Showing 15001 words to 18000 words out of 70370 words

Chapter 6 - FANSAR FATALWA complete hausa novel

26 Oct 2025

109

da kai ta kan wata kujera ya zaunar da ita sannan yace.

"Kin ga ?anmata ki nutsu, ki dawo hankalin ki sannan ki sanar da ni mai ke tafe da ke".

Shiru Amira ta yi tare da kafe gefe guda da ido sannan ta fara ?o?arin yin magana amma sai gani aka yi jikin ta ya shiga rawa,inda ta shiga nuna musu wani dungu a cikin police station Win tana zaro ido waje lokaci guda kuma ta sulale ?asa ta sume a wajen.

Murmushi Amrah ta yi wadda take tsaye a dungun da Amira Win ta nuna cikin wata irin mummunar siffa, ha?oran ta za?o-za?o ga wani gashi da ya fito a duk wani sashi na jikin ta, hawaye take amma kuma hawayen jini kamar yadda ta saba kullum, cikin wata iriyar murya mai matu?ar tsoro tace.

"Kash!! Amira ban zo wannan wajen da niyyar cutar da ke ba, domin kuwa da kina daga cikin waWanda zan Wauki Fansa a kan su da ba zan bar ki har ki kawo wannan lokacin ba, ai ke baki cutar da ni ba kawai laifin ki Waya da ki ka kasa fitowa ki yiwa duniya bayani a lokacin da aka cutar da ni aka jefa rayuwa ta cikin tashin hankali wannan shine kawai laifin da ki ka mun, dan haka ni ba zan cutar da ke ba sai dai nasan dole daman idan kin yi arba da ni ki tsorata".

Amrah ta na kaiwa nan a zancen da take Win wanda ita kaWai ta san mai take faWa ta yi wata irin girgiza sannan ta bi ta jikin ginin police station Win ta fice daga wajen.

Ganin wannan halin da Amira Win ta shiga ya sanya wannan Wan sandan umurtar Kofur Audu da ya mi?o mishi ruwa da gaggawa.

Aikuwa ana kawo mishi ruwan ya Weba a hannun shi tare da watsawa Amira a fuskarta.

A firgice Amira ta farka tana sakin wani irin gigitaccen ihu tare da mi?ewa da gudu zata fice daga wajen tana cewa.

"Wallahi idan har ba ku yi gaggawar haWa ni da DPO ba ku ka bari har ta yi nasarar hallaka ni kamar yadda ta hallaka ?an uwana to tabbas alhakin mutuwa ta ya rataya a kan ku".

Da sauri ?an sanda biyu nan suka kamo ta tare da zaunar da ita ganin da gaske fa ta fice a hayyacin ta.

A wannan lokacin duk wani mai rai da yake kusa da cikin police station Win sai da ya farka hatta waWanda suke cikin cell a rufe sai da suka farka suka tashi suka zazzaua, sakamakon ihun da Amira Win take ba na wasa bane, inda wasu suka shiga le?owa dan bawa idon su abinci gashi lokacin ?arfe uku har ta yi.

Wayar shi wannan Wan sandan ya zaro sannan ya shiga contact Win shi ya binciko wata number tare da yin dialing Win ta.


*****

A can Clinic Win makarantar su Amira kuwa bacci mahaifiyar ta take ba ta san abun da yake faruwa ba sakamakon yadda baccin na ta ya yi nisa duba da yadda kwanakin biyun nan bata samun rintsawa, yau Win ne kawai ta samu ta rintsa da yawa har haka.

Can wajen ?arfe uku kamar wanda aka zabure ta, ta farka firgigit sakamakon wani mummunan mafarki da ta yi, inda taga Amira Win a cikin wani mummunan yanayi.

Wannan mafarkin ba ?aramin Waga mata hankali ya yi ba inda ta farka cikin sauri tare da mi?ewa zaune tana kai duban ta kan gadon da Amira Win take kwance.

Kasancewar wutar lantarkin Wakin a kunne take shi ya bata damar hango gadon da Amira Win take kwance wanda yake wayam ba alamar mutum a kai.

