Showing 18001 words to 21000 words out of 70370 words

Chapter 7 - FANSAR FATALWA complete hausa novel

26 Oct 2025

97

dube ta yace.

"In sha Allah Ummu kamar yadda kika sanni a da to ba zan taSa sanjawa kuma addu'a ina kan yin ta zan kuma cigaba da yi in Allah yarda".

Bayan sun gama cin abincin addu'a ta mishi sosai kafin kuma ya mi?e ya mata sallama, lokacin ?arfe takwas da rabi sannan ya fita, duk da irin baccin da yake ji amma haka ya fita, kai tsaye gidan su Afrah ya fara nufa.

A dai-dai bakin gate Win gidan su Afrah Win suka ci karo da mahaifin ta da kuma yayan ta Aliyu sun fito zasu tafi wajen aiki.

Gaisawa suka yi da Inspector Rasheed Win cikin sakin fuska kafin Inspector Rasheed Win ya dubi mahaifin Afrah Win ya fara mishi bayanin abun da yake tafe da shi Win.

?an shiru suka yi daga mahaifin Afrah Win har yayan nata kafin daga bisani kuma mahaifin Afrah Win ya Wago ya dubi Inspector Rasheed Win yace.

"To amma Inspector a ganina meye dalilin yarinyar na ganin dole sai a gaban mu zata sanar da komai?".

"To Alhaji nima abun da na kasa fahimta Kennan amma ina ganin ku yi ha?uri mu je idan ya so mu ji abun da yake tafe da ita Win".

"To Shikennan Inspector bari na shiga na sanar da mahaifiyar ta sai ta shirya mu wuce".

"To ni dai yanzu idan kun shirya kwa same mu a can police station Win domin kuwa yanzu haka ma zan wuce gidan sauran iyayen yaran ne".

Inspector Rasheed ya faWa yana juya sannan ya shiga motar shi ya nufi gidan su Anwar bayan ya karSi address Win shi a wajen Aliyu.

Lokacin da ya je wajen Anwar Win bai wani samu damuwa dashi ba, haka a Sangaren mahaifin Anisa ma inda shima yace zasu shirya su biyo su daga baya.

Daga gidan su Anisa gidan su Azra ya nufa sai dai bai tarar da mahaifin ta a gida ba inda mai gadin gidan ya sheda mishi cewar ya tafi office, wayar shi ya ?ira amma bai Waga ba dan haka kawai ya yanke shawarar ya je ya same shi a office Win.

Hakan kuwa aka yi inda ya nufi office Win Justice Kabir Win, bai wani samu matsala wajen ganin Justice Kabir Win ba sai dai kuma inda gizo ke sa?ar shine Justice Kabir ya daga tsallen aradu yace.

"Ni ai daman na san wallahi makashin ?ata a cikin shegun yaran nan yake,watau sai da ta bisu Waya bayan Waya ta kashe su tukunna zata wani kai kan ta police station Win ai cuta kam an riga an gama cutar mu, dan haka wallahi itama ta shiryawa karSar nata hukuncin dan kar ta ga ta kai kan ta police station ta yi tunanin cewar hakan zai sa a sassauta mata hukunci, to ba zai yiwu ba wallahi sai ta tafi inda ta aika mun ?ata".

Shi dai Inspector Rasheed ha?uri ya bashi sannan ya lallaSa shi suka tashi suka nufi police station Win.

A zazzaune suka tarar da kowa ya hallara a office Win DPO Win su kawai ake jira, ga Amira kuma a zaune a gefe ido yayi jawur tun da suka shiga cikin office Win DPO Win mahaifin Azra yake jefawa Amira mugun kallo ji yake kamar ya sha?e ta ta mutu.

Gyaran murya DPO yayi bayan kowa ya nemi waje ya zauna sannan yace.

"To yanzu dai Alhamdulillahi mun hallara kamar yadda malama Amira ta bu?ata dan haka muna sauraran ki shin mai yake tafe dake?, ga dai iyayen yaran da aka kashe nan a gefe suna sauran ki, ga kuma ?an jarida kamar yadda ki ka bu?ata su ma sun zo, ga wasu daga cikin hukumar makarantar ku su ma sun samu damar halartar wannan wajen, kowa ya baza na zumaye da na mujiyar shi yana sauraran abun da zaki faWa".

