Showing 42001 words to 45000 words out of 72389 words
sa, ya dubi Hassan cikin hawaye ya ce
*****
Ƙarar wayan ta ne ya tashe ta daga wahalallen baccin da ya ɗauke ta, ta kara wayan a kunne ba tare da ta duba sunan mai kiran ba.
"Babe..."
Ta ji an faɗa daga ɗayan ɓangaren, ta sake ware idon ta sosai tana miƙa.
"Yes babe...., Ina wuni"
"Lafiya lau, ya sch"
"Fine" ta amsa a takaice
"Babe kin san problem ɗin ki yayi aure kuwa?"
Guntun murmushi ta yi, ta ce
"Na ɗauka ka daɗe da sanin na fi ka kusanci da shi"
Girar sa na sama a dage kaman tana ganin shi
"Au na manta fa, to ya na ji muryar ki somehow?, Ko kishi n...."
Ƙit ta katse wayar tana jan tsaki. Yau kwana uku kenan rabon da su yi chat da problem, tun da ta saka wayar ta a Flight more bata sake kunnawa ba sai ɗazu. Yau tun da ta tashi take jin matsanancin kewar sa, ji take kaman ta yi tsuntsu ta gan ta a inda yake, sai kallon hoton sa take tana ayyana abubuwa da yawa a ran ta. Daga karshe dai zuciyar ta ta rinjayi fushin da take yi da shi, a kan laifin da bata san na menene ba, ta duba active status ɗin sa, sai ta ga ma rabon shi da hawa online tun ranar da suka yi chatting last, ta duba message ɗin ta dry, babu sakon sa, tuni ta ji hankalin ta yayi bala'in tashi, ta san ba lafiya ba, babu abin da zai sa Problem ya mata shiru har na tsawon kwana uku. Ta yi dialing numban sa har ta gaji baya tafiya, daga ƙarshe tayi jifa da wayar ta kwanta tana kuka, a nan bacci ya ɗauke ta, kiran Ibrahim ne ya tadata, ga shi kuma ya sake ɓata mata rai.
Tsaki ta sake ja a karo na babu adadi, numbar Mohan din take kira babbu kakkautawa tana jerawa da tsaki amma baya shiga sam, daga bisani ta kafe kan ta a kan wayar ta shiga rubuta masa saƙo mai tsayi da zafi bata dago kan ta ba har sai da taji alaman shigowar mutane cikin ɗakin.
Koda ta dago kai already Idanuwan ta sunyi jazur da ruwan hawaye kai zaka rantse wuta aka kunna a cikin su.
Khadijah ta hawo gadon cikin damuwa da tashin hankali ta ce.
"Ke ƙawata me ya faru?, Mutuwa aka yi"
Ta rintse idon ta, hawaye masu zafi da ciwo sosai suka ciko idanuwan ta,
MOHAN IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF ADDICTION INTO AFFECTION.
KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA*
FIRST 30 SUBSCRIBERS WILL BE GOING FOR #300
Pay
*VIA 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*
EVIDENCE TO *09125491597*
YOU CAN SEND MTN CARD SEND To *07046627683*
Be the first subscriber ❤️
NB _Part one is free_
©BINTOU.
Na yi gabas 🚶🏽♀️.
14th December.
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *016*
Hawayenta da take dannewa suka sauko da ƙarfin su. Saboda she is emotionally weak. Duk ƴan ɗakin suka zura mata ido, a ruɗe Rakiya da Khadija suka haɗa baki wajen tambayan ta me ya faru?, A karo na biyu. Karamin Kukan gajiya da rayuwa ne ya kufce mata, ta rasa me zata faɗa masu , da ƙyar ta iya dakatar da hawayen ta, ta ce
"Daddy ne yayi accident"
Rakiya Tace "How?, Ya ji ciwo ne?"
Ahankli ta goge hawayen snn tace
"Eh, ya samu spinal cord injury amma da sauƙi"
Gabaki ɗaya suka ruba mata ido cikin matsanancin tauyawa don har ga Allah sun yadda da maganar ta, saboda basu taɓa ganin ta cikin wannan yanayin ba, duk da kasancewar ta mai saurin kuka.
