Showing 9001 words to 12000 words out of 70370 words

Chapter 4 - FANSAR FATALWA complete hausa novel

26 Oct 2025

98

labari mai daWi game da matata, likita dan Allah ka cemun matata ta farka".

Duk a lokaci guda Justice Kabir ya jefawa Likitan waWannan tambayoyin.

Zare glass Win shi likitan yayi sannan ya dubi Justice Kabir cikin tsananin tausayawa kafin yace.

"Justice Kabir sai dai ha?uri Allahn da ya baka ita ya karSi abin shi".

Saurin ri?o hannun shi Justice Kabir Win yayi yana zaro ido waje kamar zasu faWo ?asa sannan yace.

"Likita bangane ba?, Mai kake shirin faWa mun?".

"Justice Kabir Allah ya yiwa matar ka rasuwa kasan duk wani mai rai mamaci ne ba wanda ya zo duniya domin yayi gadin ta dan haka ay........".

Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da mutanen wajen suka fara faWa cikin tsananin tausayin halin da Justice Kabir Win zai shiga.

Sai a wannan lokacin inspector Rasheed ya Wan ji wani tausayin Justice Kabir Win ya kama shi.

Tabbas tsayawa faWin irin tashin hankalin da Justice Kabir ya shiga Sata lokaci ne domin kuwa a take ya fara wasu irin surutai marrassa kan gado wasu ma saSo kawai yake dan?arawa.

Mutanen wajen ne suka kama shi ganin abun nashi yana neman wuce gona da iri sannan aka nufi motar shi da shi, inda wasu kuma suka je suka Wakko gawar Hajiya Ikilima aka sanya ta a mota domin a je a mata sutura.

Tabbas duk wani mai zuciyar imani sai ya tausayawa halin da Justice Kabir Win ya shiga domin kuwa zan iya cewa shima mutuwar ne kawai bai yi ba. Mutane da yawa sun mishi uzuri domin kuwa mutuwar da aka mishi mutuwa ce dai sai mai ?arfin imani ne zai iya tawakkali,ga ?a ga mata duk a kwance ba rai.

Su kuwa wasu daga cikin talakawan da suka san halin shi musamman ma'aikatan da suke ?ar?ashin shi take su ka rin?a Allah ya ?ara duba da yadda daman ba wani kyautata mu su yake ba. Shiyasa a rayuwa duk abun da zaka aikata ka zama ka aikata mai kyau ko dan gudun goben ka. Allah ka kar ka sanya mu daga cikin masu wula?anta na ?asa damu Ameen.

An je an sallaci Hajiya Ikilima inda aka dangana ta da gidan ta na gaskiya.

Har aka je aka kai Hajiya Ikilima Justice Kabir bai bar surutai ba, domin kuwa wasu ma cewa suke ?wa?walwar shi ta taSu.

*****

A can asibitin da aka kai su Anisa da Amira kuwa sai da suka kwana suka yini ba tare da sun san duniyar da suke ba.

A hankali Anisa ta fara buWe idanunta da suka mata nauyi tare da jin kan ta kamar zai rabe gida biyu saboda yadda yake mata ciwo.

Wata irin faWuwa gaban ta yayi sakamakon jin abu kamar ruwa ya Wiso mata a fuska.

Hannu ta sanya ta gogo wajen da taji Wisar abun, innalillahi wa'innailaihi rajiun mai Anisa zata gani! Jini ta gani a hannun nata.

Saitin wajen da abun ya zubo mata tabi da kallo duk da irin matsanancin faWuwar gaban da take ji.

Jini ta gani yana biyowa ta jikin silin Win Wakin da suke kwance Win.

Gaba Waya saitin wajen da take kwance Win jini ne yake Sullowa har ya bada shape Win Star, kafin kuma ya fara Wisowa Wis Wis Wis akan fuskar ta.

Jikin Anisa idan ban da rawa ba abun da yake yi, wani gigitaccen ihu ta sake wanda ya sanya ma'aikatan asibitin saurin shigowa cikin Wakin da gudu hankali tashe.

Suna shigowa suka ganta kwance a gadon illahirin jikinta idan banda rawa ba abun da yake ga jini da suka gani a fuskar ta kamar an mata feshi.

