Showing 30001 words to 33000 words out of 72389 words

Chapter 11 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4946

sa ki makara a zane ki,shegiya munafuka mai suffar mayu"

Kan ta a ƙasa ta wuce ɗakin siddiƙa, tana bin ta da masifa kamar zata ari baki, mai gadi da drivern Daddy sun riga sun saba da ganin irin azaban da Siddiƙa take ganawa Zakiyyah kullum, wata zubin ma hayaniyar ta ke tashin su bacci, ga shi duk abin da za'a yi uwar ba zata tanka ba. Dauda mai gadi ya dubi Shamsu direba yace

"Wannan yarinyar tana ganin rayuwa a gidan nan, a ce mutum da gidan ubanta amma a ce kwanciyar hankali ya gagareta?, ƴaƴan kwalta ma su fika gata a gidan ubanka?, Ni wallahi laifin uban nake gani, yana sane da komai, ya bari mace ta maida shi saƙago sai yadda ta yi da shi"

Dauda ya ce
"Ni kuma wallahi na fi ganin laifin uwar yarinyar, ita ta basu dama ai suka raina ta, in da a ce tun a fari bata bada fuskar da zai kawo wata karuwa cikin gidan ta ba da babu abin da zai sa ta ga lagon ta har ta fara tunanin taɓa mata ƴaƴa, ta bar ƙaruwa ta shigo cikin gidan ta sai juya su take son ran ta, ita kuma ta zuba ido kaman doluwa sai yadda aka yi da ita, sai kace ba haifan su ta yi ba".

Tana gama sharar ɗakin ta wanke bayi, ta share ɗakin ummanta da na abbanta, ta yi moping, ta saka turare, sannan ta yi wanka ta saka uniform ɗin ta waɗanda suka yi duƙun duƙun tsabar dauɗa, ta fito da sauri ko abincin bata tsaya ta ci ba, a makarantar ma sai da aka mata horo da dukan latti karfe biyu ta dawo a gajiye, ta yi Sa'a mahaifin ta ya fita, shi da siddiƙa, sun kai Jabeer asibiti, aka bar mahaifiyarta da Ammar da jabeer.

Direct kitchen ta nufa don ta ɗauko abincin ta, amma wayam, babu alamar an yi girki a kitchen ɗin, ta je ɗakin Ummanta ta tambayeta ina abincin ta, fuska cike da damuwa ta ce

"Ya kulle store, ya tafi da makulli, nima ban ci komai ba"

tun kan ta rufe bakin ta hawaye suka wanke mata fuska, tace
"Maman mu yanzu babu abin da zamu ci?"
Umman ta kwance gefen zanin ta ta ɗauko wata naira hamsin ta miƙa mata "Ga hamsin, ita kaɗai ta rage min, ki je shagon iliya ki siyo garin rogo gwangwani ɗaya naira ashirin, sai ki siya sugan goma, tun da ke bakya shan ruwan gidan nan ki siya piyo wata na naira biyar, da gyaɗan goma"

Ta ƙarɓi kuɗin, tana share hawayen ta, ta fice umman nata na mata kallon tausayi, Garin ta siyo, gwangwani ɗaya Naira ashirin sai sugan goma da gyaɗan goma, sauran goman kuma ta siya Omo da shi, sai da ta wanke uniform ɗin ta sannan ta sha garin a haka babu ruwa, saboda bata shan ruwan famfo da ruwan rijiya, sai pure water, tun ba bayan wani typhoid da ta taɓa yi lokacin tana primary likita ya ce ta daina shan ruwan da ba na gora ba....

A last update na yi mantuwa, a gafarce ni 😜 Bayan Nusaiba da Imam, mahaifiyarta ta haifi Nana firdausi, Julaibib da autan su Aiman wanda ake kira siyam, saboda a cikin watan azumi aka haife shi. Ita kuma Siddiƙa bayan ta yaye Zayd ya aureta, sai a lokacin aka san da ƴaƴan da ta haifa masa tun kamin ya auri Maman su Zakiyyah. Kafin ya aureta sai da rayuka suka ɓaci, amma hakan bai hana auren ba.

