Showing 45001 words to 48000 words out of 70370 words

Chapter 16 - FANSAR FATALWA complete hausa novel

26 Oct 2025

115

da Anisa da Azra suka ?araso wajen da gudu suna ?o?arin taSa Amrah Win,sai dai wata irin sha?a da na kaiwa wuyan Azra Win shi ya dakatar da ita daga abun da take shirin aikatawa Win.

Cikin wata iriyar murya wadda kamar ba tawa ba na fara magana.

"Na rantse da girman Ubangiji idan har Amrah ta mutu wallahi tallahi sai na kashe ku gaba Waya sai dai nima a kashe ni tsinnannu kawai waWanda suka kwashe kayan su daga gaban ma'aiki,wallahi sai rayuwar ku ta tagayyara domin kuwa tun a nan duniya na tabbatar Allah ba zai bar ku ba dan wallahi sai kun ga sakayya mafi muni".

Duk irin yadda Azra ta so ta ?wace kan ta daga irin sha?ar da na mata abun ya gagara,tsananin tsoro da tashin hankali ne ya bayyana a fuskokin su Afrah da Anisa ganin cewar har Azra Win ta fara fita a hayyacin ta.

Mutanen wajen ne suka shiga kiciniyar ?wace Azra daga hannun nawa amma ina! Duk irin yawan mutanen wajen sun kasa ?wace Azra daga hannuna domin kuwa wani irin ?arfi nayi ba zaka ce mutum bane da wannan ?arfin.

Da ?yar dai aka samu aka ?wace Azra Win a hannun nawa wadda tunin ta daWe da sumewa.

Nima a take kuma na yanki jiki na faWi tare da sumewa a wajen.

Sosai mutanen wajen suka cika da mamakin wannan al'amarin.


*MANGA*
'?
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_=؀? &?).

_Tsarawa/Rubutawa_

*? SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

-------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*023*
________________________________

Ambulance aka samu inda aka sanya Azra da Amira a ciki,in da ana ?o?arin Waukar Amrah matasan makarantar suka ce ai wallahi ba za'a Wauke ta ba gara a barta ta mutu,domin kuwa bata da wani amfani a cikin al'umma.

Nan fa hayaniya ta kware a wajen wasu daga cikin mutanen wajen suna goyon bayan a Wauki Amrah Win a taimaka a kai ta asibitin inda wasu kuwa suka yi tsallen aradu suka ce ba za'a Wauke ta ba. Sai dai kun san an ce majoraty carry the both wannan ya sanya masu i?irarin cewa ba za'a kai Amrah asibitin ba suka rinjayi masu cewa a taimaka mata Win.

Hakan ya sanya duk yadda wasu suka so a taimaka mata amma abun a ci tura gashi suna kallo rayuwar ta tana tsaka-tsaki domin kuwa a wannan halin da ake ciki ma basu sani ba shin Amrah Win tana da rai ko kuma ta mutu ne.

Hayaniyar da malaman da suke cikin Conference Hall Win suka ji tayi yawa ne ya sanya su fitowa da sauri dan ganin mai yake faruwa.

Ganin Amrah suka yi a yashe a ?asa ba alamar numfashi a tare da ita,ga matasan makarantar kuma sun cika a wajen maza da mata ana ta cece-kuce wasu har suna cewa a basu ita kawai suje su binne ta da ranta,wasu kuwa cewa suke a banka mata wuta kawai ta mutu, kasancewar tun ranar da abun ya faru Amrah bata sake fita koda nan da can ba,duk da cewa ko a cikin Hostel Win ma ba tsira tayi tun da wani lokacin har cikin Wakin su ake shigowa a ci mata mutunci,babu irin ba?a?en maganganu da ba'a gayawa Amrah Win,kullum cikin kuka take karatu kuwa tunin ta ajiye shi a gefe domin kuwa da ace ba'a koreta a makarantar ba to tabbas ta san wannan semester Win ba abun da zata iya tsinanawa wata?ila ma a mata repeat.

