Showing 57001 words to 60000 words out of 72389 words

Chapter 20 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4937

ina nufin idan mutum ya ce ya tuba ya daina shaye shaye bai kamata a guje shi ba, domin a lokacin ne yake buƙatar kusanci da mutanen arziki wadanda za su tarairaye shi su taya shi mantawa da ƙwayoyi, amma ni duk lokacin da na yi niyyan dainawa ƙyama da hantaran family ɗina shi ke sa ni komawa"

Ya faɗa zuciyar sa na matsewa sannan wani d'aci ya cika k'irjin sa, yayin da wasu hawaye na tausayin kan sa suka ƙawata ƙwayar idanun sa. Da kyar Zakiyyah ta dago ta kalle shi da jajayen idanunta da suka kara cikowa da hawaye jin yayi shiru, sai yayi murmushin yaƙe yana maida hawayen sa
" Ba yabon kai ba problem, ni ba mutumin banza bane, zan iya faɗa with full chest and confidence a ko ina cewan ni ba mutumin banza bane, though shaye shaye ya sa ni aikata manyan laifuka a baya, amma duk da haka bani da mugunta, bana neman mata, sannan ina da bautan Allah, kuma ina son kyautata mu'amala da kowa"
Ya furzar da wata iska mai zafi daga bakin shi, yana feeling kan shi free, yanda yake warware mata damin da ya dami zuciyar sa yayi setting ɗin sa free
"Shaye shaye ya sa na yi asarori da dama problem...
"Babban asaran da shaye shaye ya ja min shi ne, lokacin da nake ganiyar shaye shayena na yi loosing faith ɗina bana sallah da wuri, bana karatun Alkur'ani, bana azkar, har ta kai ta kawo akwai lokacin da idan na tashi da safe sai in hada sallolin ranar gabaki ɗaya, saboda wanda nake sha a lokacin mai ƙarfi da tsada ne sai mutum yayi 24hrs yana maye kuma bana so in je gaban Allah ina maye, duk da na san haɗa sallan da nake yi ma ba daidai bane, bayan wannan ma shaye shaye ya sa na yi loosing love, care and concern from my family kaf family ɗina kallon mutumin banza suke min, babu mai raɓana sai ɗan uwana da matar sa, kuma bayan haka problem na yi sace sace, na saci kudin Abba na, kuɗaɗen da ni kai na ban san iya adadin su ba, shaye shaye ya sa na rasa Nihaal a karo na farko a yanzu ma idan na sake rasata shaye shaye ne sila 💔🥲,, don mahaifin ta ya rantse matuƙar ina shaye shaye ba zai bani ita ba, na yi loosing aikina, yanzu bana aikin komai, sai dai a yi aikin a bani, bani da takamaiman abu na kaina duk na siyar da su, babban abin da na siyar a cikin dukiyata shi ne babban motata mafi daraja, a lokacin da na siyar ko? In cash aka bani kuɗin, my thoughts was like kawai na fara business da kudin a ɓoye in yaso sai na rinka using profit ɗin ina siyan kayan mayen tun da a gida an hana ni kuɗi, but guess what ko sati biyu basu rufa ba suka ƙare tasss, idan na gaya miki kudin motar wlhy sai kin girgiza, don kudi ne wanda bana tunanin nan da shekara biyar ma in kina tara Naira dubu goma a kullum za ki iya mallakar ta, problem i loose alot.. na yi asara da yawa"

hawayen da suka taru a cikin idanun sa suka sauko zurrrrr, itama kuka take yi sosai, tana kukan sosai ta ce

