Showing 21001 words to 24000 words out of 72389 words
ya ɗauko ɗaya daga wanda aka yi hanging a mirror ya ɗaura ya koma ban ɗakin, ya haɗa ruwa mai ɗumi sannan ya faɗa ciki, yana sauke ajiyan zuciya a hankali.
Minti talatin ya fito jikin sa na ƙamshin sabulun da ya yi amfani da su, suman kan sa da ke nan kamar na arab ya mammane da fatar sa, ya tsaya gaban mirror ya fara shafa mayuka masu tsananin ƙamshi.
Lungu da sako na jikin sa babu inda bai ji tattali ba, kafin kace wani abu ƙamshin mayuka da turaruka ya kama ɗakin har da jikin sa. Motsi ya ji ta bayan shi, ya waiga, bai ga kowa ba, hakan ya sa ya cigaba gyara jikin sa yana wasu abubuwa a gaban mirror kaman ƙaramin yaro, (Irin yadda kowa yake yi idan ya ƙebance a gaban mirror, musamman idan babu mai kallon mutum 😂)
Motsi ya ƙara ji, wannan karon motsin mai ƙarfi ne, a razane ya juya, yana damƙe towel ɗin sa gam don ba ɗaure shi yayi ba. Mutum ya gani tsaye a bayan sa sai wani kallon sa take. Gaban sa ya faɗi da ƙarfi, ya ja da baya yana furta innalillahi wa'innailaihirraji'un, wani irin shiru ne ya gifta a cikin ɗakin, ta tako inda yake cikin kissa, ya ƙara ja da baya, bakin sa na rawa ya ambaci sunanta
"Maryam..."
"Mmm... Me ya kawo ki nan?, Tun yaushe kike nan?"
Gabaki ɗaya ya ruɗe, bata ce komai ba sai ma kallon shi da take yi tana wani shegen murmushi da ita kaɗai ta san fassarar sa.
"Ki fita.... Maryam don Allah ki fita, ki jira ni a falo ina zuwa"
Ya faɗa a rarrabe yana sake damƙe towel ɗin sa, zuciyarsa na luguden daka wani ɓari na tunaninsa na gaya masa cewa da wuya idan Maryam ba mayya bace.
Maryam ta saki murmushi, tana jin ta kaman tana reto a sararin samaniya wani shauƙi na ɗiban ta, ji take kaman ta rungume shi, don amon muryarsa kaɗai wani irin sauti ne da bata taɓa jin makamancin shi ba, murya ce mai cike da jarumta duk da tsoron da ta hango a idanun sa ƙarara amma hakan bai bayyana a muryar sa ba, ga kuma yawan mayen da ya maida sautin shi kaman yana waƙa idan yana magana.
"Ki fita na ce!"
Ya faɗa a ɗan tsawace da muryar sa zurfi da kauri sannan a naɗe da wani irin zak'in da ya kara haska kwarjininsa.
Sai ta had'iye yawun da bata san dashi a bakinta ba sannan ta lumshe idanun ta, tana jin soyayyar sa na ratsa jini da ɓargon ta, tana jin a yau ko kashe ta zai yi wallahi ba zata fita ba, har sai Hassan da Alhaji sun shigo, idan kuma basu shigo ba, babu shakka sai ta mamaye shi ta yi masa fyaɗe.
"Da kaina na shigo, ta ƙofa kuma..."
Yar ƙaramar muryarta ta ba shi amsa a natse, babu alamun fargaba ko damuwa a tattare da ita.
Then get out, ki fita....!"
Ya faɗa cikin tsawar da ta kaɗa hatta 'ya'yan hanjin cikinta ba hantar ta kad'ai ba. Ƙoƙarin matso shi ta sake yi, tana bin shi da wani kallo mai wuyar fassaruwa. Yayi tsalle ya dire kan gadonsa, a tsaye, ya nuna mata ƙofa.
"Don girman Allah ki fita, ki jira ni a falo, bari na sa kaya..."
Dai dai wannan lokacin ƙofar ɗakin ta bud'e kuma ba tare da b'ata lokaci ba, cikakkiyar muryar Alhaji Naseer Batta tayi sallama a sanyaye cikin ɗakin, ya shigo sanye da fararen kaya na babbar riga kan sa babu hulla, ɗan gaban goshin sa a yanzu Hassan yana biye da shi.
Dukkansu suka juya a tare, Maryam taja numfashi cikin k'irjinta kamar mai shirin shid'ewa.