Na ƙaramin ƙura aka tayar ba mahaifin sa ya ce ba zai auri karuwa ba, shi kuma Ahmad yana da kalar wata zuciyan da idan yana son abu babu wanda ya isa ya hana shi wannan abun, koma waye, idan yana son abu baya ji baya gani. Shi ba ma ta kan laifin da yayi yake ba, cewa yake babu wanda ya isa ya hana shi auren Siddiƙa, sai ya aureta koda hakan zai zama silar rabuwan shi da kowa, dama ai shi kaɗai yake rayuwa, ba zai damu ba don wani ya bar rayuwar sa a kan abin da yake so. Haka dai ya cigaba da faɗin maganganu, maganganun da suka yi matuƙar bawa Kowa mamaki, don duk wanda ya san Ahmad, ya san mutum ne nagartacce mai kunya da girmama manya, amma cikin lokaci guda ya rikiɗe ya koma wani mutumin na daban. _Yo ai ba abin mamaki bane, me kuke expecting a kan gogaggen namijin bariki. Namijin da ya ajiye ƙatin ƴƴa har uku a bariki, ya kuma kawo karuwar sa gida, ya bata fifiko fiyeda matar sa ta sunnah.

(Wani ya ji wannan labari zai yi tunanin ko asiri Siddiƙa ta yi masa?, Don a wannan zamanin maza basu auren matan bariki, specially matan da suka lalata, amma a zahirin gaskiya akwai mazan da ke auren karuwar su, barin ma idan karuwar tana da tsafta, idan ta iya tattali, tarairaya da iya mantar da namiji dukkanin damuwa, Siddiƙa full option CE and more, ga shi nata takun ya haɗa da matsanancin soyayya da yake yi mata... Siddika ko a barikin classic mace ce wacce ba kowane gara take kulawa ba, a kan Ahmad ta fara bariki tun bayan fyaɗen da aka yi mata a ƙauyen su (a cewan ta), sannan ta saye zuciyar sa da ladabi da bin duk wani abin da yake so.
koda ta zo gidan ba da niyyar muzgunawa yaran sa ta zo ba, ta so ta aure shi ne kawai ta ƙwace shi ya zama nata, da fari ta fara jan yaran sa a jiki da salon makircin sa, sai ta ga alaman shi ma ba son su yake ba, don haka ta yada duk wani munafurcinta ta fito masu a mutum,shi kuma ya goya mata baya.

hankalin Siddiƙa ba ƙaramin tashi yayi ba jin abin da Daddy ya gaya mata, tana mugun son sa, bata so ta rasa shi shine rayuwar ta, ganin yadda ta tada hankalin ta ya sa ya kwantar mata da hankali, ya ce kar ta damu, babu wanda ya isa ya raba shi da ita, ranar wata laraba ya sami limamin anguwan su da maganar, ya ce yana so a ɗaura masu aure nan da ranar juma'a, ba tare da wani dogon magana ba liman ya amince, sosai ya zage ya gyara gidan, ya ce Farida (Mahaifiyar SU ZAKIYYAH) ta koma boys quarters kafin ya sami kuɗi, yana so ya gyara upstairs ne, sai ya sakata a nan. Sai a yanzu iyayen su suka yadda da zancen Farida, ƙararrakin da take kawo masu suka ƙi fahimtar ta. Sai yanzu suka gane cutar da suka yi mata. Haƙuri suka shiga bata da cewan ta yi haƙuri, komai zai wuce.

Ranar da iyayen sa suka zo gidan, suka inda ya maida Farida da yaran sa hankalin su yayi matuƙar tashi, mahaifin sa Alhaji Abdul azeez ya ce, ba zai yarda da wannan sakarcin ba, ya maida Farida sashen ta su raba sashen, in ya so daga baya in ya kammala ginin sai ya raba masu. Ahmad ya dubi mahaifin sa sheƙeke, babu ko shakkar sa ya ce

"Abba... Ko a musulunce babu kyau shiga cikin rayuwar mutum, wannan rayuwata ce, Farida iyalina ce, ku kuka aura min ita, ta riga ta zama mallakina, babu wanda ya isa ya gaya min yadda zan gudanar da rayuwata"

Alhaji Abdul Azeez ya dubi ɗan sa cikin nadama mai nauyi tare da da na sani mara adadi, idanun sa cike da ƙwalla ya ce

"Ni kake gayawa wannan maganganun?, Ni kake cewa ban isa ba..."