"Amma duk da haka me yasa baka daina ba?, Baka jin tausayin kan ka ne?"
Sai da ya share ƙwallan sa, sannan yayi manup, ya daidaita Muryar sa, sannan ya ce
"Problem... Wallahhi ina so na daina, na sha zuwa rehabilitation duk don na daina, Abbana ma ya sha kai ni wajen malamai, har ta kai ga cewan malaman da idan an kaini wajen su ni ke koyar da su wasu abubuwan, saboda ina da ilimin addini daidai gwargwado, koda a ce na daina shaye shayen, na wani lokaci ne, amma da zarar an matsa min a gida, ko idan an takura min sai in ji kaɗaici in ji an tsane ni, sometimes idan Abba na yayi min faɗa har na kan kasa bacci, saboda sometimes idan yana min faɗa har hawaye yake yi, ki fahimci ɗacin abin..., wannan tashin hankalin ke hana ni bacci, ni kuma idan na kasa bacci sai in nemo abin na sha, in yi bacci"
Ya furta yana share fuskan shi dan har yanzu akwai ruwan hawaye kan fuskan.
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un"
Sosai hawaye ke bulbulowa ta saman fuskanta. Ya kalleta a raunane.
"Ke ma kin fara ƙyamata ta ko?"
Da sauri ta sa hannu ta toshe masa baki tana girgiza kai...
"Ba zan taɓa ƙyamar ka problem, koda abin da kake sha ya fi ƙwaya"
Hannun ta ya riƙo da hannu ɗaya, ya sa ɗayan yana share mata hawayen da ya zubo mata , a hankali cikin weak tone ya ce
"Solver... Between me and you, na yi miki alƙawarin ba zan sake shaye shaye ba, har na koma ga Allah, be my strength please"
Tace
"Please problem idan an yi maka faɗa ka dinga yaƙar zuciyar ka, idan ka sha wani abu don manta komai, su babu abin da zai same su, Kai ɗin dai da aka ɓatawa rai kai ne zaka kwana a ciki, ka duba yadda shaye shaye ya rabaka da komai, kai mutum ne mai daraja problem, amma a wajen masu shaye shaye kai banza ne, babu mai respecting ɗin ka, yanzu kana da iyali, You need to stop ko dan nan gaba kada a kalli ƴaƴan ka da abin, loneliness da faɗan da ake maka all these are not enough reason zai sa kiyi embarking on shaye shaye, be strong.,. , duk problem din da kake da shi always face Allah ka gaya mai, problem daga lokacin da ka fara tunanin akwai wani abin da zai sa ka farin ciki bayan Allah daga wannan lokacin rayuwar ka ta fara taka hanyar asara, you are too young to understand some situations and circumstances in this life, stop believing drinking this and that smzai sa ka manta da damuwanka, akwai wahala idan mutum zai daina, especially addicted person kaman kai, akwai wahala sosai, amma ka jure kana wuce wannan process din za ka ga gabaki ɗaya ka daina sha'awar shaye shaye"

Sosai ta ba shi shawara kuma ya gamsu, ya kuma sake jaddada mata cewan shi da shaye shaye har abada, haka suka rabu cikin tsananin bege da kewan juna. Koda ya koma Hotel ɗin sa sai ya tarar da Alhaji Naseer da kan sa ba driver ba kaman yadda ya ce, cikin shi ya ɗan hautsina, ya ƙarasa wajen sa gwiwa a sake yana gaishe shi, shi ma Alhajin bai ce komai ba don zuwan shi kenan, a da yayi niyyar tura driver ya ɗauko shi ne kawai, sai ya tuna akwai gaisuwan da zai yi a Zaria, kuma yana buƙatar rakiyan Mohan ɗin.

*Zaria*
"Lale maraba da manyan baƙi, ran ka ya daɗe da kan ka ka zo?, Ai da ka aika an kira ni da kai na ma zan zo"

"A'a Alhaji Ahmad, wannan zuwan naka ne, sai muka ji mummunan labari, ohhh Allah ya cigaba da karewa"

"Amin ya Allah"

"Amma ƴan sanda sun kamo wanda ya aikata kuwa?!"