DPO ya faWa yana mai zuba idon shi a kan Amira.

?ago jajayen idanun ta ta yi tare da sanya hannu ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta fara magana cikin kuka.

A dai-dai sannan kuma ?an jarida suka saita camera Win su da abun Waukar sauti a dai-dai fuskar Amira Win.

*MANGA*
'?.
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_=؀? &?).

_Tsarawa/Rubutawa_

? *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book Win gaba Wayan Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

---------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*011*
____________________________

A hankali Amira ta Wago fuskarta sannan ta fara magana.

"Kamar yadda na faWa in sha Allah a yanzu zan sanar da duniya irin cin amanar da aka aikatawa Amrah, tabbas an ci amanar Amrah wadda duk wata mace da aka mata haka an jefa rayuwar ta a cikin tashin hankali inda za'a ja mata tsana da ?yara daga wajen al'umma, Azra, Afrah,da kuma Anisa sun kasance mutane da zamu iya ?iran su da green Sneak, su Win azzalumai ne ma su bala'in son kan su, ina son kafin na fara baku labarin gaskiyar abun da ya faru ku Wauki kan ku ku sanya a matsayin Amrah shin idan ku ne wane irin hukunci zaku aikatawa wanda ya aikata muku irin wannan aika-aikar da aka aikatawa Amrah?, Kasancewar Amrah macece wadda bata iya Soye sirrin ta ga waWanda suke tare ba wannan ya sanya babu abun da bamu sani ba game da labarin rayuwar Amrah hakan shi ya bawa su Azrah damar cutar da ita domin kuwa sun yi amfani da irin matsayin mahaifin ta da kuma yadda suka fahimci cewar kaf iyayen su sun fi na Amrah rufin asiri wannan ya sanya ba suji shayin su tarwatsa mata rayuwa ba.Da farko dai bari na fara sanar daku labarin wacece Amrah?, da kuma su waye Azra?, Da kuma irin zaluncin da aka aikata mata duk kuwa da cewar nima ina da kamasho a wajen lalacewar farin cikin Amrah duba da yadda na san gaskiya amma na kasa bayyana ta a lokacin da ya kamata har na bari azzalumai suka yi nasara a kanta, na tabbata idan ku ka ji abun da aka aikata mata daga haka zaku ?ara tabbatar da cewa an cuce ta cuta mafi girma da za'a yi duk wani Wan Adam.

*FLASH BACK*

*Wacece Amrah* *?*

Asalin sunan ta Amrah Kabir ?ar asalin garin Giwa da ke ?aramar hukumar Zaria a jahar Kaduna, mahaifin Amrah babban malami ne da ba wanda bai san shi a cikin garin na Giwa ba har ma da wasu Sangare daga cikin jahar Kaduna an san shi, sai dai su Win talakawa ne wanda rufin asirin Allah ne kawai yake ri?e da su. Tun tasowar Amrah Allah ya sanya mata son karatun boko inda bata da wani buri wanda ya wuce ta ga ta zama cikakkiyar likita. Mahaifiyar Amrah ta rasu tun a wajen haihuwar Amrah Win Allah ya mata rasuwa to sai Amrah ta ta so a wajen matar mahaifin ta mai suna Sa'adatu sai dai kuma Amrah ta yi dacen kishiyar mahaifiya domin kuwa gwaggo Sa'adatu macece mai kyakkyawar zuciya kuma ta ri?e Amrah tsakani da Allah kamar ita ta haife ta a cikin ta,Amrah tana da yayu maza guda uku Waya uwar su Waya uban su Waya sauran kuma ?a?an gwaggo Sa'adatu ne, Hashim,Umar, Sai kuma Usman su ne yayun Amrah Win. Mahaifin Amrah mutum ne da mutane suke ganin mutuncin shi da girman shi a cikin garin Giwa Win kasancewar shi malami babba kuma ga dattako, gashi shi mutum ne da baya iya danne ha??in ?a?an shi duk abun da ?a?an shi suka nuna suna so yana musu matu?ar abun bai kaucewa Shari'a ba,saSanin wasu iyayen da zaku ga basa iya baiwa ?a?an su dukka ha??in da ya rataya a wuyan su inda zaku ga wasu iyayen suna nuna ai kamar su kaWai su ke da ha??i akan ?a?an wanda hakan kuma babban kuskure ne da wasu iyayen suke aikatawa dalilin haka sai kuga an zo an haifi Wa marar ido.