Ahmad ya dakatar da shi cikin hargowwa
"Eh baka isa ba Abba, me ka taɓa min a rayuwa?, Banda nuna iko da kuka yi kuka liƙa min wannan kucakar matar, wane uba na ƙwarai ne zai toye haƙƙin ɗan da ya haifa sannan ya hana shi jin daɗi?, Abba ka cutar da zuciyata, ka tauye min ƙuruciyata, ka tilasta ni na zauna da wannan matar duk da bana son ta, na yi maka biyayya duk da ba son ta nake yi ba, na haɗa jiki da ita ba don ina so ba, amma haka nan nake ɗaukan nauyin buƙatun ta, sutura, lafiya da ciyarwa duk babu wanda na gaza saukewa, in fita nema dare rana cikin sanyi, ruwa da wahala, haka nake jurewa duk don na faranta maku, me kuke so? shikenan don kun haife ni bani da tawa rayuwar?, Na yi maka biyayya na yi maka ƙoƙari, bana son ta, amma ban sake ta ba saboda ku, ga shegen haihuwa kaman ƴar akuya, ƴaƴanta shida kuma haka nake ɗaukan nauyin su duka ban taɓa gazawa ba, sai yanzu da na shirya yin rayuwata cikin jin daɗi sannan za ka zo ka ce za ka hana?, Wallahi babu wanda ya isa ya hanani gudanar da rayuwata yadda na tsara"

Ranar da baƙin cikin Ahmad Alhaji Abdul Azeez ya koma gida, ya koma shuru shuru walwalar sa da maganar sa ya ragu, bai faɗawa kowa cin mutuncin da Ahmad yayi masa ba, don ya san idan har ya faɗa abin da yayi, sai rayuka sun ɓaci, bayan kwana aka tarar da gawan sa a gida, zuciyar sa ta buga ya mutu. Bayan rasuwar Alhaji Abdul Azeez da sati ɗaya, Ahmad ya tada fitina cewan sai an raba gado, ba'a ja maganar ba aka tara yayyin sa da ƙanne har da ƴan uwa aka tattaro komai, aka samu lauya da ƙwararru aka raba gado, kowa ya kwashi rabon shi, cikin rabon Alhaji Ahmed har da ƙaton gidan Alhaji da ke nan cikin garin Zaria, bayan kwanaki ya tattara iyalan sa suka koma sabon gida, sai a lokacin Farida ta samu sakewa don flat ɗaya ya ware mata ita da yaranta, gidan na da faɗi sosai, don kowa da nashi ɗakin, gidan yana da faɗi sosai ta gaba da ta baya, har da swimming pool da garden, tsarin gidan yayi daidai da mafarkin Siddiƙa, don ita mace ce mai son a huta, tana son raguwar ƙarya, bata damu ta kashe last card dinta ba indai hakan zai kankaro mata martaba a idon duniya, danginta dama tuni ta watsar da su, tun da aka yi mata fyaɗe ta baro garin su, ta samu wasu dangin waɗanda suka shigar da ita harkar bariki daga nan bata sake waiwayan su ba..

Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa, Nusaibah na bording, kullum wahalar da sidd take ganawa Zakiyyah, ƙaruwa yake, ƙannenta Imam, Nana julaibib da ayman, ko zaman gidan ba su yi, sai dai su fita yawon su, in lokacin cin abinci yayi su dawo su ci, su ƙara fita. Sosai fitan da Nana take yi ya buɗe mata ido kaf anguwar babu wanda bai san ta ba, tsokana, rashin mutunci, sata, da ɗaukan abun wani ba komai bane a wajen ta, duk girman ka in ka yi mata sai ta rama, idan ka nemi ka ci mutuncin ta kuma ta tara maka jama'a, yarinya ce, amma bata gudun abin kunya. Idan ƙaddara ta sa ta ɗau kayan ka, da kan ta za ta gaya ma ta ɗauka kuma babu wanda ya isa ya ce don me, don koda an kai ƙara wajen mahaifin ta cewa yake babu ruwan shi, in sun ga dama su dakata, su ƙarbi kuɗin su, idan suna so kudin su ya fito su je wajen mahaifiyar ta....