"Hmm...Ga su nan dai, kullum cikin bincike suke, ni na ce da za su bari kawai tun da kaman masu laifin sun fi ƙarfin hukuma"

"A'a dai kada ka ce haka Alhaji Ahmed, babu wanda ya fi ƙarfin hukuma, in sha ƴan sanda za su kama waɗanda suka yi garkuwa da kai sannan su yi maka adalci"

Ameen
Tashi Daddy yayi ya kira matar sa don su gaisa, nan da nan Siddiƙa ta cika musu gaba da kayan ciye ciye, ta zauna suka gaisa.
Alhaji Naseer ya ce
"Ni ban ji motsin mutuniyar ba, dama ka jima kana mana rowan fuskar ta"
"Wai Blacky?."
Alhaji Naseer ya ce eh.
Shi dai Mohan baya gane komai sai kallon su yake, yana nazartan prof Ahmad Abdul Azeez, akwai wani abu dangane da shi wanda ya sa yake jin kaman ya haɗa damgantaka da problem ɗin sa, kamannin su yayi yawa, ko dai moments ɗin su na ɗazu ne ya sa yake ganin fuskar ta a jikin kowa?, Dan koda Zayd ya zo wucewa sai da ya ga tsantsan kamannin yaron da ita.
"Lah tana makaranta aii, a can take kwana wlhy. Dama tun da nagan ku na san zuwan ta ne tunda baku taɓa zuwamin ba."
Dariya Alh Naseer yayi ya ce.
" a'a dama gunka muka zo, mu jajanta maka abin da ya same ka...ga angon ƴar ka, na san baku taɓa haɗuwa ba tsawon shekaru"

Dam Dammm!, Gaban siddiƙa ya yanke ya faɗi, wannan santalelen saurayin shi ne mijin Zakiyyah?, ai Daddy ya gaya mata tsoho aka aura mata, ta ya za'a nuna mata Balaraben saurayi a ce shi ne mijin ƴar da ta tsana fiyeda ranar mutuwar ta?, sai ko ta zabura ta nuna shi tana cewa

"Kai ne m mijin baƙar yarinyar can?"

Yanda tayin ba Daddy ba hatta Alhaji Naseer sai da ya ji kunya ya kama shi, Daddy bushe da dariyan yaƙe, yanda kasan wadda taga wani fatalwa haka ta rikice tana jera masa tambaya, Daddy yayi ƙarfin halin cewa
"Shi ne mijin da aka aurawa ƴar ki, lokacin da aka ɗaura auren yana Egypt, ya je ƙarban wasu talardun sa, shi yasa baku gan shi ba a lokacin, da ya dawo kuma sai ya kasance shaye shayen da yake yi a baya yayi worse shi yasa na yi tunanin anya ya dace da ƴar ka kuwa? Saboda har cikin rai na bana so a cutar da rayuwar yarinyar, don a yanda na gan ta a lokacin she's very young a ce ta fara dealing da miji mai shaye shaye, bana so auren ya rabu shi yasa nake yawan tunatar da kai nauyin da ke kan ɗana.... yanzu ma zuwa na yi mu duba ka, sannan na gaya maka a yanzu ɗa na ya bani tabbacin ya daina shaye shaye, mu fara shirin biki"

"Au ba tsoho bane dama?" Maganar ta subucewa Siddiƙan, Mohan ya kalle ta, Daddy ma haka bai gane inda maganar ta ma ta dosa ba yace
"Eh mana, ni na gaya miki tsoho na aura mata?, Alhaji Naseer batta abokina ne tun yarinta, lokacin da na fara kasuwanci ma tare muka fara, sai dai shi baya harka da naira ya fi amfani da dala shi yasa muke kiran shi Batta Dala, da ya zama babba kuma sai muka koma kiran sa, Alhaji mai dala" ya furta da zuciyar sa ɗaya.

"Zancen banza ma kenan, ita zata zauna da wannan santalelen saurayin?, Kuma ɗan wannan hamshaƙain? Wlh ba zai yiwu ba" ta idasa kwance ƙullin haukarta. Mohan ya gyara zama ganin cin kan matar gaba yake yi, da alama kishiyar uwa ce irin mugayen nan, shi dai yana ganin ta kan sa mata iri iri Abbba ke aura masa, daga wacce batada kamun kai sai wacce gidan su babu tarbiyyah, Abba ya kama hannun Siddiƙa, ya nufi hanyar ɗakin ta da ita, Ita kuwa daddagewa take tana faɗin

"Lallai ma wannan rainin wayo ne ƙarara, Ahmad ni zaka manafurta?, wlh bazan dauka ba, ni za'a mayar mahaukaciya?, Ni zaka yaudara ka ce min tsoho ka aura mata sannan yanzu ka ce wannan santalelen saurayin, natsattse shi ne mijin Zakiyyah?"

