Showing 15001 words to 18000 words out of 72389 words

Chapter 6 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4944

daɗe wasu ƴan sanda ne a bakin ƙofa, sun ce suna sallama da kai"

Siddiƙa ta waro ido
"Ƴan sanda kuma?, Da sanyin safiyar nan"
Mudi Haruna ya ce "Eh ranki shi daɗe"
Daddy ya ce
"Ka je ka ce masu su shigo"

Siddiƙa ta dube shi.
"Ya za ka ce masu su shigo?, ƴan sanda fa?"
Ammar da gaban sa ke faɗuwa ya miƙe, yana goge bakin sa da tissue, tsabar firgicewa a nan ya bar wayar sa da agogon sa, ya bar falon, ya shige cikin gida, ya zagaya ta ƙofar bayan ya bar gidan, a tunanin sa messenger ɗin sa ce ta haɗa shi da ƴan sanda a kan abin da yayi mata. Sai dai me?, Ƴan sanda na shigowa suka tasa ƙeyar Alhaji Abdul Azeez, bayan sun karanto masu arrest warrant da aka ba su tun daga ofishi. Siddiƙa ta fashe da kuka tana kururuwan neman agaji, ta bi su a baya ita a dole tare za su je, amma ƙiri ƙiri suka hanata shiga motar, suka ja motar su suka bar ta a yashe tana birgima.

Ƴan aikin ta kuwa sai kallon ta suke suna "Ƙus ƙus"


****
*Zakiyyah*
Ƙarfe takwas a Kaduna yayi mata, ta kira Khadija ta ce ta zo ta tayata ɗaukan kaya, baiwar Allah har ta manta rashin mutuncin da ta yi mata, ta kira Rakiya suka fito tare. Sai dai suna ganin juna abin ya faɗowa kowannen su a rai. Suka harari juna a tare, Khadijah ta kai mata duka ta goce tana dariya.

"Mara mutunci, da kin sani kin yi zaman ki ai"

Rakiya ta ce

"Hala wani rashin mutuncin Mela ta sake yi miki?"

Khadijah tace
"Eh mana, kin san jiyan nan da muka shirya za mu je karatun malama Bilkisu na je ɗakin da take zuwa, aka ce min ta fita, da na kira wayar ta sai ce min ta yi tana Zaria, ga littafanta duka a hannuna da na yi magana ta nemi ta ci min mutunci, ni ko na ce bata isa ba”

Zakiyyah ta ce
"To ki daina shisshige min rayuwa, bana so"

Khadijah ta ce
" Ki daina cewa kina da rayuwa, ina rayuwar yake?"

"Ni ko nake da rayuwa, me kika sani a rayuwata?, Khadijah rayuwata ba guda ɗaya bace, a cikin rayuwan da nake da shi ko kashi ɗaya baki sani ba, da a ce kin sanni ba za ki ce min haka ba"

" Sannu Narendra MODI da Rajnikanth mutanen da suka fi kowa tarihin jarabta a rayuwa, kowa da kika gani a nan yana da nashi rayuwar da ba kowa yake fahimta ba, kuma hakan bai sa su sun wulaƙanta mutanen da ke tattare da su ba, ƙawata son ki nake shi yasa kika ga kaman ina shiga rayuwar ki, kuma ko me za ki ce ba zan daina tunasar da ke abubuwan da ya kamata ba, sai dai mu ci uban juna... Ehe"

Zakiyyah ta yi ƙwafa ta ce

"Ai kam za ki bugu"
ba za su gane ba, babu wanda zai fahimce ta, tafiya Zarian da take yi ba da son ran ta bane, ba za ta iya zama a hostel ba tare da provision ba, kuma dole sai ta yi aiki kafin ta samu kuɗin siyan kayan abinci, bata son roƙo, infact bata roƙo, koda maggi ne bata da shi ta gummace ta ci abincin haka nan babu maggi. Shi yasa take tafiyan ta Zaria duk bayan sati biyu, koda exams suke da shi.

