Showing 27001 words to 30000 words out of 72389 words

Chapter 10 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4949

gaya masa gurguwar alaƙanta da mahaifin sa,duk da ba komai ta gaya masa ba, ya san mahaifin ta baya ƙaunar ta, kuma a zahiri yake nuna baya ƙaunar ta.

Da a ce mahaifin ta ne ya kamata da wani namijin, ba aura mata shi zai yi ba, zai iya kai ta police station ya ce a horata, karuwanci take yi, za ta ɓata masa suna.

Ya haɗiye wani yawu da ƙyar, tausayin ta na ƙara tsuma shi, yayin da ƙaunar nasa iyayen yake daɗa lulluɓe shi. Gidan su Maryam suka je, da shi da Ameen da manajern Abba. Hassan ya so ya je, amma ya samu kiran gaggawa a Kaduna, Asibitin da yake yi wa aiki.

kyakkyawar tarba suka samu a gidan, sun ci sun sha, sun ga sakin fuska a tattare da kowa, kai ka rantse don Allah ake yi. Daga ƙarshe aka bar su su gana da Maryam, ta ba shi haƙurin abin da ta yi masa ya kalleta cikin taɓe baki, ya ce

"Maryam.... Aure na da ke ƙaddara ce, don haka ba sai kin bani haƙuri ba, ina so ki sani, ina da wacce nake so, soyayya a zuciyata guda ɗaya ce, ba zan taɓa son wata mace bayan Nihaal ba, ita nake jira, shi yasa na jima ban yi aure ba, da a ce mahaifin ta ya bani auren ta da yanzu ƴaƴan mu uku ko huɗu, don haka in kin shigo gidana, da ni da ke za mu haɗu mu jira zuwan ta, tukunna za mu tsara yadda za mu rayu da ke..."

Maganganun sa sun yi mata zafi kwarai! Amma duk da haka sai ta tattaro dauriyar ta da matsayinta na mace tayi masa uziri, duba da abin da ta yi masa, kuma shi namiji ne, mai zuciya a ƙirji, ta yi masa ƙazafi amma ko kallon banza bai yi mata ba, Idan ma ta faɗi hakan ne don ta nuna kishin ta to ba za ta tanka ba..

Da daddare suna chatting da Zakiyyah yake gaya mata ya je gidan su Maryam, har ya tura mata hoton da ya ɗauka da shaddar. Tace

"Allah ya sanya Alkhairi, yaushe amarya zata tare"


"Abba ya ce, next month, saboda ina tunanin zan koma psychiatric in ƙara treating wannan abin, saboda ina so ina daina shaye shaye har abada"

"Na ji daɗi...."

Ta ce, a taƙaice.
Ko kaɗan bai ji daɗin reply ɗin ta ba, sai yayi tunanin ko wani abu ne ke damun ta
"Problem...."

Ya yi typing sunanta
"Na'am..."
Ta amsa ba tare da ta amsa yadda ta saba ba.

"Meke damun ki"

"Toh ba kai bane....?"
Yayi murmushi a yayin da ƙwaƙwalwar sa ta harba wasu shekaru da suka gabata, ranar da suka haɗu da ita, a facebook. Yana murmushin ya maida mata martani.

"Ni mai na yi?"
Yana turawa ya sake turo mata da wani saƙon.

"Yawwa problem, Ina maman mu?, Kin daɗe baki ba ni labarin ta ba!.

Itama sai hakan ya tuna mata da ranar da ta fara sanin shi. Ta zauna ta buga tagumi da waya a hannun ta tana tunanin irin rayuwar da ta wuce a baya, kafin ta ƙwatowa kan ta ƴancin ta, Siddiƙa ta gana mata azaba iya azaba, tun yar shekara goma sha huɗu take aikin bauta, bata da wani lokacin farin ciki kullum tana cikin wahala, bata ko samun isashen abinci, wannan dalilin ne yasa ko da yaushe in kaga Zakiyyah bata cikin walwala yanayin da ya sa har yanzu bata cika wani walwala ba, bata kula kowa koda a makaranta ne, magana ma mata wuya yake mata, ko tana tare da mahaifiyar ta ne, hakan ya sa wasu suke mata kallon mai girman kai.