Hannun ta ta Waga tana ?o?arin nuna musu sama sai kuma ta tafi luuuu ta sume.


*****

A Sangaren Anwar kuwa tun da ya ji labarin mutuwar Azra hankalin shi ya ?ara tashi, take mutuwar Afrah da ta fara bin jikin shi ta sake dawo mishi sabuwa.

Gashi kullum sai Amrah ta zo mishi watarana a fili watarana a cikin bacci, sannan kullum cikin kuka taka zuwar mishi ya rasa dalilin hakan.

Duk ranar da tazo mishi a farke ba'a bacci ba to sai ya suma idan ya farfaWo kuma to a take zai manta duk wani abu da ya faru Win.

Idan kuwa a mafarki ta zo mishi to idan ya farka yana iya tunawa da mafarkin sai dai bai taSa yun?urin sanarwa wani ba, shidai kullum cikin addu'a yake.

Yau ma kamar kullum kwance yake akan gadon shi yana bacci lokacin ?arfe Waya na dare ne.

Mafarki ya fara yi wai gashi a wani ?atoton fili inda ba gida gaba bare baya.

Wata iska ce take kaWawa ?arar ta mai cike da abun tsoro, suuuuuiii ka ke jin ta tana wucewa.

A can nesa dashi ya hango ta zaune a ?asa ta haWa kan ta da gwaiwa.

Sannu bisa hankali ya fara tafiya har ya ?arasa inda take Win.

Isar shi wajen yayi dai-dai da Wago kan ta, tare da kafe shi da ido. Murmushi ta fara mishi kafin kuma daga bisani ta fashe da wani irin kuka mai sauti.

A maimakon ya ga hawaye yana fitowa a idanun ta sai ya ga jini hadda guda-guda suna fitowa daga cikin idanun nata.

"Amrah!".

Ya ?ira sunan ta cikin tsananin ruWani.

"Anwar sun cuce ni!, Anwar sun kashe ni da rai na!, Anwar shin zaka ga laifi na dan na dawo Waukar fansa".

Shikam tun da Amrah ta fara magana ya kasa fahimtar inda maganar tata ta dosa, buWe baki yayi da niyyar tambayar ta su waye suka cuce ta Win sai dai kuma take ya fara ganin ?asar wajen da Amrah Win take zaune ta fara zaizayewa, a hankali sai ga wani rami ya bayyana a wajen take kuma Amrah ta shige cikin ramin, shigewar ta keda wuya ?asar wajen ta koma tare da haWe kan ta.

A dai-dai wannan lokacin kuma Anwar ya farka daga wannan mafarkin da yake gaba Waya jikin shi ya ji?e sharkkaf da gumi.

Mi?ewa yayi zaune cike da Wumbin mamakin wannan mafarkin da yayi Win.

Shin mai yake shirin faruwa ne dashi?, Shin mai yasa Amrah take yawan zuwar mishi a cikin bacci?, Shin su waye suka cuce ta haka har take i?irarin Waukar fansa.

Ganin bashi da amsar tambayar tashi ko Waya ne ya sanya ya tashi tsaye tare da shigewa toilet ya Wauro alawla sannan ya fito.

Sallah ya zo ya tayar kafin kuma daga bisani bayan ya idar ya Waga hannun shi ya fara addu'a, sai da ya yiwa Afrah addu'a sosai kafin kuma daga bisani ya tashi ya koma ya kwanta zuciyar shi cike da zulumi.

*MANGA*
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_=؀? &?)

_Tsarawa/Rubutawa_

? *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

-------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*006*
____________________________

Yau kwanan su Anisa da Amira uku a gadon asibiti kuma a yau ne likita ya sallame su suka koma Hostel.

Sai dai har zuwa yanzu mutuwar Azra tana nan a cikin zukatan su ta kasa goguwa duk da kuwa mutuwar daman ba wani lokaci ta Wauka ba.

A cikin kwana biyu Win da suka yi a asibiti babu wani abun tsoro da ya sake razana Anisa Win tun na ranar da taga wannan jinin, sai dai kuma kullum zuciyarta cike take da fargaba da tsoro. Gashi sai tayi niyyar sanarwar da Amira abun da ya faru ranar can Win sai taji bakin ta kamar an sanya zare an ?ulle shi.

