Showing 3001 words to 6000 words out of 70370 words

Chapter 2 - FANSAR FATALWA complete hausa novel

26 Oct 2025

93

ne ya ?arasa inda Anwar yake tsugune sannan ya dube shi cikin tausayawa ya fara magana.

"Haba mana aboki na be a man mana,ya zaka zauna kana kuka kamar wata mace, common share hawayen ka dan Allah,ka sani kamar yadda na muku al?awari inshAllah zamu yi iya bakin ?o?arin mu dan gano wanda yake da hannu a cikin wannan kisan". DPO Win ya ?arashe maganar cikin ?arfafa gwaiwa.

Hannu Anwar ya sanya ya share hawayen da suka Sata mishi fuska sannan ya dubi DPO Win yace.

"DPO dole nayi kuka domin kuwa an cuce ni matu?ar cutarwa, DPO wannan wana irin zalunci ne ace sai ana saura kwana uku aure na a kashe mun mata,ai kuwa kaga kuka ya zama dole, Allah ya ji ?anki Afrah, Allah ya tona asirin duk wanda ya miki wannan aika-aikar".

A dai-dai wannan lokacin ne kuma mahaifiyar Afrah ta farka daga suman da tayi Win,inda ta farka da wani razannannen ihu ta koma kamar wata taSSaSiya ta dinga wani irin fisge-fisge tana wasu irin surutai marrassa kan gado.

"Ku ?yale ni in je wajen ?ata wallahi ?arya kuke mun ?ata bata mutu ba bacci take", Haka ta dinga faWa inda daga baya sai ta koma daga ta yi kuka sai kuma tazo ta kwashe da wata irin dariya irin dai ta mahaukata sabon kamu,da ?yar aka shiga ri?e ta tana fisgewa duk wanda yake cikin falon sai da ta bashi tausayi, da yawa sai suka daina kukan mutuwar Afrah suka koma kukan tausayawa mahaifiyar ta.

Waya DPO ya Waga inda ya ?ira ma'aikatan asibiti akan su zo su wuce da gawar Afrah mutuary har sai an kammalla bincike, lokacin da ma'aikatan lafiyar suka ?araso sai da likita ya ?ara duba Afrah inda ya ?ara tabbatar mu su da cewar Afrah fa ta riga mu gidan gaskiya. Ita kuwa mahaifiyar Afrah sai da aka mata allurar bacci wai dan ta yi bacci amma kamar wanda aka ?ara kunnata haka wannan allurar ta maidata.wani tashin hankali ma sai da aka zo fita da gawar Afrah a nan ne fa aka kafa sabuwar sumewa daga wajen ?anne da yayun Afrah Win ita kuwa mahaifiyar ta daman tunin ta sume ya kai sau ba adadi.

Haka dai suna ji suna gani aka fice da gawar Afrah Win aka kaita asibiti aka ajiye ta a mutuary har zuwa sanda ?an sanda zasu gama binciken su.

*****

Yau Sati guda Kennan da mutuwar Afrah amma gidan su afrah kamar yau aka yi mutuwar domin kuwa su kullum mutuwar sabuwa take zamowa a wajen su.

A Sangaren Anwar ma kullum a gidan su Afrah yake yini har zuwa dare kafin daga bisani ya tafi gidan su. Yau ma kamar kullum ?arfe goma ya tashi tafiya gida kamar yadda ya saba, lokacin da ya isa gidan bai tarar da ?an gidan su a falo ba kowa ya shige Waki ya kwanta, shima Wakin nashi ya nufa,inda ya tura ?ofar Wakin ya shiga,kasancewar wutar Win Wakin a kashe yake ya sanya ya nufi wajen makunnar wutar ya kunna, tabbas da Anwar ya san abun da zai yi tozali da shi idan ya kunna wutar da bai fara kunnawa ba, lokacin da haske ya gama gauraye illahirin Wakin ne ya juya da niyyar nufar wajen gadon shi. Turus! Ya ja ya tsaya sakamakon arba da mace da yayi a zaune a tsakiyar gadon shi ta juya mishi baya kanta ba Wankwale gaba Waya gashin ta ya barbazu a kan gadon, wani mugun tsoro ne ya mamaye zuciyar Anwar Win har sai da ya haWiyi wani yawu ji kake Mu?uttt wucewar yawun zuwa ma?oshin shi, a hankali ya fara takawa ya nufi wajen gadon duk da irin bugun da zuciyar shi ta ke mishi hakan ba sai ya dakata da isa wajen gadon ba,hannu ya mi?a da niyyar juyo da fuskar ta ta sai dai tun kafin hannun nashi ya sau?a a jikin ta ta juyo da kanta suka yi arba da juna fuskarta shaSe-shaSe da hawaye sai dai kuma a maimakon ya ga ruwan hawaye sai ya ga jini ne yake kwaranyowa daga cikin idanun nata, suman tsaye Anwar yayi cikin rawar murya ya fara nuna ta da hannun shi yana ?o?arin furta sunan ta Amr..... Amma ina! Tun kafin ya ?arasa yaji kamar an saka igiya an Waure mishi wuya take ya yanki jiki ya faWi a wajen.

