Showing 45001 words to 48000 words out of 72389 words
shaida ta wannan lambar *09125491597*
Haka zalika zaka iya biya a matsayin katin MTN a wannan lambar *07046627683*
MOHAN IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF ADDICTION INTO AFFECTION.
KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA*
FIRST 30 SUBSCRIBERS WILL BE GOING FOR #300
Pay
*VIA 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*
EVIDENCE TO *09125491597*
YOU CAN SEND MTN CARD SEND To *07046627683*
Be the first subscriber ❤️
NB _Part one is free_
©BINTOU.
Na yi gabas 🚶🏽♀️.
15th December.
*017*
Da wata irin kasala ta farka da Asuba sakamakon damuwa da ta sa wa ran ta, jiya bata sha ice cream ɗin ba har Muhajir ya tafi, kuma ko girkin dare bata yi ba, haka ta kwana da damuwa. Ita kaɗai ta san yadda take ji a ran ta. Buta ta ɗauka ta ɗibi ruwa a roban ruwan su ta je ta yi alwala, ta yi sallah sannan ta tashi sauran ƴan ɗakin, suna idar da sallah aka tasa hira, bacci take so ta koma amma surutan su ya hanata, Ta kalli Mrs Morh dake masifar da babu dalili hira suke a kan wata sabuwar ƴar ɗakin su wacce bata cika kwana a ɗaki ba. A da su ashirin ne a ɗakin, common room ɗin hostel aka ba su saboda shekarar da suka shigo makarantar an ɗebi ɗalibai da yawa, har ya kasance allocation yayi ƙaranci, shi yasa aka yi sacrificing common room aka mai da masu shi ɗaki.
Ƴan ajin su goma sha biyar ne a ɗakin sannan ƴan nursing su biyar, sakamakon weeding ɗin da aka yi an kori ƴan nursing biyu, da ƴar ajin su guda ɗaya. Hakan ya sa suka samu space ɗin mutum huɗu, lokacin da aka yi weeding Zee Cindo bata hostel, sai bayan da aka yi weeding ta dawo space empty space ɗin common room da zama, ita ma midwifery take karanta.
Kaf hostel ɗin nan babu wanda bai san Zee ba, ƴar gayu ce kuma ƴar masu kudi, da fari babu wanda bai yi mamakin dawowan ta a hostel ba, a hostel ɗin ma a common room, inda aka ba marasa galihu ta bakin su Deeje. Amma wata ƙila ta dawo hostel ne don ta burge su, but wait...! Waye su da za ta yi abu don ta burge su?🤔.
Yarinyar ta gaya masu cewa baban ta minister ne, maman ta ba ƴar Nigeria bace, duk sun yadda da ita saboda tana kama da turawa a kyan fuska, idanuwanta da kuma gashin kanta sune suke kama da na turawan, idan za ka iya saka ta a jerin mutanen nigeria, sai dai a danganta ta da jinin shuwa arab, ko fulanin Maiduguri. Amma kana ganin ta zaka san ba haihuwar ghetto bace, skin care products ɗin ta da ire-iren kayan da take sawa, da desiners perfumes ma abin kallo ne, she get cash, she get car she get driver, ƙwaɗayayyun ƴan ɗakin enjoyment wan kill them, sosai take masu ɓarin naira wasun su ma maimakon a ce sun kawo provisions daga gida, sai dai su kai gida iyayen su yi ta masu godiya, ko restaurant Zee ta je sai ta biyawa kowa, hmmm wai hausawa suka ce abin faɗa na baki ne, ko a aji ma in za su yi presentation ita take biyawa kowa, hakan ba ƙaramin kankaro mata mutunci yayi ba, ba students ƙaɗai ba, lecturori ma ganin girman ta suke, wasu kuma neman ta suke amma bata taɓa bada fuska ba, a iya watannin da suka yi a makarantar, da a ce za'a ce su ƙirga iya Zafafan samarin da Zee ta yi soyayya da su zai fi a ce aikin tsintan wake aka baka, rabuwa da samari ba komai bane a wajen ta, kuma a haka ba kowa take kulawa ba, sai ka kai matsayin da take so, wato idan uban ka na da kuɗi, dalilin da ya sa take yawan rabuwa da saurayi kuwa ta kan ce idan mutum ba zai iya kula da ita yadda mahaifinsa yake kula da ita ba to bata ga amfanin Kasancewanta tare da shi ba.
Labari suke a kan yadda ta wulaƙanta wani malamin su wanda kowa ke shakkar sa a makarantar, a gaban kowa saboda ya ce yana son ta, daga nan aka shiga gulma ka'in da na'in.
