Showing 9001 words to 12000 words out of 72389 words
maytarsa, jikin sa ya shiga tunasar da shi akwai abin da yayi sabo da shi a wannan ƙasa, taste da daɗin abin ya shiga dawo masa, yawun sa ya tsinke a take. Kan sa ya shiga sarawa ya dinga ji kaman idan bai samu ya shaƙi Cocaine ba zai iya mutuwa, kafin drivern da zai kai shi gida ya iso har ya sulale ya nufi wurin masu canjin kuɗi, ya basu dala suka bashi naira, daga nan ya hau abin hawa, ya nufi joint ɗin yan maye, ya miƙa masu kuɗi suka ba shi hoda. Washegari ma ya dawo, wannan karon kuɗin da ke hannunsa ba za su ishe shi ba, sai ya miƙa masu wayar sa, ya ce a siyar, a kwafe masa komai cikin memory sai a ba shi canji, wayar da a ƙalla zai kai dubu ɗari uku, ya siyar da ita a lalace aka ba shi 75k, ya siya cocaine na dubu hamsin, sigarin dubu biyar. Sannan ya dafe sauran dubu ashirin ɗin da zummar zai yi sadaka da shi, don yana so Allah ya dubi lamarin sa ya cire masa kwaɗayin shaye shaye har abada. Da isar sa gida sai ya raba dubu ashirin ɗin wa ma'aikatan gidan, suka karɓa da murna kowanne da kalar addu'an fatan alheri da yake bin sa da shi, zuciyar Mohan yayi fari ƙal, yana son addu'a, duk ƙanƙantar addu'a idan aka yi masa daɗi yake ji
Sai ya zamana kullum in zai fita, sai ya raba masu kuɗi, hakan sa suke ƙaunar sa, don ta kowane fuska halayyansa sun banbanta da na sauran ƴan uwan sa Ameen da Hassan.
Ameen da yake karatun sa a ƙasar Cyprus ma idan ya dawo ko hausa baya yi, kuma ba'a isa a masa hausa ba idan ya shigo gidan gaisuwar sa daban, ga aukin tara abokai su cika gida da hayaniya. Shi kuma Hassan halin auta gare shi, baya kwana a sashen sa, sai sashen hajiyar sa, shagwaɓa kaman jariri, sangartacce ne na fitan hankali, ga shi ba shi da mutunci, baya ganin kowa da gashi, duk abin da aka masa sai ya rama, Hajiyar sa da Alhaji su ne kaɗai mutane a nahiyar sa, wajen hajiyar sa komai yayi daidai ne, haka Alhaji baya ƙwaɓar sa. Gynecology ya karanta, yayin da Muhammad Ameen da Morhan suka karanci Business administration, da niyyar aiki a ma'aikatan mahaifinsu.
Mohan ya fara aiki a campanin mahaifin sa, a matsayin manaja, cikin ikon Allah kuwa har zuwa wannan lokacin babu wanda ya fahimci ɓoyayyen halin Mohan na shaye shaye, a sashen sa yake komai, babu mai shigowa ɓangaren sa, cikin ma'aikatan companyn Alhaji Naseer na Abuja akwai waɗan da suka fahimci yana shaye shaye saboda gane mai shaye shaye sai mai harkar, amma babu wanda yayi yunƙurin tunkarar Alhaji da maganar, wasu ganin haka suka yi a matsayin wata dama na cikar muradin su, suka fito masa a mutum har office ɗin sa suke kawo masa ƙwaya ya sha yayi tatul su sa shi ya sa masu hannu a wasu ayyukan da suka ci burin Alhaji ya sa masu hannu ya ƙi. A ranar da ya fahimci ɓarnar da suke sa shi yayi hankalin sa ya tashi, ran sa ya ɓaci, sai ya bi su da sack letter, hakan ba ƙaramin tunzura su yayi ba, suka nemi Alhaji, suka haska masa halin ɗan nasa, faɗin irin tashin hankalin da wannan ahali suka shiga a wannan lokaci ba abu ne mai sauƙi ba, karo na farko da ya ga hawaye a fuskar mahaifiyar sa, Alhaji Naseer ya tara ƴan uwan sa, ya gaya masu abin da Mohan ya aikata, gabaki ɗayan su suka haɗu suna caccakar sa da yi masa Allah wadai da ɓacin sunan da ya ja ma su, Alhaji Naseer ya yi masa hakan ne don ya nuna masa ɓacin ran sa, amma a wajen Mohan gani yayi kaman ahaifin sa ya fara tsanar sa.. hakan ya sa ya janye jikin sa daga Alhajin, ya fara tsoron haɗuwa da shi, nadaman abin da ya aikata ya lulluɓe shi, ya ɗau aniyar daina shaye shaye daga wannan lokacin.
