Showing 24001 words to 27000 words out of 72389 words

Chapter 9 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4943

lumshe idanun ta, ta ɗago kai a karo na farko bayan shekaru kusan goma ta kalli fuskar sa...

Sakan ɗaya, biyu, sai ta yi saurin kauda idon ta jin zuciyarta yay skipping. Ya zauna gefen ta cikin wani irin rauni, ji yake kaman ya rungume ta, ya fashe da kuka, ko zai samu sassaucin abin da yake ji cikin zuciyarsa.

Sai dai raunin sa a zuciyarsa yake, a zahirinsa baka isa fahimtar hakan ba kai tsaye. A hankali ya ɗan kauda idanunsa da ke binta da kallo yana rissinar da kansa dai-dai tana zama a gefen ta. Ita kuma bata sake kallon inda yake zaune ba.. Sun ɗau tsawon minti biyar a hakan kafin ya motsa lips ɗinsa a hankali ya furta.
“Barka da yamma Ummie...."

Bata amsa ba, raunin sa ya ƙaru, bai damu ba ya cigaba da faɗin,
"Ummie.... An ɗaura min aure da Maryam..."




Not edited
1st December
Bintou🌹
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *009*

Shuru ta yi kaman bata ji shi ba, ya ɗago kai ya kalleta. Idanun ta a kan tv, tana kallon hiran da ake yi da Maheer a wani arabian channel.


Dattijuwar mace ce da kallo ɗaya zaka yi mata daga nesa zuciyar ka ta motsa saboda kwarjini da haibar ta, musamman in zaka ganta a lokacin da fuskar ta yake a murtuƙe ko kuma idan tana dariya, sai zuciyarka ta matse saboda waɗannan yanayi na matukar tasiri wajen fitar da kwarjinin ta. Hakan ke matuƙar tasiri wajen ƙara dasa tsoron mahaifiyar tasa a cikin zuciyar sa. Har gara Alhaji maza don shi yana sakin masa fuska lokaci zuwa lokaci. Ya matse hannayen sa a waje guda, yana jin bargon kaɗaici na lulluɓe shi, duk da haka bai sajuda ba, sai da ya sake magantuwa, yace.
"Ummi... Bana son ta, ki taimaka min, ki ce Abba ya haƙura, sai in bata tankardant...."

Sai ya kasa ƙarasawa, ba don an dakatar da shi ba, sai don nauyin da maganar ta yi mishi a yayin da yake furtata.
Shiru ya ratsa falon na wasu daƙiƙu, baka jin sautin komai sai muryoyin da ke fita daga talabijin din da ke kunne. Suna zaune har aka gama shirin, ta ksshe kallon kuma har a lokacin bata kalle shi ba, balle ta furta masa wata kalma, ta miƙe zata fita, shima ya miƙe yana mata magiya

"Ummie... Ko sau ɗaya, ki min magana, .. ko kalma ɗaya, don Allah.."

Chak ta tsaya, sai dai bata juyo ta kalle shi ba.
" Ummie zuciyata tana min nauyi... Don Allah ki yi min magana"

Muryar sa ta fito tare da dukkan raunin sa, nan ma shuru ta yi, ya kumshe idanun sa, wani yawu mai ɗaci ya zarce maƙogoron sa, ya kaɗa kai tare da nufar hanyar fita.

"Muhammad...."kaman daga sama, ya ji yo muryarta mai ɗauke da wata cikakkiyar dakiya ta kira shi, ya dawo da sauri, idanun sa na tara ƙwalla
Bakin shi na rawa ya amsa
"Na...na'am Ummiena"

Ya yi maganar yana ƙoƙarin riƙe hannayenta, ta janye tare da juyar da kan ta. Ta sake kiran sunan sa a karo na biyu, sannan cikakkiyar muryarta mai cike danjarumta ta fara amsakowwa cikin kunnen sa

