Showing 51001 words to 54000 words out of 72389 words

Chapter 18 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4938

gan sa kin san daga ina yake?, Ke ba a bayan idon ki ba ma, a gaban ki a gaban idanun ki idan namiji ya ga dama sai ya ci amanar ki, kuma hakan ba zai hana shi dawowa gare ki ba ya yaudare ki da daddan kalaman sa, ke kuma shasha dole ki dawo gare shi, omo You funny oo, you funny anyhow, you fit even stand here sef the man go dey date all your gang members you think say na Friendship, don kina ba shi kudi, da shi kika dogara?, Ana alfahari da hakan ne?, Kar ki ji mamaki idan na ce miki da kuɗin ki yake sharholiyan sa, You dey put yourself for trap, tsabar rainin hankali ma kin zo zaki mare ni a kan mutumin da ya maida kan sa bunsuru!, Good girl, you are fighting for your man a bayan idon shi!, E go still red for your eyes, idanun ki za su yi ja soon, ya kamata ki bude idonki ki san abin da kike yi, because if na marriage dey hungry you idan auren sa kike son yi, bayan kun yi aure da ƙafar ki za ki gudu, kar ki ce baki san abin da nake magana a kai ba, kina sane, kin san abin da nake nufi.. But You will still do your mind anyways!, Akwai maganganu a bakina, akwai magana da yawa a cikina, bana so in faɗe su a nan, bana son darajar ki ta girgiza, because I'm in a good mood today, but sister kar ki ce ban gargade ki ba, better get sence, ki bar yaron nan kafin lokaci ya ƙure miki, idan don kudin da kika kashe mishi ne gara ki lissafa ya biya ki, ki fara rayuwan ki afresh..."

Ta ƙarashe maganar tana komawa cikin gadon ta, ta tattaro taliyan da ta zubar mata, ta haɗa da na cikin kwanon ta cigaba da ci tana magana idanun ta a kan sauran ƴan ɗakin da suka sandare suna mata kallon mamaki, maganganu ke fitowa cikin bakin ta kaman ruwa, yarinyar da za ka zagi uwar ta da uban ta a gaban ta ba za ta ce maka komai ba?, Kaf ɗakin in ba Khadijah ba babu wanda take kulawa, sai dai in maganar su ta shafeta ne, hakan ya sa suke mata kallon mara wayau sosai, they were in shock irin daukewar brain dinan basu ma san me za su yi ba, kallon ta suke kawai, yayin da take cin abinci ta cigaba da faɗin.

"We all need to help this lady, because a woman who is desperate about marriage no care about her happiness, next time idan an gaya miki an gan ni da shi ki zo ki tare ni ki ce za ki min rashin kunya, if them born you well ki fuskance ni, kin san ni, kin san inda za ki sameni, i no hard to find, I dey my lane 24/7, if i do my own don't call am bullying, don't call am witch craft oo, because I dey my own una dey jump, Ina zaman zamana kika nemi ki shiga gonata, both you and your boyfriend una dey craze, you don't see una life?, The same pattern, you dey with man who no love you, man dey with you out of pity, you dey pay am like say na job, ku kuma idan kun cewa san mutumin nan ya taɓa neman ku ku yi magana tun wuri, if not you will forever remain silent, a nan ɗakin ma na san wasu mutanen da basu kwana a hostel duk saboda shi, akwai waɗanda Maleek ya biyawa kudin makaranta, gara ku yi magana a yi ta ta ƙare...!, Say it with proof maybe una open the nonsense eye, maybe she go come back to her senses, abege comot for my front before I stab you, mumu"


Zee Chindo da ta tabbata da cewa wai Zakiyyah ta gama da ita, tun tana sauraron abin da take cewa har ta daina fahimtar komai har ta dasa aya, sai ta ji gaba ɗaya duniyar na juya mata, hawayen baƙin ciki da kunya suka shiga gangarawa saman fuskan ta, hawayen da ta manta rabon da ta ji ɗumin su a fuskar ta, ta juya jiki babu laka zata fice daga ɗakib sai dai shock din ya riga da yayi mata yawa ko wani fita bata yi ba jiri ya kwashe ta ta fadi a jikin babban ƙawar ta Maryam dembo da ta yi sauri wajen rikota. Ta riƙeta suka bar hostel ɗin a kunyace.