***
*Hajiya Siddika*

Bayan tafiyan ƴan sandan ta kakkaɓe jikinta ta miƙe shiga ciki, ta ɗauko mayafinta da mukullin mota tana kuka ta ƙwalawa driver kira, ta miƙa mai mukullin ta ce ya kai su police station, suna isa station ƴan sandan suka ce ba'a yi kame a office ɗin su yau ba, tashin hankali wanda ba'a sa masa rana, sai a lokacin ta tuna ashe basu faɗa masu sunan station ɗin da suka kai shi ba, ranar wuni suka yi suna zagaye stations amma duk inda suka je sai a ce ba'a kama mai makamancin sunan Daddy ba, hankalin siddiƙa ya tashi, fuskantar yayi jazur saboda kuka, hancin nan ya ƙara tsini, idanu suka yi ciki ciki.




Tun ana sa ran dawowan Daddy a ranar har dare yayi babu labari, a ranar babu wanda ya rintsa a cikin su, duk suka kasa cin abinci, abu har washe gari, ranar ya shuɗe babu labarin daddy, ga shi suna tsoron kada su yi report ya zamana wani mummunar aikin ya aikata, hakan ya zama kaman tonon asiri a wajen su. A rana ta uku aka kirata video call da international number, fuskar ɗaya daga cikin ƴan sandan da suka kama Daddy ya bayyana, ya ce Daddy na wajen su cikin kwanciyar hankali, sai dai suna buƙatar ƴar sa Zakiyyah ta dawo gida, nan da 48hours, idan ba haka ba ta kwana tana kallon BBc don abin da za su aika masa, tabbas sai ya firgita gidan jaridun ƙasar nan. Hankalin Hajiya Siddika ya daɗa tashi, sai dai kuma tashin hankalin da take ciki bai hanata yin cikin cikakken adon da ta saba yi ba mai ɗaukan hankali, ta sauko kasa izuwa babban falonta fuskarta a mugun murtuƙe ta wani sha heavy makeup kaman bata da wata damuwa, tana taku akan dogon heels mai shegen tsada sai taku take ƙwas ƙwas har ta sauko ƙasa cikin babban falonta.

Gabaki ɗaya ƴaƴanta ne zaune a falon, suna kallon wani American series, Ammar da Jabeer ne kaɗai babu a cikin su, sun tafi wajen aiki, su kuma suna hutu, shi yasa basu da aiki sai kallo.

Tsaki ta ja ganin yadda hankulan su ke ga kallon, rashin mahaifin su a gidan ma bai dame su ba, a fusace ta ce

"Meye haka?, Menene wannan?, ku tashi ku bar min falo"

Kashe kallon suka yi duk suka bar ɗakin suna gunguni. Har sun fice ta ɗaga murya ta kira Imam, ya juyo gaban sa na dukan uku uku.

"Kai zo nan"

Ya tako gaban ta a tsorace gaban sa na faɗuwa. Da kallon raini ta bi shi, kaman ba ɗan mijin ta ba, fuska a yatsine tace

"hhh mtsww... Ina dai fatan ka karanta saƙon da na sa a tura maka"

Yace
"Eh Mum..."

Cikin katse shi tace
"Ni ba uwar ka bace, kada ka sake kira na da wannan sunan"....

Comment and share please 🥺😩

24 November 2024
Na yi gabas🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *006*
Siddiƙa ta gyara zaman ta cikin isa ta ce
" Bari na kara maimaita maka, ƴan sandan da suka kama baban ku har gida sun kira wayana ɗazu, sun ce mayyar Yayar ka, ita suke buƙatan ta dawo gida kafin su sake min miji, dan haka nake so ka kira ta, ka lallaɓata ta dawo cikin gidan nan, ko kuma in kira uwar ku na in ci mata mutunci, ka san ni ba mutunci ne da ni ba, dan wallhy a kan Baby babu abin da ba zan iya aikatawa na, kuma ka sani... ka faɗa mata idan Baby ya sake kwana ɗaya ba'a gidan nan ba sai na ɗauki mummunar mataki a kan kaff dangin ku"

Shi dai Imam kan shi a ƙasa bai tanka ba, ta sake gyara zama tana jera ƙwafa,"Hmmm... Hmmm"

Gaba ɗaya sai ta kasa magana, Imam ya ɗaga kai ya kalleta cikin uni guda har ta rame, idanun ta sun shige ciki ga hancin nan ya ƙara tsini kaman mara lafiya, ta harare shi....

