Showing 69001 words to 72000 words out of 72389 words

Chapter 24 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4954

wanda zai siya daga baya zai biya normal Price #500

*Za'a biya ta wannan lambar 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*

Sai a tura receipt ko shaida ta wannan
lambar *09125491597*
Haka zalika zaka iya biya a matsayin katin MTN a wannan lambar *07046627683*

MOHAN IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF ADDICTION INTO AFFECTION.

KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA*
FIRST 30 SUBSCRIBERS WILL BE GOING FOR #300
Pay
*VIA 9122107940*

*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*

EVIDENCE TO *09125491597*

YOU CAN SEND MTN CARD SEND To *07046627683*

Be the first subscriber ❤️

NB _Part one is free_

©BINTOU.
Na yi gabas 🚶🏽‍♀️.
27th december
*025*



Wani shauki na angonci da farinciki yake jin kansa a ciki, tun da aka daura auren be taba jin nauyin ya hau kansa ba sai a yau.

Yana kamshi ya doso bakin kofar yana murnushi, Ya shigo ɗakin da sallama, hannun sa riƙe da ledar kaji da fresh milk.


Sai dai farin cikin sa bai kai ko ina ba a wannan daren Amarya ta sa ƙafa ta yi fatali da shi. Babban bakin cikin sa shi ne abin da yake wa rawan ƙafa na riga an rabar wa ƴan kwalta, shi da yake tunanin ɓula leda sai ya ɓige da faɗawa rijiya. Mero's Opueh na second hand. Bai samu Maryam a budurwa ba, na biyu Maryam bata iya wankan sallah ba innalilahi wainna ilaihi rajiun wannan balai da me yayi kama, shi kam ba zai iya ba. Wannan jarabawan ta yi masa nauyi, ba zai iya zama da mazinaciya ba.

A cikin daren ya danƙa mata saki biyu, ya ta kwashe kayan ta tabar masa gida gobe, ya bar ɗakin zuciyar sa na zafi yana jin baƙin ciki mara misaltuwa, ya bar ta tana ta iface itace kaman zata yi hauka. A yanda yake jin kan sa a da ne da yanzu ya nemi abin shaye shaye ko sigari ne don ya ɗebe masa damuwa, amma a yau ko sha'awan su baya yi, da zarar ya tuna da shi sai ya tuno alƙawarin da yayi wa Zakiyyah, da kuma girman alƙawari.

Haka suka yi kwanan baƙin ciki ranar, ko da ta tashi babu sallah da rigan baccinta ta zumbula hijabi ta ɗaga ƙafa ta nufi gidan Abba, ta haɗa masa gaskiya da ƙarya, tace haka kawai ya hau ta da duka sannan ya danƙa mata saki har biyu, sosai ran Alhaji Nasser ya ɓaci, a tunanin sa shaye shaye Mohan ya koma har yayi mata saki ba a cikin hayyacin sa ba.
Ya ɗaga waya ya ce ya zo yanzun nan, daga jin muryar Abba ya san akwai matsala. Zuciyar sa babu daɗi ya nufi gidan, yana saka ƙafar sa a falon Abba ya shiga kashe shi da maruka ta ko ina. Ko gezau bai yi ba har ya gaji don kan sa ya tura shi yana masifa. Idanun Mohan sun yi ja.

"Na yi nadamar amincewa da kai, na yi nadamar nema maka auren yarinyar nan, sakayyan da zaka min kenan?,zunubi da kunya a tattare suke. Idan ka yar da mutuncin ka ba za ka sha ba. Na yi nadamar yi wa mugun mutum alheri, a yayin da nake da tabbacin zaka min rashin adalci" .

Abba kenan, shuwagaban masu yanke hukunci ba tare da bincike ba, wannan kusan halayyan sa ne, sam baya ba mutum dama ya kare kan sa daga duk wani laifin da ake zargin sa da shi, duk wanda ya fara kawo ƙara shi ne mai gaskiya. Da Mohan zai buɗe baki ya faɗi abin da ya faru har yayi sakin Abba cewa zai yi yana jayayya da shi, ko kuma ya ce yana faɗa yana faɗa. Don haka yayyi shuru, har Abba ya gama faɗan sa bai ce komai ba, kan sa a ƙasa. Haka Abba ya sa ya maidata ɗakin ta ba tare da ya ji asalin dalilin sakin daga bakin sa ba. Bai ce mata komai ba har suka koma gida zuciyar sa banda tafasa babu abin da take yi.

