba ?aramin tashi hankali na yayi ba domin kuwa nasan halin ta sarai idan har ta furta abu to ba wanda ya isa ya sanja mata ra'ayi.

Ita kuwa Afrah har makarantar su naje na same ta na buga mata warning a kan idan har ta kuskura ta yarda da wannan auren to wallahi ta kuka da kan ta. Sai dai rashin sani yafi dare duhu idan da nasan abin da hakan zai janyo da ban fara zuwa na tunkari Afrah da wannan maganar ba domin kuwa ina gama buga mata warning Win ta ?ira mahaifiyata ta kwashe komai ta faWa mata cikin kuka sannan ta ce ta fasa auren nawa kawai zata ha?ura dani,sosai ran Mahaifiyata ya Saci inda ina dawowa gida ta ce mun wallahi duk ranar da na kuskura na ?ara sanya Afrah kuka ko na Sata mata rai Allah ya isa tsakani na da ita bata yafe ba sannan kuma tana so a yanzu na koma na bawa Afrah ha?uri kuma in shirya nan da sati biyu za'a Waura mana aure. Innalillahi wa'innailaihi rajiun tashin hankali wanda ba'a sa ma sa rana a ranar na yi kuka kamar raina zai fita na ji kamar na mutu nima na bi Amrah ko na huta a raina,gashi a rayuwa ta ni irin mutanen nan ne masu gudun Sacin ran iyayen su,haka na juya na je na bawa Afrah ha?uri sannan kuma tun daga wannan ranar na shiga nuna wa Afrah cewar ina son ta alhali kuma ?asan zuciyata ba haka bane ba kawai ba yadda na iya ne shiyasa na kuma bi umarnin Mahaifiyata.

Tun da Afrah ta samu wannan damar a wajena shikennan ta fara ?o?arin ganin ta ?ara cusa mun tsanar Amrah ganin cewa har zuwa wannan lokacin ban yadda da abin da aka ce Amrah Win ta aikata ba,sai dai zuwa wani lokaci Afrah ta yi nasarar sanya wa zuciyata yarda da abin da aka ce Amrah Win ta yi duk da kuwa cewar wani sashi na zuciyar tawa yana ?aryata yana kuma ?ara tuno mun da kyawawan halayen Amrah. A wani Sangaren kuma shine Kullum idan na kwanta bacci sai Amrah ta zo mun tana kuka wanda a da ban fahimci dalilin bayannar ta ta a mafarkin nawa ba sai a yanzu na gane ashe wannan kukan da nake ga tana yi Win duk dan ta na so ta nuna mun cewar an zulunce ta ne. A ta?aice dai har an sanya aure na da Afrah kuma sai gashi saboda ba Alkhairi a cikin sa Allah ya kawo ?arshen abin".

Tun da Anwar ya gama bada wannan labarin ?ananan maganganu suka shiga tashi a cikin police station Win kowa da abin da yake faWa wasu suna ganin laifin Anwar Win in da wasu kuma su ke ganin laifin mahaifiyar wadda nima na shiga sahun ma su ganin laifin mahaifiyar ta shi.

A Sangaren Justice Kabir kuwa kuka sosai ya ke kamar wani ?aramin yaro tare da Allah wadai Win mummunar Wabi'ar da ya gina ?ar ta shi a kai,Tabbas ya san cewar ?a?a amana ce da Allah ya bamu kuma kowane bawa sai Allah ya tambaye shi akan amanar da ya bashi Win,yanzu shi da wana ido zai tsaya a gaban Ubangiji ya kare kan shi akan abin da Azrah Win ta aikata ya san tana da laifi amma shima yana da kaso talatin cikin Wari na kamashon abin da ta aikata Win,yayi danasani ba adadi wadda zamu iya ?iran ta danasani a ?urarren lokaci kuma marar amfani.

Haka suma iyayen su Afrah kowa ka kalla fuskar shi tsantsar nadama ne da kuma danasanin abin da ?a?an na su suka aikata.