Not edited
Me kuke tunanin zai faru a nan?🤔
Mai Hassan ya shirya?
Na yi gabas
Comment and share
Bintou🦋
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *008*
Sakan ɗaya, biyu uku,....Shiru ya gifta na wasu 'yan sakanni a ɗakin yayin da tarin abubuwa ke yawo a cikin kwakwalwar Alhaji, kuma a ciki ya rasa wanda zai kama ya rik'e a matsayin tunani, yana ƙoƙarin ƙaryata azahirin abin da idanun sa ke gane mai.
Mohan kuwa tsabar tashin hankali, bai san sadda ya zube a ƙasa ba, jikin sa ya hau rawa, zuciyar sa na mamaki da fargaba suka haɗe mai a lokaci guda.
Ya kasa ɗago kan sa ko sau ɗaya,ya riga ya sani cewa ta sa ta ƙare Abba ba zai yi masa uzuri ba, ragowar mutuncin sa da ya rage a idanun Abba ya gama zubewa.
A b'angaren Maryam kuwa, ji tayi bata tab'a tsintar kanta a wani irin gigitaccen hali irin lokacin ba, duk da cewan hakan ta so, amma ganin Abba a gabanta ya sa lissafinta ƙwacewa, ta gigice, cikin matsanancin tashin hankali ta durk'ushe gwiwoyinta ita ma, cikin kwakwayon irin tsugunnon da Mohan yayi.
Alhaji Nasseer batta ya kalli Mohan, daga shi sai towel, ga towel ɗin ba a ɗaure yake a ƙugun na shi ba, sai faman rirriƙe shi yake gudun kada ya zamo, Maryam kuma wani material ne a jikin ta ya ɗan kamata kaɗan, amma tsabar yadda idanun Alhaji Naseer ya rufe, gani yake kaman tsirara take, hakan ya sa ya kau da idanun sa a kanta tun kallon farko.
Hoton da zuciyar sa ke haskawa ya banbanta da zahirin abin da ya faru, tuni kwakwalwarsa ta fassara masa shi da wata irin zato na daban, zaton da bai tab'a haskowa a akan kowanne mutum na duniya ba balle kuma Morhan.
Gani yake kaman lalata yarinyar yake yi, shigowan sa ya sa ya sake ta, ya kuma ɗaura towel. Yaji kansa ya sara a lokaci guda ya ji ciwon zuciya na shirin kama shi. Maganar da ta kawo su wajen Mohan a kan auren sa da suka Zainab sai ya ga babu amfanin shi a yanzu, don ba zai yiwu a haɗa auren kamilar mace kaman Zainab ƙanwar matar sa da shi ba.
"B...B.Barka da ju... Juma'a Abba..."
Muryar Mohan ya katse shi a rarrabe, kan Abba ya ƙara sarawa, ya yi shuru cikin takaici. Shurun da yayi ya ba Mohan daman aron jarumta ya fara ƙoƙarin kare kan shi, duk da cewan ya san abu ne mai wuya Alhajin ya yadda da shi.
"Abba.... dawowata daga masallacin juma'a kenan, na shiga ban ɗaki, n...na yi wanka, in.. ina fitowa sai... na tarar da ita ...ni kaina ban san yadda aka y..."
Sai Maryam tayi saurin katse shi da faɗin
"Abba... Ka yi haƙuri, mun yi kuskure, sharrin shaidan ne..."
kan ta a ƙasa, hakan ya ƙara zurma zuciyar Alhaji cikin ƙogon zato, cikin jin raɗaɗi a zuciya Mohan ya ɗago idanunsa da launinsu ya koma jazur, fuskar sa abin tausayi ya ce.
"Maryam ki ji tsoron Allah..."
Maganar nasa ya yanke ba don wani ya tsaida shi ba ko kuma don wani abun ya katse shi, sai don yanayin fuskar Alhajin dake tsaye a gaban su, wani yanayi da tunda yake a rayuwarsa bai taɓa shiga irinsa ba...
Ita kuwa Maryam duk da tsoron da take ji, hakan bai sa ta sake ɗagowa ba, ta yarda ta rasa komai ciki har da mutuncin ta in dai za ta mallaki Mohan.
Abba ya juya idanunsa cikin ɓacin rai, ya haɗiye wani abu mai nauyi da ya tokare mai ƙirji. Ya dubi Hassan, da ke tsaye yana ji kaman ya zuba ruwa a ƙasa ya sha tsabar farin ciki. Yace ya yi wa Maryam rakiya zuwa gidan iyayenta, sannan ya nema masa izinin zuwa nemawa Mohan auren ta bayan la'asar
****
"Mummy Good News..."