Ya ɗauka dainawa abu ne mai sauƙi, bayan kwana uku sai ya koma jin matsanancin yanayin da ya baro a Egypt, yanayin da ya ji lokacin da ya daina shaye shaye, har ma fiye da da ma gabaki ɗaya ya bi ya firgice, ya fita a hayyacin sa fuskarsa ta yi busu busu, babu wanda ya san halin da yake ciki, kowa ya fita harkar sa, Alhaji ya hana shi zuwa wajen aiki, ya ƙarɓe wayoyin shi, da makullan motocin sa hakan ya sa ya shiga matsanancin yanayi mara misaltuwa.
Da kan shi ya sami Alhaji, ya ce a nema masa magani, a kai shi psychiatric su duba shi, yana gab da zaucewa, kan sa na ringing, idan ba'a nema masa magani ba zai haukace , amma Alhaji ya ce sai dai ya haukace, babu inda za'a kai shi. Morhan ya durƙushe a wajen hannayen sa dafe da kan shi, cikin magiya yake roƙon Alhaji.
"Abba.... Ji nake kaman zan haukace, ƙwaƙwalwana yana rawa.. ka taimake ni Abba"
Yayi maganar cikin rauni, idanunsa na nuna tsantsar gaskiyan kalamansa, tausayin sa da yake ƙoƙarin dannewa ya fito fili, duk lalacewan ɗanka naka ne, hankalin Alhaji ya tashi ganin yadda Mohan yake kuka, tausayin sa yake ji sosai har cikin ran sa, tuni ya yada makaman sa, ya rungumi ɗan sa, a karo na farko da ya ji ya damu da ya ji damuwan ɗan sa, ya ɗaga shi ya tafi da shi sashen sa, ya yi Sa'a ranar girkin Ummien sa ne, suka haɗu suna ba shi kulawa cike da tsantsar soyayya, tare suka kwana da Alhaji a ɗakin sa, ko a mafarki Mohan bai taɓa kawowa zai iya haɗa shinfiɗa da mahaifin sa ba, da daddare Mohan ya kasa bacci, sai farkawa yake yana surutai ga ƙaikayi ya addabi rayuwan sa, ya rasa ya zai yi da ran sa.
A ranan yadda suka ga rana haka haka suka ga dare, kaman yadda Alhaji bai samu baccin kirki ba, haka Ummie damuwan duniyan nan ya yi mata yawa, tana son ɗanta, bata so ta rasa shi, dama kawaici ne kawai da tsoron bakin jama'a, tana tsoro kada ta ja shi a jiki a ce tana goya masa baya ko a ce tana da hannu wajen lalacewan sa, ta yi kuka ta yi kuka sosai, kukan da ta dade batayi irin shi ba idonta ya kumbura sosai. Throughout daren ba su yi bacci ba, Abba ya kunna masa alƙur'ani, yana tofa masa addu'oi.
Washe gari aka garzaya da Mohan psychiatric, kan kace me?, Labari ya yaɗu a gari, *An kawo Malam Muhammad Sani wanda aka fi sani da MOHAN babban ɗan Alhaji Naseer Batta asibitin mahaukata saboda shaye shaye*...
A nan psychiatric kuwa bayan an duba shi aka masa allura, da magani, sannan aka ajiye shi a toxicology ward (Ɗakin da ake ajiye mutane masu irin matsalar sa), a nan ya fara ƙarɓar magani, nan ne ya haɗu da mutane kala kala wanda ƙaddara ta jefa su cikin wannan halin.