Komawar su Hostel Win da kwana biyu aka kafe musu time table Win exam wanda hakan ya sanya Suka du?ufa wajen karatu ba kama hannun yaro.

Rana bata ?arya sai dai uwar Wiya taji kunya,kamar yadda aka kafewa su Anisa circular Win exam Win to yau ta kama ita ce ranar da zasu fara exam.

Babban abun da yafi Waurewa Anisa kai kuma ya tsorata ta,bai wuce karatu da idan sun yi tana shiga Wakin jarrabawa zata ji ta nemi komai ta rasa kamar ma ba'a taSa koya mata ba.

Wannan abun ba ?aramin tsorata ta yake ba domin kuwa tun tana ganin abun kamar wasa har ta zo ta fara tsorata da lamarin.

Yau ma kamar kullum zaune suke ita da Amira suna karatu, Wago kai Anisa tayi ta kalli Amira sannan tace.

"Amira nikam akwai wani abu da yake Waure mun kai wanda na rasa yadda zan yi".

Ajiye littafin hannun ta Amira tayi sannan tace

"Anisa wannan wane abu ne haka?, kar ki manta lokacin da muke, wannan lokacin ba lokacin da zaki na sanya abu a ranki bane domin kuwa kin fi kowa sanin cewa daga wannan jarrabawar da muke rubutawa sai ta kammalla makarantar mu".

Ajiyar zuciya Anisa ta sau?e sannan tace

"Hmmm Amira kennan!, wallahi a wannan halin da nake ciki jarrabawar ma ba lalle na ci ba, domin kuwa kullum da kike ganina ina karatu ne kawai amma da zarar na shiga Wakin jarrabawa komai yake ?wace mun na rasa mainene dalili".

Anisa ta ?arashe maganar kamar zata yi kuka.

"Subhannallah Anisa mai nake jin kina faWa haka!, dan Allah ki bar wannan maganar ma yanzu ba wasa ne ya kamace mu ba".

Amira ta faWa tana kawar da kai gefe domin kuwa duk a tunanin ta Anisa kawai wasa take mata kasancewar ta san wacece Anisa a kaf cikin ?awayen su tafi kowa nacin karatu, idan har za'a yi exam to ba wanda yake finta ci daga Azra sai ita sune ?warin mate Win nasu wanda kowa ya san ?o?arin na su duk da kuwa ita ma Amira ba baya ba wajen ?o?ari.

"Amira kennan kina Waukan wannan lamarin kamar wasa ko?,wallahi ba wasa nake miki ba amma koma mainene result zai nuna"

Ta faWa tana mai mi?ewa ta shige toilet ganin duk irin bayanin da zata mata ba yadda zata yi ba.

Yau ita ce ranar ?arashe ta jarrabawar su zaune suke a exam hall Win hankalin kowa yana kan amsa tambayar da take rubuce a jikin question paper Win shi amma banda Anisa wadda take zaune in banda juya biro ba abun da take.

A hankali taji wata murya wadda har duniya ta naWe ba zata taSa mantawa da wannan muryar ba tana ?iran sunan ta cikin murya mai firgitar wa.

"Anisaaaaaa! Anisaaaaaa! Anisaaaaaa!"

Da sauri ta Wago kanta tare da bin wajen da take jin ana ?iran sunan nata da kallo sai dai tana kai kallon ta wajen taga fitar ta waje.

Kamar wadda aka tsikara da allura haka taji gaba Waya zaman hall Win ya gagareta inda kuma ta wani Sangaren taji ba abun da take so kamar ta fita tabi bayan ta.

Mi?ewa tsaye tayi sannan ta fice daga cikin hall Win inda ba wanda ya lura da fitar ta ta.

Wata hanya daban taga Amrah ta bi inda hanyar jeji ne.

A hankali Anisa ta shiga bin ta domin kuwa da ta tsaya sai taji jikin ta kamar ana watsa mata ruwan zafi.

Haka ta dinga binta har suka ?urewa ganin mutanen.

Anisa bata ankara ba sai ganin su tayi a wani ?asungurmin daji mai cike da wasu irin bishiyoyi masu duhu da raishen su kamar zai taSo sararin samaniya saboda tsawo.

Waige-waige Anisa ta fara domin kuwa shigowar su jejin keda wuya ta nemi Amra sama ko ?asa ta rasa.