Anwar bai tashi tsintar kan shi a ko ina ba sai a gadon asibiti ana mishi ?arin ruwa, ?o?arin mi?ewa zaune yake amma ya kasa a hankali ya fara ?o?arin tuno abun da ya faru dashi amma abun mamaki hakan ya gagara duk wani ?o?arin sa na ganin ya tuno abun da ya faru Win ya kasa inda take ya ji kan shi ya Wauki wani matsanancin ciwo,dafe kan nashi yayi tare da runtse idanun shi, mahaifiyar shi ce ta fara mishi sannu.

"Sannu Anwar ka tashi ya jikin dai?". Ta jefa mishi wannan tambayar da sauri yayi saurin buWe idanun shi da suke a runtse dan ganin wanda yake mishi sannun domin kuwa a maimakon ya ji muryar mahaifiyar shi sai ya ji wata murya daban wadda ko shekara Wari yayi wannan muryar bazata taSa zama sabuwa ko ba?uwa a gare shi ba,ga mamakin shi yana buWe idon nashi sai yaga mahaifiyar tashi ce take mishi sannu, Innalillahi wa'innailaihi rajiun ya shiga maimaitawa a cikin ran shi tare da jefawa kan shi tambayar to mai hakan yake nufi?, Mai yasa muryar ta take mishi gizo?. A hankali ya fara jin alamar kuka a kusa dashi saurin juyawa yayi dan ganin waye aikuwa a take yayi arba da ita a zaune a kusa dashi fuskar ta sharkaf da hawaye, wani ras ya ji gaban shi ya faWi,da sauri ya juya ya dubi inda mahaifiyar shi take zaune ko ita ma taga abun da ya gani Win,sai dai daga yanayin fuskarta ya fuskanci cewa bata ga abun da ya gani Win ba,sake juyawa yayi inda take zaune Win still tana zaune sai dai a wannan karon murmushi take mishi, addu'a ya fara yi duk addu'ar da tazo bakin shi, aikuwa ba'a Wauki lokaci ba ya nemeta ya rasa, kallon mahaifiyar shi yayi sannan ya buWi baki da niyyar sannar da ita abun da ya faru Win sai dai kamar mai cutar mantau haka yaji komai ya kuma shafewa a ?wa?walwar shi.

*****

*AHMADU BELLO* *UNIVERSITY ZARIA*

Babbar jami'a ce da ta amsa sunan ta jami'a domin kuwa tana Waya daga cikin manyan jami'o'in da muke da su a Nigeria,ko ina ka waiga a cikin jami'ar Walibai ne ta ko ina kowa yana harkar gaban shi. Wata matashiyar budurwa na hango wadda a ?alla bazata haura shekaru ashirin da biyu zuwa da uku haka,tafe take a cikin makarantar ta fito daga wajen Admin Block inda ta nufi hanyar hostel Win mata, fuskarta kaWai zaka kalla ka fuskanci tsananin farin cikin da take ciki,wayar ta ce ta fara kuka alamar tana neman agaji,Waukan wayar tayi murmushi shimfiWe a kan fuskar ta sannan ta kara wayar a kunne tare da furta.