Not edited 😒

Allah ya sa ban yi shirme ba
6th December
Bintou
Nayi gabas🦋🌹
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *012*



......Ita ke basu haƙuri har ta biya kuɗin. Duk abin da Nana take yi yana dawowa kunnen Daddy, tun abin baya damun shi har siddiƙa ta fara zuga shi, kuma ta yi nasarar dasa masa tunanin abin a ran shi, cikin makirci ta saita shi, ta sa ya cire ta a makarantar jeka ka dawo, ya maidata boarding a cewan ta idan Nabila ta cigaba da ɗauke ɗauken da take yi a abubuwa abin zai taɓa mutuncin shi, kuma mutane ba za su rinƙa ganin girman shi ba.

Ra'ayin Siddiƙa shi ne ra'ayin shi, gani yake kaman ta fi shi sanin kan duniya saboda wayewa da iya salon makirci. Ita kuwa Umman su ba'a yi shawara da ita ba, kwatsam sai ta ga ya jido mata provision, ya ƙarɓi passport ɗin ta sannan, ya haɗata da yayarta Nusaiba ya kai su makarantar kwana, ita kuma Zakiyyah ya bar ta a makarantar jeka ka dawo a cewan sa ta fi kowa amfani a gidan. Haka rayuwa ya cigaba da gungurawa, kowa da abin da ya saka a gaba, ban da Zakiyyah da mahaifiyar ta, wanda rayuwar su take a lanƙwaye kaman kan ludayi, Siddiƙa da ƴaƴan ta sun ƙwace gidan, yaran ta su ne ƴaƴan Daddy, sauran kuma kaman tsinto su yayi dan ko cewa aka yi ya siffanta kamannin su ma ba zai iya ba, baya shiga ɗakin Farida sai da dalili, kuma bata isa ta bar fita a gidan sa ba in babu dalili, ta inda take samun sauƙi ɗaya ne baya tauye masu haƙƙin su na tufatarwa, ciyarwa da kare lafiyan su, a yanzu da harka ta buɗe masa ma duk wata sai ya ba Farida dubu hamsin, makarantar da yaranta ke zuwa mai tsada ne, duk da kasancewar wanda su Ammar ke zuwa ya taka nasu a tsada da komai. Ya ce baya son Farida, amma ba zai iya rabuwa da ita ba, zai bar ta a gidan sa ta reni ƴaƴan ta, sannan ta ƙarasa rayuwar ta tana ibada har ta mutu.

Yau Daddy ya bar Farida ta je Maiduguri ta ga iyayen ta, bayan shekaru da suka ɗauka babu waya babu ziyara, Su Imam sun tafi yawon da suka saba, siddiiƙa da yaran ta sun tafi shopping, ita kaɗai ce a gida, tana shirin fita Islamiyya bayan ta gama gugan tulin kayan da Siddiƙa ta jida mata. Daddy ne ya shigo tare da wasu mutane, ya ce ta yi masu girki kafin ta fita, cikin ladabi ta ce to, haka nan ta je ta cire kayan islamiyanta ta shiga kitchen ta yi masu girki ta kawo masu, tana shirin barin wurin ta ji abin da ya gigita, Daddy da mutanen ne ke cinikin mata kaman suna cinikin gyaɗa, farashin budurwa daban farashin baƙa daban da na fara, haka mai ƙiba daban da siririya, a yanda ta ji hiran nasu ma aikin nasu bai tsaya a iya ƙasar nan ba, suna ɗeban mata daga sassa daban daban na ƙasar nan bayan haka su yi ordern farare daga ƙasashen ƙetare, hankalin ta yayi ƙololuwan tashi. Da alama Daddy ya jima a harkar, kenan da wannan kasuwancin ya gina companyn sa har yake ciyar da su?.