Tun a ranar farko Maryam ta kun sa masa bakin ciki ya ƙara tsanar ta, da farko ga kazanta, ga rashin kunya da rashin kamun kai kirikiri take dura masa ashar. Amma baya iya jurewa zafin zuciyasa dan bak isa ya rama ba saboda Abba ya ce bai yafe ba idan ya sake ɓata mata, bata iya girki ba don ran da ta girka masa indomie sai da yayi amai, sai dai ta iya haɗa shayi sosai bayan shi babu abin da ta iya. Tsantsan kiwuya bata wanka sai ta ga dama gata da body odour tsantsan kazanta, ba zata yi wanka ba amma ita idan ta caɓa ado sai ka yi tunanin sarauniyar america ce. Kullum abin ta gaba yake yi, da farko yana jurewa yayi banza da ita, amma da ta kai shi bango sai da ya fito mata a asalin kalan ta. Ya yi forcing out other side of him, ya birkice mata rana guda, ya koma tunzurarre, masifaffe, abu kaɗan sai ya hau faɗa kaman zai hau ta da duka, idan ta yi magana ya ce a yanzu baya tsoron komai, igiya ɗaya ya rage a tsakanin su, zai iya datse alaƙar su har abada. Mohan din da ta raina a da cikin ƙanƙanin lokaci ya koma mata abin tsoro, idan suna zaune a waje ɗaya ba shi da aiki sai jan tsaki, ƙwaƙƙwaran motsi ta yi sai ya hau ta da masifa.
A fannin mu'amala kuwa baya neman ta ita ke neman shi, idan ta zo gare shi sai ya sa ta yi wanka sau uku sannan yake taɓata, sannan tun daga ranar amarcin su bai sake kusantar ta kai tsaye ba, condom ya siyo da uban yawa, shi kyankyaminta yake ji duk wannan adon da takeyi kafin auren su yanzu babu shi.

A satin auren su ya fara aiki, masifan sa da saurin ɗaukan abu da zafi bai tsaya a iya gidan sa ba, hatta ma'aikatan sa suna ƙarban gwale gwale, mistake kaɗan zaka yi ya baka querey gabaki ɗaya ya koma mara mutunci idan yayi wani abin ma shi kan shi har mamaki yake yi, ba haka yake ba, me ya sa ya koma mai saurin fushi?, Me ya sauya shi haka?. Wataƙila saboda a baya idan abu ya ɓata masa rai yakan sha abu domin ya manta da komai, a yanzu da ya daina shaye shaye kuwa sai ya koma yaƙin da kan sa, Yana fighting duk wani emotion da feelings ɗin sa, shi yasa abubuwa ke cakuɗe masa, yayi bursting into anger.

Kaman yadda yayi alƙawari cewa zai dinga zuwa yana duba matar sa ta Zaria kafin tarewan sa, haka yayi niyyar zuwa yau, tun da ya tashi Maryam take ta amai, a da yayi banza da ita, sai ta ba shi tausayi ya taimaka mata, ya gyara inda ta yi amai, ya haɗa mata shayi. Sannan ya fara shiryawa, already abokin tafiyan sa Ahmad yana zaune yana jiran sa tun 30minutes ago.

A hankali yake saukowa daga stairs katafaren falon su, yana sauka ahankali yana gyara zaman necktie din wuyanshi da hannu daya kasancewa dayan hannun na rikeda wata briefcase brown,

"Wannan kwalailaita ko mace sai haka, please Sir kayi da jiki mu tafi, wai halan baka duba time ne?"
Ahmad abokin sa wanda a yanzu yake matsayin personal assistant ɗin sa ya faɗa cikin ƙosawa, yana daga zaune cikin ɗaya daga cikin kyawawan kujerun fakon. Ko nuna alamun ya ji shi bai iba bare ya tanka.