Daram gaban ta ya bada wani irin sauti mai ?ara lokaci guda kuma ta dafe ?irjin ta tare da mi?ewa tsaye tana furta.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun mai nake gani haka!, Ina Amira ta shiga kuma?".

Ta faWa tana nufar hanyar toilet dan dubawa duk kuwa da cewar bata ga alamun cewar akwai mutum a cikin toilet Win ba.

Sai da ta fara ?wan?wasa ?ofar sannan ta fara ?ira sunan Amira Win.

"Amira kina jina kuwa".

Ta faWa tana kasa kunne a jikin ?ofar ko zata ji alamar motsin mutum, sai dai shiru ba alamar da mutum a cikin toilet Win.

Tura ?ofar tayi inda ta shiga cikin toilet Win sai dai wayam ba alamar cewa ma wani ya shiga cikin toilet Win.

"Hasbunnallahu wa ni'imal wakil innalillahi wa'innailaihi rajiun" .

Su ne kalmomin da suka shiga fitowa daga bakin mahaifiyar Amira Win wadda hankalin ta ya yi masifar tashi, lokaci guda kuma ta ji wata irin hajijiya tana shirin kwasar ta, da sauri ta dafe jikin bangon toilet Win sannan ta fara sulalewa a wajen tana yin zaman ?an bori.

Wasu hawaye ne masu zafi suka shiga biyowa ta kuncin ta cikin kuka ta fara magana.

"Shikennan abun da na daWe ina gudu ya faru ya faru!, Shikennan Amira kema sun kashemin ke!, Ai ni daman tun da naga an kashe aminan ki jikina ya ban ba za'a ?yale mun ke ba, innalillahi wa'innailaihi rajiun, yanzu wannan wana irin tashin hankalin ne hak, yanzu wana la'annanne ne yake bibiyar ku Waya bayan Waya shin mai ku ka aikata mishi haka?".

Ta Wauki tsawon lokaci a zaune a bakin ?ofar toilet Win kafin wata zuciyar ta ce mata.

" _Kinga zama bai kama ki ba, kamata ya yi ki tashi ki fita ki duba waje ko Allah zai sa ki ganta_ ".

Aikuwa tana kaiwa nan a zancen zucin nata ta mi?e da sauri sannan ta fice daga cikin Wakin, Kasancewar dare ne ya sanya bata haWu da kowa ba a filin makarantar.

Kai tsaye bakin gate ta nufa inda taje ta tarar da jami'an tsaro a tsaitsaye kamar masu jiran ko ta kwana.

Tun da Inspector Rasheed ya hango mace ta nufo inda suke Win cikin sauri kamar zata kifa da bakin ta jikin shi ya bashi ba lafiya ba.

Gaba Waya jami'an tsaron ido suka zuba mata suna jiran su ji da wacce ta zo.

Tana isowa wajen ta fashe da kuka sannan ta buWi baki cikin rawar murya ta fara magana.

"YallaSai sun sace Amira na tabbatar da cewa a yanzu sun riga da sun hallaka ta kamar yadda suka hallaka sauran ?an uwan ta, yallaSai ku taimaka dan Allah nikam ko gawar ta a kawo mun na ganta kaf.......".

Kasa ?arasa maganar ta yi sakamakon wani kuka da ya ci ?arfin ta.

Dafe kan shi Inspector Rasheed yayi cikin tsananin tashin hankali, anya kuwa makashin ?an mata nan mutum ne?, Idan kuwa har mutum ne to tabbas a cikin makarantar nan yake rayuwa, domin kuwa abun shikam ya fara bashi tsoro ya za'a yi a ce suna tsaye a wajennan ko rintsawa ba su samu damar yi ba amma ace an shiga har cikin Clinic Win an kashe yarinyar, to amma yanzu kana da tabbacin an kashe ta Win ne?, Wata zuciyar ta jefa mishi wannan tambayar.

Aikuwa cikin sauri ya kawar da tunanin da yake sannan ya juya ya dubi mahaifiyar Amira Win da take dirzar kuka kamar ran ta zai fita yace.

"Kin ga ki nutsu ki mun bayanin abun da ya faru da Amira Win".