Sai da Daddy ya turata ɗakin ta sannan ya kullo shi ta waje, ya dawo ran sa duk a jagule, shi ma ba irin mijin da ya so Zakiyyah ta aura ba kenan, amma ya yaiya?, already kafin wannan incident din ya faru Alhaji Batta ya sha neman alfarman su haɗa zuri'a da shi saboda wani taimako da ya taɓa masa a shekarun baya, cike da kunyan abin da Siddiƙa ta aikata ya zo yana saukr da kai tareda basu haƙuri, Alhaji Ahmad batta ya ce, dole ma su ɗauke yarinyar don daga gani tana shan wahala a gidan, Daddy da har cikin zuciyar sa ya ƙagu su tafi da Zakiyyahn ya ce ya ce in sha Allah da kan sa zai kai masu ita ma. Daga nan hira suka shiga yi, Mohan dai shuru yayi yana nazarin mutumin da yake gani a matsayin sirikin shi, sam mutumin bai yi kamada mutanen kirki ba, kalaman bakin sa kaɗai ma irin na tsofaffin kilaki ne duk da yana ƙoƙarin ɓoyewa, amma a matsayin sa na wanda yayi alaƙa da ire iren su ya gano mutumin ba mutumin ƙwarai bane, bayan kamar minti30 suka mik'e tare da alk'awarin nan bada jimawa ba za su zo ɗaukan amaryar su.

Ƙarfe takwas da hamsin da biyu na dare jirgin su ya sauka a Abuja. Suna saukowa wayan Mohan ta hau ƙara, mamaki ya kama shi, a iya sanin sa bai taɓa kiran wani da numbar ɗin ba bayan Zakiyyah, tunanin sa ya tsaya a lokacin da yayi tunanin ko Zakiyyahn ce. Ya ɗaga tare da sallama yana murnushi, sai dai sallamar tasa bata je ko ina ba wata kakkaurar muryar mace ta doki dodon kunnen sa.

"Ka riƙe sallamar ka dan batada amfani a nan"

Ya cire wayar a kunne don kalaman sun yi masa muni da yawa, saidai kafin ya sake wani tunanin har ya tsinkayo muryarta ta cigaba da cewa

"Please ina magana da Problem ɗin Melanin ne?"
Da mamaki ya ce
"Waccece Melanin sannan wacece ke?"

"Sanin wacece ni ba shi da wani mahimmanci, Sannan Melanin ita ce problem ɗin ka, idan ban yi kuskuren layi ba, asalin sunan ta Zakiyyah Ahmad"
Mohab ya ji k'arar amsawan ta har cikin kwakwalwarsa yayin da ta cigaba da faɗin

"Shin ta ka san tana da aure?"

Ya ɗan yi shuru zuciyar sa na harbawa da sauri.

"a'a... Problem bata da aure"

"Wow..,Lol, i like your confidence"

Shuru yayi, sannan ta nisa ta cigaba da cewa
"Ka tambaye ta, She is married for 3-4 years!"



*LITTAFIN MOHAN NA KUƊI NE*
Mutane talatin da za su fara siyan littafin za su siye shi a kan farashin #300, duk wanda zai siya daga baya zai biya normal Price #500

*Za'a biya ta wannan lambar 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*

Sai a tura receipt ko shaida ta wannan lambar *09125491597*
Haka zalika zaka iya biya a matsayin katin MTN a wannan lambar *07046627683*

MOHAN IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF ADDICTION INTO AFFECTION.

KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA*
FIRST 30 SUBSCRIBERS WILL BE GOING FOR #300
Pay
*VIA 9122107940*

*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*

EVIDENCE TO *09125491597*

YOU CAN SEND MTN CARD SEND To *07046627683*

Be the first subscriber ❤️

NB _Part one is free_

©BINTOU.
Na yi gabas 🚶🏽‍♀️.
23rd ecember.
[12/25, 10:32 AM] Star: *022*

"A yadda na samu labari ma likita ya ce tana ɗauke da juna biyu na tsawon wata biyu, sannan mijin ta matafiyi ne shi yasa take zaune a hostel, amma tana komawa Zaria duk bayan sati biyu, na ɗau numban ka ne a wayan ta ba tare da ta sani ba, a lokacin da na ji tana cewa za ta kashe auren ta ta aure ka, kuma mijin ta babu abin da ya rageta da shi bawan Allah, shi yasa na kira dan na sanar da kai ka san matakin da zaka ɗauka"
Tun da ta ambaci ciki, wani abu ya sarƙafe shi a tsaye, wani abu da bai san menene ba balle har ya fassara shi da suna, Ƙwaƙwalwar sa na ɗaukan duk kalaman ta yana sake biya su ne a ɓangaren ƙwaƙwalwar sa mai tankaɗewa da fahimtar kowanne bayani, amma sam ya kasa riƙe komai. Abin da ya sani kawai shine ya fahimci abubuwa guda biyu kwarara, Zakiyyah tana zuwa weekend duk bayan sati biyu don ta ga mijin ta, sannan bayan haka ma tana ɗauke da juna biyu.

Dukkan maganganun da take faɗa yana sauraron su ne a matsayin shiririta, eh , shiririta mana!, ta ya wata total stranger zata kira shi from no where ta fara zuba masa tatsuniya kuma a tunanin ta zai yadda da ita?. Ya yadda da problem ɗin sa 99/100, yarinyar da a kullum suna tare a waya?, ya san duka motsin ta, idan sun yi nesa da juna na wani ɗan lokaci ne kuma da zarar ta dawo zata zayyane masa duk wani abin da ya faru bayan sun rabu, abu ɗaya kawai take yawan ɓoye masa, alaƙarta da ƴan gidan su, ta kan nuna suna zaune lafiya, duk da kasancewan ya san basu son ta, don duk yadda ta so ta ɓoye masa yau da gobe ya fi ƙarfin haka, kuma zaman tare na sa ka san wani abu na faruwa da ɗan uwanka koda bai buɗe baki ya faɗa maka ba.


Sauraren ta kawai yake kamar yadda bata dakata shiru ta yi shiru ba, haka ta yi ta zubo zance har da hujjojin ta, dukkan jikin sa yayi la'asar kuma ya kasa dakatar da ita, gaɓobin sa na girgizawa da wata irin karkarwa yayin da zuciyar sa ke dokawa a ƙirjin sa har yana jin ƙarar bugun ta a cikin kunnen sa, bugun da bai san ko ta menene ba, shi dai ya san bai yadda da ita ba, amma ya kasa riƙe kan sa daga abin da yake ji..

"Ya... Ya isa Please, I heard you.., can you please hang the call?"

Ya furta da ƙyar bayan ya tattaro natsuwan sa.

"I dey tell you oo, you need t..."
Kit!, Ya katse wayar haɗe da jan guntun tsaki, ya ja jakan sa ya shige mota, driver ya ja suka bar wajen.


*Kaduna state College of nursing and midwifery* Female Hostel block "B"

"Say it...!, The money don enter!"
"The money don enter" yebo
"E sweet pass baby I love you"
"Ehhnnn....!'"
"E sweet pass baby I miss you"
"Ehn"
"After matel"
"Na hotel"
Leave the matter
"For cartel"
"After Mattel"
"Na hotel"
Leave the matter
"For cartel"
"Say osare"
"Ehn..."
"Orebose"
"Yebo"
"Osare"
"Ehn"
"Orebossee....Yebbbooo!"

Shara suke yi ita da Khadijah tana rera waƙar, Khadijah na yi mata amshi har da rawan su, duk wanda ta zo wucewa sai ta juya ya sake kallon ta, don basu taɓa ganin ta cikin farin ciki irin haka ba, kullum fuskan ta a cakule yake, babu alamun rahama a cikin ta, bata magana da kowa sai ya zama dole, a yau da suka ga tana waƙa cikin farin ciki sai hakan ya zama sabo a wajen su, ta zama abin kallo, ita kan ta Khadijah mamaki take, kusan kaf makarantar babu wanda ya kai ta kusanci da Zakiyyah, amma wannan shi ne karo na farko da take ganin dariyan ta haka cikin farin ciki.

Suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login