Showing 39001 words to 42000 words out of 70370 words

Chapter 14 - FANSAR FATALWA complete hausa novel

26 Oct 2025

114

baiwar Allah tana zaune a gefe kamar wata mutum-mutumi kamar an dasata.

Hayaniyar da ma?otan Wakin su Afrah suka jini ya sanya su saurin fitowa tare da nufar Wakin nasu, sannan aka shiga tsakanin su aka raba su, amma fa kowa sai da taji a jikin ta,duk sun haWawa kan su jini da majina kowa ka kalla sai huci yake suna aikawa junan su harara.

Haka dai aka samu aka ja su Khadijah aka fitar da su daga cikin Wakin sai aikawa su Afrah da zagi suke ta uwa ta uba.

Su Khadijah wasu clique ne a class Win su Afrah waWanda basu da ma?iya sama da su Amrah ba dan komai ba sai dan yadda su Afrah suka fi su ja a cikin class Win wannan dalilin ya sanya suka tsane su musamman Amrah da kowa yake son ta a cikin makarantar daga malamai har Walibai burin kowa shine yayi mu'amala da Amrah saboda ?o?arin ta da kuma kewawan halayen ta,sunan clique Win su Khadijah shine IRON LADIES ko Zafafa shida. A lokacin da clique Win su Khadijah suka samu labarin abun da ya faru da Amrah sai da suka Wauki videon suka ?ara reposting a Instagram da Twitter sannan suka dinga jin kamar su zuba ruwa a ?asa su sha.

*****

Allah Sarki a Sangaren Anwar kuwa bai san abin da yake faruwa ba kasancewar shi ba ma'abocin hawa social media sosai ba, domin kuwa shi Whatsapp ma kawai yafi yi Whatsapp Win ma ba wani sosai ba. Hakan ya sanya ko Amrah bai barta ta buWe shafuka a social media ba iya Whatsapp itama ya amince mata take yi. Kuma daman itan ma ba wata ma'abociyar son chatting Win bane sosai ba, yawanci idan ka ganta a Whatsapp to group Win class Win su ta shiga ko kuma irin suna da online class Win nan haka, ko kuma Anwar ya ce ta hau su yi video call.

Kwance yake a cikin Wakin shi yana danne-danne a cikin Computer Win shi, akwai research Win da yake yi.

Bugo ?ofar Wakin nashi da aka yi aka shiga da ?arfi ne ya sanya shi saurin Wago kai ya kalli wana mai Wanyen kan ne haka.

?anin shi ya gani tsaye mai suna Nazir yana ri?e da waya jikin shi sai rawa yake.

Kallo Waya zaka mishi ka fahimci tsantsar tashin hankalin da yake ciki sannan ka gane cewa akwai wani babban al'amari da ya Waga mishi hankali

"Subhannallah Nazir lafiya kuwa?".

Anwar ya faWa yana mi?ewa tsaye tare da rufe Computer Win sannan ya sa??o daga kan gadon.

A dai-dai wannan lokacin kuma mahaifiyar shi itama ta faWo cikin Wakin kamar an jeho ta.

"Ina kuwa lafiya, Anwar kai daman ashe karuwa kake shirin auro mana ka kawo mana ita cikin gidan nan bamu sani ba?".

Da sauri Anwar ya dubi mahaifiyar tashi cike da mamakin maganar tata sannan yace.

"Mama bangane karuwa ba!, wacece karuwa Win?".

"Eh dole kace haka mana tun da an mana rufa-rufa ana ?o?arin ?a?aba mana karuwa a cikin zuri'a, to wallahi anyi wal?iya mun gano halin kowa munafukai kawai, in dai ina numfashi a doron ?asa wallahi ba zaka taSa auren wannan tsinnanniyar yarinyar ba,karuwa wadda ta gama tallatawa duniya jikin ta, kai ko bayan raina ne ban amince daka auri wannan yarinyar ba".

Wani irin sarawa Anwar yaji kan shi yayi lokaci guda ya dafe kan sannan ya fara takawa a hankali ya ?arasa wajen mahaifiyar tashi sannan ya dube ta yace.