Da gudu ta shigo cikin gidan fuskar ta kana gani kasan ba ?aramin farin ciki take ciki ba, tana shigowa ta faWa kan cinyar gwaggo Sa'adatu wadda take zaune a tsakar gida tana gyaran kayan miya.

"To Sallani hankalin ki ya kwanta kin ji Amrah, ni wallahi ban san sai yaushe zaki girma ba,mutum yana girma kullum kamar ana mai da shi baya, ni Waga ni dan Allah kar ki ?arasa ni".

Gwaggo Sa'adatu ta faWa tana ture Amrah daga jikin nata.

ShagwaSe fuska Amrah ta yi sannan tace.

"Gwaggo wallahi yau ina cikin farin da ban taSa shiga ba".

Ta faWa tana ware wata paper da take hannun ta.

"Gwaggo wannan result Win mu ne na Waec and Neco ya fito duka na cinye ina da nine credit, yanzu saura na jamb zamu jira muga abun da Allah zai yi".

Murmushi gwaggo Sa'adatu ta faWaWa fuskar ta dashi sannan tace.

"Ai ni daman ban taSa kawo miki faWuwa ba Amrah kawai dai kece kike ta abun ki, Ubangiji ya sanyawa wannan sakamakon albarka".

"Ameen ya Allah gwaggon mu kice mun kusa mu samu likita a gidan na mu".

Yaya Hisham ya faWa da yake ?arasa shigowa gidan yanzu.

"Wallahi kuwa Hisham ga dai result ya fito Alhamdulillahi sai kuma mu jira wancan Wayan jan yake ko meye ma?".

Gwaggo Sa'adatu ta faWa fuskarta tana faWaWa da Murmushi.

Dariya muka yi gaba Waya nida yaya Hisham kafin kuma nace.

"Kai gwaggo Jamb fa ake cewa dan Allah meye kuma wani jan kamar a ?auye".

Hira muka Wan taSa kafin kuma lokaci guda su lura da fuskata da ta sanja idanuna suka ciko da hawaye.

"Subhannallah Amrah mai ye kuma haka muna hira zaki Sata fuska?".

Gwaggo Sa'adatu ta faWa tana janyo ni jikin ta itama fuskar ta da alamar damuwa.

"Gwaggo a duk lokacin da aka fara maganar karatu na sai na dinga jin faWuwar gaba, a wani Sangaren kuma gwaggo ina tausayin Abba kasancewar na san bashi da ?arfin da zai biya mun kuWi na yi karatu,sannan gwaggo kin san a wannan zamanin karatu ya zama sai Wan wane da wane musamman ni fannin da nake son karanta, sannan gashi a wannan garin na mu har yanzu ba'a Wauki ilimin mace da muhimmanci ba inda wasu suke yiwa abun kallo na daban,duk lokacin da na tuna abubuwan nan sai naji duk wani farin ciki na ya koma ciki".

Amrah ta ?arashe maganar hawayen da take ?o?arin tare suna zubowa daga cikin idanun ta.

Shiru gwaggo Sa'adatu suka yi da ita da Hisham cikin tausayin Amrah Win,tabbas sun san cewar duk maganganun da ta faWa gaskiya ne to amma kuma a yanzu su ya kamata su kwantar mata da hankali su nuna mata cewar duk abun da Allah ya tsara a rayuwar bawa shi yake kasancewa da shi. Hisham ne yayi ?arfin halin duban Amrah Win sannan ya fara magana cikin sigar rarrashi.