Ta kasa tafiya makarantar ta jira har sai da ta ga tafiyar su, Daddy ya shigo bayan yayi masu rakiya, ta bi shi ɗakin shi, yana waya da abokan kasuwancin sa, ta samu waje ta zauna, ta jira har ya gama wayab, ya ɗago ya kalleta da mamaki.
"Baki tafi makarantar ba?"

Tace "Eh Daddy, dama wata magana nake so mu yi"

Yace "to ina jin ki"

"Daddy da gaske kuna safarar mata kuna kai wa ɓatattun ƴan kasuwa da ƴan siyasa suna lalata da su?"

Zuciyar Daddy ya Harzuƙo, cikin fargaba da ɓacin rai yace

"Wato laɓe kika tsaya kina yi mana ko?."

"Da gaske ne ko ƙarya ne?"

Ta faɗa cikin katse shi, ya haɗiye wani yawu mai nauyi yau duk rashin kunyar sa sai ya tsinci kan sa da jin kunyar ta, amma da yike namiji ne, sai ya waske, ya ɗaure fuska tamau, ya ce

"Da gaske ne, sai aka yi ya?, tashi ki fitan min a ɗaki"

Ta kafe shi da ido kuma ta ƙi fita babu alaman tsoro a tattare da ita, kuma ta ƙi fita. Ya daka mata tsawa.
"Ke wai menene?, Kin wani kafe ni da idanu, tashi ki ɓace min da gani"
Bata tashi ba, sai ma ƙara kafe shi da mayatattun idanun ta da ta yi, idanun ta a kan sa ta ce
"Daddy Wallahi ka ji tsoron Allah, ka yi tunanin ya rayuwar ahalin ka za ta kasance ko bayan ran ka, ka tuna cewa ka haifa, kuma kana da ƙanne mata, kana da ƴaƴa mata, matanka duka biyu mata ne, idan aka yi wa ƴar ka haka ya zzz...."

"Zakiyyah...!"
Ya daka mata tsawa.
"Get out...!, Ki fice min a ɗaki tun kan ran ki ya ɓaci"
Sai dai ina, a wannan lokacin zuciyar Zakiyyah ya riga ya kafe, kafiya da taurin kan da ta gado a wajen shi ya motsa, bata hango komai sai munin sana'ar mahaifin ta, burin ta tunasar da shi illan abin da yake aikatawa ba, wata ƙila ma tun kan a haifeta yake ciyar da su da haram, hawaye suka cika mata ido, ta ƙi fita ko motsawa bata yi ba.
Ta buɗe baki zata sake magana ya hau ta da duka ta ko ina, cikin fushi yana zagin ta, bata yi ƙoƙarin kare kan ta ba, ko motsa wa bata yi ba, sai hawayen da ke fita a idanunta.

Dukan ta yake da iya ƙarfin sa yana zaginta fa uwa ta uba. Sai da ya gaji dan kan sa sannan ya ƙyale ta, ya bar mata ɗakin yana zage zage kaman taɓaɓɓe, zuciyar sa cike da ƙunci da tsanar Zakiyyah.
Bata faɗawa kowa halin da ake ciki da dukan da mahaifin ta yayi mata ba, sai dai ta sa wa ran ta daga rana mai kama ta yau, har abada ba za ta sake amfani da abin da ya fito daga cikin dukiyar Daddy ba. Da dare ta raba wa su Julaybib abincin ta, da safe ma haka, bayan ta yi wankin kayan Siddiƙa da yaran ta duk da yunwan da take ji, ta shanya wasu, ta bar sauran a bakin famfo da niyyar idan ta dawo za ta sake ɗaurayewa sannan ta shanya su.

Haka ta tafi Makaranta da yunwa, ta dawo jiri na ɗiban ta, amma tsabar kafiya da taurin zuciya irin nata ta ƙi cin abincin gidan ba za ta sake cin haram ba, ta saka hijabin islamiyyan ta ta bi hanyar islamiyya, sai dai yunwar da take ji ya hanata ƙarasawa, ta canza hanya tana tunanin inda za ta samu aikin da za'a rinƙa biyan ta, wani restaurant ɗin da ke bayan layin su ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login