Showing 63001 words to 66000 words out of 70370 words

Chapter 22 - FANSAR FATALWA complete hausa novel

26 Oct 2025

101

da wani irin kuka mai taSa zuciya ba duba da yadda aka famo mata ciwon da yake zuciyarta wanda ya kasance Wanye bai gama warkewa ba.

"Dan Allah alfarmar da nake nema a wajen ku shine ku taimaka ku yafewa ?ata abin da ta aikata wa ?ar ku saboda ba ita kaWai ta cutar ta sanya a cikin matsala ba harda ku ma ta Wauki ha??in ku,amma dan girman Allah ta ci albarkaci na ku yafe mata. Na sani cewar abin da wahala sosai domin kuwa ko kun ce ba zaku yafewa Azrah ba ba zan taSa ganin laifin ku ba dalili kuwa shine an cutar da ku an muku tabon da ba zaku taSa mantawa dashi ba sannan Azrah bata cancanci yafiya ko tausayawa daga gare ku ba,amma ku yi ha?uri ba dan halin ta ba ba kuma dan ni ba dan Allah nake neman wannan alfarmar a wajen ku".

Justice Kabir ya faWa yana haWe hannayen shi waje guda alamar neman afuwa tare da Sunkuyar da kai ?asa.

Wani irin kallo Umar ya watsawa Justice Kabir wanda na kasa fahimtar na menene kafin daga bisani yace.

"Kai ko kunyar haWa ido da mu baka yi ba da sunan kana nemawa azzalumar ?arka yafiya?, Kar ka manta irin cin amanar da ?arka ta aikatawa Amrah wadda ko a lokacin jahiliyya sai an tona kafin a samu wanda zai iya aikata abin da ?arka ta aikata. A sanadiyyar ?arka muka rasa ?ar uwar mu mafi soyuwa a gare mu!, A dalilin ?ar ka muka zo mu ka rasa Wan uwan mu wanda mu ke so!, A dalilin ?ar ka mu ka rasa martaba, ?ima, mutunci da duk wata daraja da mahaifin mu yake da ita har ta kai ta kawo mun yi nisa da garin da mu ke so mu ke jin daWin zama a cikin shi,lokaci guda masoyan mu suka rikiWe suka koma ma?iyan mu duk ta dalilin ?ar ka, ta ya kake tunanin zamu manta da wannan azzalumar? ta ya ka ke tunanin zamu iya yafewa wadda ta cutar da mu tare da sanya mu a cikin irin waWannan matsalolin dana ambata?, To bari kaji har abada idan nace har abada ina nufin har gaba da abada ba zan taSa yafewa ?ar ka ba ko da kowa ya yafe mata to nikam ba zan yafe mata ba,kai in ta?aice maka labari ma ko da Amrah zata dawo duniya idan har ta yi niyyar yafe maka sai na hana".

Umar yana kaiwa nan a zancen na shi ya mi?e da niyyar barin gidan saboda yadda yake jin zuciyar shi tsaf zai iya ma?ure wa Justice Kabir wuya saboda kallon shi yake kamar Azrah ce a gaban su take zaune tana neman su yafe mata.

Muryar Malam Kabiru da yaji ya ?ira sunan shi ne ya dakatar da shi daga shirin ficewa daga gidan da yake yi Win.

"Umar dawo ka zauna".

Shine kawai abin da Malam Kabiru Win ya furta.

A hankali Umar Win ya juyo ya dawo ya zauna a gefen Usman wanda shi kam har a wannan lokacin bai ce ?ala ba.

"Umar ka yi ha?uri ka sassauta zuciyar ka kasani Ubangiji Allah yana son bayin shi masu ha?uri da yafiya,dan haka mu yi ha?uri wannan yarinyar ta ci albarkaci mahaifin ta da ya taso takanas ya zo har garin nan domin neman yafiyar mu,sai kaga dalilin yafiyar da muka mu su Allah ya kawo mana wani abin alkhairin, sannan ita rayuwa da ka ke gani kullum nasha faWa muku duk wanda zai zo neman alfarma a wajen to ku yi ?o?ari ku mishi wannan alfarmar idan har kuna da halin yi domin kuwa shi Alkhairi da ku ke gani dan?o ne baya faWuwa ?asa banza,yau idan ka taimaki wani to kai ma baka sani ba wata?ila gobe shi zai taimake ka".