"Muhammad....!,Babu wata dalili a rayuwar ka idan har ba za ka bi umurnin iyayen ka ba, Abbanka gata yayi maka, gatan da a yanzu ba za ka fahimci manufar sa ba... Ina so ka kyautata mata, koda a bayan idon mu, idan ka muzgunawa Maryam, ban yafe maka ba, ita ce rufin asirin ka har abada, kai namiji ne, kana da ilimi, ba sai na gaya maka ba, a yanzu nauyi ne a kan ka, haƙƙin ka ne ka kare mutuncin ta, ciyarwa, tufatarwa duk sun rataya a wuyan ka, ba alfarma nake nema a wajen ka ba umurni nake baka, ba don na isa da kai ba, sai don haifan ka da na yi ina so ka riketa amana, idan ka sa ta kuka ban yafe maka ba"

Ta ƙarashe muryarta na rawa, ta dafe zuciyarta da ke mata zafi, tana rintse idanu
"Na ɗauki ciwo na tsawon shekaru saboda kai Muhammad, idan ka kyautata mata ka biya ni da komai, ka tashi ka tafi, sannan ka yi wa mahaifin ka godiya, don gata yayi maka.."

Ya kasa gane me kalman Ummie na "Gata" yake nufi.

Har ya koma sashen sa maganganun Ummie basu daina masa amsakowwa a cikin kunnensa ba.

Ya zauna a falon sa yana ta danne dannen remote ya ma rasa wani channel zai kama tsabar bai saba zama haka idle yana kallon tv ba, so yake ya ji hayaniya ta ko ina ko zai samu sassaucin abin da yake ji a zuciyar sa.

Da ƙyar ya iya kamo tashar waƙa, ya ƙure volume, ya ɗauko giyarsa na Mendis coconut brandy mai uban tsada, tsabar tsadar sa ya sa ba kasafai yake sha ba, sai dai ya kan siya ya ajiye saboda irin wannan rana, yayi mixing ɗin shi da wani mara ƙarfi ya haɗa a glass, ya kurba ya kora baƙincikin auren da Abba ya ɗaura masa wanda ya cika masa kirji, sannan ya haɗa da taba ya kunna tsinke ɗaya, ya saka a bakin sa ya fara zuka yana fesar da hayakin shi a hankli.

Rabon sa da ya sha tabar ya jima, ya fi ganewa Alcohol da cocaine.Kan kace me? wajen ya kaure da hayaki, sai da ya karar da sigari kara uku kafin ya ji sauƙin abin da ke damun sa. Ya buɗe ƙofar sa don warin sigarin ya fita, sannan ya haye ɗakin sa hannun sa riƙe da glass din fitar, sai da yayi wanka, sannan ya kwanta a rigingine yana tunanin yadda rayuwa ke buɗe masa file na sabon jarabawa a kowane lokaci. Wayar sa da ke bedside yayi ƙara alaman shigowar saƙo, ya kai duban sa ga wayar, sunan ta da ya ga yana yawo a fuskar wayar ya sa ya miƙa hannu ya ɗauka.
"Solver ka san wani abu?"
Kan sa ya ɗan sara kaɗan, ya rintse idanun sa da ƙarfi, yana jin jiri na ɗeban sa.

"A'a sai kin faɗa, problem"

Shuuru ne ya biyo baya, ya duba wayar har yana tunanin ko ta sauka a online.

"Meke damunka problem?"

Bai yi mamakin yadda aka yi ta san yana cikin damuwa ba, saboda duk yadda ya kai ga ɓoye damuwar sa ko rashin lafiya, suna fara chatting take ganewa, tun yana mamaki har ya daina. Ya lula cikin damuwa, wayar da ta ƙara ƙara alamar shigowar wani saƙon .

"Ka ƙara shan abin ko?"

"Kaɗan na sha"

"Me yasa ka sha?, Make damun ka"

Ya had'iye yawu a hankali cikin mak'ogwaronsa, lokaci guda ƙwaƙwalwar sa ta tuna masa abin da baya don tunawa... Wai shi ango ne

Guntun tsaki ya ja kafin ya maida mata da martani.
"Abban mu ya ɗaura min aure da wata yarinya.... "

Maimakon ta yi masa reply, sai ta kira shi video call.

"Problem me kake nufi?, Ban gane rubutun ka ba"

Ta furta bayan bayyanar fuskar sa a jikin screen ɗin. Yayi sipping alcohol ɗin sa, idanun sa yayi jazur.