Dr Gana ne ya ?arasa inda Amrah Win take a yashe ganin shi da ?an makarantar suka yi ya sanya suka fara darewa suna bashi hanya wajen kuma yayi tsit kasancewar shi yana daga cikin malaman da Walibai suke shakka a cikin makarantar saboda baya sakewa kowa fuska balle a raina shi.

Ba wanda ya saurara yana ?arasawa inda Amrah Win take ya sanya hannu ya sunkuceta sannan ya fice daga cikin Admin Block Win da ita ya nufi motar shi duk sai idanun mutanen suka dawo kan shi inda ?ananan maganganun suka shiga tashi.

A bayan motar ya sanya Amrah sannan Anisa da Afrah suma suka shiga motar waWanda suka biyo bayan shi a lokacin da suka ga ya Wakko Amrah Win.

Da gudu ya figi motar sannan ya fice daga cikin makarantar ya nufi babban asibitin da yake cikin garin Zaria Win da Amrah Win.

Tsananin gudun da yake shararawa akan titin ya sanya motoci da yawa suka fara kaucewa suna bashi hanya gudun kar ya haWa da su a tafiya lahirar tun da sun lura kamar wanda yake tu?in motar baya son rayuwar shi ne.

Kan kace kwabo har ya ?arasa asibitin, ko parking mai kyau bai yi ba ya fito daga cikin motar da sauri sannan su Anisa ma suka fito.

CiWak ya Wakko Amrah a hannun shi ya nufi Emergency unit da ita,inda suma su Afrah suka bi bayan shi sai sharar hawayen munafurci suke.

Hango shi da ma'aikatan asibitin suka yi ya sanya su nufo shi da gudu sannan suka karSi Amrah Win suka Waura ta akan gadon da ake tura marrasa lafiya suka nufi cikin Emergency unit Win da ita.

A dai-dai wannan lokacin aka ?araso da su Amira da Azra ma inda suma aka sanya su a Wakin da yake gefen na Amrah.

Likitoci ne suka du?ufa akan Amrah suna bata agajin gaggawa,sun Wauki tsawon lokaci a kan ta kafin suka samu numfashin ta ya daidaita, amma sun sha matu?ar wahala kafin su shawo kan daidaituwar numfashin nata.

Drip aka sanya mata sannan aka mata allurai inda suka fice suka barta kafin a ga lokacin farfaWowar tata.

Dr Gana yana tsaye a bakin ?ofar Wakin da aka shiga da Amrah Win sai kaiwa da komowa yake hankali a tashe.

Yana ganin fitowar likitocin ya nufe su da gudu yana cewa.

"Dr ya jikin nata, dan Allah karka sanar dani cewa ta mutu?".

Dr Gana Win ya faWa tare da ri?o hannun likitan,jikin shi sai rawa yake.

"Ku biyoni office Wina".

Shine kawai abun da likitan ya iya faWa sannan ya nufi hanyar komawa office Win nashi.

Jiki a sanyaye Dr Gana da su Afrah suka bi bayan likitan gaba Waya sun gama bayarwa Amrah ta mutu.

Shigar su office Win likitan ya nuna musu wajen zama sannan ya shiga musu bayani ba tare da Sata lokaci ba.

"Maganar gaskiya Dr Gana rayuwar wannan yarinyar tana cikin haWari,yanzu dai mun samu mun daidaita numfashin nata sannan a kowane lokaci zata iya farfaWowa daga doguwar suman da tayi sai dai akwai yiwuwar cewa idan ta farfaWo ta farfaWo da ciwon hauka domin kuwa, ?wa?walwar ta ta taSu sannan ya zuciyar ta da itama ta fara kumbura,dan haka a yanzu wannan yarinyar addu'ar ku kawai take bu?ata".

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun, likita yanzu Meye abun yi,wallahi duk abun da ake bu?ata zan bayar matu?ar za'a ceci rayuwar ta,pls Dr do something I beg, dan Allah a taimaka".

Dr Gana ya faWa cikin tsananin tashin hankali da ruWewa.

Su Anisa da suke zaune a gefe ma take suka ji zuciyoyin su sun shiga bugawa a lokaci guda jin abin da likitan ya faWa, Wannan shine karo na farko da Anisa taji nadama da tausayin Amrah sun shige ta.