*Bari mu koma baya kaɗan mu ji wacece Zakiyyah*

Dare ne mai cike da dumbin rahama, kowa na cikin gidan shi sakamakon ruwan da ake tsugawa mai ƙarfi, matafiya sun fake, yayin da masu bacci ke tsaka da jin daɗin baccin su.

A wannan lokacin Zakiyyah na cikin ruwan tana wankin kayan jinjirin da Siddiƙa ta haifa, jinjirin da ba ta hanyar aure aka haife shi ba, jinjirin da haihuwan sa ya sake ƙarawa Siddiƙan fada a cikin zuciyar mahaifin ta, wanda a wannan lokacin har alƙawarin aure yayi mata, iyayen ta suka ce ta koma gidan sa da zama har ta yaye yaron, sai a ɗaura masu aure, a lokacin yaran Siddiƙah biyu tare da mahaifinta, duk ba ta hanyar aure aka haife su ba, Ammar wanda a lokacin yake da shekara goma sha bakwai, sai kuma Jabeer mai shekara bakwai, da jaririn da ke da watanni biyu a duniya. Tun kan ta san kan ta take yawan ganin Siddiƙa tana zuwa gidan, wata rana har kwana take yi, kuma babu wanda ya isa ya ce don me, saboda ba ita ta kawo kan ta ba, kuma wanda ya kawo ta yana goyon bayan hakan. Kuma a zahiri mahaifin su yake nuna fifiko a kan Siddiƙa da ƴaƴan ta a kan kowa na gidan, har ya kan yi ikirarin rabuwa da kowa a kan ta, wani irin soyayya yake mata wanda ya sa baya ganin laifin ta, kuma ba don komai yasa bai aureta ba sai saboda iyayen ta sun ce ba za su aurawa mai mata ba, shi kuma yayi mata alƙawarin zai rabu da matar sa saboda ita, amma sai iyayen sa sun rasu, don Auren zumunci aka yi masu da alƙawarin tsinuwa a kan sa idan ya saketa, duk shagalin da yake yi shi da Sidd, babu wanda ya sani cikin dangin sa, saboda babu mai ziyartar su duba da nisa da tazarar da ke tsakanin shi da iyayen sa, su suna garin Maiduguri ne, shi kuma aiki ya kawo shi nan garin Zaria.

Daga lokacin da ta dawo gidan zaman lafiya da kwanciyar hankali suka ƙare tsakanin mahaifan ta, makirci kala kala babu wanda basu gani ita da mahaifiyar ta da ƙaninta Imam, idan Daddy baya nan ko fitowa basu yi saboda gudun makircin siddiƙa, yanzun nan za ta ƙulla masu sharri, shi kuma ya hau ya zauna, ita kuma Zakiyyah kusan wuni take yi tana aikace aikace tana zagin ta, haka za ta gama aikin ta wuni da yunwa zuciyarta cunkushe da tunani.

Mahaifiyar ta na gani, amma babu abin da za ta iya yi, wa zata kaiwa kukanta ya bata mafita dan ita a iya wayo da dabararta bata san me zata yi ta kaucewa afkawa wannan wawakeken ramin dake a gabanta ba. Makirci da tuggun da Siddika kullum ƙaruwa yake yi. Ga shi bashi da fahimta, ta sani a koda yaushe maganarta itace daidai babu ruwansa da jin bangare domin yin alƙalanci akan abu wannan halin, hakan ya sa Siddiƙa ta samu wurin zama take shimfiɗa mulki son ran ta.

Yawan ruwan da ake yi bai sa siddiƙa ta tausaya mata ba, yayin da ita kuma take dakin Daddyn su, kan katifar sa, warmer a kunne suna shan dumi su da Zayd, Ammar da Janar na ɗakin su.