"Ni fa yarinyar nan ban yadda da ita ba, ko kun lura Zee tana da ƙoƙari da maida hankali a kan karatu?, Ni ban taɓa ganin inda ƴaƴan masu kudi suke maida hankali wajen karatu ba, aradu kafin ku samu ƴaƴan ɗan mai kudin da yake da ƙoƙari... Na connection, ƴaƴan masu kudi sam basu da ƙoƙari, saboda basu damu da karatun ba, suna zuwa makaranta ne for the certificate "
Mrs Moh ta faɗa, Zulfah Isah ta amshe da faɗin
"To su da ake masu komai me za su yi da wani karatu, mu dai ƴaƴan malam Shehu mu da bamu da wata mafita mu ne karatu ya zame mana dole, in ba haka ba uban mu za mu ci"
Mrs morh ta ce
"Ah to, shi yasa na ce ban yadda da yarinyar ba, ku da kuke da kudi why Are you intelligent like this?, like me za ki yi da karatu?, wallahi Idan kun ga yanda Zee take karatu sai abin ya baka tsoro, ita da ta ce babanta ministar ne, yana da kudi kaman ruwa me yasa take karatu haka?, ta bar mana karatu mu ƴaƴan malam Shehu, mu yi saboda bamu da wani mafita bayan shi".
Safiyyah jibril tace
"A'a kar ku ga laifin ta, kun san karatun mu na nan ba kaman sauran karatuttuka bane, idan bata yi karatu ba a ina za ta samu experience?, Koda ta samu certificate ɗin da take nema zata ji kunya a ce bata iya komai ba, because she can't go and be killing people's children"
Khadija ta taɓe baki tace
"To idan mutum kaman Zee ta yi karatu haka mu a su waye da ba za mu yi karatu ba?, Person wey dey command lecturers , her papa na minister, she get cash, she get car and driver, we wey one wheel barrow wey get one driver our papa no get who we be wey we no go read?, Kun ga kuwa in dai karatu muka zo yi a makaranta dole mu dage, don iyayen mu su yi alfahari da mu"
Duk hiran nan da suke yi fa kowacccen su na cikin bunk, babu mai ganin wani, an kunna gas an ɗaura ruwa, ruwan da tuni na kowacce ya fara tausa, amma tsabar gulma babu wacce ta yi yunkurin tashi a kashe gas ɗin.
Zakiyyah ta ja guntun tsaki, ita duk maganar da bata shafe ta ba bata l tsoma bakin ta a ciki, duk maganar da za ka yi in har baka sakota a zancen ba, ba zata tanka ba, haka take, shi yasa bata da abokin faɗa a ɗakin, in ta yi cacar baki da wata to Khadijah ce, kuma dama sun saba, kusan kullum sai sun raba hali, don Khadijah akwai tsokana da son sai an kulata ko ba'a so.
Fita ta yi ta ɗau bokiti, Khadijah ta ɗaura ruwan wanka amma tsabar gulma har ruwan ya fara tausa bata sani ba, kashe gas ɗin ta yi, Shuuu ta juye ruwan zafin a bokitin ta. Karaf suka haɗa ido da Khadijah da ke saman gadon ta a up bunk.
"Kan uba!, Ruwan nawa za ki juye?"
Towel ta ɗauka, kafin ta sauko ta fice wanka da Ruwan tana dariya, a kan ruwan zafin da ta juye sai da suka kusa tada block B da masifa, dan Zakiyyah cewa ta yi ba zata ɗebo wani ba, ita kuma Khadijah ta dage sai ta biyata ruwan ta, daga ƙarshe room mate ɗin su ƴar Nursing Zainab tanko ce ta raba faɗan, ta ɗorawa Khadijah wani ruwan a gas ɗin ta.
Takwas saura suka fita class bayan sun karya, suka jero a tare, babu abin da Khadijah ke yi sai aikawa Zakiyyah harara, ta kauda kai kaman bata san tana yi ba, ita ba ta kan ta take yi ba damuwar ta kaɗai ma ya ishe ta.
A ajin ma bata da wani kuzari, har lecturer ya fita bata fahimci komai ba, ita ba tunani take yi ba, kuma ba zata ce ga abin da ya hanata fucusing ba, jikin ta dai a sanyaye yake, kuma babu abin da take so da bege sama da ta ji muryar problem, tun da Ibrahim ya sanar da ita yana kaduna take jin kan ta a wani yanayi, yanayin da ke matuƙar buƙatar kusanci da shi, sai sai jin kan ta da jan aji sun hana ta nemi Ibrahim ya kai ta asibitin ta gan shi.