"Dr Gana Sorry to say a yanzu kam ba wani abu da zamu iya yiwa Wannan yarinyar domin kuwa duk wani abu da ya kamata mun yi,dan haka zamu jira har zuwa lokacin da zata farka muga a wana hali ta farka,ku yi ha?uri".

Tashin hankali shine abun da Dr Gana ya faWa sannan ya dubi likitan yace.

"Amma likita zamu iya shiga mu ga a wane hali take".

"Gaskiya ba zai yiwu ba,domin tana bu?atar a keSeta ita kaWai, a yanzu haka ?arar abu kaWan zata iya sanyawa ta farka,mu kuma bama son farkawar tata a yanzu".

Haka Dr Gana da su Anisa suka tashi suka fito daga office Win likitan fuska cike da damuwa.

A Sangarena kuwa ba'a wani Wauki tsawon lokaci ba na farfaWo inda ina farfaWowa na juya gabas da yamma naga ba kowa a cikin Wakin. Cikin sauri na sanya hannu na cisge ?arin ruwan da ake mun Win sannan na tashi da gudu na fice daga cikin Wakin ko takalmi ban tsaya sanyawa ba,dagani sai Wan kwali.

?akunan da suke gefena na shiga dubawa inda cikin ikon Allah na hango Amrah kwance a cikin Wakin da yake tsakiyar namu ni da Azra kamar ka ?ira sunan ta ta amsa.

Da gudu na nufi Wakin naci Sa'a kuwa ?ofar Wakin ba'a rufe take ba ina turawa ta buWe.

Tura ?ofar tawa yayi dai-dai da farkawar Amrah inda kafeni da ido kamar yadda nima nayi ina tsaye a bakin ?ofar Wakin.

Kamar wadda ta tuno wani abu kawai sai gani nayi ta mi?e da sauri tare da dirowa daga kan gadon sannan ta sanya hannu ta cisge ledar ruwan da ake ?aramata Win.

Da gudu na ?arasa wajen ta sannan na fashe da wani irin kuka mai taSa zuciya.

"Amrah nasan an cuce ki,amma kuma tabbas nima na bada gudummawa wajen faruwar hakan, Amrah nasan abun da aka shirya aikata miki amma na Soye ban sanar da ke na bari har ma?iya suka yi galaba a kan ki, Amrah dan Allah ki yafe mun, Amrah zan sanar dake duk wani abu da ya faru da kuma waWanda suka aikata miki hakan duk da nasan cewar faWar a yanzu bata da amfani".

Nan na shiga sanarwa da Amrah duk abun da su Azra suka shirya mata tiryan-tiryan ban Soyemata komai ba,har na gama sanarwa da Amrah labarin bata ce ?ala ba sai dai irin kallon da take mun kaWai ya Isa ya fahimtar da kai irin halin da take ciki da kuma cewar tana jin abin da nake faWa Win.

Gani nayi ta sanya hannu ta ture ni gefe sannan ta nufi ?ofar fita daga cikin Wakin.

Da sauri na sha gaban ta ina cewa.

"Amrah ina zaki?, Amrah dan Allah ki tsaya ki saurareni, Amrah ina miki magana da........."

Kallon da naga Amrah Win ta watsa mun ne ya sanyani shan jinin jikina sannan na tsinci kaina da jan bakina nayi gum.

Ficewa Amrah tayi daga cikin Wakin sannan ta nufi hanyar barin cikin asibitin, ai ina ganin haka nima na shiga bin bayan ta da sauri da sauri har ina haWawa da Wan gudu.

Har muka bar area Win Emergency unit Win bamu haWu da su Anisa ba,balle Dr Gana.

Tun da muka fito daga cikin Wakin duk inda muka wuce sai an bimu da kallo ganin cewar ?afafuwan mu ko takalmi babu, ga ko hijab babu a jikina daga ni sai Wan kwali,ita kuma Amrah da hijabi amma itama ba takalmi a ?afar ta.