Duk wannan abin da ke faruwa mahaifiyar ta na ɗakin ta, ta yi tagumi tana leken yar ta da ke faman aiki cikin ruwa, zuciyar ta na zafi amma bata da yadda za ta saboda Daddy da dadiron sa sun fi ƙarfin ta, auren dangi aka yi masu da Ahmad Abdul Azeez, tun kafin a yi auren suke tare da siddiƙa har ta haifa masa ɗa, amma babu wanda ya sani, da kan sa ya gaya mata don ta tubure, hakan kuwa aka yi don sosai ta kafe tace ba za ta aure shi ba, saboda da kan sa ya ce yana da wacce yake so, har ta haifa masa ɗa, amma iyayen ta suka ce sam sharri take masa, kuma kada ta bari maganar ta fita don babu makawa sai an ɗaura auren. Haka kuwa aka ɗaura auren cikin su babu wanda yake son ɗan uwan sa, zagi, da muzgunawa iri iri babu wanda bata gani ba, haka ta haƙura take zaune da shi, ana haka ta haifi ƴarta na farko *Nusaibah* bayan haihuwanta ya fara tsiro mata da wasu halaye na rashin kunya da wulaƙanci, har cikin gida yake kawo mata mata, yayi lalata da su a gadon auren su. Tun tana haƙuri har ta kasa jurewa, ta kai ƙarar shi wajen mahaifiyarta, mahaifiyar ta ta zaunar da ita ta zageta tasss ta ce ƙarya take masa, don kowa ya shaida halin Ahmad, ba mutumin banza bane, sau uku tana kai ƙarar sa a kan same problem ana dawo da ita da zazzafar kashedi, daga ƙarshe da abin ya isheta ta je direct wajen mahaifin sa ta gaya masa abin da ke faruwa, mahaifin sa ya zauna da mahaifan ta aka kira su aka sa su gaba, Ahmad yayi ta rantsuwa cewan ƙarya ta yi masa, daga ƙarshe aka ba shi haƙuri tare da yi wa Farida (Mahaifiyar Zakiyyah) kyakkyawar gardaɗi a kan kada ta sake kawo ƙarar shi, idan bata son shi ta yi haƙuri, ta zauna da shi, a sannu za ta fahimci nagartattun halayen sa, kuma innsha Allah za ta ji daɗin zama da shi, haka tana kuka ta baro gidan iyayen ta, ta cigaba da zama da Ahmad, rashin mutunci iri iri babu wanda bata gani a wajen Ahmad, ana haka ya samu aiki a ABU zaria, suka tattara suka bar Maiduguri suka koma Zaria da zama inda dama nan ne mahaifan Siddiƙa, a nan likafa ta cigaba, Nudaibah na da shekara biyu ta haifi Zakiyyah, bayan wasu shekaru itama Siddiƙa ta ƙara ajiye masa wani ƙwan, ta haifa masa Jabeer, har zuwa wannan lokacin babu wanda ya san yana tare da wata bayan matar sa.

Iskanci da baɗala iri iri babu wanda Farida da ƴaƴanta basu gani, tun tana damuwa har ta bar hakan a matsayin ƙaddarar ta kuma Allah zai kawo mata mafita, a wannan halin ta sake samun cikin Abdullahi, wanda ya ci sunan mahaifin ta, hakan ya sa ake kiran sa da Imam...


Allah Allah takeyi ta gama ta shiga dan karamin dakinta da bai wuce taku biyu ba, tana gamawa ta gyara gurin da sauri saboda ruwan kamar dada ƙaro shi ake yi, tayi maza ta tsaya bakin kofar dakin su ta cire kayan jikinta saboda kar ya jika masu daki ta matse kayan ta shanya shi a gefen kayan da ta gama wankewa, ta shige ɗakin ta tana kare jikin ta, tasa wasu tsofaffin kayan ta da suka koma tamkar tsumma saboda tsufa, ta hau kan katifarta da sauri, jikinta na rawan sanyi, tana sharce majinan da ke gangarowa a hancin Yunwa sosai take ji dan yau Daddy ya hana su taɓa kayan abincin gidan, saboda maman su ta ɗagawa Jabeer murya a kan ya fasa mata show glass, haka yake hora su a duk lokacin da aka taɓa masa ƴaƴan gwal, lamarin Siddiƙa dai kaman ta yi masa asiri, amma babu wani sihiri, tsabar kissa ne da iya makirci. Nusaiba na gama primary siddika ta zuga mahaifinta ya turata bording, inda ake gana mata azaba don ko visiting ya hana a je mata, a cewan sa ya tura ta boarding ne don ta ƙaro wayau, idan tana ganin na kusa da ita sangarceewa za ta yi.


