Showing 54001 words to 57000 words out of 72389 words

Chapter 19 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4960

ƙarya da zai nuna tana tarayya da Maleek tun da can, har da cikin sa ta zubar, fitan da suka yi a motar sa ma asibiti ya kai ta don a juye mata mahaifa, ke kuma baki san suna tare ba, daga an faɗa miki an gan ta da shi kin zo jin ba'asi sai ta ci miki mutunci, wannan sharrin tsaab zai sa a koreta a school ɗin ku, saboda na sha jin labarin yadda ake koron mutane a nursing school"

Hassan yayi dariya a hankli sai ya koma ya yi relaxing bayan sa a kan single sitter yana kallon Yusee, tabbas yaron hatsabibi ne, Zee tace


"Shegiya Yusee kan ka yana kawo wuta, amma ta yaya za mu ƙulla duk wannan ba tare da ta nemi kare kan ta ba?, A ina za mu samu likitan da zai bada shaidar an zubar da ciki?"
Yusee yace
"Idan da hujjah ai bata isa ta kare kan ta ba, ko Oga Hassan"

Hassan yace
"Ka iya tsara zance Yusee, i wish na nemeka a lokacin da nake bukatar shawara, ga shi na aikata gaban kai na, familyn tsohon sun kai magana gun ƴan sanda"

Zee ta ce
"Wane tsoho kenan?"
A hankali ya ɗau glass ɗin juice ɗin da ke gaban shi, yayi small sip yana lashe labbansa da yayi wani irin taushi and pink yana dan taɓewa girarsa daya a dage yace
"Baban wata yarinya... I don't even know her, ta yi min rashin kunya, sai na rama a gun ubanta"
Nan ya kwashe abin da ya faru tsakanin sa sa Zakiyyah ya gaya masu, ya ƙara da cewa
"Na sa an ɗauko shi ne don in azabtar da shi, sannan in yi masa video tsirara in watsa a internet ta yadda idan ta gani sai zuciyar ta ta buga ta mace a banza, sai daga baya na samu labarin cewa yarinyar bata son Mahaifin nata, hasalima idan na watsa hotunan shi babu abin da zai ƙara mata illa ma farin ciki"
Murmushin gefen baki zee ta yi ta ce
"Hassan...!, Abin da ka yi ka yi daidai, ai koda a ce bata son Mahaifin nata ba zata so ta gan shi a wulaƙance ba, kar ka manta duk lalacewan uba uba ne, so squeeze him more, ka azabtar da shi yadda ka so, ka masa videon sannan ka jefar da shi a wulaƙance, ka yada a duniya, dole ya girbi abin da ƴar sa ta aikata idan ita ƴar halak ce hakan ba ƙaramin taɓa ƙimar ta zai yi ba, koda nan gaba aka zo neman auren ta sai an tada maganar"

Sosai Hassan ya ji daɗin huɗuban Zee, a take a nan ya kira yaran sa da ke tsare da Daddy ya ce su yi masa tsirara su yi masa video a wulaƙance, su ma suka yi yadda ya umurce su, suka kunna music, suka tilasta masa yayi rawa, yana rawa suna ɗaukan sa, bayan sun gama abin da za su yi sai suka ɗauke shi a motar su bayan sun rufe masa fuska suka yasar da shi a bolan bayan gidan sa.

Zuciyar Zee Fesss ta koma Kaduna, aljihun ta cike da dalolin da Hassan ya bata, ta kama hotel, don ta rantse ba zata koma hostel ba sai komai ya lafa, ba zata iya fuskantar mutane da tarin kunyan nan ba, a ranar Abdul maleek ya kirata ya kalailayeta da kalamai har ta yadda da shi, suka koma kaman da. Kuma a washe gari ta samo manafuƙar da zata shiga jikin Zakiyyah don sanin kowacece ita.

Ita kadai ta ringa sakin murmushi lokacin da ƴar leƙen asirin ta ta gano mata headlines ɗin labarin Zakiyyah. Satin ta uku bata zuwa makaranta. Tun mutane na expecting da tsimayin ganin Zee da ƴan sanda sun zo kama zakiyyah har suka haƙura, suka yadda Zakiyyah ta ci Zee da yaƙi. Kuma kunya ce ya hanata zuwa makaranta, wasu ma cewa suke halan ma barin makarantar ta yi.