Cikin ƙanƙanin lokaci zance ya yaɗu a hostel, babu wanda bai san Zee ba saboda iyayin ta da yanda take rarrabawa mutane kuɗi, Zakiyyah ce dai ba'a sani ba, har ɗaki ake zuwa ana kallon kowacece Zakiyyh, a ranar ko ina ka shiga a hostel zancen ake yi, wasu ma har da ƙari, suna cewa Zakiyyahn har marin ta tayi, kuma Zee ɗin ta kasa ramawa, masu zuwa ganin Zakiyyah a common room kuwa ba za su ƙirgu ba.


*Maryam*
Sai da ta gasa jikin ta sau uku sannan ta samu sauƙin azabtar da take ji, don ba ƙarya ta daku. Ta kira mahaifiyarta tana kuka ta sanar da ita komai. Mahaifiyarta ta ce, ai wannan wulaƙanci ne da rashin sanin darajar dan adam, ta dawo gida kawai, kuma dole Mohan ya saketa, tun da bai san darajar ta ba. Maryam ta rikice ta fashe da kuma.

Ganin ta daburce sosai sai ta hau lallabata ta ce mata wai kaza ne ta mance bata ci ba shi yasa take jin kaman ba zata iya rayuwa babu shi ba.

Nan mahaifiyar ta, ta gyara zama kamar abin kirki ta fara lallashin ta tana bata shawara kamar uwa ta gari,tana nuna mata cewa ita dai harga Allah bawai bata son auren ta da Mohan bane, kawai bata son yarta ta aure namijin da bai san darajar ta bane kwata kwata, a ce tun bata tare ba ya fara sawa ana dukan ta inaga in ta tare?, tacewa Maryam inda ace Mohan yana sonta kamar yadda take son shi da sosai zata bata hakur, wata ƙila kuskure ne ya sa ya ki tankawa lokacin da ake dukan ta, amma duk wata uwa bazata so taga yar ta tana bautawa soyayyar namiji ba, idan mace ta auri namiji yana son ta ma ya ka kare bare ace kaine kake son su?.

Babu abin da Maryam take iya fahimta a cikin maganganun mahaifiyar ta har suka yi sallama, lallai kam, wato har sun manta da arzikin da suka kwasa a sanadin auren ta da Mohan shi ne daga kawo ƙarar sa za su ce ta rabu da shi tun bata tare ba, lallai ma, ai ko duniya zata haɗe ba zata rabu da Mohan ba. Ita da shi mutu ka raba.


_To kedai Mero Allah ya baki Sa'a_ 🤣.

*MOHAN*
Bayan fitan Maryam Khalid ya matso gare shi, Khalid shi ne mutum guda ɗaya mai hankali wanda ya isa ya tsawatar masu idan sun yi laifi, kuma ya hana su abu su hanu, saboda shi ne president din ward ɗin, shekarun sa da hankalinsa ya sa aka ba shi matsayin, yana zaune lokacin da suka daki Maryam, bai tanka ba shi ma kawai don ya ga Mohan ya ƙi tankawa, kuma da alama wajen shi ta zo. Duk yadda aka yi ya bar ta ne su koya mata hankali.

"Ustaz, sai na ga rashin dacewan abin da ka yi , ka kasa hana tsawatar wa yaran nan a yayin da suke dukan baƙuwar ka "
Ɗan murmushi Mohan yayi ya ce

"Matata ce"
Cike da mamaki Khalid presido ya ce
"Dama matar ka ce?, Kuma ka bar su suka wulaƙantata haka?"