"Mama wallahi kin sanyani a duhu, gaba Waya maganganun ki sun kulle mun kai, Mama dan Allah ku fitar dani haske".

Kallon shi sama da ?asa mahaifiyar tashi tayi irin kallon ka raina mun hankali ma tukunna tare da jan tsaki sannan tace.

"Kai Anwar ka kalleni da kyau shekaruna hamsin a duniya dan haka,kar kayi ?o?arin wasa da tunani na ka nuna mun cewar baka san abun da yake faruwa ba,to ni dai na faWa maka wallahi ba Amrah ba ko uwar ta ce, kai zuri'ar su Amrah ma baka isa ka nemi aure a cikin ta ba, shima uban nata ashe munafuki ne kwanta-kwanta ya yiwa mutane ya sanya ake masa kallon allaramma har yake jagorantar mutane ashe munafuki ne, to wallahi Allah ya tona musu asiri, kuma kuWin mu da suka ci wallahi biyar ba zamu bar musu ba sai sun biya komai ko na maka su a kotu"

Tana kaiwa nan a zancen ta ta fice a cikin Wakin tare da banko ?ofar kamar zata karyata,ta bar Anwar a tsaye cike da al'ajabin wannan ba?on lamari.

Bayan fitar mahaifiyar ta su daga cikin Wakin daga Anwar har ?anin nashi rasa wanda zai yi magana aka yi, sun Wauki tsawon lokaci a haka kafin dai Anwar ya tattaro duk wani ?arfin hali da ya rage mishi sannan ya taka a hankali har ya ?arasa gaban Nazir sannan ya fara magana cikin sanyin murya.

"Nazir ka mun bayani mai yake faruwa?, Jikina ya riga da ya gama bani cewar ba lafiya ba".

Wayar hannun shi kawai Nazir ya mi?awa Anwar bayan yayi playing videon Amrah Win yana jin zuciyar shi kamar zata fito waje dan yadda yaji ya tsani Amrah Win.

A lokacin da idanuwan Anwar suka sau?a akan videon Win kallo Waya ya yiwa videon ya Wauke kan shi tare da furta.

"Auzubillahi minna shaiWannir rajim"

Ya faWa ba tare da ya lura da fuskar wacece a jikin videon ba, har ya buWi baki zai ce wani abu sai kuma maganganun mahaifiyar shi suka shiga mishi yawo a kunnuwa.

" _Ina kuwa lafiya Anwar kai daman ashe karuwa kake ?o?arin auro mana ka kawo mana cikin_ _zuri'aaaaaa. Eh dole kace haka mana tun da an mana rufa-rufa ana_ _?o?arin ?a?aba mana karuwa a cikin zuri'a,_".

Haka Anwar ya dinga jin Kalmar Karuwa tana masa yawo a cikin kunnuwa. Lokaci guda yayi saurin zubura tare da ?ara kai duban shi a kan wannan videon a karo na biyu.

Wani irin sarawa kan Anwar yayi a lokaci guda tare da jin wata irin hajijiya tana ?o?arin kayar dashi, ga wani irin gumi da ya shigar karyo mishi tun daga tafin ?afa har tsakar kan shi.

Nazir bai yi auni ba sai ganin Anwar yayi ya zube yashe a ?asa ko ?wa?waran motsi bai yi ba.

Da gudu Nazir ya nufi kan shi yana ?iran sunan shi amma shiru, nan fa ya ruga waje da gudu yana ?walawa mahaifiyar shi ?ira cikin tsananin ruWani da tashin hankali.


