Showing 36001 words to 39000 words out of 72389 words

Chapter 13 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4955

da Farida har abada ba dan haka ta shirya ta kuma tsara komai yanda zata fara azabtar da Faridan da yaran ta kamin daga baya ta kora su duka su tafi su bar mata gida. Tun kan ya aurota da ta ga yadda yake wulaƙanta ta, ita kuma take shakkar sa, sai abin ya bata dariya ta san ba zata sha wahalar azabtar da ita ba, tun da dama iyayen su basu damu da ya rayuwar auren su yake kasancewa ba, su dai sun haɗa, kuma sun tilasta mata dole ta zauna da shi, shi kuma a yadda ta lura da shi ba zai iya rabuwa da ita bane saboda iyayen sa ne suka haɗa. Shi yasa tayi amfani da nakasun sa da soyayyar da yake mata tayi galaba akan sa, ta zama kalar macen da yake so, har ta zarce wacce yake muradi, a wasu lokutan ma ya kan yi tunanin ta fi ƙarfin shi. Ta karanci shidin mutum ne me son classy mace, wayayyiya, wacce ta iya soyayya, zazzafar soyayya irin ta turawa. Shi kan sa Daddy wayewar Sidd da yadda ta iya narkar da namiji duk jarumtar sa har mamaki abin yake ba shi tamkar wacce ta tashi cikin turawa ko wasu gogaggun mutane shiyasa yake biye mata a kan duk abin da take so ya tabbatar da ya burgeta, sam baya so ta yi fushi. Idan tana wuri ko bata yi magana ba iya yadda take juya fararen idanun ta baya sanin sanda yake aikata duk abinda ta saka shi. Da ta fahimci Faridan bata da wayau babu abinda ta sani, zaman ƴaƴan ta take da biyayya wa Mijin da bata gaban shi, sai ta ƙara dagewa wajen ganin gida ya zama nata.

Saboda damuwa da yayi ma Farida yawa hakan ba ƙaramin rama ya sata ba. Idan ta je ziyara garin mahaifan su sai su yita tambayanta ko ciwo take yi, Dalilin da ya sa ya hanata zuwa Maiduguri kenan a cewan sa tana ƙara masa baƙin jini wajen dangi.
****
Wata yammacin Litinin bayan su Imam sun dawo daga islamiyya, Farida na zaune da yara suna cin abinci ita kuma ta zura wa Tv ido tana tunanin abinda ya faru ɗazu dambe ne aka sha a gidan tsakanin Zakiyyah da Siddiƙa, don yanzu bata raga mata, fargaba ne fall a ran ta, don ta san dawowan Zakiyyah cikin gidan daidai yake da sharan fagen ranar mutuwar ta.

Tana zaune ta ji sallamar siddiƙa tsoro da fargaba ya kama ta, ko dai ta biyo ta ta fanshe a kan ta ne?, ta san cewa idan dukane tsaf Sidd zata babballata ƙasussuwan ta.
Bata gama tunanin ba Daddy ya shigo, da fara'ar sa, har da Sallama

Tsabar mamaki Farida sai ta hangame baki ta yi, ta kasa ce mata komai.

Yaran suka bar falon da gudu kaman sun ga mala'ikan mutuwan su, ya zauna a kan two sitter kusada Sidd, wacce ta hakimce kaman ɗakin uban ta yana tambayan
"Ina Zakiyyah?"

Gaban ta ya sake faɗuwa, ta kai duban ta ga Sidd, murmushi ne a fuskar ta, haka shi ma daddy, zata iya rantsuwa ta ƙara bata faɓa ganin yayi murmushi a ɗakin ta ba sai yau. Ta kasa bashi amsa
"Baby, ka ga daga dawowan ka ana nema a ɓata maka farin cikin da ka shigo da shi, mu je ka fara yin wanka, sai ka sanar masu"

Sidd ta fada tana fari da ido, Farida kuwa sunkuyar da kai ƙasa ta yi tana masa sannu da zuwa tare da gaishe shi ya amsa cikin walwala, hakan ya sake dasa shakku a zuciyar ta. A fakaice Sidd ta galla mata harara, duk sun gani, amma ya gaza cewa komai, hakan ya sa ta gasgata fargaban da zuciyar ta ke yi, tabbas ba alheri ya kawo su sashen ta ba.
"Baby ka san me?"
"A'a sai kin faɗa sweetheart"
Ya amsata yana tuɓe babbar rigar sa.