Mohan ya ce
"Can we please switch this chapter?, Bana son maganar"

Khalid ya ce
"Ok.... But I was shocked, dama kana da mata?"
Ɗan murmushi yayi ya ce
"Matana Biyu ma, kana min kallon yaro, alhalin inda a ce auren ƙauye na yi sai na ajiye kaman ka"

Dariya Khalid yayi ya ce
"Tun da da an haifi mutum yake haihuwa ba"

"Da kuwa haka ake yi da na yi jika da kai”
"Ba jika ba sai dai tarfasa kunne"
fashewa yayi da dariya sosai harda rike ciki
"Wai tarfasa kunne, tattaɓa kunne ake cewa..."
Da yike tasu ta zo ɗaya da Khalid, hira suke yi cikin natsuwa, cikin ƙanƙanin lokaci suka saba, Khalid sai mamaki yake wai matan Mohan biyu, ba wai ya raina shi bane, kawai don ganin yadda ya kwashe kwanaki a asibitin ba tare da wani ya ziyarce shi ba, sai yau da matar sa ta zo ya yi mata kora da hali, tun da yana da tabbacin abin da aka aikata mata ba zai sa ta iya tako ƙafarta Asibitin ba.

_Hmm dey play_

*Zeeeee*
A ranar bacci ta yi cike da munanan mafarkan Zakiyyah, da ta rufe ido sai ta ga ta kafeta da oily eyes din ta tana gasa mata maganganu.
Washe gari tun da asuba Zee ta kama hanyar Abuja gidan ɗan yayar ta sauka, shi ne abokin shawaranta ya bata shawara ko zata samu sauƙin abin da take ji, kafin ta fice a hostel din basu kwashe shi ƙalau da ƴan hostel ba, mutanen da suka fito suna nuna Maleek ya taɓa neman su sun fi a ƙirga, da ta bar hostel ɗin ma har ta DM ɗin ta aka bita ana antayo mata hotuna, Zee ta tayar da bala'i babu rufa rufa tace ba laifin kowa bane sai na Abdul Maleek, ya raina mata wayau, watau duk ƙarfin soyayyar da take nuna masa, da alƙawurran da yake mata ashe yaudaran ta yake yi? to billahillazi ba zata yarda ba sai ta ɗauki mataki, sai ta yi maganin duk macen da ya taba gani ya ce yana so, ta ringa masifa tana bala'i ita kaɗai da ƙyar ta iya bacci tsabar tashin hankali, da safe kuwa ƴan hostel sun ɗauka za su ga ƴan sanda sun yi masu dirar sanyin sassafe sun tafi da Zakiyyah, ko kuma takardar korar ta a makaranta ya isketa a aji, sai suka ga akasin haka, hankalin Zakiyyah a kwance ta yi attending lectures kuma har aka tashi ba'a ga Zee ba, tambayan a nan shi ne da ma akwai wacce ta isa ta hana Zee zuwa class?, cikin ƙunci da bakin ciki ta kira dribern ta ya ajiyeta a gidan ɗan yayan ta wato Hassan.


"Yanzu ke meye abin daga hankali a nan Anty Zee? Wannan ai abinda zaki koma gefe kiyi dariya kisha kallo ne idan ma da gaske yana kule kulen ƴan mata ke ai gaba ta kaiki dan kin ga a yanzu kuɗaɗen ki za su huta, za ki rabu da shi, ga samari nan masu aji sai wanda kika zaɓa, kin wani like ma wannan sakaran baki kalli kan ki bane?, Wlhy Anty Zee , kin fi ƙarfi ki rinƙa raɓan talaka, ni wlhy mamaki ma kike bani Anty Zee, ina kika baro class ɗin ki da ƙyamar talaka?, Ina taurin kan ki da tunkahon ki yake?"

Hassan ya fada bayan da ya ji bayanin ƙanwar mahaifiyar sa Zee.