Goge hawayen ta tayi tare da sanya bakin hijab Win ta ta fyace majinar da ta zubo mata sannan ta fara mishi bayani tun daga farkawar da tayi bata ga Amira Win ba har zuwa yanzun da take tsaye a gaban su.

Hankalin jami'an tsaron wajen ba ?aramin tashi yayi ba, musamman Inspector Rasheed.

Har ya buWi baki zai yi magana sai kuma ?ira ya shigo wayar ta shi, ganin wanda yake ?iran nashi ya sanya ya yi saurin Waga wayar tare da karawa a kunnen shi.

*MANGA*
'?
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ =؀? &?).

_Tsarawa/Rubutawa_

? *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book Win gaba Wayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

-------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*010*
____________________________

*Not Edited* .

Shiru Inspector Rasheed ya yi ina sauraran abun da ake faWa mishi a cikin wayar kafin daga bisani naji yace.

"Ok to shikennan ku barta a wajen kar ku barta ta tafi ina zuwa nima akwai ?ar wata matsala ce da ta ta so in sha Allah idan na shawo bakin ta zan shigo zuwa nan da asubah, amma kasan DPO a wannan lokacin ko ka ?ira shi ba samun wayar shi zaka yi ba,so kar ka ?ira shi ka bari mu ga zuwa safiya".

Inspector Rasheed ya faWa, ban ji abun da aka ce mishi a Waya Sangaren ba sai ji nayi yace.

"Ok to shikennan duk yadda zaku yi dai kar ku ?yale ta ta tafi".

Yana kaiwa nan a zancen na shi ya katse wayar sannan ya juya ya dubi mahaifiyar Amira da har a wannan lokacin bata daina kukan da take Win ba.

"Uhmm Mama dan Allah ki daina wannan kukan kiyi ha?uri in sha Allah daga yanzu zuwa safiya zamu yi duk ?o?arin da zamu yi domin ganin mun gano wanda yake da hannu a wajen Satan Amira Win".

Ya ?arashe maganar cikin sigar rarrashi.

"YallaSai ni wallahi a yanzu bu?ata ta ko gawar Amira na kalla domin kuwa na tabbatar i zuwa yanzu sun daWe da hallaka ta,na tabbata ba zasu ?yale ta ba itama kashe ta zasu yi kamar yadda suka kashe sauran ?an uwan ta, Allah ya ji ?anki Amira ya saka muku a kan duk wanda yake aikata muku wannan zaluncin".

Mahaifiyar Amira ta faWa tana dur?ushewa a wajen sakamakon kukan da yaci ?arfin ta.

Shikam Inspector Rasheed rasa abun da yake mishi daWi yayi wannan bala'in har yaushe, tabbas duk wanda suka kama da hannu a wannan aika-aikar ba zasu mishi da daWi ba,har ya hango irin hukuncin da za'a zartar mishi.

Da ?yar dai ya lallaSa mahaifiyar Amira ta tashi daga wajen sannan suka sanya ta a mota suka mayar da ita gidan ta.

*****

Lokacin da suka mayar da ita gidan nata har asubah ta kawo kai domin kuwa a lokacin har ?arfe biyar ta yi dan haka suna kai ta gidan nata suka dawo wani massallaci da yake Wan gaba da gidan kaWan suka gabatar da sallar asubah kafin suka mi?e suka nufi police station Win.

Shigar su cikin police station Win ne suka yi arba da abun da ya yi matu?ar ba su mamaki.

Amira suka gani a zaune a bakin kanta ta kafe ?ofar shigowa cikin police station Win da ido ko ?iftawa bata yi.

Wata zabura Kofur Bala yayi ya ma?ale a bayan Inspector Rasheed yana furta.

"YallaSai Fatalwa, innahu min sulaimanu wa innahu bissimillahir rahmani rahim ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba, yallaSai ka ga abun da idanuna suka gane mun kuwa".

Ya ?arashe maganar yana ?ara shigewa jikin Inspector Rasheed Win domin kuwa shi har ran shi yayi tunanin Fatalwa ce kuma yayi tunanin shi kaWai yake ganin Amira Win.