*****
*GARIN GIWA*

Ba wanda ya san abun da yake faruwa da Amrah Win a can gidan nasu, sai dai kafin wani lokaci wasu daga cikin tsirarun ?an garin sun fara cin karo da videon inda kan kace kwabo har video ya fara yawo a cikin garin tunin rabin ?an garin sun samu ganin wannan videon rashin kunyar na Amrah domin kuwa har waWanda basu da waya ma sai da suka ga videon wannan nunawa wannan wannan nunawa wancan haka aka rin?a fasin-fasin da videon inda magana ta shiga tashi a cikin garin irin ?ananan maganar nan,da yawa take suka shiga yin Allah wadai da wannan halin da Amrah Win ta Wakko,inda wasu kuma suka shiga yin Allah ya ?ara daman ai shi Malam Kabiru laifin shine ba ya dage sai ?ar shi tayi karatu ba,to ai ga irin ta nan tun ba a je ko ina ba ta janyo mishi abun kunya. Wasu kuma cewa suka yi daman kwaWayin abun duniya ne da kuma son duniya ya sanya shi har ya kai ?ar shi makaranta wata uwa duniya, cikin waWanda suke waWannan maganganun hadda manyan abokanan Malam Kabiru Win,waWanda lokacin da suka samu labarin cewar Malam Kabiru zai tura ?ar shi karatu jami'a sun same shi sun bashi shawara akan kar ya kaita Win inda suka nuna mishi illar hakan amma sai baiyi amfani da shawarar ta su ba,abun da ba a fiye yi a garin ba shine a kai yarinya makarantar gaba da secondary, yawancin yara daga secondary school an musu aure.

Da yawa daga cikin masu maganar sun fi ganin laifin Malam Kabiru akan laifin Amrah domin kuwa cewa suke da ace bai kai Amrah Win makarantar ba da duk haka bata faru ba, sai dai bakin al?alami ya riga da ya bushe ?addara ta riga fata!.

Haka dai kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa kan kace mai duk wani alkhairin Malam Kabiru ya disashe a idon mutane inda aka shiga jifan shi da munanan maganganu saSanin da da duk wanda zai buWi baki ya faWi magana a kan Malam Kabiru Win to alkhairi ne zai biyo ba, daga shi har iyalan shi ba wanda yake da wani mummunan aibu a idon mutane, amma gashi yau an wayi gari mutane sun buWawa idon su toka sun manta da waye Malam Kabiru a wajen mutanen garin dalilin abun kunyar da aka ci karo dashi na ?ar shi.


Hmmmm Wan Adam Kennan!.


*MANGA*
'?
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*!
( _Horror Story_=؀? &?).

_Tsarawa/Rubutawa_

*? SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

----------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*021*
______________________________

Malam Kabiru ne ya fito daga cikin rumfar ?ofar Wakin nashi,sanye yake cikin babbar riga wanda kana gani shi ka san mutum ne mai cike da dattako da kamala.

Buta ya Wauka a wajen randa inda ya nufi bayi domin kama ruwa kasancewar lokacin sallahr Azhar ya ?arato.

Bayan ya fito daga bayin ne ya tarar da Gwaggo Sa'adatu tsaye a bakin rumfa tana jiran shi hannun ta ri?e da asuwaki, tana ganin fitowar tashi tayi saurin ?arasawa ta karSi butar hannun shi sannan ta kai mishi wajen alawla sai da ta mi?a mishi asuwakin ya fara yi domin kuwa hakan yana daga cikin al'adar shi in dai zai alawla to sai yayi asuwaki haka bayan ya kammalla ma.

?an rusunawa Gwaggo Sa'adatu tayi Win kafin daga bisani tace.

"Malam dan Allah ko zan iya cewa wani abu?".

Zama Malam Kabiru yayi akan dutsen da yake alawlar kafin ya dube ta yace.

"To Shikennan kiyi maganar ki Allah dai ya sa ba doguwar magana bace ba".

"Malam yau Win ne naga kamar wani abu yana Wan damun ka?, Allah dai yasa lafiya".

Dogon numfashi Malam Kabiru Win ya ja sannan yace.

"Bakomai, amma idan na dawo daga massallaci zamu yi magana".

Ya faWa sannan ya cigaba da yin asuwakin.

Bayan ya kammalla asuwakin ne ya fara gabatar da alawlar cikin nutsuwa ya idar da alawlar sannan ya yi addu'ar bayan idar da alawla tare da Waga hannun sama yayi addu'a sannan ya tashi tare da duban Gwaggo Sa'adatu yace.

"To ni zan fita sai kuma Allah yayi dawowar mu".

"To Shikennan Malam a dawo lafiya".

Sa kai yayi tare da ficewa a cikin gidan sai dai mai yana fita ya ji massallacin da yake jan su Sallah har an fara ?iran sallar, ko kaWan malam Kabiru bai kawo komai a ranshi ba ya cigaba da nufar masallacin a tunanin shi yayi lattin fitowa ne shiyasa wani ya karSi limancin duk kuwa da cewar wannan shine karo na farko da hakan ta taSa faruwa.