Saturday 21st December, a ranar aka sallamo Mohan,ya fito yana mai daukawa kan sa alƙawarin in sha Allah har ya koma ga Allah ba zai sake shaye shaye ba.
Alhaji Naseer Battta ya turawa manager ɗin sa na kaduna kuɗi domin yayi provision sannan ya kama hotel ya kwana, washe gari zai turo driver ya ɗauke shi. Manager ya ciro kuɗaɗen ya ba Mohan Cash, mohan ya ciri wasu kaso daga cikin kudin ya siya waya da sabon layi, sannan ya je shopping ya siya kayan sawa, sabulan wanka masu ƙamshi, turaruka da takalma daga ƙarshe yayi booking hotel. Yana isa ɗakin ya loda kati ya kira numban Zakiyyah wanda dama ya riga ya haddace shi a kan sa. Bugu ɗaya ta ɗauka

Da husky and Coarse voice nashi mai cike da natsuwa plus professionalism ya yi sallama, abinci take ci a amma sai da ta ƙware ta hau tari babu ƙaƙƙautawa, da ƙyar ya lafa mata bayan ta sha ruwa. Bai ce da ita komai ba har ta gama.

"Problem...."

Ta kira sunan shi harshen ta na harɗewa.
"Solver..."
Muryar ta kasa ƙasa ta gaishe shi
"Good afternoon"
Cikin lumshe ido da budewa ya amsa
"Evening my Solver"
"Kai problem neman magana, Evening fa nace''
Yace
"Yanzu ake evening a garin ku?, It's already 5pm "

Batasan sanda murmushi mai sanyi ya kufce mata ba, yau bata jin jayayya, amma da za ta biye masa haka za su ƙarar da katin wayan sa suna jayayyya a kan maganar.

"Kin yi shuru, video call?"
Tace "Eh,..." Ta amsa masa a takaice, ya katse wayar sannan yayi downloading Whatsapp ya buɗe da sabon layin sa sannan ya kirata video call, har yanzu abincin take ci.

Ya zuba mata idanu yana kallon yadda take cin abinci tana murmushi she looks really happy nevours and emotional at same time.

"Abinci kike ci?"
Ta ce
"Za ka ci ne?"
Ya girgiza kan sa
"A'a abincin nan ai sai ku"

"Eh a bar mana kayan mu, mu da muka zo duniya don mu ci abinci, wasu kuma sun zo duniya don su sha sigari"
Ƙaramin dariya yayi sannan ya ce
"Malama ba dai da ni kike yi ba ko?"
Ta ce
"Ka ji na kira suna ne?, Tukunna ma, nan ina ne?, Ka fito ne ko an sallamo ka?"
Yace
"Abin da ya kamata ki tambaya kenan tun tuni, an sallame ni gobe zan koma gida"
A raunane sosai take kallonshi tace
"Shi kenan za ka bar Kaduna ba za mu sake haɗuwa ba?"

Idanunshi ya yi rolling zai bata attitude, sai taji ranta ya fara baci, shekaran su 7 suna tare, basu taɓa haɗuwa ba sai ranar da suka haɗu a asibiti, kuma basu samu wani lokaci tare ba, idan da amana ma ai shi ya kamata ya nemi su sake haduwa don wata ƙila wannan zuwan ya zamo zuwan sa Kaduna na karshe tuni idanun ta suka fara ƙwalla, wani irin soyayyar sa na mamaye jini da ɓargon ta, soyayyar da take da tabbacin shi zai yi ajalin ta, don Mohan bai ma san tana yiba

"I'm just kidding, sarkin kuka, hawayen ki suna da arha da yawa, wasa nake miki.... za mu iya haɗuwa gobe?"

Da sauri ta gyaɗa masa kai, idanun ta na zuban hawaye.
"To ki daina kuka".
Ta share hawayen ta sannan ta ce
"Na daina"
Ya ce zai zo makarantar su da safe, ta shirya za su yi yawo har sai sun gaji. Daren ranar yayi mata tsayi sosai, koda ta farka tana idar da sallan asuba ta tsaya jiran kiran sa, sai kusan goma ya kirata ya ce ta same shi a gate, sai da ta ɓata minti talatin tana shiryawa kafin ta fito.