Ganin hankalin kowa baya jikin shi ga kuma yadda jikin mutane da yawa yayi sanyi ya sanya Inspector Rasheed ya bada umarnin kowa zai iya tafiya.

Hakan kuwa aka yi inda suma ?an jarida suka kwashi kayan aikin su su ka ?ara gaba,itama Amira Inspector Rasheed ne ya mai da ta gida sannan yace dan Allah idan ba damuwa gobe zai zo akwai abin da yake so zasu ?ara tattaunawa.

Shi kuwa Justice Kabir yana komawa gida ya fara shiri inda ya shirya zai je garin Giwa domin ya binciki inda iyayen Amrah su ke don nemawa ?ar shi yafiya daga gare su.

A ranar gidan telebijin da radiyo duk idan ka kunna ba abin da zaka ji sai Muryar Amira tana ba da labari da duk wani mai imani idan ya saurara sai jikin shi yayi sanyi.


*GARIN GIWA*

Samari ne sun fi ashirin zaune a teburin mai sai da shayi,wasu suna cikin rumfar wasu suna ta waje, wata ?atuwar Radio ce ajiye a tsakiyar su gaba Waya hankalin su ya tafi kan Muryar da ake saurara a gidan radiyo Win watau Muryar Amira da take bada labari a kan Amrah,duk wanda ka kalli fuskar shi a wannan lokacin ba abin da zaka gani face tsantsar damuwa da danasani ga wani gumi kuma da yake zubowa daga fuskokin wasu daga cikin mutanen wajen.

Malam ?alha kuwa da yake zaune a gefe tunin hawaye sun gama wanke mishi fuskar shi sakamakon tunowa da abin da ya yiwa abokin na shi,gashi a halin yanzu bai san a wace duniyar abokin na shi yake ba gaskiya bai kyauta ba sannan bai cika aboki na gari ba da har ya bari zuciya ta yi tasari a kan shi ya manta da waye Malam Kabiru da kuma ahalin shi.

Har aka gama jin labaran ba wanda ya iya motsawa daga inda yake sai can dai da ?yar wasu tsiraru daga cikin matasan wajen suka fara tashi Waya bayan Waya suna barin rumfar mai shayin cikin matsananciyar kunya ga kuma gwaiwowin su da suka daWe da yin sanyi.

Shi kuwa Malam ?alha har aka gama barin wajen aka bar shi ya kasa tashi domin kuwa kaf mutanen wajen sun watse sun bar shi a zaune a wajen kamar an dasa shi, shi kan shi mai shayin a ranar ha?ura yayi da sana'ar shayin na shi tun da ba masu siya.

Da ?yar dai Malam ?alha ya iya tashi gwaiwa duk ta gama sakewa sannan ya rarrafa ya shiga gida.


Follow my Whattpad account @shamsiyamanga, Arewa books @shamsiyyamanga
Whatsapp number
07060943991
Phone call
09065779330
Don't forget to share and comment pls.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ =؀? &?).