"Amrah kinsan dai a rayuwa duk abun da Allah ya tsara shi yake kasancewa da bawa,to dan haka ki Wauka cewar idan har kin samu damar yin karatu to Allah yayi zaki yi ne, haka kuma idan har kika ga baki samu damar cika burin ki ba to Allah ne bai yi hakan zai tabbata ba,dan haka in sha Allah ki sa a ranki in dai muna raye burin ki zai cika kuma zaki zama likita da izinin Allah,kuma daga yau ki fara shiri Jamb Win ki yana fita zaki wuce makaranta".

Wannan kalaman da Yaya Hisham ya yiwa Amrah su suka sanya ta cikin farin ciki wanda har bata san sanda ta saki murmushi ba, sannan ta tashi da gudu ta yi cikin Waki tana jin wani daWi kamar an cemata gobe zata wuce makaranta.

Da dare bayan malam Kabiru mahaifin Amrah ya dawo gwaggo Sa'adatu ta kawo mishi abinci da ruwa kamar yadda ta saba.

Sai da Amrah ta bari ya ci abinci ya sha ruwa kafin ta fito daga cikin Wakin ta sannan ta zo ta zauna a kusa dashi tare da gaishe shi.

"Mamana (kasancewar sunan mahaifiyar shi gare ta), ya dai yau naga bakin ki kamar gonar audiga ya ?i rufuwa ga dukkan alamu bakin akwai magana ko?".

Cewar Malam Kabiru Win, murmushi Amrah ta yi sannan tace.

"Abba Albishirin ka".

"Goro Mamana, goron ma fari tatass".

Ya faWa yana faWaWa fuskar shi da murmushi.

"Abba ga result Win mu na Waec and Neco ya fito kuma Alhamdulillahi Abba na cinye duka nine credit".

Ta faWa tana mi?a mishi result Win da yake hannun ta.

"Ah ah ah Masha Allah Mamana wannan albishir dole a baki tukwaici".

Ya faWa yana buWe result Win da yake hannun na shi.

Caraf gwaggo Sa'adatu ta yi tare da amshe zancen sannan tace.

"Ai ba'a isa ba wannan tukwaicin a ni za'a bawa domin kuwa ni na fara maka albishir Win ai".

Dariya suka yi gaba Waya sannan Amrah tace.

"To ai gwaggo ko an bani tukwaicin ma kamar ke aka bawa ni da ke ai duk Waya ne".

"Uhmm kaji Sarkin wayo ko, zata rufe mun baki to Shikennan ai nayi shiru daman haka ki ke so".

Albarka Sosai mahaifin Amrah ya sanyawa result Win nata kafin daga bisani ya mata addu'a sannan ta tashi ta koma cikin Waki.

Bayan shigar Amrah Waki ne Malam Kabiru yayi gyaran murya tare da duban Gwaggo Sa'adatu fuska da alamar damuwa ya buWi baki ya fara magana.

"Wallahi Sa'adatu ranar da nake ta tunanin zuwan ta ne take ta ?aratowa,kullum da tunanin wannan ranar nake kwana nake tashi ranar da Amrah zata kammalla karatun ta na sani cewar Amrah tana son karatu sosai to amma gashi ni kuma bani da halin da zan sanya ta a makaranta domin cikar burin ta,kin fi kowa sanin halin babun da muke ciki tun da kina gani hakan zan fita yanzu na dawo gidannan hannu wayam wata ran ma sai ke kike taimaka mana,ga Hisham shima yanzu kasuwar ba wata kawo mishi take ba,ga Wawainiyar shi ga ta iyalan shi, shi kuma Usman karatun shi yanzu haka ya katse sakamakon kuWin registration da bai biya ba har na semister biyu,mai dama-daman shine Umar to shima yanzu hidimar auren shi ta sako shi a gaba, sannan abu na gaba kin san yadda ?asar ta mu yanzu ta zama karatu sai kana da kuWi,ga yadda tarbiyya ta taSarSare a manyan makatantu sai a hankali".

Malam Kabiru ya ?arasa maganar fuska cike da damuwa.

Saurin kallon shi gwaggo Sa'adatu ta yi sannan ta fara magana cikin son ta ?arfafa mishi gwaiwa.