Zazzaɓi take ji sosai, amma saboda tsabar ta yadda ta ƙosa ta shiga facebook ta karanta littafai ko lulluɓe jikin ta bata yi bai, ta dakko wayar ta visafone ta saka batir sannan ta ɗaureta da robalin, in ka ga wayar ba zaka taba cewa in an kunna zaiyi aiki ba saboda gabaki ɗaya bottiran sa sun cire, sannan an zagayeta da robalin da yawa, cikin zakuwa ta daddana botiran har ya kaita inda ta hau facebook, a lokacin ba kowa yake amfani da babban waya ba, amma wayar da ke hannun ta babba ne a wannan lokacin don ko memory ba'a sa mata, yana da space kuma yana bayyana hoto a facebook shi yasa take jin daɗin wayar, tsohuwar wayan mamanta ne da ta bata a lokacin da ta canza wata wayar, shekarar wayar ɗaya a hannun ta. Group ɗin Hausa novels ta shiga ta karanta posting ɗin da aka yi yau, sannan ta dawo feed ɗin ta ta fara kallon posting din friends ɗin ta kaman kullum har ta ci karo da wani post wanda ya ɗauki hankalin ta, har ta wuce sai ta dawo tana karanta abinda aka rubuta.

*When last did u view my Facebook stories?*
*Do sell some nice casuals foot wears and cloths*
*Check them out!🤗*
*Nation wide delivery 🚚*

Sunan wanda yayi post din ta duba Mohan Sani, bata san shi a list ɗin ta ba, hasali ma bata taɓa jin sunan ba. Sai ta tsinci kan ta da shiga post ɗin, ta yi masa comment, _Menene ma'anar Mohan?, Asalin sunan ka ne?_ , ba jimawa yayi mata reply _Sunana na ne, Moh stand for Muhammad, the last "N" stands for Nasir. Itama sai ta yi masa reply da, " Kenan sunan ka Muhammad Nasir Sani?" Maimakon yayi mata reply a comment section, sai ta ga saƙon sa ta Dm ɗin ta.

"Asalin sunana Muhammad Sani Nasir, za ki siya kaya ne ko takalma za ki siya?"

Ta waro ido kaman yana gaban ta
"A'a rufa min asiri, ni ina na ga kuɗin siyan kayan ku?"

"Babu tsada fa, kin ga wannan takalmin?, Dubu goma ce kacal, rigar nan kuma dubu goma sha biyar, akwai wasu ma bari na dubo maki"

"In kana wa Allah ka riƙe abin ka don wallahi bani da kuɗin siya"

"Ai kam baki isa ba, tun da kin yi min comment yasin sai kin siya"

Gaban ta yayi mummunar faɗuwa. Ta ƙanƙame jikin ta tana waro manyan idanun ta. Hannun ta na rawa ta yi masa reply.

"Ka san Allah, wallahi ba ni da ko sisi, Ni yarinya ce, a SS1 nake fa"

"Shekarun ki nawa?"

"14..."

"To bani numbar baban ku sai in ce ya siya maki"

Ta marairaice kaman za ta masa kuka.
"Don Allah ka yi haƙuri, idan babana ya ji labarin abin da na yi sai ya kusa kashe ni, kuma ya ƙarɓe wayar"

"Ai kuwa ko kashe ki zai yi sai kin bani numbar sa na gaya masa, kuma dole ya siya"

Ai ba shiri ta kashe wayar ta cusa shi cikin akwatin kayan ta, bata sake kunnata ba sai da yayi sati biyu, a tunanin ta ya manta da abin da ya faru, sai dai tana duba message ɗinta ta ga tarin message ɗin sa kullum sai ya tunasar da ita ta zo ta siya kaya, yanzu ma yana online, kuma yana ganin ta ya sake turo mata wani saƙon



Na yi gabas
Bintou
5th December.
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *011*


Yana ganin ta online ya sake tura mata wani saƙon

"Matsoraciya"

Ta turo baki kaman yana gaban ta,

"Ni ba matsoraciya bace"

"To ke wace in ba matsoraciya ba?"
Ta harari wayar
"To ba kai bane...?"
"Ni me na yi?"
"Ba kai ne ka ce dole sai na siya kayan ka ba?, Bayan ka san bani da kuɗi?"
Yayi dariya a zahiri
"Ki kwantar da hankalin ki, wasa nake maki, hala baki jima da fara facebook ba”

Ta ɗan yi jimm, tana ƙirgan kwanakin da suka gabata lokacin da Nusaibah ta dawo hutu, ta buɗe mata.