Kallon ta yake har ta ƙaraso gun shi bai daina kallon ta ba, sanye take da wata haɗaɗɗiyar Arabian gown mai shigen bubu kalar maroon mai adon black stones, ta yafa baƙin mayafin rigar in a simple way. Yau kam an dan yi kwalliya har da jam baki maroon, idanun ta sanye cikin medicated glasses din da ta manta rabon da ta sa shi.

Ganin ya shagala da kallon ta sai da tasa yatsunta akan fuskar, yayi murmushi jikin sa kaman a sanyaye ya ce
"Ibrahim yayi dacen ...."

wani irin kallo ta bi shi da shi, sannan ta ja tsaki mai zafi a ran ta ta maimaita sunan Ibrahim rabon da ta ji daga gare shi tun ranar da ya kai ta asibiti, fushi yake yi, itama ta yi fushi har ta goge numban sa, kalaman Mohan sun yi mata ɗaci, wato Ibrahim yayi dacen mata, bayan duk wani tanadi nata tana yi ne domin shi, shi kaɗai. Zuciyar ta ta sake tsinkewa, wani d'aci ya cika mak'ogwaronta, ta rasa meke mata daɗi, sai kawai hannayenta suka shiga rawa yayin da hawaye masu ɗumi suka fara gangarowa kan fuskarta.


"Problem kuka kumai"

Ta girgiza kan ta tana ƙoƙarin dakatar da zuban hawayen cike da sigar shgwaba tace
"nayi missing dinka da yawa nee"

"Ba wani missing, don na ce Ibrahim yayi dacen mace shi ne za ki wani fara kuka?, Ke fa dukiyar sa ce halak malak babu mai rabaku in sha Allah"

A lokacin kukan da take k'ok'arin dannewa yaci galaba a kan ta, komai ya sake hargitse mata, tunaninta ya k'ara juyewa, sai kawai ta fashe da kukan dake fitowa kamar zai tafi da numfashinta...

"Ya Ilahi, I'm sorry, wasa nake miki, ya isa haka nan share hawayen ki"




*LITTAFIN MOHAN NA KUƊI NE*
Mutane talatin da za su fara siyan littafin za su siye shi a kan farashin #300, duk wanda zai siya daga baya zai biya normal Price #500

*Za'a biya ta wannan lambar 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*

Sai a tura receipt ko shaida ta wannan lambar *09125491597*
Haka zalika zaka iya biya a matsayin katin MTN a wannan lambar *07046627683*

MOHAN IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF ADDICTION INTO AFFECTION.

KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA*
FIRST 30 SUBSCRIBERS WILL BE GOING FOR #300
Pay
*VIA 9122107940*

*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*

EVIDENCE TO *09125491597*

YOU CAN SEND MTN CARD SEND To *07046627683*

Be the first subscriber ❤️

NB _Part one is free_

©BINTOU.
Na yi gabas 🚶🏽‍♀️.
17th December.
[12/23, 9:39 AM] Star: *021*
"Ya Ilahi, I'm sorry, wasa nake miki, ya isa haka nan share hawayen ki"
Ta share hawayen ta tana hararar sa
"I'm sorry Candy”
Mohan ya faɗi a karo na biyu ya na kallon ta cikin ƙumshe dariyar shi, ta kai masa duka tana hararar sa.
"You are silly"
Ya ɗage mata gira ɗaya ya ce
"Oh I am?"
Dukan ta sake kai mishi
"Stop this jorh"
"Ok, Yanzu ina za mu je"
Ta ce
"Ni ma ban sani ba"
Shiru ya ratsa wajen, yana nasartan ababen hawan da ke kai kawo a titi kafin muryarsa ta fito cikin wata sassanyar amo mai taushi.