A bakin gate Win asibitin naga Amrah ta ja tunga ta tsaya,hannu naga ta yiwa wani mai mashin ya tsaya,inda ya iso inda muke Win ba tare da ta faWa mishi inda zai kaita ba naga ta faWa cikin mashin Win.

Aikuwa nima ban tsaya wata-wata ba na afka cikin mashin Win ganin har mai mashin Win yana shirin tayar da mashin Win.

Tafiya muka fara yi,inda na cigaba da yiwa Amrah magana amma har a sannan bata juyo ta kalleni ba balle ta tanka mun.

Shima mai mashin Win sai tambayar mu yake inda zai kaimu amma ba wanda ya bashi amsa.

Mun yi tafiya mai Wan tsaye kafin mu kazo wucewa ta wajen tashar da ake shiga motar garin su Amrah.

"Sau?eni a nan".

Muka tsinkayi muryar Amrah wadda sai a sannan tayi magana, sai dai jin Muryar tata da nayi sai da ya kusa sanya ni na saki fitsarin da ban yi niyya ba domin kuwa wata irin murya naji daban wadda ban taSa sanin Amrah Win da ita ba.

Tana sau?a daga cikin mashin Win naga ta kama hanyar barin wajen ba tare da ta bawa mai mashin Win kuWi ba

"Hajiya kuWi na?".

Kallon Amrah nayi wadda tayi alamar bata ma san yana magana ba.

Da sauri na juyo na kalle shi sannan nace

"Dan Allah ka jirani zaka mayar damu zan baka kuWin".

Ban jira naji abun da zai faWa ba,na bi bayan Amrah da gudu wadda naga ta nufi wata mota da naji ana ta ?iran.

"Giwa! Giwa! Giwa! Saura mutum Waya".

Daf da zata shiga motar na ri?o hannunta sannan nace.

"Amrah dan Allah ina zaki?, Sai magana nake kin shareni?".

Sai a sannan Amrah ta juyo ta kalleni sannan tace.

"Zan tafi gida,amma ina son na baki sa?o ki sanarwa su Azra cewar kar suga sun yi galaba a kaina a yanzu,to wallahi ba galaba suka yi ba faWuwa suka yi,kuma ki sanar dasu cewa su tsoraci ranar da zan waiwayo gare su, sai na jefa rayuwar su a cikin u?uba, u?uba mafi muni,yanzu wasan zai fara".

Har ta fara tafiya kuma sai ta juyo ta dubeni sannan ta buWe baki cikin sha?ewar murya ta cigaba da magana.

"Amira kin san irin tashin hankalin da na shiga dalili wannan videon da aka mun aka sakar a duniya?, A dalilin haka har yau ?an gidan mu ba wanda yake Waga ?iran wayana,a dalilin haka ya sanya iyayena da suke ji dani suka juya mun baya domin kuwa tun ranar da abun ya faru har kawo yau ba wanda ya amsa ?iran wayata a cikin ?an gidan mu ke daga ?arshe ma idan na ?ira wayar ma bana samu,a yanzu haka fargabar abun da zanje na tarar nake a gidan namu. A dalilin haka saurayina wanda zan aura shima har yau ban sake samun wayar shi ba,nasan cewar na rasashi rasawa ta har abada. Shin kina ganin ya dace na ?yale waWanda suka zama silar tarwatsewar farin cikina?, Shin kina ganin ya dace na bar mutanen da suka yi sanadiyar tarwatsewar burina dana daWe ina son ya cika?, Wallahi ko wana irin hukunci zan Wauka a kan su ba zan taSa goge tabon da suka mun a zuciyata ba,domin kuwa sun mun tabon da har yauma ta?ummu Sa'a ba zai goge ba,sun bar wa zuciyata ciwon da mutuwa ce kaWai zata zama maganin shi".

Tana kaiwa nan a zancen nata ta shige cikin motar ta bar ni tsaye kamar an dasa bishiya.

Ina tsaye a wajen kamar yadda Amrah ta barni har motar su ta tashi ban motsa ba,ta gabana motar ta zo wucewa in da Amrah ta le?o ta window da idanunta da suka yi jawur sannan tace cikin Waga murya.