"Ni wlh na rasa gane kan ka, kaida baka da Africa time yau kana neman ɓata mana lokaci, ka san sai dole sai mun halacci meeting ɗin nan kafin mu tafi, kuma yau juma'a....."

"Ohhhh! Please Amady, wai kai bakin ka baya zugi ne? Dan Allah free me, Allow me"

Ya fada da muryar sa mai sanyi amma cikin faɗa kamar zai rufe shi da duka.

"Oh fine, Ahh..ahh..wannan irin kwalliya haka?, duk don uwar gida aka yi...?"

"Dalla shut up Ahmad, maganar ce bana so, kana cika min kunne, zaka samun headache..., idan na sake jin Muryar ka sai na baka suspension, try me and see"
Ya fada da muryar sa dake nuna zahirin haka. Ahmad ya ɗaga hannaye sama alamun surrender sannan ya juya ya cigaba da kallon t.v sbd ya san ƙaramin aikin shi ne ya aikata abinda yace din, a iya wata ɗaya da ya fara aiki a Company ɗin su Mohan ya ba shi 3days suspension ya fi sau bakwai, kuma da aka zo biyan salary ba'a biya shi na ranakun suspension ɗin ba, shi yasa a yanzu yake kaffa kaffa kada harshen sa ya ƙara ja mishi .

Sai sa Mohan ya ƙara wasting kusan 10mins yana gyara agogo sannan ya gama shiryawa, izuwa yanzu ƙiris ya rage Ahmad ya fashe don haushi da takaici, ya dai ya danne ne.

"Shall we?" Inji Mohan yana gyara necktie din shi. Ahmad ya mishi banza ya tashi, ya wuce waje fuuu .

Mohan ya taɓe baki, sannan ya bi shi a baya.Mota daya suka shiga da Ahmad dayan kuma excurt din sa ne a ciki suka cilla baƙaƙen motocin sukan kwalta. Sai da suka fara halattan meeting kafin su kama hanyar Zaria.

*Zakiyyah*
Tun da ta daina ganin Mohan a online ta rasa natsuwan ta, ta kirashi ya ƙi a ƙirga amma baya ɗaga wayar ta, ta tura masa text bila'adadin amma baya duba ko ɗaya. A da ta ɗauka zata iya rayuwa babu shi, ta ɗauka rabuwa da Mohan abu ne mai sauƙi, ashe ba haka bane.

A baya in ta ga mace tana kuka a kan soyayya tsayawa take ta zageta tasss, ta riga ta yadda cewan babu namijin da ya isa ya sata hawaye, amma sai ga shi yanzu a kullum sai ta yi kuka a kan sa, tana son shi, tana son ta ji yaya yake, atunanin ta yana son ta, shi ma yana cikin matsanancin damuwa kaman yadda take ciki, kulawan da yake nuna mata a baya ta ɗauka so ne.

Haka suka zana jarabawan har suka yi hutu tana jinyar da bata ciwon jiki ba, jinyar zuciyar da soyayya ta riga ta yiwa illah, amma ta yi alkawarin cin nasara da addu'a da jajircewa ta hanyar ƙarfafa zuciyar ta. Zuwa yanzu ta fara karaya sosai take son cusa wa kan ta tsanar Mohan, tare da alkawartawa ran ta ba ita ba Mohan da ƙyar ta iya dakatar da kan ta wajen tura masa saƙonnin da har yau ya kasa buɗe ko guda ɗaya, koda shi ne autar Maza, ba zata kara texting nashi ba, kuma ko a hanya ta gan shi zata dauke kai,ya je yayi rayuwar sa yadda yake so ba tare da ta takura shi ba.

Wani ɓari na zuciyar ta na tabbatar mata da cewa wata ƙila ma mijin da aka aura mata alheri ne a gareta, tun da ta sanadin shi ta rabu da mutumin da ta yi shekara takwas tana dakon soyayyar sa a ran ta, wata ƙila watarana in ta gama karatun nata, ta tare a gidan sa za ta samu farin cikin da take hangowa a tarayyan ta da Mohan, wataƙila alherin auren sa ne yayi silar rabuwan su da Mohan, Dan tabbas Allah baya kuskure.