Sai dai mai! Tun daga lokacin da ya fito daga cikin gidan nashi ya lura da cewar duk indai ya wuce majalisar mutane sai ya ga ana nuna shi ana ?an maganganu ta ?asa-?asa. ?arin wani abun mamakin ma shine duk inda ya wuce ya musu sallama sai ya ga ana Wauke kai ana sunkuyar da kai ?asa, saSanin da da idan ya nufo majalisar mutane ma tun daga nesa za'a fara Waga mishi hannu ana gaisheshi cikin girmamawa.

Kan Malam Kabiru ne ya Waure ganin ba?on al'amarin da yake cin karo da shi Win,haka dai ya daure ya ?arasa cikin massallacin amma zuciyar shi tana raya mishi wani abu yana shirin faruwa.

Wasu mutane ya gani tsaye daga gefen masallacin sun idar da alawla suna jiran a yi ?iran shiga salla su shiga cikin massallacin.

?aya daga cikin mutane aminin Malam Kabiru ne ?ut da ?ut tare suka taso, sannan kuma shine wanda ya ?ira salla a yau Win.

Da sallama Wauke a bakin Malam Kabiru Win ya ?arasa wajen mutanen sannan ya mi?a musu hannu yana cewa.

"Malam ?alha sannun ku dai, da alamu yau nayi lattin fitowa sallar nag......".

Maganar Malam Kabiru Win ce ta katse ganin cewa duk mutanen da suke tsaye a wajen sun yi gaggawar barin wajen sun shige a cikin massallaci an bar shi a tsaye ba tare da kowa ya tanka mishi ba

Sororo Malam Kabiru ya tsaya tare da bin hanyar da suka shige massallacin da kallo yana jin zuciyar tana wata irin harbawa.

Jin alamar tayar da i?ama da limami yake shirin yi ne ya sanya Malam Kabiru jan ?afafuwan shi da suka mishi sanyi ya shiga cikin massallacin.

Sahun da yake gaba ya nufa ya tsaya, sai dai nan fa mutane suka shiga darewa suna matsawa daga gefen Malam Kabiru Win har ya zamana cewar shi kaWai ya rage a sahun.

Duk da cewa abun ya zamar mishi sabon abu kuma abun ya taSa mishi zuciya amma sai ya daure ya tayar da kabbarar sallar kamar yadda ya ji liman ya tayar da kabbarar sallar, a ranshi yana ayyana cewar in dai aka idar da sallar zai tsaya ya tambaya ko wani abu ya musu na Sacin rai wanda bai sani ba sai ya basu ha?uri.

Bayan an idar da sallar sai da Malam Kabiru ya zauna ya yi lazimi kamar yadda ya saba kafin ya shafa addu'ar sannan juyo ya duba gabas da kudu da arewa na massallacin ba kowa sai shi Waya.

A hanyar shi ta komawa gida yaci karo da Malam ?alha ya fito daga shagon wani mutumi hannun shi ri?e da leda alamar abu ya siya.

"Malam ?alha".

Malam Kabiru ya ?ira sunan Malam ?alha Win ganin cewa shiWin ya Wauke kai kamar bai gan shi ba.

Manna mishi Malam ?alha Win yayi tare da cigaba da tafiya kamar bai ji ?iran da Malam Kabiru Win yake mishi ba, hadda Wan ?ara saurin tafiyar tashi.

Ganin cewa Malam ?alha Win bashi da alama ko niyyar tsayawa ya sanya Malam Kabiru ?arasawa da sauri ya sha gaban shi sannan yace.

"Haba Malam ?alha wai mai yake faruwa ne dan Allah?, Idan ma wani abu na aikata muku ai ba haka addinin mu ya koyar da mu ba, sai ku same ni ku sanar dani amma sai wa........".


Saurin dakatar dashi Malam ?alha Win yayi tare da fara magana.