Ta numfasa tace
" Ni ma ban sani ba Hassan, ban san meke damuna ba Hassan, ina son Abdul maleek so irin wanda ban yi wa kai na ba, ina kishin shi fiyeda yanda nake kishin duk wani abu nawa, zan iya kashe mashi ko nawa ne idan har zai rufe idanun shi ya daina ganin kowace mace sai ni, Hassan zan iya yin komai a kan sa"

"Lallai Anty Zee kin haukace, dama ke shasha sha ce ban sani ba?, So kike ki yi wasting life and happiness din ki a kan talaka!?, For God sake Anty?"

"Dakata Hassan, kar ka ce za ka min haka, na san zan samu mafita a wajen ka shi yasa nake nan, I'm hurt, zuciyata zafi take min, ka san me zaka faɗa min don't hurt me more"

Ya jinjina kan sa
"Taɓ ai kam Anty Zee sai dai zuciyar taki ta buga amma ba zan goyi bayan ki ki lalata kan ki a kan faƙiri macuci ba"

Ya faɗa yana ƙoƙarin barin wajen, da dai ta tabbatar da gaske Hassan yake ba zai goya mata baya ba, sai ta kira shi, ta canza akalar maganar da maganar zakiyyah, ta bashi labarin abin da ya faru, ta ce

"Yarinyar a yanzu ta san ko ni wacce, ya riga ya faɗa mata komai a kai na, ina tsoron aikata mata wani abun da zai sa ta fallasa sirri na, ina matuƙar tsoron fallasuwan asiri na"

Hassan ya ja tsaki, sosai Anty Zee din take ba shi haushi, ji yake kaman ya hauta da duka ta ko ina har sai ya huce takaicin sa
"Mtsw....'' Ya sake jan tsaki

"Wai ke Zainab tun farko me yasa kika zaɓi ki yi makaranta a kaduna?, Me ya sa baki bi su Anty Jumoke kun yi karatun ku a Cyprus ba?"

Zee ta rausayar da kan ta cikin yanayi mai ban tausayi ta vw
"Ka san ni ina son mulki, idan na je Cyprus babu wanda zan iya mulka, sai dai a mulke ni, dalilin da ya sa na baro Lagos kenan na dawo nan, na kuma yi ƙaryan cewa Uncle shi ne daddy na, ba don ina da kai ba Hassan da yanzu ni ba kowa ba ce'"

Ta ƙarasa wasu hawaye na taruwa a idanunta, Hassan yayi murmushi ya ce

"To ai kenan ba Maleek ne matsalar ki ba a yanzu, maganin yarinyar nan za ki yi, ta taɓa miki ƙimar ki, ya kamata, ki dasa mata tsoro a zuciyar ta, ta yadda idan ta gan ki daga nesa ma sai wandon ta ya jiƙe da fitsari, ta hakan ne kawai za ki iya dawo da martabar ki a idon ƴan makarantar ku"

Zee ta ce
" Zancen ka gaskiya ne amma ta yaya kake tsammanin haka zata faru?, Yarinyar babu tsoro ko ƙanƙani a tattare da ita, rayuwar ta take yi ita kaɗai, bata shiga sabgar kowa ƙawayen ta da suke wasa da dariya da ita su biyu ne kacal, amma duk yawan ƴan dakin nan yarinyar nan bata kula kowa, kuma babu wanda ya san komai a tattare da rayuwar ta, she is living private life, a yadda bata da tsoro gaskiya bata tsoron rasa komai"

"Ranki shi daɗe ya kamata a sake bincika ta, mutanen da suka yawan shuru shuru da ɓoye abubuwan da ya shafi rayuwar su, su ne suke da scars a rayuwar su, su ne suke da abin da idan sun bayyana sai duniya ta girgiza"

Yusee ɗan daudu mai gugan Hassan da ke ta guga hankalin sa na kan hirar su Hassan ya fada. Zee ta harare shi tace

"Yusuf idan muna magana kada ka sake tsoma mana baki, idan aiki ka zo yi ka gama abin da ya kawoka ka fice, na tsani munafuki wlhy"