Tsawar da Inspector Rasheed Win ya buga mishi ne ta dawo dashi daga haukar da yake Win.

"Wai kai Kofur Bala mai yasa wani lokaci lamarin ka sai a hankali ne, yanzu fisabillillahi ina Fatalwar take a wannan wajen?, Ko kuma an ce maka ita wannan Win gawa ce?, Kuma wai a hakan kana i?irarin kai jami'in ?an sanda ne ko?, Dallah ni malam sakar mun kaya".

Inspector Rasheed ya faWa yana SamSare hannun Kofur Bala Win daga jikin shi.

A sannan ne kuma waWannan ?an sandan suka fito daga wani Waki alamar salla suka yi.

"Inspector Rasheed har kun iso kennan?".

Da sauri Inspector Rasheed ya ?arasa wajen shi yana ri?o hannun shi suka nufo wajen da Amira take rakuSe sannan ya fara magana fuskar shi da alamun mamaki.

"Asp Sadiq a ina ku ka samo wannan yarinyar?".

Murmushi Asp Sadiq yayi sannan ya nuna Inda Amira take yace.

"Wannan ai ita ce yarinyar da na ?ira ka a kan ta wadda na sanar da kai cewar ta zo tana son ganin DPO".

Wata doguwar ajiyar zuciya Inspector Rasheed ya sau?e tare da furta godiya a Ubangiji a fili.

Kllon shi Asp Sadiq ya yi fuskar shi da alamar tambaya sannan yace.

"A'a ya naji kana sau?e numfashi haka ko dai ka santa ne?".

"Tabbas kuwa na santa, ina case Win da yake hannu na na waWannan ?anmatan da aka kashe har guda uku a jami'ar Ahmadu Bello?".

Inspector Rasheed ya faWa yana kafe Asp Sadiq da ido.

"?warai kuwa na gane,kar fa kace mun wannan yarinyar tana da hannu a cikin wannan kisan da ake yi Win?".

Ya ?arashe maganar cikin zaro ido waje.

"Ko kaWan ba hannun ta a ciki asali ma yanzu haka rayuwar ta tana cikin haWari domin kuwa gaba Waya waWanda aka kashe Win tana da ala?a ta kusanci sosai da su,idan ka yi duba da irin zazzafan amintar da take tsakanin su ba wanda bai san irin ?awancen na su ba,yanzu haka maganar da nake maka mahaifiyar ta tana can hankali a tashe a tunanin ta an kashe mata ?a kamar yadda aka kashe sauran abokanan ta, to amma abun da ya bani mamaki shine mai ya kawo ta police station Win?".

Inspector Rasheed ya faWa yana kai duban shi inda Amira take rakuSe wadda har a wannan lokacin idanun ta ba su daina zabur da hawaye ba.

"To gaskiya ni dai ban ba zance maka nasan takamaiman abun da ya kawo ta nan ba domin kuwa lokacin da ta zo ta sanar da mu kawai ita Dpo take son gani".

Shiru gaba Waya suka yi kafin a hankali Inspector Rasheed ya ?arasa wajen Amira da take ta rarraba idanu kamar a ce mata firit ta ruga da gudu.

"Amira".

Inspector Rasheed Win ya ?ira sunan ta yana mai tsugunawa a kusa da ita.

?ago ido Amira ta yi ta kafe shi da ido ba tare da tace uffan ba.

"Amira kina jin yunwa a kawo miki abinci".

Saurin jijjiga mishi kai ta yi, wanda sai a wannan lokacin ta samu damar yin magana cikin rawar murya tace

"A'a bana son in ci komai, dan Allah bu?ata ta nidai kawai ku haWani da DPO saboda nasan wallahi nima ta kusa kashe ni, nasan ba zata bar ni ba kashe ni zata yi dan haka tun kafin lokaci ya ?ure ku haWani da DPO domin na bayyana mishi wata Soyayyar gaskiya wadda burin ku shine ku gano ta".

Ta ?arashe maganar cikin sakin wani irin marayan kuka.

"Kin ga Amira ki nutsu in sha Allah ba wadda zata kashe ki, yanzu ki nutsu ki sha ruwa sannan kimun bayanin abun da yake tafe da ke".