"Bar kallona mayen mutum...Yanzu Yanzun nan nake so ka kirata, ka yi mata yaren da ta fi ganewa gabana, ta dawo a fito min da miji, in baza ka iya ba ka kira ta ka bani waya zan yi mata bayani"

Kasa cewa komi Imam yayi, ya san ko ya kira Zakiyyahn da wuya ya sami layinta, don sim card din ta sun fi ashirin, sai ta so kiran mutum ake samun ta a waya. Sai bata hakuri yake, amma ta juya ƙeya, dole ya ɗaga waya ya kira Zakiyyah, layukan ta uku yake da shi, ya kira duka a kashe.

Zuwa wannan lokacin Siddiƙa ta gama cika ta gama batsewa, sai surfa masifa take kaman ta haɗiyi bomb, tana cewa

"Duk yadda zaka yi ka kira ta, duk wanda ka san yana tare da ita ka kira su ni dai bana so in sake kwana a gidan nan ba tare da mijina ba, in ba haka ba wallahil azeem sai na ƙulla maku sharrin da ba za ku iya fita daga ciki ba".

Dama Imam ga shi ba kaman ƴar uwar sa ba, tsoron matan yake ji kaman ranar mutuwansa, tuni ya sake tsurewa, sai binciken lambobin wayansa yake, ko zai yi karo da wani numbanta. Da ƙyar ya iya lalubo lambar ƙawarta Khadijah, ya danna kira, jikin sa har rawa yake yi, bugu daya ta ɗauka , dawowan su kenan daga ajin Malama Bilkisu sun fito C.A ɗin Foundation Of Nursing, part ɗin malama bilkisu, fuskokin su babu yabo babu fallasa. Sallama yayi ta amsa.

"Anty Khadijah, kina tare da Anty Zakiyyah?, Mom ce take son magana da ita Please"

Cikin natsatttsiyar muryarta ta ce
"Da wa nake magana??"

Yace
"Imam ne ƙanin Zakiyyah..."

Sai da ta ɗaga ido ta kalli Zakiyyah , ta kanne mata idanu, sannan ta sa wayar a handsfree
Ta ce "Auuu Abdullahi ne, ya kake?, Ba Zakiyyah tana tana Zaria ba?,Ba zata dawo ba ko?, Mun yi test ma bata nan"

Da mugun mamaki ya ce

"Kaiii?, Tun ranar Saturday fa ta bar gida"

"Gaskiya bata dawo ba, Amma da akwai matsala ne?"


"Uhn.... Ba matsala..."

a daidai nan Siddiƙa ta ƙwace wayar tace

"Keh baƙauyiya ƴar talakawa, saurareni nan, ki aiko min da account number ɗin ki, zan tura miki dubu talatin, da zarar yarinyar nan ta dawo makaranta, ki sanar da ni, kar ki ga kaman na sa a kira ki, ki yi tunanin alfarma za ki min, talaka bai isa ya min alfarma ba"

Khadijah ta ce
"Da kyau Mrs Ɗahiru Mangal"

Ƙit ta kashe wayar, Hajiya Siddiƙa ta bi wayar hannunta da kallo, da mamaki mai yawa, bata yi zaton akwai talakan da za'a masa tayin dubu talatin ya bijire ba, koda uwar sa da ubansa aka zaga, amma Khadijah ta yi mugun bata mamaki, bata san Khadijah ba amma haka kawai zuciyar ta take gaya mata Khadijan ƙasƙantacciyar ƴar talakawa ce don a nata tunanin babu ɗan masu arzikin da zai so ƙulla alaƙa da Zakiyyah, ganin irin gwagwarmayar da take yi, babu irin sana'ar da bata yi don ta samu kuɗi. Shi yasa tunaninta ya bata kaff ƙawayen ta irin ta ne, a wajen talla suke haɗuwa. Ta yi nisa a tunani har bata san lokacin da Imam ya sulale ya bar mata falon ba, ta daɗe a zaune a wurin kafin ta miƙe ta koma ɗakin ta, ta ɗau nata wayan, ta kira Ammar, ta labarta masa yadda suka yi.

"Mum, mu kai maganar wajen ƴan sanda mana...."


"A'a Ammar, mu dai jinkirta kaɗan tukunna, ai sun san za mu iya kai ƙara wajen ƴan sanda amma hakan bai sa sun sako shi ba, ina tunanin wannan trap ne, fallasuwar maganar nan ka iya jawo wani abin na daban....kawai mu bi abinda suka ce, mu ga iya gudun ruwan su"

Bayan sun gama waya da ita, Ammar ya lalubo numbarta, cikin Sa'a kuwa wannan karon ya samu ya shiga, bugu ɗaya ta ɗaga.