Kowacce da addu'an da take masa cikin tausayawa, yayin da take amsa wa da amin zuciyarta na raya mata da ma accident ɗin yayi da gaske, ya kwanta jinya ta yadda fita ma zai gagare shi, sai dai a kwantar a tayar, Allah ya nuna masa ikon sa ko na wata biyu ne ta yadda zai gane cewan matar da ya ɗauka a matsayin rayuwa da ƴaƴan ta da ya fifita a kan komai ba za su iya sadaukarwa don ɗaukan nauyin sa ba. Tana da tabbacin koda mura mai ƙarfi Daddy yake yi, siddiƙa ba zata haɗa numfashi da shi ba balle ta yi ɗawainiya da shi.
Cikin dabara ta zame kan ta, ta koma block A, ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun da ke muster point zuciyar ta a jagule, kewan sa take ji sosai haɗi da kishi na dabaibaye ta, sanyi ma take ji, ta rasa me ke yi mata daɗi a duniyar nan. Ta rasa wanda za ta kira ya dubo mata lafiyan sa, saboda bata san kowa nashi ba. Tunowa ta yi da Ibrahim abokin sa ne tun a Egypt tare suka yi karatu, kuma ta sanadin problem ta san shi, har ya ce yana son ta, kasancewan shi a Kaduna yake. Tabbas zai iya sanin abin da ya same shi, ko kuma dalilin rashin samun sa da take yi.
Tana tsaka da wannan tunanin kiran wayar sa ya shigo wayar ta. Ɗan halak, ya ƙi ambato. Ta yatsina fuska kafin ta ɗaga, tana jin zuciyar ta babu daɗi a kan tsakin da ta yi masa ɗazu, bawan Allah ga shi bai yi fushi ba. Kamar ko yaushe cikin taushi yayi mata sallama ta amsa tare da gaishe shi sannan tayi shiru, tana so ta ba shi haƙuri, sannan ta lallaɓa shi ta ji labarin inda problem ya shiga, amma bakin ta yayi mata nauyi, ta kasa furta komai, yanda take ji ma da a ce za ta ji muryar problem din ta na seconds biyu, sai ta yi minti biyu tana masa kuka, don ta yi kewan sa ba na wasa ba.
"Babe.... Ban ji daɗin tsakin da kika min ɗazu ba" ya faɗa a sanyaye, ta sauke ajiyar zuciya tana jin babu daɗi a ranta tace
"Kayi haquri, daga bacci na farka lokacin, kuma ai kai ne ka ja, me yasa za ka ce ina kishin problem?, Ka san dai in soyayya zan yi da problem ko kallon ka ba zan yi ba ta the first place ballantana wata soyayya ta shiga tsakanin mu"
"Babe masifa ho!, yanzu ni me na ce?, Daga magana?, Ɗazu ina miki magana baki bari na ƙarasa ba kin ja tsaki kin kashe min waya yanzu kuma daga na yi magana na ce ban ji daɗin abin da kika yi ba sai cibi ya zama kari?"
Abin ka da me neman abin kuka, tuni idanun ta suka sake karo ruwa tace
"Babe... Shi ne kake min tsawa?"
Ya kwantar da murya
"To ki yi haƙuri...."
Ta yi shuru, tana share ƙwallan da ya zubo mata.
"Babe kuka kike yi?, Ba na baki haƙuri ba?"
Shuru ta sake yi, shessheƙan ta ya fito fili.
"Oh my God, babe ki rufa min asiri don Allah ki bar kukan nan, ke komai kuka?"
Da ƙyar ya rarrrashe ta har ta daina kukan, yace
"Ya makarantar? Ya lecturer? Ya su Rakiya?"
Kunya ya so kamata jin abin da yace kuma bai yi fushi ba, tace
"Lafiya lau, Rakiya na ɗaki, baka tambayi Khadijah ba"
Ya taɓe baki
"Kawar nan taki bata so na fa, but anyways, my regards to them, ki gaya Rakiya idan ta je weekend ta kawo min makaɗen su na nupawa".
Ta guntse dariyar ta tace
"Zan gaya mata, kace kana so ka koma baƙi irina kenan" ta faɗa tana fashewa da dariyar dan ta kasa ruƙuwa.
"Nidai babu ruwana bani na faɗa ba" cewar Ibrahim shima yana dariya.