Muryar Hassan ta ratsa falon Halimah mahaifiyar sa tun kan ya shigo.
Momi da ke zaune a katafaren falon ta na alfarma ta murmusa ta ce.
"Hanzarta ka faɗa min Shalelena"
"Mummy, Ina wancan ƙanwar matar ya Ameen, Maryam, yarinyar nan mai shegen rawan kai, ƴar tiktok ɗin nan?..."
Mommy ta ɗan yi shiru tana sauraren sa, don ba gane yarinyar ta yi ba, fahimtar hakan ya sa ya kamo hannunta..
"Kin dai san matar ya Ameen, ai tana da wata ƙanwa wacce fita zakka a gidan su, na ji labari an ce har bin maza tana yi, kuma tana.... Bari dai ina yi shuru, amma a taƙaice Mum, idanun yarinyar nan a buɗe suke sosai, amma idan kin gan ta a zahiri, sai ki rantse ko yatsa kika sa mata a baki ba zata iya ciza ba."
Ita dai idanu ta zuba mai, tana sauraron muryansa da ke fitar da amo mai sanyi da dadin ji, ta rasa me yasa take yawan shagala da sauraron muryar sa, domin cikin baiwar da Allah yayi wa zuri'ar ALHAJI Naseer, akwai baiwar sautin murya mai sanya natsuwa.
yanayin kallon da take masa zaka fahimce cewa t ƙosa ya faɗi asalin tushen zancen.
"Abba zai nema wa ya Moha aurenta.....""
A zuciye cikin rikicewa Hajiya Halimah ta lailayo wani ashar ta narka masa
"Dan kaza kazan Alhajin ni zai yi wa cin amana?, Nan muka gama magana da shi ya ce nnjima da yamma bayan la'asar za su je su nema masa auren ƙanwata Zainab, mun gama magana da shi sannan zai zagaya ya ce zai aura masa wata?"
Da mamaki Hassan ke kallon ta.
"Me kike nufi ne Mum?"
Tace
"Burina kenan tun Mohan na ɗan ƙaramin yaro, na daɗe ina addu'an Allah ya nuna min ranar da ƙanwata zata auri Muhammad, don bata dace da kowa ba sai shi"
Yatsine fuska ya yi a ransa gace "_Romon baka bana kwarya bane, hmmm ai Aunty Zee ta fi ƙarfin wannan lusarin_ " , a fili kuma cewa yayi.
"To ke Mum wace ƙadddara ce ta kai ki yin wannan banzan tunanin?, Allah na tuba mai Mohan yake da shi da za'a so haɗa zuri'a da shi?, Kina gani fa ko aiki baya zuwa, ba ya neman na kan sa, ga shi a rame, duk shaye shaye ya gama tsotse shi. idan kyau don kyau ya sa kike so ki haɗa su ma a banza don shaye shaye duk ya lalata shi, ga shi ba shi da wani kuzari, kina gani dai wannan yayan nawa gawa ne da rai don babu wani amfanin da yake iya taɓuka wa kan sa balle a yi tunanin samun wani abu a ƙarƙashin shi, ni wlhy haushi yake bani, shi yasa na haɗa mai wannan tuggun ta yadda Alhaji zai fasa auren..."
"Don't tell me kai ne silar rugujewar plan ɗina"
"Eh mana mum..."
Nan ya labarta masa abinda ya ƙulla
"Kai wallahi baka isa ba, sai an fasa auren nan, dole Zainab ta auri Mohan"
Ta faɗa tana ƙoƙarin latsa wayarta, Hassan ya ƙarbe wayar
"Mum, anya kan ki ɗaya kuwa, lamarin nan naki fa kullum ƙara gaba yakeyi gara a tari abin tun beyi nisa ba, Alhajin za ki kira ki ce mai ya fasa abin da yayi niyya?, Mohan ne fa?, Shi kike yi wa wannan hargowan?"
Hajiya Halima ta nufoshi tana haki, cikin ƙanƙanin lokaci har ta fita a hayyacin ta tsabar firgici da sa wa kai masifa.
"Dan ubanka Hassan ka bani wayata, kai na ɗaya? mahaukaciyar kake so kace mun?"