"Ya aka yi?"

"Ƴan sanda sun zo sun kama Daddy''

Daga ɗayan ɓangaren, Zakiyyah ta d'auke goran ruwan ta daga drawer sannan ta fito daga ɗakin su zuwa hanyar da za ta kai ta block B na hostel ɗin su.
"Na sani"
"Toh... ki dawo..."
Sai kuma ya kasa ƙarasawa, don ya rasa ta ya zai yi mata maganar, shuru ya ɗan ratsa na tsawon lokaci.

Zakiyyah ta nemi kan d'aya daga cikin kujerun da ke tsakanin block ɗin su da Block B ta zauna sannan ta kai goran ruwan bakin ta.
"Uhum?, Ina sauraron ka"
"Na ga kaman baki damu ba ya kamata ki dawo, mahaifin mu ne..fa"

Dariyar rainin hankali ta yi, ta ce
“Ammar... In tambayeka mana"
Yace
"Ina jin ki"

"Daddy babana ne ko naka?"

Da mamaki ya ce
"Ban gane ba, wannan wace irin magana ce?"

"Tambaya ce kawai, babana ne ko babanka?"

Yace
"Baban mu ne, ni da ke"

Jin haka yasa ta mik'e ta cigaba da takawa zuwa hanyar da zai kai ta block B, ta ce
"Ƙarya kake Ammar, akwai banbanci tsakanin ɗan halak da na gaba da fatiha, Daddy ba mahaifin ka bane, don haka ka binciki Siddiƙa, ta nemo asalin ubaku kai da Jabeer"

"Keh....kar ki gaya min magana"

"An gaya maka"

Ta katse shi

"Kasancewar ki ƴar halak me ya amfanar da ke?, Ƴar halak ɗin da bata isa ta ci albarkacin ubanta ba?, Mu ɗin dai, mu da kike kira ƴaƴan gaba da fatiha, mu ne nan masu gida"

Murmushi ta kuma yi mai ciwo.
"Kai dukiyar Daddy ya dama Ammar, da a ce dukiyar Daddy na gabana kana tunanin zan bar ku ku sha ruwa a gidan nan?, Don haka ka kwantar da hankalin ka dukiyar sa baya gabana, kai dai ka maida hankali wajen neman wanene uban ka, don sanin hakan zai yi maka amfani ko nan gaba"

"Zakiyyyah... Don't piss me off"
Muryar sa ta fito a kausashe cikin wani irin amo dake shaida tsananin ɓacin rai da ƙunci.
"So nake ran ka ya ɓaci Ya Ammar, ka tambayi uwar ka, how many Men fuck her before she born you?, Maza nawa ne suka ratsata kafin a haife ka, ina tantama if Daddy was your real father!"

Ƙitt ta kashe wayar, a cikin idonta hoton yadda kalaman ta za su jawo ɓacin rayukan mutane ne ke haskawa, ta hasko yadda Siddiƙa za ta tara yaran ta su tattauna yadda za su zo har Kaduna su dakata a turmi, su ƙulla namanta a leda su taho Zaria da shi...

Ta yi tunanin za su biyota Zaria, amma har satin ya ƙare, wani ya kuma shiga, babu wanda ya sake kiran ta, kuma har a lokacin ba'a sako daddy ba, a sati na uku ta yanke hukuncin komawa Zaria, don ta fara yin broke,amma wannan karon bata sauka a gidan Daddy ba, kai tsaye gidan su mahaifiyarta ta nufa, mahaifiyarta ta yi tafiya, kakarta ce kawai a gidan, da ƙannenta.

Tana sauka a gidan jaka kawai ta ajiye, ta fice daga gidan cikin shiganta kaman kullumr, shirt da wando, ta nufi kasuwa, ta saro lemun kwalba da na roba ta nufi tasha fuskarta rufe cikin facemask, don tana tsoron wani cikin ahalin siddiƙa ya gan ta, ƙarfe biyar da rabi na yamma ta koma kasuwa, ta siyar da kifin ta, sai kusan taran dare sannnan ta baro kasuwan, ta ɓoye fuskar ta cikin facemask gudun kada wani ya gan ta.