Ta yadda cewa ta yi kuskure na ƙin gaya masa cewan tana da aure , amma kuma wanene yake sama da kuskure?, Auren da ita kan ta bata ɗauke shi wani abu ba. A shekara takwas ɗin da suka yi tare ya kamata ya san halin ta, bata taɓa masa ƙarya ba, kuma ba komai take ɓoye masa ba ya kamata yayi mata uzuri.

Haka ta dawo Zaria da wannan ciwon, tana fatan Allah ya jiƙan ta, ya cire mata Mohan a ran ta gaba ɗaya. Tun da ta tashi ake ta faman girke girke a gidan, da alama wani gagarumin baƙo za'a yi, sai da ta yi shirin fita kasuwancin ta Daddy ya faɗa mata zata yi baƙo, mijin ta zai zo, da fari abin dariya ya bata, har sai da ta murmusa, wai miji. Bata ce masa komai ba ta shige ɗakin ta tayi kwalliya kaman da gaske, so take ta ga kalar mijin sannan ta tambaye shi me yasa ya ƙi ya sauwaƙe mata tunda baya buƙatar ta. Amma ganin har ƙarfe biyu bai zo ba, yana neman ɓata mata lokaci sai ta cire kayan, ta saka riga da wando ta fice wurin sana'ar ta..

Sanye take cikin wata fern green shirt mai faɗi, da Wide Leg jeans trouser me buɗaɗen ƙasa, kaman fella, ta nannade kafa daya iya gwiwarta ta manne shi da pin, hakan ya bayyana dogon baƙar safar da ke sanye a ƙafarta, cikin farar canvas ɗin ta mai kyau, kan ta sanye da wata fern green p cap, kunnuwanta rufe cikin ear phone.

Hannun ta na dama riƙe da kwando cike da soft drinks, ta rike wayar ta da hannunta na hagu, tafiya take tana ɗan rausaya jikin ta, da ka gan ta ka san waƙar da take ji na shigar ta sosai, kuma ba don komai take haka ba, tana haka ne don ta jawo hankalin mutane, su zo su sayi soft drink din ta, ,tafiya take yi tana amsa duk wani mai siyan kayan ta, wanda ya zageta kuma ta rama.

Bata kula kowa sai an kulata kawai kwana take sha tana ciniki abinta, har ta fito daga cikin tashar, ta tsaya a gefen titi duk wata mota da zata wuce sai ta tsayar da ita, wasu ta masu Hausa wasu ta caƙuɗa masu turanci kaman bata fahimtar turanci duk cikin salon cinikayya ne..

"Oga you wan buy?, Nutri milk dey, Pop cola dey, bottle water dey, which one you want?, You know say bottle water baya sa yawan fitsari, su siya kada ku ji fitsari a hanya, idan babu cash Ina ƙarban transfer, Ina siyar da data idan baku da data..."

Ta furta tana tsaye jikin wata mota, a tsakiyan titi, bata tsoron wani mota mai ganganci ya zo wucewa ta ɗayan side din ya kaɗeta, already ta riga ta saba.

"Lady....!, Bani mr v"

Wata murya ya dakatar da ita daga bayan ta, da sauri ta juya ta nufo motar da gudu.
"Yallaɓai guda nawa za'a baka?"

Ta furta daidai lokacin da take ƙoƙarin kwance catton ɗin ruwan. Ahmad ya ce
"Bamu guda uku...."

Mutumin da ke zaune a driver sit ya ja tsaki yace
"Ka siya naka kai kaɗai ni bana sh..."
Ƙasa ƙarasawa yayi, sanda ta ɗago fuskar ta, suka haɗa ido da shi.
"Problem...?."