Malamin na fita ajin ya ƙara kaurewa da hayaniya, bata son hayaniya ko kaɗan idan surutu ya fiye yawa a waje hankalin ta tashi yake, ganin zaman ajin ba zai yiwu ba sai ta ƙarɓi key ɗakin su ta koma hostel, ta cire fararen uniform ɗin ta, ta ninke, ta kwanta tana jin zuciyar ta na nauyi, kaman ta fashe ko zata ji sauƙin abin da ke damun ta. Ta kunna data ta hau Whatsapp, ta fara dudduba status, har da na Ibrahim wanda bai daɗe da ɗorawa ba, tana ganin status ɗin ya kirata video call. Sai da ya kusa yankewa sannan ta ɗaga bayan ta rufe jikinta da bargo dan daga ita sai vest ko ɗankwali babu a kan ta.
"Babe... Ina hulan ki?"
Ya faɗa yana duban fuskar ta. Ta ɓata fuska
"Yanzu da a ce ka kira ni ban ɗauka ba zaka ce na yi lefi ko?...."
"Allah ya baki haƙuri, a taimaka a rufe kan nan don Allah"
Sai da ta harare shi, sannan ta miƙa hannu ta ɗauko farin hulan uniform din ta mai blue line guda ɗaya ta saka tana murnushi.
"Yawwa to ko ke fa, yau ba lecture ne?"
Ta dan yi shiru kaman mai gajeren tunani kafin ta girgiza kanta.
"Akwai... Bai shigo ba tukunna."
Sai ya gyaɗa kan sa, ta hango yanda Adam's apple ɗin sa suka motsa kafin hannunsa ya miƙa a hankali zuwa fuskarta ta jikin wayar, kunya ya ɗan kamata, ta kauda kai tana murmushi, hulan kan ta ya ƙara zamewa.
"Kina da sanyayyan kyau wanda ba kowa yake iya gani ba..."
Muryarsa ta fito kaman mai jin bacci yatsar sa na yawo a jikin screen ɗin wayar sa, sai ta ji kaman fatarta yake taɓawa.
Zakiyyah ta haɗiye wani yawu da ya tokare a maƙogwaronta, sannan ta aro wani juriya don gabaki ɗaya muryar sa ta saukar mata da wani irin kasala, a sanyaye tace...
"Ehn... Uhm... Babe, za ka iya zuwa yanzu"
Ya ɗaga kansa har a lokacin bai daina taɓa screen din shi ba. Cikin muryan sa mai taushi ya ce
"Yes, kina so in zo ne?."
Ta ɗaga kai
"Ina so ka kai ni asibiti...."
Sai ta yi shuru, ta kasa ƙarasawa
"Za ki je gaida problem ne?"
Ta ɗaga kai, ya sasssauto da muryansa kasa kasa yana dariya yace
"Yau dai problem za ta ga solver ɗin ta, gani nan zuwa".
Kitt ta kashe wayar, ta dafe ƙirjin ta da ke bugawa da sauri, wani baƙon yanayi ne ya so shigan ta a lokacin da suke waya, a wannan lokacin tabbas da tana ɗauke da irin ciwon zuciya, babu abinda zai hana zuciyarta bugawa a wajen, don jin muryar sa take kamar saukan nakiya, ga touching screen ɗin da yake yi, ya haɗa mata biyu. Ta rasa me ya kawo wannan yanayi.
**
Sai ya yi wanka ya dauki wanka sannan ya nufo makarantar nasu .
Cikin minti ashirin ta gama shiri, ta fito ta same shi a inda ya faka motar sa. Tun daga nesa yake kallon ta, zuciyar sa yayi skipping beat na wasu sakanni. Yanda take takun ta with confidence, fuskar ta kaman kullum babu annuri ko kaɗan acikin ta.
She's fucking classy, ta haɗe cikin tsadadden golden yellow oily material na Abaya irin na matan shuwa arab na maiduguri, da sallan da ya wuce ta siya, sawan ta ɗaya, ta yane kan ta da ƙaramin baƙin mayafi, hannun ta sanye da siririyar bakar agogo mai kyau da tsada.
Shigar ta dace da yanayin jikin ta, ko ina fresh ne ajikin ta barin ma hannun ta sai ka rantse ba ita ce yarinyar da ke tallan pure water da lemu a tasha ba, sosai take ware kuɗi na musamman ta gyara fatan ta, amma bata cika son sa kaya ba, shi kan shi Ibrahim tun da ya san ta bai taɓa ganin ta yi kwalliya irin na yau ba, duk in ya zo wurin ta shigan da take yi guda ɗaya ne, wato shigan riga da wando kaman wata tomboy.
A cikin nitsuwa take latsa wayarta alaman bata ma san wata hira ta haɗa su.
Jin motar ta dauki shiru sosai ya sa shi miƙa hannunshi nadama ya kunna aux din motar yasa waƙar *monalisa* na Christ brown.
Ahankali waƙar ke tashi acikin motar in a very emotional mode. a hankali yake bin waqar yana jan ta da hira tana amsa shi sama sama har suka isa asibitin
*Federal Neuro psychiatric barnawa kaduna*
_Toxicology ward_
Yana zaune yana danna counter Maryam ta shigo dakin dauke da tray.