*****

A Sangaren Inspector Rasheed kuwa sosai ya du?ufa wajen bincike domin gano makashin su Afra da Azra Win.

Sai dai har zuwa yanzu ba wata ?wa?warar shaida da ya samu wadda zata taimaka mishi wajen gano wanda yake aikata kisan.

Zaune yake a cikin office Win shi yana ?an rubuce-rubuce, haka kawai jefi-jefi sai ya saki tsaki sakamakon ji da yayi kwata-kwata baya son yin aikin yau Win.

Tashi yayi daga kan kujerar sa sannan ya fita bakin kanta inda ya tarar da su kofur Bala a zaune.

Duban shi ya kai wajen Kofur Bala Win sannan yace.

"Kofur Bala a fito da mota zamu je asibiti da gidan Justice Kabir da kuma gidan su marigayiya Afrah".

Sara mishi Kofur Bala yayi sannan yace.

"Ok Sir".

Motar aka fito mishi da ita inda suka shiga suka nufi asibitin da gawarwakin su Afrah suke.

Sai dai rashin sani yafi dare duhu domin kuwa inda Inspector Rasheed ya san irin aikin da zai ?ara rattaSowa kan shi da bai je asibitin ba.

Lokacin da suka isa asibitin kai tsaye suka wuce Wakin adana gawarwakin.

Kasancewar ma'aikatan wajen sun san shi yasa basu hana shi shiga ba.

Suna shiga cikin Wakin ya bu?aci da a janyo akwatin gawar da Afrah take ciki.

Abun mamaki da Waure kai ana janyo akwatin suka tarar da akwatin wayam kamar ba'a taSa ajiyar gawa a ciki ba.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da Inspector Rasheed ya shiga maimaitawa duk kuwa da cewar bai tabbatar da hassasshen nashi ba.

Gaba Waya suma mutanen da suke wajen take mamaki da ruWani ya ziyarci fuskokin su a lokaci guda.

Kofur Bala kuwa ji yayi kamar ace mishi ?it ya fice a guje domin kuwa shi daman wallahi tun farko ba san wannan Case Win yake ba.

Saurin kallon ma'aikatan wajen Inspector Rasheed yayi hankalin shi a matu?ar tashe sannan yace.

"Mai nake kallo haka?, Ina gawar cikin akwatin nan take?".

Ya faWa fuska ba annuri.

"Ranka ya daWe ai wannan lamari sai dai mu tambayi juna domin kuwa wallahi ban san amsar da zan baka ba".

?aya daga cikin ma'aikatan Mutuary Win ya faWa.

"Wannan wane irin zancen banza ne kake son gayamun alhalin kune masu gadin Wakin, idan ban tambaye ku ba wa ku ke so na tambaya?"

Inspector Rasheed ya faWa cikin tsawa.

Gaba Waya wajen shiru ya Wauka,domin kuwa wannan ba?on al'amari ne kuma sabon abu a wajen mutanen asibitin baki Waya, duba da cewar wannan shine karo na farko tun daga lokacin da aka kafa asibitin da aka taSa neman gawa aka rasa a cikin Wakin.

"A fito da akwatin Waya gawar".

Suka tsinkayi muryar Inspector Rasheed ya faWa fuska ba fara'a.

Su kam ma'aikatan wajen duk jikin su yayi sanyi aka rasa wanda zai iya tunkarar akwatin da Azra Win take ciki balle a buWe shi.

Kallon su Inspector Rasheed yayi sannan yace.

"Wai ko baku ji abun da na faWa bane?".

A hankali Waya daga cikin su ya nufi akwatin da aka sanya Azra Win a ciki ?irjin shi sai bugawa yake, mi?a hannun shi da yake rawa yayi ya janyo akwatin sannan ya buWe.

BuWe akwatin da Azra Win take ciki keda wuya mutanen wajen suka shiga tashin hankali fiye da na farko sakamakon tozali da akwatin Azra Win da suka yi shima wayam sai wasu irin ?ananan tsutsotsi ne suke shawagi a ciki.

A wannan lokacin da zaka tsaga jikin rabin mutanen wajen to ba zaka tarar da jini ba Saboda yadda suka shiga matsanancin tsoro.

