Showing 33001 words to 36000 words out of 70370 words

Chapter 12 - FANSAR FATALWA complete hausa novel

26 Oct 2025

108

ta ta sha kuka kamar ranta zai fita,ba wanda ya sani a tsakanin mu.

*****

Yau ta kama weekend ne inda tun safe muka fita karatu kasancewar ni da Amrah muke karatu tare, sai ya zamana mun bar Anisa da Afra da kuma Azra a Wakin.

Zaune suke a cikin Wakin in da suke tattaunawa akan yadda zasu Sullowa lamarin Anwar Win.

Azrah ce ta dubi su Anisa sannan tace.

"Afra ki ?ira Anwar a waya ki bayyana mishi abun da yake zuciyar ki a yanzu muji abun da zai ce".

Kallon Azra Afrah ta yi da niyyar yin magana tare da fito da ido waje,sai dai da sauri Anisa ta dakatar da ita tare da cewa.

"Wai Afrah wace irin matsoraciya ce?, Wallahi shiyasa wani lokacin ki ke bani haushi ni idan da nice da tunin an daWe da wuce wannan zancen,da tunin wani zancen ake ba wannan ba,sai kace ba mace ba,haba dan Allah!".

Anisa ta faWa cikin son ta ?arfafawa Afra Win gwaiwa.

A hankali Afrah ta sanya hannu ta Wakko wayarta da take gefe sannan ta cire sim card Win ciki ta sanya wani sannan ta nemo number Win Anwar ta shiga dialing tana jin zuciyarta kamar zata fito waje saboda tsoron abun da zai je ya dawo.

Sai da ta yiwa Anwar Win ?ira uku ana huWu tukunna ya Waga,bai yi magana ba ya yi shiru in da a hankali cikin sanyin murya ta furta.

"Hello!".

Daga Waya Sangaren Anwar ya amsa bai jira abun da zata ce ba yace.

"Da wa nake magana pls?".

Shiru tayi bata amsa ba, jin da Anwar ya yi anyi shiru ne ya sanya shi katse wayar domin a tunanin shi mistake aka yi wajen ?iran.

Sai dai ko dawowa daga zancen zucin da yake bai yi ba ya sake jin wani ?iran ya shigo mishi cikin wayar, yi yayi kamar ya share sai kuma dai ya Waga.

A wannan karon duk wani ?arfin gwaiwa Azra ta laluSo ta azawa kan ta sannan ta furta.

"Anwar kana jina".

Ta faWa tana ajiye wayar a tsakiyar su bayan ta sanya ta a handsfree.

"Ina jin ki wacece bangane ba?".

Anwar ya faWa kamar an mishi dole.

"Anwar dan Allah ina son muyi magana idan ba damuwa mana?".

Shiru Anwar Win yayi kamar ba zai ce wani abu ba kafin kuma daga bisani yace.

"Ok Ina jinki".

Ya faWa a ta?aice.

"Anwar sunana Afrah shin ko zaka tuna wata number da kwanakin baya ake ta tura maka message?".

Shikam Anwar jin sunan da ta ambata Win ko kaWan bai kawo a ranshi cewar wai Afrah ?awar Amrah bace,domin kuwa bai taSa sanyawa a ranshi cewar hakan zata iya faruwa ba,gashi kuma ko muryar ma bai ji ta mishi kama da wacce ya sani ba,duk kuwa da cewar sau biyu ne ko sau uku suka taSa gaisawa.

"Anwar kayi shiru,ko baka ji abun da na faWa bane?".

Ya tsinkayi muryar Afrah daga Waya Sangaren ta faWa.

"Eh na tuna"

"Amma kuma shine Anwar ko sau Waya baka taSa mun reply ba?".

Shi maganar ma dariya ta bashi inda har sai da ya dara.

Jin muryar Anwar Win yana mata dariya ne ya sanya ta kalli su Azra idanun ta suna cikowa da hawaye,sannan cikin rawar murya ta furta.

"Anwar dariya ma na baka?".

Sai da yayi dariya mai isar shi kafin yace.