"Baby mutumin da kake gaya min na san shi, ba ƙaramin mutum bane, how comes harkar kasuwanci ta haɗa ku?"
Ta yi maganar tana shafa masa fuska cikin yauƙi kaman za ta sumbace shi, shi kuma ya biye mata yana wani yawota jiki kaman zai maidata ciki. wani abu ya sako ƙirjin Farida, ta kau da idon ta, ta ji kaman ta miƙe ta bar masu falon, amma wani zuciyar ta ƙwaɓeta gudun kada ta yi wani laifin, shi kuma kamar wani gaula haka ya biye ta Sidd yana cewa
"Anya kin san shi kuwa?".
Ta yi wani fari da ido tana sake narkewa a jikin shi.
"Baby waye bai san Alhaji mai dala ba?"
Wani abu ya tokare ƙirjin Farida, ta ji ba zata iya jurar wulaƙancin nan ba, ta miƙe za ta bar masu falon ya dakatar da ita.
Hawaye taji sun zubo mata tayi saurin sharewa, ta ce ruwa zata kawo masa, daga nan bata tsaya jin mai ze faɗa ba, ta fice don kawo masa ruwan. Tana dawowa ta yi mummunar gamo don abin da suke aikatawa ya zarce misali.

Hawaye masu zafi suka zubo mata, wannan ai cin fuska ne, a dakinta zasu ringa irin wannan abin?, a baya da suke yin abun su baya damun ta don basu shiga sabgar ta, a yau kuma wane sabon wulaƙanci ne ya tashi suka sakata a gaba suna baɗala ko kunya basu ji yara su shigo su same su a haka?. Ɗakin ta ta koma, tana kuka zuciyarta na zafi, shigowan Zakiyyah ne ya sa ta miƙe tana share hawayen ta, cikin kulawa Zakiyyah ke dubanta tana tambayan ta me ya faru?, ta ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali ta ce, abu ne ya faɗa mata ido. Zakiyyah ta rausayar da kai cikin damuwa tace Daddy na kiran ta. Suka nufo falon, Daddy ya bi su da kallo masifa na cin su, Sidd na jin kaman tayi tsalle ta fizgo Zakiyyah ta saɓa mata kamanni, damben da suka yi da safe ya kasa goguwa a ran ta, kuma ta dau alwashin ramuwar gayya a gare ta.

"Kin san zuwan da na yi ɗakin ki da dalili, amma tsabar hauka sai kika tafi kika bar ni ina jiran ki?, Ko so kike na bi bayan ki?, bana son irin haka, ku gyara zama ku ji ni nan, ku saurari abin da zan faɗa"
Ahmad Abdul Azeeez ya fada yana kallon Zakiyyah, wacce ta haɗe girar sama da na ƙasa
"Kayi haquri"
Farida ta fada muryarta na karyewa kafin ta samu wuri ta bi umarninsa. Kamar ba dakinta ba haka suka samu guri suka rabe ita da Zakiyyah gabaki ɗaya sun kasa sakewa, ita ko hamshaƙiyar ta bararraje akan kujera, tana manne da shi kaman zai maidata ciki. Tsaki ya ja, ya wani karkace, ya fiddo wasu rafas na ƴan dubu dubu daga aljihun sa, ya tura gaban Farida, ran sa a harɗe in a very bossy tone yace

"Ga sadakin ƴar ki Zakiyyah, an ɗaura mata aure da abokin kasuwanci na, ɗazun nan a masallaci, ba za ta tare yanzu ba sai ya neme ta da kan shi, ba ƙaramin mutum bane, ba talaka bane, kuma yana da ilimi na addini da na nasara, ya san darajar zamantakewa, i guess irin mutumin da kike so ne, wanda ba zai ciyar da ke da haram ba, ja'irar yarinya mai baƙar zuciya...."