"Mu miƙa hanya, mu yi tafiya mai nisa a ƙasa muna hira, idan mun gaji sai mu yi stopping a street food joint mu yi ƙwalama"
Ta ɗan waro ido
"A kafa?"
"Yes Darling"
"Idan na gaji fa?"
"Sai in goya ki"
Muryarsa tayi amsa amo a cikin kan ta, ta sake hararar shi a karo na ba adadi. Shi kam tuni ya fara takawa, bata da wata zaɓin da ya wuce ta bi bayan shi. Ba da sauri yake tafiyan ba amma har yayi mata nisa
"You know you're annoying"
Ta furta lokacin da ta isko shi bayan ta haɗa tafiyar nata da gudu, ta riƙo hannun sa gefen rigar sa tana roƙon sa da ya rage sauri.
Ya cije leɓensa kaɗan sanda ya sha kwanar da zata sada su da layin lemu, wasu tarin yara ne ke wasa hankalin su a kwance, ya kau da kan sa daga kallon su yana murmushi, da ya tuna tasa yarintar a ƙauyen da aka haife shi.

Cikin unguwa suka bi, suna tafe suna hira, wani yanayi da basu taɓa tsintar kan su a ciki ba, yanayin da kalmar farin ciki yayi ƙadan a misalta shi da shi, she both wish this should last forever, da a ce su biyu ne a duniyar su da sun zaɓi kasancewa a wannnan yanayi na iya tsawon rayuwar su, a wajen wata bayarbiyar mata mai suyan doya da ƙwai da Chips Mohan ya tsayar da su, suka yada zango a joint ɗin ta, ya ce a basu doya da ƙwai harda chips ɗin na 1,500 da lemu biyu, ta ce bata sha sai dai a bata malt, shi ma sai ya canza nasa zuwa malt, ya buɗe mata bayan ya buɗe nasa, ita dai Zakiyyah kallon sa take, problem yana mugun burgeta, komai nasa cikin natsuwa yake yi, kaman wani mace, yanda yake wasu abubuwan ma sai ta ji kaman ta haɗiye shi, he is so unique in all ways, ga shi ba shi da girman kai, duk abin da zai sa shi farin ciki shi yake yi.

“Story time!...”
Muryar sa ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta zurma, sai gyara zamanta da kyau, tana buɗe duka kunnuwanta dan ta ji labarin da zai bata. Ta san labaran Mohan, babu na yarwa, don ya saba bata labarai iri iri tun kan su haɗu a zahiri. Ko me ya tuna oho sai ya yi guntun tsaki yana cewa.
"Let's skip the story kawai...."
Ya cigaba da cewa
"There is something I want to tell you problem...."
Ya furta in an emotional way, idanun ta a kan sa, amma sai kuma ta rufe su a take, tana fatan ta ji kalmar da ta jima tana son ji daga gare shi.

“Shin kin san da cewan kowane irin mutum zai iya son ki, amma shin wannan soyayyar zata iya tsayawa a lokacin da ka samu kika samu kan ki a halin da ba zaki iya..or ba soyayya zai yi miki wahala...like.... Huh Hausa is a twist language though, let me repeat myself in English"

Ya furta sannan ya juya harshe zuwa turanci, don hausar ta kasa fitar da maganar da yake son yi.

"I mean Any man can love you, but will that love remains on the days when you're difficult to love?"

Yana maganar ne yana kai mata doya da ƙwai ɗin haɗi da chips, ta buɗe bakin ta a lokacin da zuciyar ta tayi k'ulik'ulin kubra sannan ta fad'o daga wata saman ƙirjin ta, ta rintse ido tana jin wani nauyi a ƙirjin ta, bata fahimci mai kalaman sa suke nufi ba, bata san inda ya dosa ba, duk yadda ta so ta fassara kalaman ta ta kasa, sai kawai ta ajiye tunanin, a yayin da ya ɗauko wata hirar. Abincin ya ci gaba da bata ya na bata wasu labaran, sai da ta ga ta kusa cinyewa, sannan ta sa hannu, ita ma ta shiga ba shi a baki, bayarbiyar matar da ke suya sai kallon su take tana taɓe baki, suna fitowa titi ya tare masu napep, suka nufi National Commission for Museums and Monuments, (Museum na Ungwar Shanu), museum wuri ne inda aka fi ajiye kayan tarihi da tsoffin artefacts, sculptures, objects, history da sauran su, Zakiyyah ji ta yi kaman ta koma zamanin da tafawa balewa yake mulki, sai ɗaukan hotuna suke da tsadaddar wayan sa, wishing the moment could last forever, abin da basu sani ba shi ne, wata ƙila Allah ya ƙaddara haɗuwar su a yau ne domin hakan ya kasance abu na ƙarshe da za su rinƙa tunawa na farinciki a tsakanin su, sakamakon kusantar wata ƙaddara da ke tunkaro su. Wata ƙaddara da zata haddasa tazara a tsakanin su.