"Sosaima wallahi, saboda gaba Waya maganar taki ne naji ta wani bambarakwai,kawai saboda nine wanda ban san ciwon kaina ba daga ganin message a wayata sai na hau yin reply,to an gayamiki Anwar irin mazan da kika saba turawa message ne marrasa aji irin ki, tukunna ma mai yasa kika ?irani?".

Hawayen da Afrah ta ke ri?ewa ne suka shiga sintiri ta kan kuncin ta,tun da take ba'a taSa faWa mata maganar da ta ?ona mata rai irin wannan ba,amma bakomai ko da zai zage ta yau dai zata bayyana mishi sirrin zuciyarta.

"Amma Anwar ina so ka sani duk wanda zai so ka to ai da alkhairi ya nufeka,sannan soyayya bata taSa zama ?iyayya, wallahi Anwar ina son ka kuma da gaskiya,ban taSa ganin wani Wa namiji da naji son shi irin yadda naji naka ba, pls Anwar dan Allah ka so ni".

Shikam Anwar mamaki ne ya mamaye shi lokaci guda jin wai ?a macece take requesting soyayya a wajen namiji,lalle duniya ta lalace.

"Uhmmm wa kika ce ma sunan ki?".

"Afrah"

Ta maimaita a hankali.

"Yawwa Afrah dan Allah zan ro?e ki da girman Allah ki fita a rayuwata domin kuwa ni da kika gani ina da mata,dan haka tun muna cikin ganin darajar juna ki fita a rayuwata sannan kar ki ?ara garajen turamun message ko kuma ki ?irani saboda ranar na farko kin sanya matata a cikin damuwa dan haka idan kika ?ara yin na biyu wallahi zan wula?anta ki duk kuwa da cewar wul?anci ba Wabi'ata bace amma kuma idan kika kaini bango zaki sha mamaki dan akan matata Amrah ba abun da ba zan iya ba,kuskuren da zaki aikata wanda zai zamar miki damuwa a rayuwar ki shine sake ?iran wayata ko kuma ki turamun message".

Anwar yana kaiwa nan a maganar shi ya katse wayar sannan ya danna number Win Afrah Win a blacklist.

Wani mahaukacin kuka Afrah ta fashe dashi tare da dafe ?irjin ta da yake mata suya kamar wuta.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun Azra kunji abun da yace!, Azra ni daman nasan wallahi Anwar ba zai taSa sona ba matu?ar Amrah tana raye, Azra mutuwar zan yi wallahi matu?ar ban mallaki Anwar ba, Azra dan Allah ku taimaka mun".

Afrah ta faWa tana kuka wiwi harda majina.

Sosai Anisa da Azra suka ji tausayin Afrah Win da ?yar Azra suka rarrashe ta ta sassauta kukan nata, sannan Azra tace.

"Afrah ki daina kuka in sha Allah Anwar zai dawo gareki kuma zaki mallake shi,kuma Amrah tana cikin duniyar nan,sannan in sha Allah ke ba zaki taSa shiga damuwa ba sai dai Amrah ta shiga, ina mai tabbatar miki nan da wasu kwanaki Anwar zai zama bashi da wata wadda ya tsana kamar Amrah, ke in ta?aice miki labari ma sai Anwar ya dawo ko sunan Amrah baya bu?atar ya ji an ambata balle ya ga fuskarta".

Cikin sauri muka Wago muka kalli Azra ni da Anisa cikin matsanancin mamakin maganganun nata.

"Azra ta yaya hakan zata kasance?, Ina tunanin a duniya ba abun da zai sa Anwar ya tsani Amrah koda kuwa asiri aka musu".
Wani murmushi Azra ta sake sannan tace.

"Sanin hakan ne ma ya sanya ba zamu taSa amfani da asiri wajen yi musu farra?u ba domin kuwa Satawa kan mu lokaci kawai zamu yi saboda ba zai yi tasiri ba, amma wannan hanyar da zamu bi tabbas hanya ce da zamu yi nasara".

"To fah! Azra wannan wace irin hanya ce?".

Su Afrah suka tambayi Azra Win.

"Karki damu zan sanar daku in sha Allah yanzu dai mu bar maganar tun da kinga lokacin dawowar su daga karatu ya kusa, sannan Afrah ina son ki mannawa Anwar ki fita a harkar shi kar ki ?ara neman shi,bayan mun samu nasara a abun da muka sa a gaba sai kuma mu Wora daga inda muka tsaya".