Inspector Rasheed ya faWa yana tsiyayo ruwa a cikin wani kofi da Kofur Bala ya kawo mishi sannan ya mi?a mata.

KarSar ruwan Amira ta yi amma bata sha ba sai ma kafe ruwan da ta yi da ido sannan ta Wago kai daga bisani tace.

"Ina mahaifiya ta?".

Kallon ta Inspector Rasheed yayi cike da mamaki kafin daga bisani yace.

"Mahaifiyar ki tana nan cikin ?oshin lafiya tana gida".

?an shiru ta yi kafin tace.

"Ina son kafin na sanar da ku abun da ya faru dan Allah ina son na nemi wata alfarma daga wajen ku".

"Ok to shikennan ki faWa in sha Allah za'a miki ita".

"Ina son dan Allah a ?ira iyayen su Afrah da Azra da Anisa da kuma Anwar domin a gaban su ne kaWai zan iya bayyana irin mummunar aika-aikar da ?a?an su suka aikata har yake bibiyar su".

Kallon Asp Sadiq Inspector Rasheed yayi sannan kuma daga bisani ya mayar da kallon shi kan Amira yace.

"Meyasa sai a gaban iyayen su zaki iya sanar da mu abun d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a yake faruwa?".

"Saboda hakan ne kawai zai wanke musu raWaWWin kisan da aka yiwa ?a?an su, sannan kuma hakan zai sa su gane cewa kowane abu aka yiwa ?a?an su su suka janyo, kuma hakan zai sa su daina ganin laifin wanda yake kashe mu su ?a?an su daga haka sai su koma ganin laifin ?a?an su domin kuwa ko mai ne su suka janyo wa kan su, idan da hali ma ina bu?atar a gayyato ?an jarida da kuma hukumar makarantar mu domin a samu a yaWa labari a duniya ko hakan zai sa masu son zuciya irin ta su su shiga hankalin su".

Mamaki ne ya kama su Inspector Rasheed inda suka shiga kallon-kallo da kuma mamakin kalaman Amira Win.

Duban agogon hannun shi Inspector Rasheed inda ya ga har ?afa shiga ta gota sannan ya dubi Asp Sadiq yace.

"Asp bari naje gida na yi wanka daga can zan biya ta gidan iyayen yaran can dan na sanar da su ko zasu samu damar zuwa dan mu ji abun da yake tafe da wannan yarinyar".

Inspector Rasheed ya faWa yana mikewa daga tsugunen da yayi da sauri Asp Sadiq ya dube shi yace.

"Ai nima tare zamu wuce domin kuwa kaga jiya ban kwana a gida ba, wallahi wasu yara aka kawo wanda yasa dole aka ?irani na zo to kuma na zo kennan ban daWe ba wannan yarinyar ta zo ta".

Asp Sadiq ya faWa yana bin bayan Inspector Rasheed Win inda su kuma sauran ?an sandan suka tsaya jiran ma su aikin safe su zo su karSe su suma su tafi.

Sai da Inspector Rasheed ya fara biyawa ta gidan su kasancewar ba shi da aure, wanka ya fara yi kafin ya fito ya je part Win mahaifiyar shi inda ya same ta zaune ta kammalla haWa breakfast.

Waje ya nema ya zauna a gefen ta kafin ya shiga gaishe ta.

Amsawa tayi sannan ta dube shi tace.

"AbdulRasheed naga kwana biyu wannan case Win da ka ke gaba Waya ya sa ka fara fita a hayyacin ka, ni dai dan Allah abun da nake so da kai kuma wanda kullum na sha faWa maka shine ka kula kuma ka ri?e gaskiya da amana kar a baka kuWi ko wani abu wanda zai sa ka danne ha??in mai gaskiya har ka bawa marar gaskiya gaskiya, sannan addu'a kullum ina faWa ma addu'a ita ce jagaba a komai idan har ka ri?e addu'a to tabbas ka ri?e babban makami wanda zai kare ka daga dukkan wani sharri dan haka ka kula kaji".

Sosai maganar mahaifiyar ta shi ta shige shi inda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login