?an shiru ya yi kafin daga bisani ya Juya ya ya dubi gefen da Justice Kabir Win su ke zaune sannan ya cigaba da magana.

"Bakomai kamar yadda ka taso ka zo nemar wa ?ar ka yafiya mun yafe mata Ubangiji Allah ya yafe mana gaba Waya,yanzu zaku iya tashi mu tafi massallaci tun da kun ga magariba ta gabato".

Allah Sarki Justice Kabir Win jin kalaman Malam Kabiru Win bai san lokacin da ya zube duka gwaiwowin shi a ?asa ba tare da fashewa da wani irin kuka na nadama. Tabbas Malam Kabiru ya cika mutum sannan samun irin shi a duniyar mu a yau sai an tona domin kuwa ya tabbata yau idan da shine a matsayin Malam Kabiru aka yiwa ?ar shi Azrah haka sannan mutumin da ?ar shi ta aikata musu haka yazo neman yafiya wajen shi to wallahi sai ya sanya karnuka sun yi mishi yaga-yaga da naman mutumin. Amma yanzu duba ikon Allah yadda Malam Kabiru ya tarbe shi sannan ko musu bai yi ba yace ya yafewa Azrah.

Haka suka tashi duk suka yi alawla suka nufi masallaci itama Gwaggo Sa'adatu tashi ta yi sannan ta haWa musu abinci dare wanda ta gama tun Wazu ta ajiye mu su tana jiran su dawo.

*****

Kamar yadda Mahaifin Farida ya faWa yau tun asubar fari suka gama duk shirin su na tafiya garin Yobe Win, daman daren ranar gaba Waya mahaifin Farida bai iya wani isasshen bacci ba gani yake daren ya mishi tsawo da yawa ya kasa wayewa gashi ya rasa wani irin hali yake ciki murna ne ko kuma akasin haka.

?arfe Shida dai-dai suka fito cikin shirin su na tafiya sai a sannan na ?ara ganin tsantsar kammannin ta da Amrah.

Sanye take cikin wata sea green Win abaya wadda ta fito da tsantsar baiwar kyawun da Allah ya mata.

A dai-dai wannan lokacin Anwar ya ?araso gidan Wayyo zo ku ga idon Anwar a lokacin da ya yi arba da Farida,take kewar Amrah ta dawo mishi sabuwa haWe da ?aunar ta.

Kafeta yayi da ido har bai san cewar mahaifin ta ya lura da hakan ba sai da ya ji sau?ar hannun shi a kafaWar shi yana cewa.

"Malam Anwar mu je ko kar mu makara daman kai kaWai muke jira".

?an sosa kai Anwar yayi yana jin wata kunya ta rufe shi sannan suka nufi motar suka shiga suka bar gidan. Anwar ne yake jan motar inda Farida da mahaifiyar ta suke baya mahaifin ta kuma yana gefen Anwar a kujerar gaba.

A haka suka kama hanyar jahar Yobe Win sai dai mu musu fatan sau?a lafiya.

*****

Washe gari sai wajen ?arfe sha Waya su Justice Kabir suka fito cikin shirin su na komawa Zaria.

Har wajen motar su Malam Kabiru suka fito suka raka su.

Tsayaawa yin sallama suka yi Umar kuwa yana da tsaye a gefe sai cika yake yana batsewa tare da aikawa Justice Kabir harara.

A dai-dai wannan lokacin motar su Anwar ta tsaya a gefen motar su Justice Kabir a ?ofar gidan Malam Kabiru Win.

Tun da motar ta tsaya Malam Kabiru ya kafe motar da ido a lokaci guda kuma yana jin zuciyar shi tana matsanancin bugawa.

A hankali aka buWe murfin motar aka fito.