Kullum suna rufe a ward ana kawo masu lafiyayyen abinci, sai wanda suka zaɓa da fari Mohan ya ɗauka warkewa daga drug addiction yana da sauƙi, sai da ya kwana uku, ya ji kan sa na neman kwancewa kwaɗayi da urge na son shan ƙwaya ya hana shi sukuni, a lokacin wallahi ji yayi kaman ya mutu ko zai huta da azabar da ke addaban sa, kullum sai Alhaji ya zo, in banda kuka da surutai babu abin da yakeyi, treatment ake yi amma kaman ana daɗa manna masa ciwon hauka, kullum cikin rokon Alhaji yake a kan ya taimaka ya ce ma Nurses ɗin su ba shi abin da zai sha'ƙa, koda powder ne, su barbaɗa masa yaji, haka Alhaji Naseer zai yi ta rarrashin sa yana ji kaman ya yi masa kuka, sai ya fita yake samu yayi kukan shi hankalinsa a tashe, gabakiɗaya harkokin sa sun tsaya cak, hankalin sa ya koma ga samun lafiyan ɗan sa, fatan sa da burin sa Morhan ya samu lafiya, ya daina shaye shaye.
Watan sa ɗaya a toxicology, a lokacin ya ji sauƙi sosai, ya daina soshesohen da yake yi da sumbatu, sai aka tura shi rehabilitation, nan ya sake haɗuwa da mutane na daban waɗanda nasu ƙaddarar ya sha bambam da ta sa, kafin wata ukun da ake yi a rehabilitation ya cika, Mohan ya dawo cikakken mutum, aka sallame shi ya koma gida, farin ciki wajen Alhaji Naseer kaman zai yi me?, Nan ya maida ma shi muƙamin sa, ya cigaba da jan ragamar kamfanin sa na Abuja, har Allah ya nufe shi da samun sauyi zuwa babban branch ɗin su na Lagos. A Lagos ne ya sake haɗuwa da wata ƙaddarar...
Hmmm....!, Na san wasu za su yi tunanin cewa wata ƙila wannan shaye shayen yana da alaƙa da sihiri, wasu su ce akwai lauje cikin naɗi, Hhhhh.
Ga tambaya ga readers👇
Shin kin taɓa haɗuwa da ɗan shaye shaye?
Ya daina ko yana kan sha?
Idan ya daina ki tambaye shi kafin ya daina wane irin ƙalubale ya fuskanta.
Idan kuma bai daina ba ki tambaye shi sau nawa yake yunƙurin dainawa amma ya kasa dainawa.
*Addiction* guba ce 🖋️.
Na yi gabas🚶🏽♀️
Comment and share please 🥺 I take God beg you 🙏.
Bintou❤️
17th November.
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *004*
A Lagos ne ya sake haɗuwa da wata ƙaddarar.
*NIHAAL*
Sadiyyah Yusuf (Nihaal) pochy and classic rich Lagos girl ce, babban ma'aikaciya ce a companyn su, ko a wajen aikin mata ƴan uwan ta are seriously admiring her bare aje ga Mazan wajen da ke jin cewa Nihaal din ba sa'ar ƴan kasar bane sai dai ƴaƴan Oga irin su Mohan. Duk da dama baƙar fata ce, ya so ta kaman ran sa, sun yi soyayya ta gaskiya , ya hidmta mata kaman bawan ta, ita ma ta so shi kwatankwacin yadda ya so ta, sai da suka saki jiki da samun cikar muradin su, mahaifin ta yace ba zai ba ma ɗan ƙwaya auren ƴar sa ba, kuma yayi mata miji da ɗan yayan sa, ya kuma dakatar da Nihaal daga zuwa aiki, ya amshe wayarta duk don ya nisanta ta da Mohan. Sosai Morhan ya shiga damuwa, rayuwa ya daɗa maida shi shuru shuru, ya daɗa nesanta kan sa da jama'a duk wani abin da zai sa shi busy shi yake yi, damuwa ta yi masa yawan da ya fara exposing Cognitive impairement symptoms na depression wato yanayi ne da mutum tsinci kan shi a cikin ruɗewa da rikicewar tunani, mutum ba zai yanke wani decision ba a take ba, mutum ya zama a birkice, zuciyar sa da ƙwaƙwalwar sa su kasa natsuwa wajen yin cikakken nazari da tunani, ga yawaitan mantuwa jefi jefi. Barin garin yayi zuwa kano, ya zauna a gidan aminin mahaifinsa, Alhaji Madu, da kan sa ya nema magani a asibitin malam Aminu kano. Watannin sa biyu a kano yana ƙarɓan albashi, daga ƴan gidan su kuwa babu wanda ya damu da sanin inda ya shiga da dalilin tafiyar sa.