Ta kira sunan shi lips din ta na shaking numfashin ta na neman ɗaukewa ganin yanda ya ƙara wani kyau da haske alaman yana cikin kwanciyar hankali.
Kallon juna suka shiga yi kirjinsu duka na bugawa da wani irin karfi.
Da ƙyar ta budi baki kenan zatayi masa magana, ya kawar da kan sa daga kallon ta, sannan ya fara ƙoƙarin jan motar da ya bar gurin, kaman daga sama ya ga ta tsaya gaban motar dole ya sa ya tsaya yana kallon ta ta cikin motan, yana jin zuciyar sa na masa nauyi. Ta zo gurin window ta tsaya idanun ta na ƙoƙarin kawo ƙwalla.

"Problem.. please ka saurare ni..."

Ta dauka ba zai yi magana ba, da mamakin ta sai ta ji ya ce
"2 minutes say what ever u want say and just leave".
Ya furta kaman dole, ko kallon ta bai yi ba, shi kan shi Ahmad kallon su yake da mamaki, ya kasa cewa komai.
Yanayin da yaYi magana yay mata ciwo sosai amma ta basar tana duban gefen fuskar sa da ya kawar, fuskarta a cakuɗe sosai

'' Problem bayan aure da na yi na taɓa maka laifi ne?, Me yasa ba zaka Duba wannan ba ka tausaya min ba? wa ya gaya maka na yi aure tukunna ma?"

Shiru yayi na dan wani lokaci yana sauraron kalaman ta wanda suka yi masa kama da rainin wayau, kansa ya ji ya fara tafasa ya ji ɓacin rai na taso masa tun daga ƙasan zuciyar sa. Cikin katseta a karsashe yace
"Wata ƙila baki fahimci wace irin alaƙa ce ta haɗa mu ba, social media friendship..., and now you're married, that friendship need to stop, kin gane? ..."

Wasu siraren hawaye suka gangaro mata, ta gyaɗa masa kai. Fuskar sa normal ya cigaba da cewa

"Bayan wannan kada ki sake tsammanin za ki sake samun wannan dama a rayuwata again and u will regret it"

A daskare take kallon bakinshi har ya kammala, jin wani irin mamaki ta yi ya rufeta, ji tay kamar a mafarki ne. Mohan ya buɗe bangon littafin rayuwanta yana ƙoƙarin rufewa. Dama hakan na faruwa?, Mutumin da ka yi sabo da shi shekara da shekaru, sai a wayi gari ya ce ya rabu da kai haka kawai?, hankalin sa a kwance kuma!.


Sosai take hawaye zuciyar ta na nauyi, murmushi ta sakar masa mai ciwo, da ya raunata masa zuciya fiye da komi, ya dafe sitiyari da niyyar barin wajen kafin sauran jarumtakan sa su tsiyaye.

Sosai take kuka kaman ran ta zai fita, bata san lokacin da ta riko wuyan riga sa ta dunkule shi da ƙarfi kaman zata masa duka ba, idanunta cike da hawaye yana zubowa fuskanta, jikin ta har rawa yake yi, me yasa ya kasa fahimtar ta? bai san wani matsayi yake da shi a zuciyar ta ba!, Me yasa zai yi mata haka?.
" Problem! Ka ma san ya nake ji kuwa? me yasa za ka yi min haka? ni fa mutum ce and you dare play with my feelings?, ina zaman zamana har na fara mantawa da kai ka dawo ka motsa min ciwon da na fara warkewa?, Haba mana ashe baka da imani? you are very heartless, ka je!, Ka tafi, Ka ci soyayyar "

Hannun sa ya sa ya ture nata dake wuyan sa, amma sai ta sake riƙe shi gamm hawayen ta na jiƙa shi, Cike da zafin rai yace
"Ya isa haka,..ki cika Ni, kina hauka ne? "

Ta kalle shi tana hadiyan bakin ciki
"Eh hauka nake yi, haukan son ka nake yi problem"
Ya ja tsaki ya girgiza kai sannan yace "cika ni nikam ko in take ki da mota... a haka zan so ki?, Ko bakida aure ba zan taɓa soyayya da ƴar tasha irin ki ba".

Tufff!, Ya ji ta tofe shi da yawu, Ya ɗago rinannun idanun sa ya kalleta ... Ta saki gaban rigan sa da ta kama.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login