Mahaifiyar Farida ce ta fara fitowa sai Farida da Anwar sai kuma mahaifin Farida da ya fito a ?arshe.

Wata irin sarawa kan mahaifin Farida ya yi a lokaci guda shima Malam Kabiru ya ji haka sakamakon sar?ewar da idanuwan su suka yi a cikin na juna.

Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin su Umar da Farida kowa da abun da yake sa?awa a ?asan zuciyar shi inda Umar da Usman suka shiga kallon mahaifin su sannan su juya su kalli mahaifin Farida sannan su kalli Farida cikin matsanancin mamaki.

Haka a Sangaren Farida Win ma kallo ta shiga aikawa mahaifin nata da Malam Kabiru Win cikin tsananin mamaki domin kuwa duk yadda Anwar ya basu labarin kammannin da mahaifin nata yake da Malam Kabiru sai taga ashe ma wancan labari ne yanzu ne taga gaskiya ra'ayul aini.

Allah mai iko Ubangiji Mai hallita, tabbas Allah abin godiya ne lalle Allah shi kaWai yake yadda yaso a kan bayin shi a kuma lokacin da ya so ku ga tsantsar kammanni.

Ita kuwa Gwaggo Sa'adatu kallon Farida da ta yi sai da numfashin ta ya Wauke na wucin gadi domin kuwa duk a tunanin ta Amrah ce.


Follow my Whattpad account @shamsiyyamanga.
Arewa books @shamsiyamanga.
Whatsapp number
07060943991
Phone call
09065779330
Don't forget to share and comment pls.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_=؀? &?).

_Tsarawa/Rubutawa_

? *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*38-39*
________________________________

"HASSAN ashe daman da rabon ruhikan mu zaku sake kasancewa a inuwa Waya?, Ashe daman akwai rabon mu sake rayuwa tare? Hassan ashe daman mutuwa ba zata Wauke mu ba ba tare da mun sake kallon juna ba?, Allah na gode maka bisa wannan ?udira da ka nuna a kan mu!, Mun Wauki tsawon shekaru bama tare da juna amma sai gashi lokaci guda Allah ya sake haWa fuskokin mu".

Wannan su ne kalmomin da suka shiga fitowa ta bakin mahaifin Farida take kuma hawaye ya shiga sintiri ta fuskar shi sannan ya zame a ?asa kan gwaiwowin shi kafin kuma ya saki kuka mai sauti,yana kai goshin shi ?asa ya yi Sujuddu shukriyya.

Malam Kabiru ne ya tako da sauri ya ?araso har inda mahaifin Farida Win yake dur?ushe sannan ya sanya hannu ya Wago kafin kuma ya rungume shi tsam a jikin shi,yana jin wata sabuwar soyayyar shi tana ratsa duk wani Sargo da ?ashi na jikin shi.

Kuka sosai Malam Kabiru da mahaifin Farida su ke yi kuka kuma irin mai sautin nan da taSa zuciya,duk wanda yake wajen sai da ya tausaya mu su domin kuwa abin da mamaki da kuma tausayi a ce manyan mutane irin su Malam Kabiru gasu dur?ushe a ?asa suna kuka kamar wasu ?ananan yara.

Farida kuwa da mahaifiyar ta da Gwaggo Sa'adatu suma tunin suka fara kukan duk da basu san dalilin kukan su Malam Kabiru Win ba.

Justice Kabir kuwa da mukhtar motar da basu iya shiga ba Kennan suka tsaya suma suna ganin ikon Allah.

Shi kuwa Anwar da yake tsaye a gefe tun da suka fito a motar yaga mahaifin Azrah ya cika da tsananin mamakin abin da kawo mahaifin Azrah Win wajen mahaifin Amrah sannan ya ma aka yi ya san inda su ke.

Ganin da Usman ya yi cewar har mutane sun fara taruwa a wajen su Malam Kabiru Win sun zama kamar Tv kasancewar unguwar irin unguwa ce ta mutane da yawa duba da yadda ta kasance tsohuwar unguwa. Wannan ya sanya Usman Win saurin zuwa ya Waga mahaifin na shi sannan ya yiwa mahaifin Farida da su Anwar iso cikin gidan.