Hakan ya sa koda ya dawo ya daina magana da kowa, in yana gida sai dai ka gan shi a ɗakin shi a koda yaushe, yana games, ko kallon film, ko kuma karatun litattafai. Bayan rabuwan su da wata biyar Nihaal ta yi aure, a ranar ƙaramin hauka ne kawai bai yi ba, ya kasa bacci, yayi kuka, tun yana yi da hawaye har ya koma yin na zuci.
Mohan irin mutanen nan ne masu ɗaukan abin da suke so da muhimmanci, su kan ba shi mahimmanci fiye da kan su, hakan ya sa zuciyar su yake gaza ƙarɓan duk wani lamari da ya danganci na rasa su. Kwana biyu ko bacci baya iyawa, idan ya kwanta ma sai ya farka yayi ta tunani, hakan ya sa ya koma shan ƙwayoyi, idan ya ji damuwa don ya dinga manta komai....
Cikin ƙanƙanin lokaci ya koma ruwa, ya koma shaye shaye tuburan, har yanayin yanzu ya so ya zarce na baya. Yanzu a gaban kowa yake shan abin sa, ko a wajen aiki, babu ruwan sa da kowa, hakan ba ƙaramin taɓa daraja da ƙiman Alhaji Naseer yayi ba, har Allah Allah ake a ga Mohan yana shaye shaye, yanzu zaka ga hotunan sa a media da magazine, sau biyu Alhaji yana maida shi psychiatric burin shi ya ga Mohan ya daina shaye shaye, amma da an sallamo shi yake komawa. Malaman addini da na gargajiya babu wanda Alhaji Naseer bai gayyato ba a kan matsalar Morhan, wasu su ce jifa ne wasu su ce asiri aka yi mishi, wasu su ce aljannu ne, shi dai ya san babu abin da ke damun sa ƙaddara ce kawai, yana so ya daina, amma ko uni yayi bai sha ba ji yake kaman zai mutu. Athma ɗin shi yayi masa kamun kazar kuku, akwai sanda ciwon ya kwantar da shi har aka cire rai da sake samun rayuwar sa, yayi wata ɗaya a kwance baya iya gane wanda yake tsaye a kan shi ya sha wahala sosai, duk rashin imaninka idan ka gan shi a wannan lokacin sai ka yi masa ƙwalla, kullum sai Ummie ta yi kuka, ba ƙaramin tausayi sa take ji ba, ya rame yayi wani fari, bayan an sallamo shi Abba (Alhaji Nasir) ya tara iyalansa gaba ɗaya, ya ce Morhan yayi masa Alƙawarin ba zai sake shaye shaye ba, kan Mohan a ƙasa ya ce ba zai iya ba. Ran Alhaji ya ɓaci, ya dubi Ummie, ya ce ta umurce shi ta yadda zai fahimci abin da yake nufi, amma ba zai iya ba, addu'a kawai yake buƙata.
"Ummie... Bana so in yi miki ƙarya, ko na ce zan daina, ba zan iya ba, idan ban sha ba, sai in ji kaman zan mutu..."
Ya faɗa, fararen idanun sa na ƙwallin hawaye, Alhaji Naseer ya ce shi kenan tun da shaye shaye ya zaɓa, ya je ya cigaba da shaye shanyen shi, amma daga ranar babu ruwan shi da rayuwar sa ba zai sake aiki a companyn sa ba, sannan ya janye masa duk wani tallafi na kuɗi da ake ba shi duk wata, idan yana buƙatar abu sai dai ya tambaya amma ba za'a sake barin kuɗi a hannun sa ba, sannan idan zai fita ya zama dole ya nemi izini, in ya dawo ma ya shiga ɗakin Ummie ta shaida dawowarsa kafin ya wuce sashen sa. Alhaji yayi hakan ne don a tunanin shi idan ya janye masa tallafin kudi ba zai samu kuɗin da zai siya ƙwaya ba. sai dai abin da bai sani ba, babu abin da hakan ya dakatar, idan Morhan ya ji yana jin shan ƙwayoyi, zai san yadda aka yi ya samu kuɗi kota yaya ne sai ya siya, kadarorin sa yake ɗagawa ya siyar, ya narka a ƙwayoyi, cikin ƙanƙanin lokaci ya siyar da motocin sa, agogunan sa, wayoyin sa da systems ɗin sa. Babu mai fahimtar hakan don babu mai shiga sashen sa, kuma babu mai sa masa ido.........