Wani farin ciki ne ya kama Afra ji take kamar ta mallaki Anwar ta gama.

*MANGA*
'?.
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_=؀? &?) .

_Tsarawa/Rubutawa_

*? SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

---------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*018*
______________________________

Sai dai abun da su Afrah basu sani ba shine duk wani abu da suke shiryawa ina sane da su,domin kuwa yanzu haka ma lokacin da suke waWannan zantukan ina tsaye a bakin ?ofa ina jin su,a lokacin na dawo zan Waukar mana wani littafi kawai naji abun da suke tattaunawa Win.

Fasa shiga cikin Wakin namu na yi inda na tsaya na gama saurarar abun da suke faWa Win.

Tsoro,fargaba,mamaki ne suka dirar mun a lokaci guda,jikina idan banda rawa ba abun da yake yi.

Sai da nagama jin komai kafin na juya na koma wajen karatun namu ba tare da na shiga Wakin ba.

Lokacin da nakoma wajen Amrah ta lura da yanayi na ba yadda na bar wajen ba,hakan ya sanya fara tambaya ta

"Amira lafiya kuwa naga yanayin ki ya sanja ba kamar yadda ki ka bar nan wajen ba?".

Murmushin ?arfin hali na ?a?aro sannan nace.

"Bakomai Amrah wani abu kika gani?".

Kallo na Amrah ta yi irin kallon ban yarda ba sannan tace.

"Haba Amira ya zaki cemun bakomai bayan duk wanda ya ganki ya san yanayin ki ya sanja,kuma da alama ma kamar kuka kika yi?".

Rasa abun da zancewa Amrah na yi inda wata zuciyar ta bani shawarar na sanar da ita kawai abun da naji,wata zuciyar kuma tace kul Amira kar ki fara ki bari muga iya gudun ruwan su.

Da wannan shawarar na yi amfani inda na dube ta sannan nace.

"Da gaske Amrah bakomai ki yarda dani ke kinsan da akwai abun da yake damuna da na sanar da ke,tun da kinsan bana Soye miki komai,kawai dai kaina ne ya Wan fara mun ciwo".

Ji na kawai Amrah ta yi amma alamun ta ya nuna bata yarda ba,kallo na tayi sannan tace.

"Ina littafin da kike je Wakko mana to?".

Sai a sannan Amira ta tuna da abun da taje yi Hostel Win, Wan sosa kai ta yi alamar rashin gaskiya sannan tace.

"Ai ban ma ?arasa Hostel Win ba saboda ciwon kan yanzu mu ce miki zan yi mu koma kawai".

Na ?arashe maganar ina mi?ewa tsaye domin bana son Amrah ta cikani da tambaya gudun kar a zo a samu matsala ta fahimci halin da nake ciki.

Fuskantar da Amrah ta yi cewar bana son maganar ya sanya ta mi?e tsaye tare da cemun mu wuce,amma ba wai don ta gamsu da abun da nace Win ba.

Lokacin da muka Hostel mun tarar da su Afrah har sun shirya mana abinci sannan suka tare mu fuska faran-faran.

Wani ?ullutun ba?in ciki ne ya taso ya tokare mun zuciyata a lokacin da na tuna da maganganun da naji su suna yi Wazun, fisabillillahi kamar ba sune suke shirin tarwatsa farin cikin Amrah ba amma gashi yanzu suna nuna mata sun fi kowa sonta,alhalin kuma idan za'a tona abun da yake a zuciyar su ba za'a ga da kyau ba,lalle Wan Adam ba abun yarda bane,tabbas su Azra sun cika masu fuska biyu,na faWa a zuciyata ina kwanciya a kan gado,tare da juya musu baya domin kuwa a yadda nake jin zuciyata idan har zan zauna na cigaba da kallon su to tabbas za'a samu matsala zan iya zagin uwar su da uban su wanda kuma ba zan so hakan ba domin kuwa ba yanzu nake son na tona musu asiri ba. Sai dai rashin sani yafi dare duhu domin kuwa da nasan abun da zai faru a gaba da nayi gaggawar tonawa munafukan asiri Amrah ta san da su wa take zaune, wannan shine babban kuskuren dana yi wanda har ya sanya su Azra suka yi galaba akan Amrah kuma wanda har yanzu ina danasanin aikata shi.