"Abba na ya ɗaura min aure da wata yarinya”
Ya furta da wani irin rauni, raunin da ita kaɗai take iya tsintar hakan a muryar sa. Ta yi shuru tana kallon sa, a buge yake amma tana iya hango gaskiyar maganar a ƙwayar idanun sa.

"Yarinyar ta shigg...go, ɗakina... Sai ..."

Cikin muryar sa irin ta masu maye ya bata labarin duk abin da ya faru, ciki har da abin da Ummie ta faɗa, ya ƙara da cewa
"Ummie tana so i MMM....mutu kafin lokaci na, bata ƙaunata, ssss...so take in yi abin da ba zan iii iya ba"

Cike da ƙarfin hali Zakiyyah ta ce
"Problem umurnin ummien ne kake gani kaman takurawa?, Har kake cewa ta takura maka?"

Yace
"Eh, solver.... Bata so na fa

Ta ja numfashi da taɓe baki
"Hmmm... Ba wai na katseka bane Problem amma ka saurareni da kyau ka ji abin da zan gaya maka"
Ta yi magana sounding so serious, ya tattaro iya natsuwar da yake da shi a wannan lokacin, ya maida hankalin sa a kan ta.
"Problem, lokacin da za ka yi rakiya zuwa inda aka binne mahaifiyar ka, a lokacin zaka gane rayuwar ka ta baya da ta yanzu ta samu canjin zahiri, ba na ɓoye ba, daga wannan lokaci za ka shiga sabon rayuwar da a yanda kake bakada ƙarfi, komai zai iya samun ka, a yanzu kana ganin iyayenka kana gani kaman su ke janye maka ƙarfin ka ko?hmm, ba za ka gane su ne ƙarfin ka ba sai ka rasa su, kar ka ɗau wannan wasa, duk wanda ya rasa mahaifiyar sa yana buƙatar kulawa ta musamman, irin kulawan da kake gani kaman an takura maka, domin a lokacin ka rasa mace ɗaya da take buƙatar ganin ka je inda bata taɓa zuwa ba a rayuwa, ka rasa wannan macen da take maka adduoin nasara a duk inda take, a zaune ko a kwance, cikin sallah da koyaushe, ka rasa macen da ke da yaƙini da yarda a kan ka sama da yadda ka yarda da kan ka, ka rasa macen da zata iya sadaukar da abin da ta fi komai so domin murmushin ka, ka rasa macen da ita kaɗai ce ba zata gujeka ba koda ka fi haka lalacewa, koda ka zama ɗan iska ne, amma a ganin ka idan ka rasata ka huta da shareka da takurawan da take maka, ka huta da gyara da matsa maka a kan inganta rayuwar ka, ka huta da bibiya da sanya idanu a rayuwar ka, ka huta da bin umurnin da kake yi a baya koda kuwa zuciyar ka bata so, amma ka sani waɗannnan abubuwa su ne suka fi komai daraja a rayuwar ka, a hankali zaka fara gane cewa ita ce dalilin da ya sa kak samune cigaba a rayuwar ka, ba jimawa za ka fahimci waɗanda da kake da alfarma a wajen su, domin ita suke maka wannan alfarmar , ba sai an ɗau lokaci ba, da kan ka za ka gane cewa addu'ointa su ne suke haska maka hanya, da a ce baka da jajirtacciyar uwar da ke maka addu'a a bayan idon ka, ka san cewa illar da shaye shaye zai yi maka sai ya fi wanda yayi maka a yanzu, ka godewa Allah shaye shaye bai taɓa sa ka kusanci zina ba, bai taɓa saka ka kwana a inda baka sani ba, mota bata taɓa bi ta kan ka a kan shaye shaye ba, halayyanka nagartattu suna tare da kai, sai ka rasa mahaifiyarka tukunna za ka gane cewa ita ce bangon da ta tsaya maka, kuma da adduan ta Allah ke kare ka, ina mai tabbatar maka tana ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Allah ke ɗaga maka ƙafa a al'amuranka, amma tun da gani kake kaman tana takura maka shi kenan, idan ka rasa ta yanzu lokaci ne da za ka rayu kai kaɗai babu waɗannan abubuwan, yanzu lokaci ne da idonka zai gane maka yadda duniyar nan take da girma, ba wai batun abinci ko kulawan da take baka bane, ko kaɗan wanda ya rasa uwa shi ne kaɗai ya san yadda yanayin yake, problem koda baka son Maryam ka danne zuciyar ka, ka bata kulawan da ya dace, ga inda za ka samu aljanna a sauƙaƙe?, solver wannan dama ce da zaka wanke kan ka daga baƙin fentin da suke kallon ka da shi, har yanzu dama bata wuce maka ba tun da suna tare gareka, ka yi wa iyayenka biyayya ka kyautata masu, Allah ba zai bar ka haka ba, za ka ji mamakin nasarar ka a rayuwa''