Hassan yayi wata dariyar shaƙiyanci ran sa fesss, yaja ja baya wayar a hannun sa, dan ya san tana iya kai masa duka yace
"Ni ba haka nake nufi ba, bafa ciwon hauka bane ciwon damuwa aka ce kamar yana damunki kuma idan yayi yawa ne yake komawa haukan kinga ba zan so haka ta kasance ba gara ki mum ɗita tawa ni kadai, ya kamata ki daure ki Asibitin nan asan abinda za'ayi dan wlh abin da kike faɗi alama ce ta taɓuwa.."
Bai dire maganarsa ba ta fashe da kuka tana cewa
"Sai dai kaga hauka a kanka dan iskan yaro, fice mun daga ɗaki kafin nayi maka baki, ɗan marasa mutunci"
"Allah huci zuciyarki Uwata ta kai na, dama fitan zan yi, za mu je mu tambayo auren babbban yayaaaa
Yana gama faɗa mata yayi ficewar sa yana fito.
****.
*4:15*
Abba ya ba su hannu suka gaisa daya bayan dayan sannan shi ma ya samu guri ya zauna. Cikin natsuwa Abba ya shiga zayyano masu abin da ya faru dalilin zuwan su. Malam Sulaiman ya ɗaga kai ran sa babu daɗi, ya ce
“Assha.... Asssha, ban ji daɗin wannan al'amari ba, Amma Alhaji, ka ce ba su aikata komai ba, amma me ya sa kake nema masa auren ta"
Alhaji Naseer ya gyara zaman sa, ran sa babu daɗi ya ce
"Saboda gudun zargi, kuma yarinyar ce ta dace da shi, sai dai ban sani ba ko za ka iya bamu auren ta duk da na san da wuya, saboda halin yaron"
"A'a.... a'a Alhaji, Ni ai taimakona kuka yi, tsakani da Allah, ba zan ɓoye maka ba yarinyar tana da rigima, anya ta dace da ɗan ku kuwa?"
Abba ya ce
"In dai ba fasiƙanci take yi ba, bani da matsala da wannan, aure na iya sauya mutum a kowane lokaci'
Malam sule ya jinjina kai
"Menene genotype ɗin yaron naku?"
"AA ne..."
"Yarinyar ta wajena AS ce, Idan babu damuwa a masu gwajin cututtuka, sannan a sanar da liman, sai a ɗaura auren bayan sallan magrib"
Alhaji Naseer yace
"Da gaske kake....?"
Malam Sule ya ɗaga kai da sauri, yana ganin ai shi za'a yi wa alfarma.
"Ƙwarai kuwa"
"To madallah, bari na kira yaron na sanar da shi, dama tare na zo da ƴaƴana biyu, da manager ɗina, sai su siyo goro a fara shiri"
Nan take ya kira likitan sa ya tafi har gida, yayi masa Rapid antibody test, itama Maryam aka kaita asibiti aka yi mata, cikin Sa'a duk basu ɗauke da wata cuta. Kafin lokacin kuwa har an siyo goro, an kirawo mutane, Abba ya sa Mohan ya shirya cikin wata farar shadda mai ɗaukan ido, da ka gan shi zaka hango wani rauni da ke tattare da shi, irin raunin nan na wanda ya rasa babban gaɓa a cikin rayuwar sa.
Abu kaman wasa, ana idar da Sallah liman ya ɗaura auren Muhammad Sani Naseer Batta, da Maryam sulaiman a kan sadaki dubu ɗari kadan. Tare da kyakkyawar kyautar tsadaddiyar agogon diamond Audemars Piguet daga hannun Alhaji Naseer Batta, shi kuwa Hassan tsabar murna har kyautar mota yayi wa amarya, Motar da Zakiyyah ta hau, ta yi masa wanka da datti, dama tun ranar ya daina hawata
Har wajen mota Malam Sule ya rako su yana gani kaman Alhaji ya gama masa komai a duniya
“Ranka ya dade na gode, Allah ya sa danka ya rike mana ita amana”
Abba na murmushi ya ce.
“Ameen, in sha Allah ba za ku yi nadamar wannan haɗin ba"
Suna isa gida Hassan ya nufi bangaren Ummie yana murmushi kana ganinsa ka san yana cikin farincikin da ya dade bai yi ba.Farin cikin sa kasa ɓoyuwa yayi, sai rabawa ƴan aiki goro da dabino yake yana shaida masu an ɗaura auren Mohan da ƙanwar matar yayan su. Kowa sai mamaki yake.