"FANSA! FANSA! FANSA! su jira dawowa ta Waukar FANSAAAAAAAAAA domin kuwa zan wula?anta maciya amana zan tozara su,dan illata rayuwar su illa mafi muni,idan har ban yi haka to ba zan taSa yafewa kaina, ko na mutu sai ruhina ya dawo ya wanzu a doron ?asa ya Wauki Fansa,domin kuwa ba zan taSa samun kwanciyar hankali ba matu?ar na tuna cewar ma?iyana suna rayuwa a doron ?asa kuma cikin kwanciyar hankali".


******

Yau kwanan Anwar Uku a gadon asibiti ba tare da ya san inda kan shi yake ba.

Mahaifiyar shi ce zaune a gefen shi tayi tagumi idanunta in banda tsiyayar hawaye ba abun da suke domin kuwa tun ranar da Anwar Win ya faWi tayi sallama da farin ciki inda ta Waura abota da kuka.

Kamar an ce ta juya ta kalli inda Anwar Win yake kawai taga ta fara motsi da hannun shi alamar zai farka.

Da sauri ta tashi sannan ta nufi kan shi tana ?iran sunan shi amma kafin ta ?arasa gadon nashi taji ya saki wata razannanniyyar ?ara sannan ya shiga ?iran sunan Amrah inda gaba Waya sai da Wakin ya amsa.

Wata irin jijjiga Anwar Win ya shiga yi kamar yadda mata masu borin haihuwa suke yi,haka ya shiga daddatse bakin shi gadon da yake kai kuwa take shima ya shiga wata irin karkarwa.

Kan kace mai Anwar ya sanya hannu ya fige robar ?arin ruwan da ake masa Win inda ya shiga ?o?arin mi?ewa tsaye daga kwancen da yake Win.

Shigowar likitoci cikin Wakin da gudu ne suka danne shi tare da hanashi mi?ewar sai dai har a wannan lokacin bai daina ambatar sunan Amrah ba.

Duk yadda likitocin suka so su hana Anwar Win tashi amma abun ya gagara haka ya dinga jifa dasu inda ya mi?e ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kamar wani namijin zaki ya diro daga kan gadon.


*MANGA*
'?
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_=؀? &? ).

_Tsarawa/Rubutawa_

*? SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai_ _muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._

*Free book*

------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*024*
______________________________

Har motar su Amrah ta ?ulewa ganina ban motsa daga inda nake tsayen ba,mamaki,tsoro,RuWani da kuma tashin hankali ne suka ziyarce ni a lokaci guda.

Ban san adadin lokacin dana Wauka a tsaye a wajen ba har sai da na tsinkayi muryar mai mashin Win dana bari a tsaye yana mun magana cikin fushi.

"Wai ke Malama wannan wana irin rashin mutunci ne tun Wazu kin barni a tsaye ina jiran ki kamar wanda kika ajiye bawan ki,sannan tsabar rashin mutunci nazo ina miki magana shine zaki mun shiru kin maida ni mahaukaci ina ta SaSatu ni a kaWai mutane sai kallo na suke".

Sai a sannan nayi saurin motsawa sakamakon dirar maganar mai mashin Win a cikin kunnuwa na da naji,ha?uri na bashi sannan na shiga cikin mashin Win muka kama hanyar komawa Kallo Waya zaka mun ka fahimci cewa bana cikin nutsuwa ta.

?ago da jajayen idanun ta Amira tayi ta kai duban ta ga mutanen da suke cikin police station Win wanda sun ci kuka har sun gode Allah, shikuwa Anwar ba'a magana.

Ganin Amira Win tayi shiru ne ya sanya Inspector Rasheed saurin kallon ta da rinnannun idanun da suka zama kamar gauta saboda ja shi sannan yace.

"Ya zaki katse labari a dai-dai gaSar da kowa ya matsu yaji ?arshen labarin,muka jure jin na baya ma balle yanzu da burin kowa bai wuce ya ji yadda Waukar Fansar ta fara ba,dan Allah kiyi gaggawar sanar damu mai ya faru da Amrah?, Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login