_Tsarawa/Rubutawa_

*? SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION*

Kai jama'a Bari nima na Wana yin wa?e =؃?=؃?=??. Rayuwa da masoyi a duniya babbar nasara ce ?an uwa=؃?=؃?>????r?>?s?=؃?. Tabbas naga ruwan ?auna sanadiyyar wannan jinyar da nayi =???>?r?=?#?. Jama'a ku bani tissue,wallahi some prayers sai da suka sanyani hawaye=???>?r? . I received a lots of messages from different places and different people,wasu mun yi magana via phones call, wasu sun tura mun message ta Whatsapp wasu ta direct message duk ana tambayar littafin FANSAR FATALWA:&?=??. Ni kaina ban san haka littafin ya karSu a gare ku ba sai da na yi kwana biyu ban yi posting ba,and hakan ya faru ne sakamakon jinyar da na yi ciwon ido mura da kuma zazzaSi>?y?>?r?.To Alhamdulillahi I'm getting much better and better know and Finally I'm back :&? =؃?=؃?>?s?>?s?in sha Allah na dawo zamu Waura daga inda muka tsaya godiya buhu-buhu gare ku masu yi mun addu'a wanda na sani da wanda ban sani ba,na fili da na Soye Musamman ma ?an group Wina na FANSAR FATALWA u people Ina son ku fisabillillahi because kun nuna mun zunzurutun ?auna wadda masoyan gaskiya ne kawai su ke nunawa ta hanyar yi mun addu'oi>?p?=? ?=??Lots of Love to u guys really appreciate ur concerned towards me>?s?>?s?>?s?. Yanzu dai jiki Alhamdulillahi amma ku yi ha?uri saboda ba lalle na dinga yin dogon
typing ba saboda idona an hanani kallon haske sosai,amma dai zamu lallaSa a haka in sha Allah =??>?p?=? ?.

*SADAUKARWA* : _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk in da ku ke ina son ku fisabillillahi._

*Free book*

-----------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*030*
________________________________

Kamar yadda Justice Kabir ya faWa washe gari kuwa sassafe ya buga sammako inda ?arfe bakwai a garin Giwa ta mishi sai dai ya bugi gurbi domin kuwa lokacin da ya isa garin yake samun labarin cewar ai iyayen Amrah Win sun daWe da barin garin.

Wannan labari da Justice Kabir Win ya tarar ba ?aramin Waga mishi hankali yayi ba domin bai taSa kawowa a ran shi cewar labarin da zai tarar Win ba kennnan.

Haka Justice Kabir Win ya kama hanyar komawa cikin Zaria zuciyar shi duk ba daWi,sai dai kafin ya bar garin ya bu?aci a taimaka mishi da hoton Malam Kabiru Win domin kuwa ya ?uduri niyyar sai ya nemo inda su ke a faWin duniya domin ya nemarwa ?ar shi yafiya ko hakan zai sa ta samu sa'ida da salama a cikin ?abarin ta.

Bayan ya isa gida zama yayi a cikin falon shi tare da ri?e kan shi lokaci guda ya fara tunanin hanyar da zai bi domin neman inda Malam Kabiru Win yake, mi?ewa tsaye yayi sannan ya fara zagaye cikin Wakin yana nazarin hanyar bi.

Ya Wauki tsawon lokaci yana kaiwa da komowa a cikin falon gidan nashi domin neman mafita kafin cikin ikon Allah wata zuciyar ta bashi shawarar kawai ya je gidan radiyo ya bayar da sanarwa sannan ya yi Albishirin tukwaici mai tsoka ga duk wanda ya gano inda Malam Kabiru da iyalin na shi su ke. Da wannan shawarar ya yi na'am sannan ya Wauki hoton Malam Kabiru Win ya Wauka a wayar shi tare da ?iran wani layi ya sanar da mai layin abin da yake bu?ata kafin kuma ya juya y???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a nufi hanyar barin falon domin zuwa gidan Radiyo Win.

Tafe yake a cikin motar shi duk tunanin duniya ya ishe shi dai-dai ya iso wajen danger ne aka tsayar da motar ta shi. Ganin cewa da goslow da yawa a gaban shi ya sanya shi kashe motar sannan ya kifa kan shi da sitiyarin motar.

Har aka fara bayar da hannu motoci suka fara wucewa Justice Kabir bai san ana yi ba,nan fa motocin bayan shi suka shiga zabga mishi horn wasu cikin Sacin rai har sun fara fitowa daga cikin motocin su domin a tunanin su irin rainin hankali ne kawai irin na wasu masu motar.

"Bawan Allah idan ba tafiya zaka yi ba ka kauce ka bamu hanya mu wuce?, Haba tun Wazu ka kasa gaba ka kasa baya ka tsaya mana a kan titi!".

Muryar da Justice Kabir ya ji ta daki dodon kunnen shi ne ta sanya shi saurin Wago wa tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login