A hankali ya ji hawaye na sauka akan kumtunsa, masu ɗumi da yawan da yaji kamar an buɗe bakin famfo, kukan da bai yi ba tun a ɗazu shi ya taho a yanzu, kewan mahaifan sa da ƙaunarta ya ji ya taho from no where ya lulluɓe shi. Zakiyyah na ganin hakan ta katse wayar.

kuka yake yi mai sauti, sanin cewa babu kowa a tare da shi daga shi sai ƙamshin turaren mahaifiyar sa da ke manne da jikin shi tun bayan dawowan shi, ya manta komai ya ajiye dukkan wata dauriyarsa a gefe ya manta waye sh, ya kuma manta shekarunsa da rabon sa da yin kuka, ya tuna cewa yana da gata, baya buƙatar shan komai a irin wannan lokacin, yana buƙatar ya ji ɗumin mahaifiyar sa, amma ko karen hauka ne ya cije shi ya san ba zai kwatanta tunkarar ta da hakan ba, don kuwa babu shakka da kumburarren fuska zai dawo, kuka yake da babu sauti sai wani irin girgizawa da jikinsa yake har yana barazanar motsa gadon yayin da hawaye masu ɗumi ke jika bedsheet din....

***

*Zakiyyah*

Maganar da tayi masa cike da dauriya, don hatta hannunta rawa yake, wani abu ya danne zuciyar ta. Ganin hawayen sa ba ƙaramin tayar da hankalin ta yayi ba, ta faɗa kan gado tana jin zuciyar ta kaman ana soyawa a garwashin mai tsire. Zuciyarta ke tsananin suya amma ko kadan idanun ta sun ƙi fitar da ƙwalla tsabar taurin zuciya. Ta kasa tsaye ta kasa zaune sai kai kawo take yi a ɗakin. Ta so shi tun bata san ma'anar soyayya ba, ta so shi tun bata mallaki hankalin da zai tantance menene so ba, ta ba shi kulawan da ya kamata a ce ya fahimci irin son da take masa. Duk soyayyar da take masa bata taɓa furta masa ba duk da kasancewar bata taɓa ganin shi a zahiri ba, amma tana da tabbacin ko ƴan uwan sa na jini ba za su gaya mata halayen da ba, ta amince da soyayyar Ibrahim ne don ta tunzura zuciyarsa ya faɗa mata yana son ta, amma kaman bai san tana yi ba.

Ta dunƙule hannun ta, ta kaiwa ƙofa naushi tana haki
"Problem.... wallahi sai ka aure Ni, Koda matan ka biyu, zan zama ta uku, idan mata uku aka aura maka zan zama ta hudu, koda matan ka huɗu sai ka saki ɗaya ka aure ni, dan na rantse da Allah Wallahi tallahi sai ta aure ni"

Ta faɗa cikin haki, zuciyar ta na zafi kaman ana hura garwashi.
Kowa yana da mafarkin sa wanda yake so ya cimma wata rana, sai dai ita nata mafarkin ƙalilan ne, so take ta rayu da wanda take so, so take ta gan ta cikin wadatan zuci, ƙawaye ɗaya zuwa biyu sun isheta rayuwa, bata buƙatar abokan shawara don zuciyarta na da ƙarancin yadda, a darasin da rayuwa ta koyar da ita, rayuwan ta ita ƙaɗai ya fi mata kwanciyar hankali. Burin ta ta samu farin ciki ta ƙare rayuwar ta tare da Muhammad Mohan.

Wannan daddaɗen mafarki ne da take fatan cimmawa wata rana.