"Dad barka da rana"

Daga Wayan Sangaren wani dattijon mutum ne zaune a wani ?ayattaccen falo wanda ya gaji da haWuwa amsawa yayi tare da furta.

"Daughter ya result domin kuwa idan ban manta ba yau kika ce zasu manna muku?".

Murmushi tayi kafin daga bisani tace.

"Dad as usual Kai ma kasan ai bazan taSa baka kunya ba,Dad result Wina yafi na kowa kyau na kasance wadda tafi kowa highest mark a Depertment Win namu".

"Masha Allah Daughter congratulations Ubangiji ya cigaba da dafa miki,ya sanyawa karatun ki Albarka".

Da Ameen ta amsa sannan suka yi sallama ta kashe wayar, a dai-dai sannan kuma ta ?araso bakin Wakin su,inda ta sanya mukuli ta buWe ?ofar,ChaSal taji ta jefa ?afarta a cikin wani abu mai yau?i, cikin sauri ta kai duban ta kan ?afarta da take ?o?arin zarewa daga cikin abun, Daramm gaban ta ya faWi sakamakon arba da jini da tayi male-male a tsakiyar Wakin nasu kamar an yanka rago,jikin ta ne ya fara wani irin karkarwa take wata irin zuffa ta fara keto mata, ai bata gama shiga ruWani ba taga wannan jinin ya fara dun?ulewa waje guda a hankali har ya gama curewa waje Waya sai gashi ya fara komawa siffar mutum, wata irin mummunar hallita ce ta bayyana a gabanta idon hallitar guda Waya ne kuma a tsakiyar ka,sai wasu ?afo masu matu?ar tsini guda biyu da suke gefen idon, tsayin hallitar kuwa ba zai faWu ba domin kuwa tsayin ta har ya tokare silik Win Wakin, lokaci guda kuma fuskar wannan hallitar ta juye zuwa fuskar Amrah. Ido ta zaro waje take kuma ta buWe baki da niyyar yin ihu sai dai kafin ta kai ga sakin ihun taji wata irin guguwa ta kwashe ta inda ta jita a sama tana gudu kamar wani jirgi,da ?o?arin da take na ganin ta buWi baki tayi ihu ko zata samu mai kawo mata agaji hakan ya faskara inda aka shiga gwara mata kai a kowane kusurwa na cikin Wakin,take aka haWa mata jini da majina,sai da ta suma ta farfaWo saboda azaba kafin daga bisani aka yi jifa da ita ta bugu da jikin ?ofar toilet Win Wakin,sannan aka shiga ?iran sunan ta da wasu irin muryoyi mabanbanta.

"Azraaaaaa?a!,Azraaaaaa!, Azraaaaaa! yau zaki girbi abun da kika shuka,yau zan Wauki Fansar abun da kuka aikata mun, FANSA! FANSA!FANSA! Na dawo Wauka". Ana kaiwa nan a maganar aka bushe da wata irin dariya mai haWe da kuka wadda tayi sanadiyar Sumewar Azraa.

*MANGA*
'?
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ &?=؀?).

_Tsarawa/Rubutawa_

? *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* .

*SADAUKARWA*: _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam_ _Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke_ _ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

----------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*003*
__________________________

Sau?ar ruwan sanyin da taji a jikin ta ne ya sata farfaWo wa daga sumar da tayi Win,a hankali ta shiga buWe idanun ta wani irin haske ne mai ?arfi da ta gani ya sanyata saurin mayar da idonta ta sake rufewa,?arar takun tafiya ta dinga ji wanda sautin tafiyar yake bayar da ?arar tafiyar dawakai,?irjin ta ne ya shiga dakan lugude zuciyarta kamar zata fito saboda tsananin tsoro da firgicin da take ciki.

Da ?yar Azra ta iya ?arfin halin sake gwada buWe idanun inda take ta tsinci kanta a wani wawaken fili a tsakiyar dokar daji ba gida gaba bare baya.

?o?arin mi?awa ta fara yi domin guduwa, Sai dai ta kasa sakamakon wata irin sar?a (ankwa) da aka sanya aka Waure ta da ita,kiciniyar kunce kanta ta fara amma ina kamar ma wanda take ?ara Waure wannan sar?ar a jikin ta gashi har a wannan lokacin bata daina jin ?arar sautin tafiyar dawakan ba.