Daga nan beach suka nufa, suka zauna gefen rafi suna kallon yanda ruwa ke tasowa yana komawa, gefe guda kuma ga mutane iri daban daban suna shiga suna yin wanka. labari yake bata a kan Fatimah, yarinyar da ta lalata rayuwar sa da shaye shaye, ta ce
"Yanzu ina fatiman take?"
Ya ce
"Ai Fatimah ta rasu, shekaru biyu kenan"

"Allah sarki, Allah ya jiƙan ta"
Ya amsa da
"Ameen, ta tafi ta bar ni da wahala"
Ta harare shi
"Ka san wahala ne dama kake sha?"
"Hmm... Kin ji ki kuma, saboda baki taɓa shaye shayen bane, kuma bana fatan duk rintsi ki tsinci kan ki a cikin wannan yanayin"
Tace "Hmm" kawai, shi kuma ya cigaba da cewa
" wato problem shaye shaye masifa ce, shaye shaye bala'i ne, Mutanen da na haɗu da su a toxicology idan suna bani labari a kan yadda suka fara shaye shaye, sai ki ji suna cewa abokai ne suka yi influencing ɗin su, ko kuma suna sha ne saboda aikin da suke yi, kaman wani abokina wanda muka haɗu da shi a asibitin shi ya ce min Drivern babban mota ne, so idan suna driving dare yayi yana gajiya sosai ga bacci da kasala and co, so sai wani driver dan uwan sa yayi mashi suggesting drug cewa ya fara sha zai ji duk duniya babu wanda ya kai shi ƙarfi, da haka ya fara sha, ya ce idan ya tashi driving sai yayi two days Yana driving ko gajiya baya ji, sai daga baya abin yake dawo masa yayi ta bacci, wani kuma tsabar iskanci ne don ya ga mahaifin sa na da kudi sai ya fara bin abokan banza suna ƙona kudi a banza, amma ni nawa ƙaddarar daban ne, i just feel like tasting it alokacin, kuma to be sincere babu abin da ya min, sai daga baya"

Zakiyyah ta taɓe baki
"Yanzu haka zaka haihu a gaya wa yaran ka ka taɓa yin shaye shaye?"

Yace
"Ina yawan yin wannan tunanin, i always try, countless times Ina ƙoƙarin dainawa amma na kasa, instead ma wahala nake sha, problem wallahi shaye shaye masifa ce, babu abin da ya kai fara shaye shaye sauƙi, amma dainawan sa ya fi komai wahala, duk mutumin da kika ga ya yi shaye shaye daga baya ya daina ya kamata a yaba masa, kuma wata ƙila ba jajircewan sa shi kaɗai bane, da yawa mutanen da suka daina shaye shaye ba jajircewan su ne kaɗai ba, har da jajircewan family da mutanen da ke tare da su, muna aikata laifuka da yawa, da yawan mu muna aikata laifukan da suka taka shaye shaye, amma idanun mu kan rufe mu kasa ganin wannan lefukan, a idon mutane da dama duk mai shaye shaye mutumin banza ne, koda ƙaddara ce ta sa ya fara sha, sai ki ga an juya masa baya ana hantarar sa...."

Zakiyyah wacce zuciyar ta ta fara rauni ta ce
"Ai dole al'umma su guji duk wani mai shaye shaye, da wuya ka ga abokin mai shaye shaye wanda baya shaye shaye, idan kana alaƙa da mai sha wata ran shaidan zai iya ruɗan ka ya ce ka gwada sha, wani kuma daga gwadawan nan shikenan"

"Baki fahimci me nake nufi ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login