Nan fa aka shiga kallon-kallo a tsakanin mutanen wajen domin kuwa lamarin a yanzu ya daina basu mamaki sai tsananin tsoro.

Duk wanda ka kalla a wajen tsoro ne zaka gani ya bayyana ?arara akan fuskokin su, idan ka ware Inspector Rasheed kaWai wanda ya shiga bin akwatunan da kallo Waya bayan Waya kamar mai nazarin wani abu.

Umarni ya bayar da a buWe wani akwatin gawar.

Da sauri ?an wajen suka kalli juna cikin tsananin tashin hankali,kafin daga bisani wani daga cikin su yayi ?arfin halin janyo wani akwati da yake kusa da akwatin Azra.

Sai dai a wannan karon akwatin da aka buWe Win gawar tana nan lafiya a kwance a cikin akwatin ba alamar wani ba?on abu a tattare da ita.

Shiru wajen ya Wauka baka jin motsin komai sai ?arara sau?ar numfarfashin su wanda yake nuni da alamar ruWani da tashin hankalin da suke ciki.

Can dai inspector Rasheed ya Wago idon shi da suka yi jawur ya buWi baki da niyyar yin magana sai kuma ya fasa ya fice domin kuwa a yadda yake j???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?in zuciyarshi tana mishi idan yace zai yi magana za'a samu matsala.

Yana fita daga cikin Wakin adana gawar kai tsaye office Win shugaban asibitin ya nufa domin kuwa wannan lamari ne da dole a san matakin Wauka tun da wuri.

*****

Haka Anisa ta shiga kai komo a cikin wannan daji mai cike da abun tsoro, ita kam a yanzu ta sadda?ar da cewar mutuwa zata yi wani irin matsanancin tsoro ne ya rufe ta sakamakon tozali da wata bishiya da tayi kaman tana mata dariya.

Bata gama shiga tashin hankali ba sai da ta tabbatar da cewa da gaske fa bishiyar dariya take mata.

Jikin ta ne ya shiga wata irin karkarwa kamar mazari take kuma ta fara jin sautin dariya ta ko ina a cikin dajin yana amsa kowa.

?aga idon da zata yi kawai tayi arba da gaba Waya bishiyoyin cikin dajin suna mata dariya, daga baya kuma kawai taga sun fashe da kuka har da hawaye.

Ai Anisa na ganin haka bata san sanda ta dur?ushe a wajen ba ta shiga rusa ihu tana neman agaji, sai dai ina babu mai jin ta balle a kawo mata taimako.

FaWowar abu da taji a kusa da ita ne ya sanyata saurin Wago kai tare da ja da baya.

Mai zata gani in ba gawar Anisa da Azra ba kwance a gefen ta wasu tsutsotsi suna biyowa ta tsakanin idanun su.

Wani gigitaccen ihu Anisa ta sake sannan ta zube a wajen sumammiya.

Tsananin zafin ranar da ake ne ya buge ta wanda yayi sanadiyar farfaWowar ta.

Idanunta take ?o?arin buWewa dan taga hasken duniya, sai dai mai duhu ta gani a maimakon taga haske.

Gaban ta ne ya faWi inda cikin sauri ta sanya hannu ta shafo idanun nata sai dai wayam taji gurbin idon nata a shafe kamar ba'a taSa hallitar ido a wajen ba.

BuWe baki tayi da niyyar yin ihu amma kuma muryar tata ta katsea sakamakon dariyar da taji a gefen ta da kuma kuka a lokaci guda suna tashi.

"Dan Allah wacece ke?, Dan Allah mai ya sami idona?,Mai na miki kike son ganin bayana?".

Duk a lokaci guda Anisa ta jefamata waWannan tambayoyin.

A maimakon taji an bata amsa sai taji an cigaba da SaSSaka dariyar da kuma kukan har dajin sai da ya ringa amsawa.

Ita kam Anisa zuwa wannan lokacin ta cire rai da sake rayuwa, take kuma duk wani tsoro ya gushe mata zuciyarta ta bushe cikin ?araji tace.

"Mai kuke jira da nine da ba zaku kashe ni ba?, Ku kashe ni nace tun da kun raba ni da abu mafi muhimmanci a rayuwata".

Anisa ta ?arashe maganar cikin sakin kuka mai tsuma rai.

"Anisa mai kike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login