Kamar wadda aka ce Waga kan ki sama aikuwa ta hango mace daga nesa cikin shigar ba?a?en kaya ta nufo inda take, tun daga yanayin tafiyar matar ta gane wacece, numfashin ta ne taji yana barazanar Waukewa sakamako arba da fuskar wadda ko ta mutu ta dawo ba zata kasa gane ta ba, ?o?arin magana ta fara yi amma kamar wanda aka sanya abu aka sha?e mata ma?oshi haka ta kasa furta ko da kalma Waya, wasu hawayen azaba ne da nadama suka shiga kwaranyowa ta kumatun ta.

Murmushi mai haWe da kuka Amra ta fara sakarwa Azra har ta iso dai-dai wajen da Azra Win take Waure sannan ta sanya hannun ta Wago fuskarta tare da fara magana.

"Azra har yanzu banga alamar tsoro ko danasani a tare da ke ba?, Azra nasan fuskata ba zata taSa zama ba?uwa a wajen ki ba".

Sai a sannan Azra taji an sake mata ma?oshi inda ta fara magana cikin rawar murya.

"Amrah daman baki mutu ba? Amrah wallahi nayi nadama, Amra dan Allah kar ki kashe ni, Amrah wallahi ban shiryawa mutuwa a yanzu ba".

Wata irin dariya mai sauti Amra ta sake wadda har sanda gaba Waya dajin ya amsa kafin kuma daga bisani ta haWe fuska kamar ba ita tayi dariyar ba sannan take ta rikiWe ta koma wata irin shirgegiyar hallita ba daWin kallo, sannan ta fara magana cikin wata iriyar murya marar daWin ji da sauraro.

"Azra tabbas zaki mutu kuma a yau ba sai gobe ba,tabbas zaki yi mutuwa marar daWin kallo,tabbas zaki wula?antacciyar mutuwa, Azra mutuwar ki zata zama mutuwa mafi muni daga cikin mutuwar da Five Stars zasu yi, oh I mean Four star's domin kuwa ni bana cikin ku, na daWe da cire ku a cikin abokanai na, Azara mutuwar ki sai ta hargitsa duk wani mutum da yake numfashi a doron ?asa domin kuwa sai na yagalgala ki yadda ko gawar ki da ?yar za'a iya ganewa,hatta ?an jarida sai sun ji tsoro da shayin yaWa gawar ki saboda tsananin munin da gawar ta ki zata yi, zaki yi mutuwar wula?anci fiye da wadda Afrah tayi domin kuwa tata mutuwar Nafila ce idan har aka ga taki,Hmmm Azra ai ko zan yafewa kowa ban da ke, Azra kin manta cewar kece ummul aba'isin duk wata cutarwa da aka mun, ki sani tun ina yarinya na yadda da wannan karin maganar ta hausawa wadda ake cewa Rama cuta ga macuci ibada ne".

Da sauri Azra ta Wago ta kalli Amra sannan tace.

"Amrah wai kina nufin ke kika kashe Afrah?".

"?warai kuwa nice ko kina tantama ne".

BuWe baki Azra tayi da niyyar yin magana sai dai wata sha?a da azra ta mata ya sanya ta kasa furta komai,kamar yadda Amra ta cakawa Afrah farce a ido lokacin da zata kashe ta haka yanzu ma ta aikatawa Azra,wani mugun ihu Azra ta sake sannan daga haka bata ?ara sanin abun da ya faru da ita ba sakamakon Waukewar da numfashin ta yayi, Amrah hannu ta sanya ta tsaga wuyan Azra Win inda ta ciro ma?oshin ta, daga haka ta dinga bin duk wani sassan jiki na Azra wanda yake guda biyu ne ta dinga cire guda Waya sai da ta gama da wannan kafin kuma ta zo ta cire mata gaba Waya kayan jikin ta ta Wauke ta a bayan ta suka Sace daga cikin dajin a lokacin Azra ta daWe da she?awa barzahu.