"Babe yaushe zaka zo?"
Yace
"Kina so in zo ne?"
Ta shagwaɓe, Tace
"Na jima ban gan ka ba, tun ranar da kare ya biyoka ka gudu ka bar ni"
Yayi murmushi har tana jiyo sautin sa
"Ba ke kika hana ni zuwa ba?, So kike in zo na sake yin wani laifin?"
"Dan na ce kada ka ƙara zuwa wajena sai ka ɗauke ƙafa ka daina zuwa?, Dama ni na san baka so na, ni kaɗai nake wahalar da kai na"
"Amman idan na zo ma asarar kuɗin motata zan yi, don na san ba za ki fito ba ma, ni rigimar nan taki ban san ranar da zata kare ba"
"Ka zo ka kira ni ban fito ba?, Wato ni kake kira riginammiya don na faɗa maka gaskiya"
"To ba riginammiyar bace?, Meye na tada jijiyar wuya a kan wannan maganar?, Bayan ke da kan ki kika ce baki son sake ganina...."
Shuru ta masa tana jan ƙwafa, ya ce
"To shikenan zan zo anjima shikenan"
Ta ce
"Kar ka zo"
Yace
"Sai na zo"
"Wallahi ko ka zo ba zan fito ba, gara ka adana kudin motar ka"
Yace
"To shikenan ai dama takura kai na zan yi innzo, dan ina da aiki a gabana"
Ta taɓe baki
"Kai ka sani ai.... Yawwa babe, kuna waya da problem?"
Ya ce "A'a..."
Gaban ta ya faɗi, tace
"Wani abu ya same shi ne?"
Yace
"A'a... ya je rehabilitation, kuma kin san ba'a bari su rike waya, yana nan kaduna ma, a barnawa yake treatment"
Jikin ta yayi sanyi, dama ya faɗa mata zai je yayi treatment, kafin tarewar amarya, ta shafa'a ne, muryar ta a sanyaye ta ce
"Allah sarki, to babe... Sai anjima"
"Alright, lokacin sallah ma yayi, bye, I love you"
Ya ja kalmar cikin kwantar da murya, Ƙirjinta ya buga kaɗan, ta yi saurin katse wayar, bata so ya ringa wani langwabar da murya yana cewa yana son ta hakan zai saka ta iya narkewa ta fara son shi. Yanda ta damƙa amanar zuciyar ta ga Mohan sam bata so ta sake ba wani namiji wannan damar. Yanda Mohan ya iya tafiyar da ita da tarairaya ta da kalamai masu kwantar da hankali bata jin akwai wani namijin da zai iya taka sahun sa a kan komai.
Guntun murmushin da bata san na mene ne ba ta yi, ta koma ɗakin su, ta yi sallah, tana idarwa wayar ta ta sake ɗaukan ƙara dama tun tana sallah yake ta ringing, ta daga a tsiwace tana cewa
"Kai wai Muhajir na ci bashin ka ne kake faman kirana sai kace zan gudu?"
Yar banzar dariya yayi ya ce
"Masifatu, kin san ko kina yi wa kowa ana barin ki ni bani bari don ramawa zan yi, first of all da wa kike ta waya ɗazu na kira ki ya ƙi shiga?"
"Sannu Ahmadu Abdul'azeez" ta faɗa, ya sake yin dariyar dake ƙular da ita yace
"Bana so kina yawan waya da samari, karatu aka turo ki kiyi a kaduna, kada ki ɓata lokacin ki da daman ki a kule kulen samari"
"Kai wa ya turo ka ka yi monitoring ɗina? Dan Allah ƙyale ni in yi rayuwata, babu ruwan ka da ni, meye kake ta kirana ma?" Ta dakatar da jan maganar don ta san yanzun nan zai fara gindaya mata dokoki kaman wani uban ta.
"Mela..i'm missing you guys, kwana biyu baki funding data account ɗin ki ba, yau na shigo asibitin ku ma ban gan ku a wurin karatu ba"
Muhajir ya faɗa, ta yi murmushi, ta ce
"Muhajir kana ina ne?"
"Ina wurin bishiyan da kuke zama in kun fito karatu".