"A haka dai kamar na kirki, ga ka nan kowa ya ganka ya ga dattijon kirki amma kuma sai gashi ka kasa bawa ?ar ka cikakkiyar tarbiya inda har ta aikata abun da ko a ?asar arna haramun ne balle mu musulmai, wai wanda ya kasa kula da tarbiyyar ?ar shi ne ake zaton zai jagoranci al'ummar ta hanyar addini, ai wannan ma ba abun da zai yiwu bane, kayi ?o?ari ka gyara Sarakar da ta Sarke a gidan ka kafin kayi ?o?arin gyara rayuwar wasu.Allah dai ya shirya wallahi, ai an yi wal?iya mun gane halin uban kowa".

Malam ?alha yana kaiwa nan a zancen shi ya ratsa ta gefen Malam Kabiru Win ya wuce ya barshi tsaye cikin kullewar kai kamar an dasashi.

Da ?yar dai ya ja ?afafuwan shi ya nufi hanyar gida zuciyar shi sai sa?a mishi abubuwa iri-iri take ga faWuwar da yaji gaban shi ya tsananta mishi.

Daf da zai shiga gida shine yaji ana ?wala mishi ?ira daga nesa.

"Malam Kabiru, Malam Kabiru".

Juyawa yayi ya kai duban shi zuwa inda mai ?iran nashi yake.

"Malam Kabiru Subhannallah ashe abun da ya faru Kennan, gaskiya ka bamu mamaki wallahi ya kamar kai ace an ci karo da videon tsaraicin ?arka yana yawo a duniya, dan Allah Malam Kabiru a garin yaya ka bari haka ta faru,gashi nan duk gari ya Wauka ko ina maganar ake".

?arasowar Hisham wajen ne cikin tashin hankali ga idanun shi da suka kaWa suka yi jawur kamar wuta alamar cewar baya cikin nutsuwar shi ya sanya wannan mutumin da yake tsaye saurin jan ?an ?afafuwan shi ya bar wajen daman gulma ce tsantsa take cin shi.

Shikam Malam Kabiru tun da wannan mutumin ya fara magana ya nemi duk wata ?ar guntuwar nutsuwar da ta rage mishi ya rasa, maganar duniya Hisham ya mishi amma shiru ba magana gashi ya kasa motswa daga wajen da yake tsaye Win.

Gani??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n hakan da Hisham yayi ne ya sanya shi saurin jan Malam Kabiru Win suka shige cikin gidan.

A tsakar gida suka tarar da Umar da Usman ga Gwaggo Sa'adatu a gefe in banda tsiyayar hawaye ba abun da idanun ta suke yi.

Kujera Hisham ya janyo a gefe sannan ya zaunar da Malam Kabiru Win.

Da sauri Gwaggo Sa'adatu ta ?araso wajen Malam Kabiru Win tare da zube duka gwaiwowin ta a ?asa sannan ta fara magana cikin kuka.

"Malam karka yadda da duk wani abu da ka gani wallahi Malam nasan cewar Amrah ba zata taSa aikata abun da aka ce ba wallahi sharri kawai aka mata,wasu ne suke son suga sun tarwatsa mata rayuwa, Malam kasan wacece Amrah ka kuma san abun da zata yi da wanda ba zata yi ba Malam wallahi ko kaffara ba zan yi ba ba Amrah bace ta aikata wannan abun ba".

Duk maganganun da Gwaggo Sa'adatu take har ta gama Malam Kabiru ko uffan bai ce mata binta kawai yake da kallo,gaba Waya kan shi a kulle yake ya rasa inda maganar tata ma ta dosa.

Saurin ?arasowa inda Gwaggo Sa'adatu Win take dur?ushe Hisham yayi sannan ya Waga ta tsaye tare da fara magana.

"Gwaggo dan Allah ki bar Waga hankalin ki akan abun da Amrah ta aikata ni na tabbatar zata yi nadama sannan idan ta yi hakan ne ma dan ta Sata mana suna wallahi kan ta ta Satawa ni dai kam Hisham na cire Amrah daga cikin ahali na ko a lahira na ganta zan nuna ban santa balle a nan duniya".

Hisham yana kaiwa nan a zancen na shi ya juya cikin tsananin jin tsanar Amrah Win ya fice a cikin gidan.


*****

A can makarantar su Amrah kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login