Kai tsaye Amrah tsakiyar cikin jami'ar Ahmadu Bello University ta wuce da gawar Azra ta yasar da ita a tsakiyar makarantar yadda kowane Walibi zai ganta gata tsirara haihuwar uwar ta, kasancewar lokacin ?arfe biyu na dare filin makarantar tsit shiyasa ba wanda ya san abun da ya faru.

*****

A can Hostel Win su Azra kuwa ?awayen ta Amira da Anisa ne suka shigo cikin Wakin inda basu tarar da Azra ba, basu kawo komai a ran su ba suka ci gaba da harkokin gaban su, inda suka yi tunanin ko tana Library ne.

Amira ce ta juya ta dubi inda Anisa take kwance hannun ta ri?e da littafi sannan tace.

"Ke Ani nifa na fara tsorata da rashin dawowar Azra, ko ta faWa miki inda zata je ne?".

Rufe littafin hannun ta Anisa tayi sannan ta dubi Amira tace.

"Wallahi nima kawai dai nayi shiru ne amma tun Wazu gaba na sai faWuwa yake, amma bari mu ga zuwa anjima idan bata dawo ba sai muje mu duba ta ko a Library Win ne".

"Ok to shikennan Allah dai ya sa lafiya ni kam".

Da Ameen Anisa ta amsa sannan ta koma ta kwanta.

Sai dai abu kamar wasa sai gashi har zuwa ?arfe goma na dare ba Azra ba labarin ta,tun hankalin su baya tashi har ya kai sun fara shiga damuwa,inda suka fara tambayar Wakunnan da suke kusa da nasu ko da wanda ya san inda Azra Win taje amma kowa sai yace bai ganta ba.

Library suka nufa suka duba amma nan ma bata nan, duk wani waje da suke tsammanin zasu ga Azra Win basu gan ta ba,gashi sun ?ira wayar ta sai ringing take ba'a Waga ba.

Abun da ya ?ara sanya hankalin su tashi shine duk inda Azra zata je bata wuce ?arfe sha Waya na dara zata dawo, sai gashi yau har sha Waya da rabi babu ita ba alamar ta.

Haka suka kama hanya suka juya suka koma Hostel zuciyoyin su cike da zulumi, suna shiga Wakin Anisa ta fara cin karo da wayar Azra a yashe a gefe,sunkuyawa tayi ta Wauki wayar gaban ta yana cigaba da bugawa sannan ta juya ta kalli Amira tace.

"Tabbas ba lafiya ba, tabbas na yadda wani abu ya faru da Azra domin kuwa ni na tabbata Azra ba zata taSa fita ta bar wayar ta ba, duba da yadda Azra take da waya ko toilet bata yadda ta shiga ba tare da ita ba".

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun, to mai yake shirin faruwa haka?" Amira ta faWa ita ma cikin tashi??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n hankali.

"Nifa wallahi daman tun ranar da aka ce an kashe Afrah jikina ya fara yin sanyi, ya Ubangiji kasa ba wani abu bane ya faru da Azra". Cewar Amira Win tana zama a bakin gado tare da dafe kan ta.

"Ameen ya Allah Amira yanzu mu bari zuwa safiya sai muje muyi repoting a School management domin a san matakin Wauka tun kafin wani abu ya faru, tun da kinga yanzu past twelve Kinga dare yayi ko".

Ita dai Amira bata iya cewa komai ba sai juyawa da tayi ta kwanta tana jin zuciyarta kamar zata fito saboda tsoro fa tashin hankali da kuma firgicin da take ciki Win.

Haka dai su Anisa da Amira suka kwana cikin taraddaddi, ba wanda ya iya wani isasshen bacci a cikin su.

*****

Yau tun asubar fari jami'ar Ahmadu Bello Win aka tashi da wani mummunan tashin hankali wanda ya gigita duk wani mazaunin cikin makarantar,domin kuwa wannan sabon abu ne a tarihin makarantar shine tsintar gawar Azraa da aka yi cikin mummunan yanayi.

Filin makarantar tunin ya fara cika da Walibai inda duk wanda yayi arba da gawar Azra Win sai ya zubar mata da hawaye, mata kuwa take wasu masu raunin zuciyar suka dinga zubewa a wajen domin kuwa kallo Waya zaka yiwa gawar ta ta kaji a ranka baka sha'awar sake ganin ta.

Da gudu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login