Comment andd share
🙏🙏


Na yi gabas🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️

Bintou❤️
11th December.
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *014*


Shiru ne ya gifta gurin kamar kowa ya mutu kodayake Zakiyyah da mahaifiyar ta daskarewa suka yi basa ma numfashi tsabar mamakin kalaman Daddy, Zakiyyah har zamowa ta yi daga kan kujera ta riƙe ƙirjin ta dake barazanar faso ƙirjin ta, kuma gaza furta komai tsabar mamaki da tashin hankali. Daddy ya cigaba da magana cikin isa da nuna iko yana cewa
"Ya kamata a yanzu kowa ya san sana'ar da nake yi, wato Farida......, na jima ina dillancin yara mata virgins da zaurawa harka nake yi international kama daga nan ƙasar har ƙasashen ƙetare , so, last week mun yi safarar mata daga ƙasar Koriya zaurawa goma budurwa ɗaya, jirgin su ya yi hatsari matan duk sun mutu, kuma ni already na riga na kashe kuɗin da aka bani, shi yasa dole na nemo masu wasu matan amma na kasa samun budurwa wacce zata maye gurbin wannan, haka yasa mutumin ya ce zai fashe da ƴa ta, saboda ran nan da suka zo gidan nan ya gan ta, kuma ta burge shi, ni kuma na ce ba zan yadda ba, ba don ina son ki ba Zakiyyah, sai don tseratar da ke daga sharrin mazinaci bayan na san ke ba mazinaciya bace, kuma idan na bar ki a haka tabbas wata rana sai ya zagayo yayi miki fyaɗe dan baya mai da ƙwaɗayin sa a kan mace, duk macen da ta shiga ran sa sai ya sameta hankalin sa yake kwanciya, da na rasa yadda zan yi sai na yi magana da sweatheart (Siddika kenan), ita ta bani mafita tace in aurar da ita kawai, ni kuma na ga dacewan haka, hakan ya sa na samu wani tsohon abokina, na roƙi alfarmar da ya bani auren ɗa......."

Farida na taro hawayen ta, ta katse shi da faɗin

"Dan girman Allah idan wani laifi nayi maka kayi haƙuri ka sanar da ni, na gaji da wannan zaman da muke yi, na gaji da azaban da kake gana mana, me muka tsare maka a rayuwa?, tun da na aure ka farin ciki ya yi kaura daga rayuwata, na rasa murmushi na, ka sa rayuwar yarana ya zama tamkar kurkuku a gidan nan, don Allah ka kwance wannan auren kada ka salwantar min da rayuwar yarinya"

Alhaji Ahmed Abdul Azeez ya ce

"Wato Farida tun da nake ban taɓa ganin munafuka irin ki ba, me na taɓa miki da za ki yi min wannnan sharrin? Wani ya ji ki ai sai a yi tunanin muzguna miki nake yi, Na taɓa nuna miki yatsa?, A iya zaman mu ko zagin ki ban taɓa yi ba, (🤔) ban taɓa fashin ciyar da ke ba, sutura da lafiyan ku ni ne mai ɗaukan nauyin ku, an aura min ke, bana son ki haka nan nake zaune da ke ban taɓa complain ba, butulu ni za ki yi wa sharri?, Yanzu me kike so ki ce?, Ban isa na zartar da hukunci a kan ƴata ba ko me?, Ko so kike ki ce auren da na ɗaura mata ma cutar da ita na yi?, Keh farida ki fita a idona in rufe, dama haka halin ki yake ban sani ba?, yaushe kika zama haka? Ko kuwa dama hakan kike kin lullubeni ne baki fito da ainihin kalar ki ba sai yanzu?"

"Ni ya kamata nayi maka wannan tambayar..,!"

Farida da maganaganun Ahmad ya daketa ta yi ƙarfin halin tarar numfashin sa.