"Malma na sani duk abubuwan da ka faWa ba wanda ba dai-dai ba a cikin maganar ka, amma ina son ka san wani abu guda Waya duk bakin da Allah ya tsaga ba zai hana shi abinci ba,dan haka kamar yadda Amrah ta kammalla makarantar ta Sakandire lafiya kuma ta samu ta fita da kyakkyawan sakamako to bi'izinillahi rabbi zata cigaba da karatu kai dai kawai yanzu mu mata addu'ar wannan result Win da ya rage mata ya fito lafiya kuma ta ci shi,sannan a halin yanzu Amrah ?warin gwaiwar mu take bu?ata dan Allah ka cire komai a ranka,ko ka manta duk sauran jarrabawar da ta rubuta da kuWi ake rubutawa kuma an biya mata ta yi to in sha Allah wannan ma ba zai gagara ba".

Sosai Malam Kabiru ya ji daWin maganganun matar ta shi in da ya shiga sanya mata albarka ya kuma godewa Allah da ya azurta shi da mata mai halin kirki irin Sa'adatu Win.

Bayan wasu kwanaki result Win Amrah ya fito na Jamb in da cikin ikon Allah ta ci maki fiye ma da yadda ake bu?ata wannan dalilin ya sanya ?an gidan su Amrah suka ?ara zage damtse wajen ganin an cika mata burin ta.

Yau gidan su Amrah an tashi ana bikin yayan ta Umar in da aka Waura aure lafiya aka gama lafiya ba wani ?arya da aka yi a bikin kasancewar auren ?a?an malam Shehu ne daga amaryar har angon.

A wannan bikin ne Amrah ta haWo da sanyin idaniyar ta Anwar wanda ya kasance abokin Umar Sai dai shi a garin Zaria yake da zama.

Tun da Anwar ya ?yalla idon shi akan Amrah ya ji duk duniya ba wadda yake so sama da ita.

Aikuwa ba tare da yayi ?asa a gwaiwa ba ya isar da sa?on shi wajen Amrah in da bai wani sha wahala ba ta karSe shi hannu bibbiyu.

Lokaci guda wata zazzafar soyayya ta ?ullua a tsakanin Amrah da Anwar,wanda Anwar ya mayar da Zaria da garin Giwa kamar unguwa, tun ba wanda ya fahimci abun da yake faruwa a tsakanin su har ?an gidan su Amrah Win suka zo suka fahimta.

Yau Amrah ta tashi da wani irin farin ciki sakamakon Anwar zai zo in da za su shiga cikin garin Zaria da Umar domin a mata siyayyar tafiya makaranta, duk da cewar tafiyar da Wan saura ba'a ma gama registration ba.

A motar Anwar Win suka tafi inda ya kai su wani babban Mall a garin Zaria Win.

Suna fitowa a cikin motar Umar ya tsaya yana ?arewa wajen kallo sannan ya dubi Anwar yace.

"Malam kasuwa fa zaka kai mu ya naga ka kawo mu wannan wajen wanda kai ma kasan waje ne da yafi ?arfin talakawa irin mu,kaga dan Allah wuce mu tafi kasuwa".

Umar ya faWa yana ?o?arin komawa cikin motar.

Murmushi Anwar ya yi sannan ya dubi Umar yace.

"Umar dan Allah ku zo ku shiga ka sani cewar ko ba wata ala?a a tsakani na da Amrah ita Win na Wauke ta kamar ?anwa ta ce,dan haka kar ka damu akwai enough kuWi wanda zamu yi siyayya a ?anwar mu,ita ma ta je makaranta ta fantama".

Ya faWa yana kamo hannun Umar Win suka nufi cikin Mall Win, siyayya ta gani ta faWa Anwar ya yiwa Amrah inda sai da Umar ya ce mishi ya dakata.

Sosai suka yiwa Anwar godiya har sai da Amrah ta zubar da hawaye ganin irin lodin siyayyar da ya mata Win, a ciki hadda waya mai bala'in tsada ya haWa mata da ita.

*MANGA*
'?
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ =؀? &?).

_Tsarawa/Rubutawa_

*?* *SHAMSIYYA MANGA*

*SADAUKARWA* : _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login