"Yau kwanaki ashirin da uku kenan na na fara facebook, amma fa bana chattin da kowa , kullum in na hau group nake shiga ina karanta novel"

"Wane irin novel kuma?"
"Hausa novel mana"
"Menene kuma Hausa novel?"
Ya tambaya cikin tsoma.

Ta ɗan ja guntun tsaki, a fili
"Kai wallahi problem ne, komai sai an gaya maka?"

Ya ce
"To ban sani ba, ba sai ki gaya min ba?, Solver"

Tace "To yanzu me kake son ka sani, problem"
Yace
"Ina so ki bani labarin littafin da kika karanta recently"

Ta ce " kai ni bana son iyayi hausar ne baka ji da sai ka haɗa da turanci?"

"Ga ki shugaban masu iyayi na duniya?, ai ke kika fara sako kalman turanci a cikin maganar mu, in ba haka ba meye na kirana problem?"
Tace
"To kai ba problem ɗin bane?"

"Ni ba problem bane, kece problem ɗin"

"Ni ba problem bace"
"A'a kece problem ɗin, keda ma kika tanka post ɗina kika kasa siyan abinda muke siyarwa'"

Tace "Ni dai na shiga uku... Yasin Adadi ko yau na samu kuɗi babu abin da zai hanani siye shagon naku gabaki ɗaya in huta da wannan mitan"

Yace " mu ba shago gare mu ba, problem, company ne, anya za ki iya siya kuwa?"

Ta ɗan waro ido.
"Company kuma?, To Ya sunan companyn naku?"

"Batta"
Ya rubuta a takaice
"Batta kaɗai?"

"Problem kenan, ko na gaya miki ba siya za ki yi ba ai"
Sosai ta saki jiki da shi, suna chat sai zuba masa shirme take, yana biye mata sun daɗe suna chatting kaman da wasa har ƙarfe sha ɗaya na dare, lokaci charjin wayanta ya ƙare, ta saka wayar a ƙarƙashin pillow ɗin ta tana murmushi.

Washe gari tun biyar na asuba ta yi sallan asuba duk da ba wani isashshen bacci ta samu ba, tsakar gida ta fito taga tulin kayan wanki da wanke wanke a kofar dakin Ummanta kayan Siddiƙa ne da ƴaƴan ta, ta kalli kayan cikin faduwar gaba saboda yawan su ga sanyin damina, ga kanta da ke masifar sarawa saboda rashin bacci da bata samu ba da zazzaɓin da ruwan jiya ya so ya dasa mata, har jiri jiri take ji. Haka ta fita cikin sanyin ta fita ta je ta ɗebo ruwa, duk da kasancewan suna da isasshen ruwa a gidan, amma Siddiƙa ta gummace ta je maƙota ta jawo ruwa a rijiya don a cewanta ruwan borehole yana saurin koɗar da kaya, haka ta gama wankin nan tun safe, har sai sai da Ammar ya fito ya tafi makarantan da mahaifin ta ya sa shi, yana mata gwalo, ƙarfe goma ya kusa ta gama, bayan ta gama ta shiga kitchen ta ɗau abincin ta wanda ummanta ta ajiye mata, ta fito tsakar gida tana ci suna hira da Dauda mai gadin su, rankwashi mai karfin da ta ji ya sa ta watsar da abincin, ta saka ƙara tana riƙe kan ta, Siddiƙa tace

"Uban wa ya baki abincin nan da kike ci?, duk ga ayyukan gidan nan babu ko daya da kika fara saboda tsabar lalaci da rashin tarbiyya, maza tashi ki je ki share min ɗaki, ki wanke banɗaki ki ƙarasa aikin ki tukunna kafin ki ɗebi wani abincin ki ci ki wuce makaranta, kuma Allah ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login