Haka suka Wunguma gaba Waya suka shiga cikin gidan harda su Justice Kabir domin kuwa tafiyar da ya ji ya fasa yin ta gaba Waya yana son ya ji ala?ar Malam Kabiru da wannan mutumin.

A tsakar gidan aka baje musu wata ?atuwar tabarma duba da yadda gidan yake da fili gashi akwai bishiyar maina ?atuwa a tsakar gidan.

Umar ne ya fita waje inda ya nufi wani shago ya karSo lemo masu sanyi guda shida da kuma ruwan leda na pure water ya nufo gidan dashi ashe ma shagon na Umar Win ne.

Gidan ya ?ara nufowa ya kawo mu su ruwan sannan ya nemi waje ya zauna tare da gaishe da su sannan ya musu barka da zuwa.

Abinci Gwaggo Sa'adatu ta tashi ta zubo musu daman bayan abincin da take matan su Umar da Usman suna kawo mata shiyasa wataran abincin har yawa yake musu.

Abincin suka shiga ci inda Farida ta kasa shiru ta Wago ta dubi mahaifin ta sannan tace.

"Dad nifa kaina ya kulle, Dad Dan Allah ku fitar damu daga cikin wannan duhun da ku ka sanya kawunan mu, Dad ashe daman ku ?an biyu ne shine bamu taSa sannin hakan ba?, Dad ko da wasa baka taSa sanar damu cewar akwai wani Wan uwan ka na jini da yake raye ba saboda kullum idan mun tambaye ka sai kace mana ?an uwan ka duk sun rasu,tun muna tambaya har mu ka daina tambaya, Dad ashe daman kana da ?an uwa ka barmu ba tare da mun san su ba balle ka nuna mana su, yanzu Dad da halin mutuwa ya kasance ya zamu yi haka zamu mutu ba tare da mun san dangin ka ba,a yanzu ma ba dan albarkacin Ya Anwar da ya zo gidan mu ya sanar da kai cewar ya ga mai kama da kai ba da shikennan nake ga har mu mutu ba zamu taSa sannin su ba. Dad mai yasa?".

Farida ta ?arashe maganar cikin rawar murya ga hawayen da suka shiga zarya a kuncin ta.

Sunkuyar da kan shi mahaifin Farida yayi ?asa sannan ya tsame hannun shi daga cikin abincin da su ke ci Win, kafin ya Wago da kan shi ya dube su yace.

"Farida ki yi ha?uri wallahi ni kaina ban san dalilin da ya sanya na kasa sanar da ku asali na da kuma dangi na ba, ki sani kullum burina bai wuce na yi ido huWu da Wan uwa na ba amma kuma ban san dalilin da yasa na kasa neman shi ba".

Ya ?arashe maganar tare da sanya hannu ya goge da suka zubo mishi.

"HUSSAIN ka sani ni kaina ban san mai yasa ban taSa jin ina son na nemeka ba duk kuwa da cewar na daWe da sanin cewa kana raye kuma har unguwar da ka ke a cikin garin Zaria da gidan ka na sani amma kuma ban taSa sha'awar na nemeka ba".

"To amma Malam ni wannan abin ya bani mamaki to wai shin ta ya aka yi ku ka rabu ma da Wan uwan na ka?, Sannan kana nufin Malam Umaru mai almajirai ba shine asalin mahaifin ka ba"

Usman ya faWa da fuskar mamaki.

Murmushi Malam Kabiru ya sake wanda kana gani kasan cewa ya?e ne wanda yafi kuka ciwo sannan yace.

"Tabbas Malam Umaru ba shine asalin mahaifin na ba in ta?aice ma bayani ma ban san shi ba sai dalilin zuwa na Nigeria,bamu da wata ala?a da shi ta ?an uwan taka sai dai ta musulunci sannan kuma shi Win malami na ne. In sha Allah a yanzu zan sanar da ku asalin mu da kuma inda mu ka fito".