Garin yayi tsittt babu alamun wani abun hawa ko daya, sai tafiya take yi, tana tunanin Kakar ta, ta san tana can hankalin ta a tashe.

Sai da tayi tafiya mai tsayi sosai kafin ta iso gida, ta na ture kofar gidan ta ga kakarta wacce suke kira Gigi ta tsaye, da sauri Gigi ta rungumota tare da matse kwalla tace
"Yarinyar nan, ina kika tsaya haka? duk kin tashi hankali na, ince dai lafiya ko?"

Zakiyyah ta kalli kakarta cikin tausayawa, tace "Babu abin hawa, da ƙafa na gangaro"

Gigi tace
"Baki ji yanda na tada hankali na ba, don naga dawowan ki kenan, ko hutawa baki yi ba, na ci kuka na ni kadai babu mai rarrashi na, na fi awa biyu gaban gidan nan ko tsoron duhun bana yi ina ta jiran ki, ga ɗan banzan unguwar nan, ba wanda zai gan ka ya tanka ka. Bari maman naki ta dawo, zan ce, dole ta siyo min waya ko dan gudun Irin wannan"

Zakiyyah tayi dariya sosai, dariyan da baka ganin irin shi a fuskar ta sai in tana tare da kakar tata ko kuma mahaifiyar ta. Cikin dariyar tace

"Gigi bari na shiga ciki in watsa, ko magrib ban yi ba wlh, ga isha'i'"
Gigi tace
"I maza, kar ki manta, ki yi wa Maman ki addu'a, ga abincin ki chan a kitchen, ɗan wake ne da lemun cocumber abin da kika fi so"

Idanun Zakiyyah ya tara ruwa, ta manta rabon da wani ya ciyar da ita cikin soyayya da kulawa kaman haka, da ace za ta zauna a gidan mahaifiyar su, da ba ƙaramin gata za ta samu ba, amma sai ta dinga ji kaman in ta zauna a tare da su ɗawainiya zai yi masu yawa, mahaifiyarta abinci take siyarwa a kasuwa, ita kuma kakarta su dadawa da bushasshen kuɓewa take siyarwa, da wannan ƴar sana'ar suke ciyar da kan su, su tufatar da kan su, sannan su biyawa ƙannenta kuɗin makaranta.

Murmushin yaƙe ta yi, ta amsa da "toh" tare da shigewa cikin gidan.

*Mohan*
"Ya Morh, Ummie ta ce ka maida su Aqib gida, sannan awa ɗaya ta baka, ka je ka dawo yanzun nan"

Autar su A'isha ta faɗa daga bakin ƙofan sa cikin ɗaga murya, an riga an dasa masu tsoron sa a zuciyoyin su, an haramta masu shiga sashen sa, in ba aiken su aka yi ba, don gani ake kaman idan suka saba da shiga sashen sa, zai koya masu mummunar halin sa na shaye shaye.
Kallon agogon dake ɗakin sa yayi, ganin karfe huɗu harda rabi na rana. Wanka yayi a gurguje, ya shirya. Sanye cikin kassaitacciyar collection din jumfa na voile material milk color da hadaddiyar hular zanna bukar me laushi, haduwar sa da hasken fatar sa is flawless.

(Aqib da Humayrah ƴaƴan ƙanin sa Ameen ne), sun zo su yi spending weekends ɗin su a gidan su ne, sai dai ko kwana ba'a yi ba, suka dami Ummie da kukan a maida su gidan su, hakan ya sa Ummie ta ce ya maida su gida.
"Assalam Alaikum" yayi sallama a kofar falon gidan, maimakon a amsa mai, sai jin ihu yayi, yayyy!!!

" Ga Uncle Moh, Ga Uncle Morh oyoyo" wasu yara biyu, mace da namiji suka zo suka rungumeshi, yayi murmushin yaƙe don dukkan su balagaggu ne, shekarar macen 21, namijin kuma 20.

Macen ta ja hannun yaran zuwa palor daga nan ta nufi fridge ta ɗauko fresh milk da cup, tace

"Uncle Morh, i know u must be hungry ga fresh milk"
Murmushi yayi yace "Aa Maryam, ciki na a koshe yake"
Ta marairaice tace
"Don Allah ka sha yogurt ne ai ba abu mai nauyi ba, please"
Ya mata murmushin da ke kashe ta yace "Maryama i'm full wallahi daga restaurant muke,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login