"Kiyi haquri hajiya ba munafurci bane, maganar gaskiya ce wanda a ganina duk abinda zaku shirya dole ya zamani kunyi akan saitin da ba za'a ruguza ku ba, Hajiya ƙiman ki da darajar ki sun fi ƙarfin a ci mutuncin ki a kwana lafiya. Akwai hanya me sauƙi da zaku bi ku ci mutuncin ta, sannan ƙiman ki ta dawo a dinga ganin girman ki fiye da da"

Yusuf ya sake fada yana rangwaɗa irin na gogaggun ƴan daudu bayan ya kashe sucket ɗin da ya yi plugging iron


*LITTAFIN MOHAN NA KUƊI NE*
Mutane talatin da za su fara siyan littafin za su siye shi a kan farashin #300, duk wanda zai siya daga baya zai biya normal Price #500

*Za'a biya ta wannan lambar 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*

Sai a tura receipt ko shaida ta wannan lambar *09125491597*
Haka zalika zaka iya biya a matsayin katin MTN a wannan lambar *07046627683*

MOHAN IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF ADDICTION INTO AFFECTION.

KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA*
FIRST 30 SUBSCRIBERS WILL BE GOING FOR #300
Pay
*VIA 9122107940*

*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*

EVIDENCE TO *09125491597*

YOU CAN SEND MTN CARD SEND To *07046627683*

Be the first subscriber ❤️

NB _Part one is free_

©BINTOU.
Na yi gabas 🚶🏽‍♀️.
20th December.
[12/22, 12:19 AM] Star: *020

Abinda ya sa tasu ta zo ɗaya da Hassan kenan, in dai munafurci ne da iya haɗa tuggu ne duk ya iya, don shi ma ba ɗan talaka bane, mahaifin sa babban ɗan siyasa ne Alhaji Musa Gala, sannannen ɗan siyasa ne a baya kafin duniya ta juya masu baya gwamnati ta daina yi da su, mahaifin sa ya rabu da mahaifiyar sa sakamakon sharrin matar uba, ya saketa tana da cikin shi, tun yana ciki ake bin sa da bita da ƙulli har ya fito duniya, aka haife shi ga shi nan dai kaman mace kaman namiji, haka mahaifiyar sa ta sha wahala da shi kafin ta samu mijin aure, koda ta sake wani auren, sai mijin ya ce ba zai reni ɗan daudu ba, dole ta maida shi wajen iyayen ta, rasuwan su ya sa rayuwa ya juya masa baya, koda ya koma wajen mahaifin sa ya sha azaba kala kala a wajen matar sa, daga ƙarshe ya koma neman na kan sa a haka ya haɗu da Hassan ya ɗauko shi a matsayin mai gugan sa.


Zee da Hassan suka yi shiru sunasauraron sa shi kuma ganin sun ba shi hankalin su yasa ya cigaba da cewa
"Ina itace naji kin ce babu wanda ya san komai dangane da ita?"
Zee ta gyada kai alamar haka ne, Yusee ya miƙe cikin tafiyar sa ta yanga yayi taku ya iso inda suke, ya samu wuri ya zauna a ƙasa cike da ladabin sauro, yana yarfe hannu yace

"Ai kam kawai Hajiya Zee Zee ki koma gefe ki sha kallo, da kan ta za ta zo ta dafe ƙafar ki sannan ta baki haƙuri, don aradu bomb za mu haɗa mata, kawai ki nemo na kusa da ita ki sa su binciko maki labarin yarinyar, dole akwai mummunar labarin da bata so kowa ya sani, idan babu kuma mu haɗu sai mu ƙulla mata sharrin da zai sa a tsane ta wata ƙila ma a kai a koreta a makaranta, plan B ɗin mu yi zai sa mutane su yi zargin dama can akwai wata ƴar tsama ne a tsakanin ku, shi ne ta yi amfani da wannan damar wajen ci miki mutunci, idan abu ya kai ya kawo ma mu haɗa hujjar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login