Zakiyyah ta dubi Khadijah wacce tun da ta fahimci da wanda take wayan ta maida hankalin ta gare ta, tace
"Ƙawata sako hijabi mu tafi"
Tun bata rufe baki ba Khadijah ta diro daga kan gadon ta, ta ɗau hijabi, tace
"Mu je, ya kai mu Ostrich mu ga gari..."
Itama Zakiyyahn ɗan kwali ta ɗaura kan kayan sanyin da ke jikin ta, ta yafa mayafi, ta fito Khadijah na ƙwala kiran Rakiya, rakiya da ke ɗaki na uku bayan nasu ta leƙo, fuska babu annuri da alama yunwa take ji.
"Ke maza maza sa hijabi ki fito mu tafi"
Rakiya ta ce
"Ku ni yunwa nake ji, bari in gama girki"
Khadijah ta ja tsaki
"Keh banza, Ostrich zai kai mu"
Ita ma Rakiya ta shiga ta shirya ta fito suka same shi a wajen bishiyan yana zaune yana jiran su, tun daga nesa yana ganin su ya fara murmushi har suka ƙaraso wajen sa.
"Melanin masoyiyata, ke kullum fuska a haɗe kaman hadari haba, Khadijah ku koya mata yadda ake murmushi mana" ya faɗa ta harare shi tana cewa
"Wace masoyiyar taka?"
"Haba Habeebaty, laifi ne in masoyi ya kira masoyiyar sa da Masoyiya?".
"Hmmm, kai yi shuru dan Allah kada a ji ka a ɗauka da gaske ne..., A me ka zo?"
Ta ture wancan maganar, ya nuna ƙafar sa
"A legxus ɗina mana"
Duk suka kwashe da dariya amma banda Zakiyyah, ya dubi su Khadijah da ke dariyar draman su ya ce
"Waennan fa?, Ba dai tare za mu tafi ba?"
Khadijah ta ce
"Ba wai bane, tare za mu je wlhy, don ka samu ban gayyato sauran ƴan squad ba?"
Yayi ƙwafa ya ce
"Da kin gayyato su ai, sai mu baje a nan mu yi ta hira abin mu, ni ina zan iya da common room members ɗin ku?, Sai kace gayyan gidan bikin?"
Rakiya ta yi dariya ta ce
"Mu je dai, Ni wlhy yunwa nake ji"
Dubanta yayi ya ce
"Ke ban gane ba, yunwa kike ji kaman ya?, Wa zai ciyar da ke?, Ni dan masoyiyata na zo, ita da ta gayyace ku ita za ta ji da ku"
Zakiyyah ta yi tsalle ta tallafe mai ƙeya ya dafe yana dariya, ta ja kunnen sa ta ce
"Oya...! Mu je"
Ostrich Bakery suka nufa, suka jido ice cream, cheese, Cookie da moon cakes da yawa, da aka je wajen biya ko kallon sa bata yi ba, ta fiddo ATM ɗin ta za ta biya, ya ƙwaɓe hannun ta yana faɗi
"Keh... Rufa min asiri, ya za'a yi na rako ku waje sannan ki biya kuɗin?, Bari dai na biya in mun fita sai ki dawo min da kuɗina"
Ya faɗa yana miƙa nasa ATM ɗin, Zakiyyah ta sauke kan ta tana murmushi yace
"Wannan uban kayan da kuka jido ma ko na bar ki ki biya kuɗin, na san da ke bankin ki za su kai ba"
Zakiyyah ta yi masa banza bata sake cewa komai ba, don kunnen ta rufe yake da earphone, ta ƙure ƙarar, sai Khadijah da Rakiya ke ba shi amsa, duk hiran da suke yi bata sake cewa komai ba har suka koma makarata, Khadijah ta ce
"Mu samu ɗaya daga cikin classes ɗin Admin mu zauna mu ci abin mu don wallahi muna zuwa hostel sunan mu sorry"
Rakiya ta ce "ai kuwa, yadda nake jin yunwar nan aka bari wani ya ga kayan nan ai na kaɗe har ganye na"
Ita dai Zakiyyah bata ce komai ba, tana danna waya da sauraron waƙa, hannayen ta zube cikin aljihu, fuskar nan cunkus babu annuri, haka suka isa Admin block ɗin.