Bai tarar da Ummie a falo ba, sai yayar su Mohan Hajiya saude sa da Aisha suna hira.
Ya zauna saman kujera yana cigaba da murmusawa. Hajiya Saude ta kalle shi da mamaki, ya ce.
“ Hajjaj Auren Muhammad Sani aka daura...”
Hajiya Saude da Aisha suka kalleshi jin abin da ya ce.
“Wane irin aure kuma?”
Hassan yayi murmushi
“Aure dai Hajiya, Wallahi aure aka daura masa yanzu nan, daga zuwa neman aure”
Hajiya jidde ta taɓe baki
“Allah sarki to su ba su da labarin yana shaye shaye ne? Ko dai duk kanwar ja ce suke neman a rufawa juna asiri?”
Dariya yayi, fuskarsa soo innocent kaganbsa zabka iya rantsewa cewa ko da an saka mai yatsan makiyin sa abakin shi ba zai iya taunawa ba. Nan kuwa taunawa zai yi tsab har da ƙashin. Cikin dariyar yace
“Hajiya yarinyar irin sa ce ai, don ana zargin har neman maza tana yi”
Saude ta riƙe baki
"Kuma Alhajin ya san da haka?"
"Aahhh....!, To ba neman kai ake yi da shi ba?"
“oo ni, wannan wace irin ƙaddara ce?, Gabaki ɗaya yaron nan ya gama zubar mana da mutuncin a idon ƙananun mutane, toh, Allah dai ya sa hakan ya zama silar shiryuwan sa"
***
Gidan su Maryam kuwa rikici ne sosai ya hautsine jin abin da Malam ya aikata.
"Lallai malam ba zan yadda ka mana wannan aika aika ba, don me za'a ɗauki ƴa sukutum a ba riƙaƙƙen ɗan shaye shaye?""
Mahaifiyar Maryam ta faɗa tana kumfar baki, Malam Sule da ke riƙe da sadakin Maryam da mukullin motar da aka aiko mata ya ce
"Keh ba za mu bane ya tadda mu je?, Eh?, haɗa auren Maryam da Muhammad Sani menene abin asara a nan?"
Hajiya larai, kishiyar mahaifiyar Maryam ta sheƙe da wata dariya na izgilanci
"To kuma menene?, Don an ɗau ƴar iska an ba wa ɗan iska mashayi?, Ai babu bashi kenan, cip cip, babu over size in ji turawa "
Maryam da ke tsaye gefen ummanta ta manna mata harara.
"Ni dai ba ƴar iska bace''
"In banda iskanci mai ya kai ki gidan sa, ke har kin isa ki ce ke ba Yar iska bace?, Uban menene bamu gani a gidan nan?, Samari da alhaxawa nawa kike canzawa a sati?, Wayar ki kuɗin ta sai ta siye gidan nan, amma ko jarin garin kwaki ubanki ba yi da shi, haka muke kwana da yunwa, ke kina can kina shimfiɗa da gasasshhiyar kaza"
"Ke larai abin naki hassada ya koma?..."
"Ƙyaleta umma, idan ma yawon nake yi ina ruwan wani da ni?, Daɗin abin yawo nake yi, ban taɓa aikata fasiƙanci ba, ƴar ki fa?, Har cikin shege an zubar mata ga ta nan a gaban ki ta kasa auruwa"
sosai hayaniya ya kacame a tsakanin su, sai da Malam ya shiga tsakaninsu da faɗin duk wacce bata shiga taitayin ta ba wllhy a daren nan zai sallameta ta tafi gidan ubanta kafin su natsu suka zazzauna suna hararar juna.
Zama Malam yayi a tsakar gida, yana ƙara basu labarin yadda abin ya faru da kyaututtukan da ta samu. Umman Maryam ta rangaɗa guɗa tana faɗin ƴaƴanta sun yi goshi.
Mama Halira ta taɓe baki
"Tabdi ai kam kila ba zata wuce gobe ba zai sake ta, da alama ba su da labari ne, shiyasa suka zo... kai kuma Malam da yike kana neman a raba ka da abun kunya ai dole ka rike su a daura auren a gurin, maimakon ka yi sadaka da ita masallac"
Malam girgiza kai yana murmushi.
"Ciwon hassada ce ke damun ki, da za ki saukar da kai ki ci arziki da ya fi muki"
******
*8:16pm*
Ya shigo ɗakin Ummie da sallama, ta amsa ciki ciki. Hadadden ƙamshin turaren sa yasa ta