Muryar Azra da naji tana mun magana akan na tashi muci abinci ita ta dawo dani daga tunanin da na tafi Win.

Da sauri na runtse idona alamar bacci nake ina jin su suna ta mun magana amma na manna musu,kasancewar sun san halina da saurin bacci ya sanya suka yi tunanin ko nayi bacci ne.

Tun daga wannan lokacin na daina sakewa su Azra fuska domin kuwa gaba Waya haushin su nake ji, su kuma sun yi yin duniya na sanar da su damuwa ta amma sai dai nace musu Bakomai.

Lokaci guda na zabge na rame duk na zama wata iri dani gashi ko hira na daina sakewa muyi dasu Azra, Amrah ce kawai ban sanja mata ba yadda muke mu'amalar mu ta da to haka muke yanzun ma.

Sai dai fa na sawa su Azra ido sosai domin kuwa nayi al?awarin sai na tarwatsa shirin su.

Kasancewar Azra tana da mugun wayo ya sanya ta fara zargin ko na gano abin da suke shirin aikatawa ne ya sanya na sanja musu.

Sai dai abun da ban sani ba shine yadda na sawa su Azra ido ashe itama Azra haka ta sanya mun ido sosai, duk wani takuna tana ankare dani.

Wata ranar lahadi da ba zan manta ba, mun fita wajen saloon nida Amrah, mun gama komai lafiya har muka tsaya a kasuwa muka yi siyayya sannan muka kamo hanyar dawowa Hostel a lokacin ma Anwar ne ya kawo mu.

Tafe muke a cikin motar in da Anwar da Amrah suke hira sosai,duk da sun so su sanya ni a cikin hirar tasu amma hakan ya gagara domin kuwa nikam gaba Waya hankali na ma baya kan su.

Anwar ne yake tambayar Amrah shin ko lafiya nake kuwa.

Amrah amsa ta bashi inda take ce mishi wallahi itama ta kasa gane meye yake damuna cikin ?an kwanaki biyun nan.

Tambaya ta Anwar Win ya shiga yi amma ba wata amsa sabuwa.

Duk wata tambayar duniya sun mun amma amsar dai itace bakomai, ganin da suka yi bani da niyya ya sanya suka ?yale ni.

A haka muka iso makaranta inda na fita daga cikin motar bayan na yiwa Anwar sallama ciki-ciki.

A mota na ?yale Anwar da Amrah suna hira inda nikuma na nufo Hostel da kayan da muka siyo.

Har na kama handle Win ?ofar zan murWa na buWe kawai naji maganganun su Azra wanda suka kusa sanya ni sumewa a wajen.

Muryar Azra naji tana cewa.

"Kamar yadda na sanar daku a baya cewar akwai hanyar da zamu bi dan mu tarwatsa ala?ar da take tsakanin Anwar da Amrah cikin sau?i, shine kun ga wannan wayar ta daWe a ajiye a jakata ina jiran zuwan ranar amfanin ta,kuma Alhamdulillahi gashi ya zo".

?an shiru tayi sannan ta dubi Afrah ta cigaba da magana tare da Wakko wata ?ar ?aramar Camera.

"Wannan Camera Win da kuke gani zamu sanya ta a toilet, kun san cewar Amrah itace sarkin yin wankan dare,a rana tana wanka sau huWu ne, to zamu daidaice lokacin da zata shiga toilet sai mu sanya wannan Camera Win,inda zata mana video Win Amrah tsirara daga nan kuma sauran bayanan zan muku shi daga baya".

Saurin zaro ido waje Afrah ta yi duk da cewar tana son a raba Anwar da Amrah amma wannan karon sai taji ba zata iya goyon bayan a Wauki videon tsaraicin Amrah ba,da ?yar ta ?a?alo kuzari sannan ta dubi Azra tace.

"Azra nikam gaskiya a sanja shawara domin kuwa wannan abun ai da cutarwa sosai a cikin sa,ni wallahi ba zan so a Wauki videon tsaraicin ?aruwata mace ba,ke ko ma?iyiyata ce ba zan so ba,balle Amrah yadda muke da ita, dan Allah mu sake wata hanyar dan.......".