Ganin tunaninsa na neman sa masa ciwon kai sai ya kwanta a rigingine yana furzar da iska daga bakin sa, duban agogon ɗakin sa yayi lokacin sallah yayi, miƙewa yayi, ya ɗauro alwala ya wuce masallaci, yana dawowa ya iske abincin sa a falon sa, haka ake masa kaman bare, da an kawo masa abinci ake direwa a falo a fice, kaman wani mai gadi.
Sai da ya sake yin wani wankan kafin ya yi shirin kwanciya, ya ɗauko wayar sa, ya kunna data, ya shiga Whatsapp, ya duba last seen ɗin ta 5 minutes ago, tana kusa kenan, ɗan murmushi yayi, yana jin natsuwa na shigar sa.
"Problem ɗina...."
Ya tsinci kan sa da typawa ya tura mata, murmushi ɗauke a fuskar sa.
Hassan kuwa ranar bai yi bacci ba sai da ya sa aka nemo masa gidan su Zakiyyah, ya kwana da ɗaukan alwashi kala kala a kan ta da iyayen ta. Sai yayi masu wulaƙancin da har abada ba za su taɓa mantawa da shi ba. Zakiyyah kuwa tuni ta manta da batun shi, don a yanda ta iya ture shi, ta masa rashin mutunci har tayi tafiyanta bai ce komai ba, bata tunanin akwai abin da zai yi mata. Don haka ta tattara batun shi ta watsa a kwandon shara.
****
Daga cikin wata haddadiyar falo da yasha kayan alatu na zamani, Hajiya Siddiƙa Mrs Ahmad Abdul Azeez Yabo ce ke zaune a kan wani katafaren royal cushion na falon, da tulin kayan ciye ciye a gaban ta ta dora kafa ɗaya kan ɗaya tana tsige banƙararren crunchy namar kaza ya ji suyan manya, gabaki ɗaya falon ya ɓige da ƙamshin masu kuɗi, sai tauna naman take uniquely tana yatsine fuska kaman ana mata dole.
jikinta sanye yake da wani kafirin yadi golden ɗinkin gown mara nauyi, tun daga sama har ƙasa gold stones ne sai walwali suke, fararen ƙafafun ta da babu takalmi ga wata siririyar sarƙan ƙafa da ya ƙara ƙawata ƙafar.
Yatsun hannunta sanye cikin zabbban gwalagwalai, ta jera su a yatsun ta kaman wacce zata taron ministocin kudaɗe na Afrika gabaki ɗaya. Hajiya Siddiƙa kenan ɗawisu uwar ado, tauraruwa mai haskawa a gidan Alhaji Ahmed Yabo, a ƙalla zata haura shekaru arba'in da shida amma da ka ganta sai ka yi tunanin she is in her early 20(s). Adon ta mai cike da aji da kississina su ne suka zame mata babban makamin da ya sace zuciyar gwarzon namiji irin Alhaji Ahmad Abdul Azeez yabo, take kuma juya shi yadda ta so.
Wayarta da ke gefen ta ya fara ruri, ta ja tsaki kafin ta aje juice ɗin hannunta ta daga wayar ganin Shalelen mijin ta ne ya saka tayi saurin rage catoon ɗin da take kallo, sannan ta kara wayar a kunne tana murmushi, ta narkar da murya a shagwaɓe.
“Baaaaby"
Ta faɗa kaman ƙaramar yarinya, daga ta can ɓangaren kuma Alhaji Abdul Azeez ji yayi notukan kan sa sun kwance lokaci guda, sai dai ya dake da faɗin.
"Angel ga mu nan a jaji mun kusa dawowa”
Siddiƙa ta sake narkar da murya kaman zata yi kuka.
"Baby I have missed you soo