"Dama haka kake Ahmad? A zatona kai ne mutum na ƙarshe da zaka fara bayar da auren Zakiyyyah bayan irin rashin gata da kake nuna mata, me yarinyar nan ta tsare maka?, Me yasa ka tsaneta haka? tun bata mallaki hankalin ta ba take maku aikin bauta kai da matar ka...."

"Ke farida kika sake sako matata a wannan maganar sai na wanka miki mari"

Daddy ya dakatar da ita a fusace, ya cigaba da cewa.

"Idan ma ta yi mata aikin bautan ba lada zata samu ba?, Yarinyar nan ran nan a titi na gan ta babu takalmi tana tallan pure water, ni na aiketa?, ko aikin sa swt hrt take sa ta ya kai wannan ne?"

Ya gyara zama yana duban su fuskar sa babu yabo babu fallasa, Sidd ta kwanto jikin da tana murmushi.
"kina ji Zakiyyah?, Ko kin ƙi ko kin so na riga na bada auren ki ga wanda ya dace da ke, Daga yau ke matar aure ce,ba ki da wani haƙƙi a kai na, dalilin da ya sa ba za'a kai ki ɗakin ki ba yanzu, saboda angon naki baya ƙasar, kuma kin yi masa ƙanƙanta da yawa, idan aka kai masa ke tsab zai lahanta ki, ni dai Allah ya ji ya gani na fita haƙƙin ku, na tsare ta daga sharrin mugun mutumin can, saboda a gaban shi ma aka ɗaura auren gudun abin da zai biyo baya"

Ya faɗa, zuciyar sa na tabbatar masa da yayi abin kirki, Hawayen ta suka ƙara gudu, itama Faridan kuka take, takaici ya kama shi, a ganin shi kamata yayi su yi masa godiya don tabbas yayi ƙoƙari, amma tsabar iskanci da butulci irin nasu kuka ma suke yi, to ya suke so a yi?, ya ja tsaki yace

"Ke share hawayen nan"

Ta sa hannu ta share hawayen ta tana jan numfashi, duk suka yi shuru baka jin sautin komai sai shesshekan kukan da Zakiyyah take yi, ita da Farida fuskan su a murtuƙe babu annuri, cikin jin haushin su ya ce

"Why are you people frauding your face?, Will you people scatter that face and chill before I give you a well grown slap to arrange that face for you"
Ya faɗa yana ware hannayen sa kaman zai kai masu marin, Zakiyyah ta ƙara haɗe rai tana turo baki. Yace

"Oya, you people should say thank you, you should thank me for the good thing i have done to you guys "
Suka yi shiru, ya duƙa ya cire takalmin shi, cikin ƴar ƙaramar tsawa yace
"I Said open that mouth and say thank you before i arrange it for you"
Suna share ƙwalla suka ce
"Thank you"

Banda dariya babu abinda Siddika ke yi, ya nuna kuɗin yace ta ɗauka, ta ɗauka tana godiyan dole, ya ja hannun masoyiyar sa suka bar ɗakin yana jin kaman ya rufe su da duka, dan a ganin shi yayi abin a yaba masa, tun da mutumin kirki ya aura mata, kuma tseratar da rayuwar ta yayi daga faɗawa halaka. Ranar baccin baƙin ciki suka yi tare da taraddadin son sanin wannene angon nata, cikin dare Zakiyyah ta haɗa kayan ta, washe gari tun gari bai waye ba ta fice daga gidan, ta nufi tasha, ta hau motan Maiduguri.

Tas ta labarta ma mahaifiyar Farida wato kakar su komai, kaka ta jinjina kai cikin baƙin ciki da danasani, ta ce ta huta tukunna, sannan ta kira ƴan uwan faridan ta faɗa masu komai, tuni yayan su Salihu ya ɗau mota ya tafi Zarian ya ɗauko faridan tun a hanya yake mata faɗan me yasa bata faɗa masu ba?, tana isowa suka tasata a gaba da masifa, yayar su Habiba ta ce
"Haba Farida yanda kika san sallamammiya?, Menene amfanin mu idan kin kasa sanar da mu abin da yake miki?, Hauka ma ake yi shi Ahmad ɗin har ya isa ya wulaƙanta ki? a masa sutura a zaɓo masa mata a dangi sannan shi dan yana ganin ya waye ya auri wayayyiya sai ki zama yar kallo sai yadda yayi da ke da ƴaƴan ki?"