Wani littafi ta ɗauko da biro, ta fara rubutu kaman yadda ta saba idan tana cikin damuwa, bata da wanda zata gayawa kukan ta, saboda bata yadda da kowa ba, shi yasa ta ƙulla abota da littafanta da takardu, a nan take bayyana duk wani abin da ya ke damun ta.

"Na kamu da soyayyarka tamkar hatsari, na zaɓarwa kai na zan buɗe maka zuciyata, na zaɓi na baka lokacina, da soyayyata, na so a ce ka gane irin son da nake maka, da ka daina wahalar da zuciyata, ina maka son mara adadi... Don Allah problem ka fahimci abin da nake nufi, ka ce kana so na"

Tana kaiwa nan zuciyarta ta ɗan yi rawa, hawaye suka taru a idanun ta, ta yi saurin maida su tana ƙirƙiro murmushi.
"Comon... No crying over men"

A ranar da ƙyar ɓarawo ya iya sace su su biyun, sai da safe duk suka rama baccin da basu yi ba daren jiya.

***

Washe gari bayan idar da sallan subh Abba ya jero tare da yan'uwansa suna tafiya suna tattaunawa a kan auren.

“Mahaifin ta yayi dabara ni ma na jidadin haka, ka ga mun tsallake ma duk wani nauyi a yanzu"

A'haji Nasr ya ce
"Shi kan shi Muhammad ɗin, sau biyu ina nema masa aure wajen abokaina amma saboda shaye shayen da yake yi maganar bata kaiwa ko ina mu kuma mun biye masa mun zuba masa idanu kaman shi ya haife mu, amman yanzu ka ga wannan duk ya kau a yanzu”

“Gaskiya haka ya fi, ka ga an huta, in an dace ma sai ta sauya shii”

“Daman ai sauyi ya zama dole, mu basu wata ɗaya”
Cewar Malam Umar, Alhaji yace

“Wannan gaskiya ne”

4th December
Not edited
Bintou🌹

Nayi gabas.....
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *010*

A sashen Halima suka karya, sannan ya sa aka kira Mohan wanda a jiya ya kwana da matsanancin ciwon kai saboda kukan da sha. Abba ya mika masa wata ɗinkakkiyar blue shadda, yace ya je ya saka, bayan ya saka Abba da kan shi ya saka masa hulla, ya feshe shi da turare, farin cikin fuskar Abba ya gaza ɓoyuwa.

Muhammad Sani Naseer Batta (Mohan) ya fito a sak angon shi, kyakkwa fari ne mai dogon hanci da fuskar uwarsa ta asalin Arab na ƙasad khindaar ya ɗauko..

Sai dai kuma da akwai wannan kamannin da kuma zubi na jinin tsatson su na cikakken bafulatanin khindar musamman a yanayin giran idon sa, da sajen sa da kuma tsayayyen siffar jikinsa har da yanayins a mai tsananin burgewa, yana da cikakken saje da dan matsakaicin gashin gemu baƙin ƙirin da kuma fasalin kamala ta kyawawan maza masu kula da lafiyar su ta hanyar gym, sam ba shi da ƙiba ko kaɗan, saboda gaba ɗaya shaye shaye ya tsotse shi, in ka gan shi ba za ka ce ya haura shekara ashirin da hudu ba, bayan a zahiri shekarun sa talatin da biyar zuwa shida.

Yanda ya ga farin ciki a fuskar mahaifin nasa, kawai sai ya tsinci kan sa da shiga cikin matsanancin farin ciki, irin wanda ya manta rabon da ya ji irin shi, ba farin cikin auren da aka ɗaura masa ba, farin cikin murnar da ya gani a fuska mahaifin sa, hawaye suka taru masa a idanu, kawai sai ya rungume Abban nasa yana wani irin kuka mai taɓa zuciya.

Lallai Zakiyyah ta yi gaskiya da ta ce shi ɗan gata ne, yana da gata tun da iyayen sa suna raye, suna farin ciki da duk wani abinda zai sama masa cigaba a rayuwa tabbas wanda ya samu soyayyar iyaye ya more. Tunanin sa ya harba can wani lokaci da ya shuɗe, lokacin da take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login