*WAIWAYE*
*SHEKARU HAMSIN BAYA DA SUKA SHU?E.*

Asalin mu mutanen ?asar Nijar ne a wani gari da ake cewa DAMAGARAM mahaifin mu buzu ne fari kyakkyawa ga gashi kamar balarabe. Mahaifin mu ba wani mai kuWi bane sai dai kawai rufin asirin Allah sai dai akwai wata baiwa da Allah ya yiwa mahaifin mu shine duk wata irin cuta idan tana damun mutum to da zarar an kai shi wajen mahaifin mu to da izinin Allah idan ya mishi addu'a ya tofa a ruwa ya bashi ya sha to zai warke. Sunan mahaifin mu Malam Hamisou shahararren Malami ne da ba iya garin DAMAGARAM ba hatta garuruwan da suke kewaye da namu an san shi,Allah ya zuba mishi ilimin addini sai dai bai yi karatun boko ba duba da cewar a zamanin su karatun boko Win ba kowa ya damu da shi ba,amma ilimin addini kuwa tun bai fi shekara goma sha biyu ba a duniya ya sau?e al?ur'ani mai girma. Da wannan ilimin da Allah ya bawa mahaifin mu ya sanya shi ya shahara sannan ya zamana ya na samun alkhairi da yawaa daga wajen mutane mabanbanta. Mahaifin mu da mahaifiyar mu wadda sunan ta NAJIDATOU ?an uwan juna ne ?a?an Baffanu su ke wannan dalilin ya sanya tun tana ?arama mahaifin ta ya bayar da ita a mahaifin mu kuma daman a gidan su mahaifin mu ta tashi bayan ta kai munzalin aure aka aurar da ita a mahaifin mu inda suka fara rayuwa mai cike da so da ?aunar juna. Sosai mahaifiyar mu take nunawa mahaifin mu kulawa sannan tana bashi girma da darajar shi a matsayin shi na mijin ta. Bayan auren su da wasu wattanni ta samu cikin mu sai dai cikin tun lokacin da ta same shi gaba Waya ta fara shiga damuwa domin kuwa sosai cikin yake wahalar da ita lokaci guda ta rame ta koWe ta fice a hayyacin ta wannan dalilin ya sanya aka bu?aci ?anwar ta mai suna Hafsatou data dawo gidan da zama. Sai dai fa Hafsatou kwata-kwata zuciyar ta bata da kyau amma ba wanda ya taSa sanin haka a fuska tana nunawa duniya cewar tafi kowa son Najidatou amma kuma a zuciyar ta ba haka bane domin kuwa idan akwai babban ma?iyin Najidatou to bai wuce Hafsatou ba gashi dai uwar su Waya uban su Waya asali ma Hafsatou ita take bin bayan Najidatou. A haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har cikin Mahaifiyar mu ya shiga watan haihuwa inda cikin dare na?uda ta kama mahaifiyar mu gadan-gadan haka Hafsatou ta kama ta suka nufi wani asibiti mafi kusa ko mahaifin mu bata sanarwa ba a cewar ta kar ta tayar mishi da hankali Aikuwa suna isa asibitin ba su kai ko Minti goma ba Allah ya sau?e ta lafiya inda ta haife yaron ta kyakyawa sak mahaifin mu, murna sosai Hafsatou ta shiga yi inda ta fito da sauri ta nufi hanyar gida domin zuwa ta sanarwa mahaifin mu tun da gashi lokacin ba waya,sai dai bayan ta isa gidan ta sanarwa mahaifin namu sai ta tarar da shi a ?ofar gida ya fito hankali a tashe ganin bai gan su a cikin gidan ba da murnar ta ta ?arasa wajen shi sannan ta sanar da shi cewa Najidatou ta sau?a, aikuwa ko gama rufe ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????bakin ta bata yi ba ya juya da sauri ya nufi hanyar asibitin inda ita ma ta mara mishi baya, sai dai lokacin da suka isa murna ta ?aru domin kuwa sun tarar da yara biyu jere reras a gefen mahaifiyar mu wannan yake nuni da cewa ?an biyu ta haifa wannan abin ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login