Zakiyyah ta ce

" Anty Habibah baki ma sani ba, u da bangon gidan babu banbanci fa, baya shigowa ɗakin mu sai idan masifar sa ta ciwo shi, yana gama zazzage mata zai fice kuma ba'a sake ganin shi sai ta shi ta kawo shi".

Hawaye ne cike a idon Farida, ta ce
"Yi min shuru Zakiyyah....!, Ku kuma ya zan yi?, Ku ne kuka ce in yi masa biyayya, umma har cewa ta yi idan na sake kawo ƙarar sa bata yafe min ba"

Habiba tace
"Idan anyi magana sai ki ce ya za ki yi?, da yadda za ki yi mana!, don an ce ki yi zaman haƙuri ai ba cewa aka yi ki zama sakarya ba, ke da kike da gindin zama a gidan sa ma?, a yadda na lura da Ahmad ko me za ki yi masa ba zai taɓa iya sakin ki ba, ki yi amfani da daman ki ki ƙwaci kan ki a hannun kishiyar ki, idan tace iskanci gadon ta ne, ki nuna mata ke taki iskancin ya fi na bariki, ki ci abu ta kazan ta, har da shi yake daurewa Sidd din ki haɗu ke da yaran ki ku kulle ta a ɗaki ku mata ɗan banzan duka, daga nan za su gane Allah ɗaya ne"

Tsabar baƙin ciki da takaici Kaka kasa cewa komai tayi se ƙwafa da take jejjerawa. Faɗa sosai suka taru suna mata kamar zasu dake ta. Banda kuka babu abinda take yi, jikin Zakiyyah yayi sanyi har ta fara nadaman zuwa Maiduguri da ta yi ,asalin maganar da ta zo masu da shi ma ba ta kan shi suke ba, gabaki ɗaya sun maida alhakin abin kan mahaifiyar ta, haka suka kwana ko baccin kirki Zakiyyah bata iya ba, data rufe ido sai ta tuna a yanzu ita matar wani ce, ta rasa ya zata yi, washe gari Ahmad yayi masu dirar safiya shi ma suka hau shi da faɗa ko a jikin sa, ya ce ya zo tafiya da iyalan sa ne, duk rashin mutuncin da kaka take yi masa babu abin da ya shiga kunnen sa, ya rufe ido ya ce a su fito su tafi, in ba haka ba daga ita har iyayen ƴan uwan nata sai sun ga rashin mutuncin da ba su taɓa zato ba, Anty Habiba ta ja Farida suka shige ɗaka, cikin ban baki take cewa .


"Ki yi haƙuri Farida, ki bi shi, amma wannan karon kada ki yadda ya sake wulaƙanta ki, auren Zakiyyyah ma ki yi haƙuri, tun da da kan shi ya ce ba mutumin banxa ya aura mata ba, ki bi shi da ido har sai ranar da za su zo ɗaukan amaryar su, kin san dai da mutumin banza ya aura mata da ya faɗa don ba tsoron kowa yake yi ba, ki kwantar da kai ki nuna masa komai ya wuce a, sannan ki bita da addu'a, ita kuma kishiyar ki, ki ƙwaci kan ki a hannun ta ke fa wayo da dabara ne baki dasu, idan ta nuna miki wayewar barikin sai ki nuna mata naki barikin ba na waje bane, har shegiyar ta isa ta sa a aurar da ƴar ki kina zaune?, Ni afa wallahi haushi kike bani, ji nake kaman na rufe ki da duka!, akan me zaki ringa bari kishiya tana juya ku?, kin nuna mata kina shakkar su ita da mijin ku a fili ba dole ta taka ku ba?, Haushi fa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login