Ita haka take in ka ga ta yi farin ciki na lokaci ƙanƙani ne, haka bata yawan magana mai tsayi sai in vibe din ku yayi matching, idan ta yi ma na taƙaitaccen lokaci ne, mood change ɗin ta yana occuring very fast, mutanen da ke tare da ita sun riga sun saba shi yasa basu cika damuwa ba, wata ran idan baƙin halin nata ya motsa sai ta wuni bata ce ma kowa ƙala ba, ta kuma ɗaure fuska ta yadda babu wanda zai yi gigin yi mata magana , so tari idan ka ga ta yi hira da dariyan da ya zarce na minti goma to video call suke da problem, sai su yi awa biyu suna video call yana sa ta dariya ba tare da mood ɗin ta ya canza ba, gaba ɗaya Muhajir bai ji daɗin sauyawan ta ba, koda suka samu wuri a class suka zauna, ko kallon ice cream ɗin da suka siyo bata yi ba, ta maida hankalin ta sosai a danna wayar da take yi, sai zuba yake amma ta ƙi tanka shi. Zare earphone ɗin yayi cikin tsokana yace.
"Wai ke Mela duk kuncin nan a kan na biya kuɗin ice cream ɗin da kuka siya ne?"
Ta kalle shi da sleepy eyes ɗin ta, ta yi rolling ɗin su a kan sa, cikin gajiya da rigimar sa ta ce
"Muhajir what did you want?"
Ya dafe zuciyar sa "Urhch!, Za ki kashe ni, don Allah ki sake rolling eye balls ɗin ki...."
Harara ta galla masa ta girgiza kan ta " Muhajir kana shiga rayuwata da yawa"
A yace
"Ke nan har wani rayuwa kike da shi?"
"Ai kam ni ke da rayuwa, saboda ni kaɗai na san matakin da na taka kafin na kai matsayin da nake a yanzu"
"Wane irin matsayi gare ki?, Matsayin da kike da shi as student ko....?"
"Idan zama student a collage of nursing ba komai bane ka kwatata zama ɗaya daga cikin mu mana, ɗan rainin hankali"
Ta faɗa tana buɗe ɗaya daga cikin robobin ice cream ɗin da suka siyo, ta sa spoon ta ɗebo dayawa ta kai bakin shi, ya buɗe bakin yana dariya, haka ta yi ta ɗura mai, da ya buɗe baki zai yi magana sai ta sa masa spoon ɗin a baki, a haka har ya shanye roba ɗaya, Rakiya da Khadijah na tsokanan su suna cewa sun dace, ta amince masa kawai tun da yana son ta, Zakiyyah ta ce
"Allah ya isar min, ina da problem me zan yi da wannan abin? "
Gaba daya suka kwashe da dariya Khadijah tace
"Ƙawata ban da cin fuska, meye a jikin Muhajir da ba za'a so shi ba?, Na tabbata koda ban taɓa ganin problem ɗin nan naki ba ba zai nuna mishi kyau ba, in ma kudi ne da problem din ba zai nunawa Muhajir ba, don kowa ya shaida muhajir ba ɗan zaman banza bane, yana da sana'ar sa mai rai da lafiya, ga iya soyayya da tattalin mace, ki duba yadda yake tolerating halin ki, wallahi da wani ne da tuni kun raba jaha".
"Gaya mata dai Deeje" Rakiya ta faɗa tana mata gwalo ta harareta tace
"Munafukai kwama faɗi gaskiya, in ma abu ya sa maku a ice cream har ya sa kuke yabon sa haka to ban sha ba, na sha tabara na sha yasin, aniyar kowa ya bishi"
Muhajir da ya gama shan azaban sanyin icecream din da take ɗura masa ya buɗe baki zai yi magana sai ta yanko moon cake ƙato ta saka mai a baki. Ba shiri ya miƙe, da ƙyar ya haɗiye na bakin shi, yana sauke numfashin azaba yace
"In kina wa Allah ki ƙyale ni haka nan, I'm the last born of my family, kada ki kashe masu ni"
*LITTAFIN MOHAN NA KUƊI NE*
Mutane talatin da za su fara siyan littafin za su siye shi a kan farashin #300, duk wanda zai siya daga baya zai biya normal Price #500
*Za'a biya ta wannan lambar 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*
Sai a tura receipt ko