"Idan har ba wannan hanyar ba to ki shirya ha?ura da Anwar domin kuwa in dai baki bi wannan hanyar ba,to ba wata hanya da zamu bi domin ki mallaki Anwar ,ruwan ki ne ki amince ruwan ki ne ki ?i amincewa,sai dai kuma rashin amincewar ki yana nufin kin rasa Anwar har abada, domin kuwa ba zaki taSa mallakar shi ba".

Itama Anisa take ta dubi Afra tace.

"Ni a ganina Afra wannan itace kawai mafita idan har kina son ki mallaki Anwar,amma kuma idan kin shirya rasa shi to shikennan ba zamu miki dole ba sai mu ?yale ki,daman saboda ke zamu yi komai domin mallakar farin cikin ki".

Shiru Afrah ta yi tana nazari ita kam gaskiya zuciyarta bata aminta da wannan shawarar ba.

Kallon Azra tayi sannan tace.

"To Amma mai zamu da videon tsaraicin Amrah Win?".

"Sanin abun da zamu yi dashi ba wani abun damuwa bane kede kawai ki amince da abun da na ce miki, koma meye daga baya zaki ji".

Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da Afrah ta shiga furtawa,wannan shi ake ?ira ga ?oshi ga kwanan yunwa. Tabbas tana son Anwar amma kuma wannan hanyar ba hanya bace wadda ta dace ba, domin kuwa babu komai a cikin ta sai zallar tozarci,anya kuwa zata amince?. Afrah ta tambayi kanta, gaskiya abun da kamar wuya domin wallahi zunubin da yawa, ha??in Amrah ba zai taSa barin su ba idan har suka tozarta sannan Allah ma ba zai ?yale su ba,tun daga duniya za su fara ganin sakamako.

Nikuwa da nake tsaye a bakin ?ofa,take ?afafuwa na suka shiga wata irin karkarwa ban san sanda na zube a wajen ba wani irin gumi ya shiga tsatstsafowa ta kowanne sashi na jiki na,ashe Azra bata da imani har haka?, Ashe Azra zuciyarta ba?ar zuciya ce?, Ashe Azra azzaluma ce?, Ashe Azra bata kishin ?ar uwar ta mace?, Yanzu videon tsaraicin ?ar uwar ta mace take son Wauka?, To mai zata yi dashi, innalillahi wa'innailaihi rajiun wannan wace irin rayuwa ce haka,mai Amrah ta tarewa Azra har haka?.

Tambayoyin da nashiga jerowa kaina Kennan sai dai bani da wanda zai bani amsar su.

Wasu hawaye masu matu?ar zafi ne suka shiga kwaranyowa ta kumatun na, a take wani irin zazzafan zazzaSi ya rufe ni???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?, wata irin tsanar Azra ce ta kamani take nayi danasanin saninta da nayi.

Saurin Wan ?arfin da ya rage mun na tattaro sannan na fara ?o?arin mi?ewa tsaye duk kuwa da wata irin juya da take ?o?arin kayar dani.

A zafafe na ?arasa mi?ewa sannan na kama handle Win ?ofar da niyyar buWewa naje na ci musu mutunci, sannan na nuna musu cewar nasan duk abun da suke shirin aikatawa.

"Amira!".

Muryar Amrah ta dira a dodon kunnuwana hakan ya sanyani dakatawa daga shirin shiga Wakin da nayi.

*Assalamualaikum dan Allah kuyi ha?uri, nayi niyyar yi muku typing da yawa to amma hakan bai* *samu ba sakamakon an kwantar da ?anwata a asibiti, Wazu da azahar, wannan typing Win ma tun safe na yi shi shiyasa, amma da yau kam ma ba zaku samu posting ba,dan haka kuyi ha?uri kuyi manage har zuwa lokacin da za'a sallamo ta, kafin ta samu lafiya,ina fatan zaku mun* *uzuri* =?O?
*MANGA*
'?.
_Comment_ ,
_share_
_fisabillillahi_

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ =؀? &?).

_Tsarawa/Rubutawa_

*? SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login