Kallo daya tayi mashi ta dauke kai don sosai take kunyar kallon shi, babu kayan kirki a jikinshi, daga shi sai singlet da 3 quarter, ba shi kaɗai ba kusan duk ƴan ɗakin haka suke zaune, ita da don nata ne da ta ce ya maida jallabiyar shi.
Ajiye tray din ta yi a gefen Bedside table ta buɗe drawer ɗin ta ɗauko toothbrush ta matsa toothpaste sannan ta ba shi. Ya yi murmushi sannan ya ƙarba ya ce
"Na gode Amarya"
Ya mike ya bar ta a wurin, ya je ya wanke bakin ya dawo. Bubbude plates ɗin abincin da ta ƙarbo masa take tana yatsine fuska, faten wake ne da kifi.
"In Banda ƙaddara me zai sa ka ci wannan abincin?"
Bai ce komai ba, ya kai idanun sa kan tray ɗin da ta ajiye, da mammaki yake kallon kayan, tea ne a flask sai Irish , kwai da kifin gwangwami, gwanin kyau sai ƙamshi suke
"Ina kika ƙarbo wannan?"
Ta ce "Ni na zo da shi"
"Amma Basu san kin kawo min abinci ba"
Ya tambaya a hankali da ɗan guntun murmushi a gefen leɓɓensa yayin da idanunsa ke kallon kayan jikinta daga ita sai wata material da bai rufe komai a shape din jikin ta ba. Sannan bata yin kitso ma, ta fito da gashin ta da ya sha gyara kaman ba matar aure ba. Ya kau da kan sa, murmushin fuskar sa na gushewa, shi dai ya ga ta kan sa☹️.
Kakkauran tea ta hada masa sannan ta zuba masa Irish din a plate ta zuba kifin a gefe, Shi dai kallon ta yake, yana mamakin ƙarfin hali da rawan kan ta.
Jiya ta biyo shi garin, ta kama hotel a barnawa, ta ce tunda ba'a bari a kwana ita zata rinƙa kawo masa ziyara kullum tana kula da shi har a sallame shi.
Zama ta yi a gefen gadon sa, da cup ɗin tea a hannun ta, ta ɗebo shayin a spoon, ta hura mishi sannan ta kai bakin sa, ya kau da kai,
"Ke.... Ni ba yaron ki bane"
Muryarsa ta fito tar daga maƙogwaron sa.
"Na sani amma kai babyna ne.... Ka buɗe bakin ka ka sha kafin ya huce"
Ta faɗa tana sake kaiwa bakin sa tare da matsowa kaman zata shige jikin sa, ko kunyar mutanen wajen bata ji, a lokacin ba shi da wani zaɓin da ya wuce ya buɗe baki ta bashi, don a yanda takaicin ta ya gama cika shi, idan ya ce zai buɗe baki yayi magana, daga shi har ita babu wata wanda zai ji daɗin abin da zai faɗa.
Da sallama suka shigo, Ibrahim ya gaisa da Nurse ɗin da ke handling ward ɗin, tun shigowan su tame waige waige ta ga ta inda zata hango shi.
"Ta can side ɗin za mu bi"
Ibrahim ya faɗa yana masu jagora zuwa side ɗin da zai kai su gadon Mohan, yanda gaban ta ke faɗuwa kaman zuciyar ta zata faso ƙirjin ta ya faɗo ta baki. Ko a mafarki bata taɓa tunanin za ta ga problem ɗin ta nan kusa ba.
"Kai... Baby ji yanda ka ɓata jikin ka.... Ka tsaya in goge maka"
Ɗago oily eyes ɗin ta ta yi ta haska su saitin inda take jin sautin muryar, suka yi four eyes da Mohan daidai lokacin da Maryam ke ƙoƙarin goge masa gefen fuskar sa da ya ɓaci.
Dam dam, gaban ta ya buga sau biyu a lokaci ɗaya, saurin ja da baya ta yi. Ibrahim ya kamo hannun ta
"Ina za ki?, Ga shi can"
Kallon hannun ta da ya riƙe ta yi, ta ɗago ta dube shi, idanun ta har sun fara tara ƙwalla hakan ya ƙara haska oily eyes ɗin ta ko ƙiftawa bata yi, ta yi masa wani irin kwarjini ya zame hannun sa daga kan nata. Ta juya da sauri za ta bar wajen
"Problem....!"
Kakkaurar muryar sa mai zurfi ya dakatar da ita, cak ta tsaya, ta rufe idanunta da sauri yayin da hawayen da suka tarun mata suka samu daman gangarowa, wani sanyi ya shiga ratsawa cikin jijiyoyinta.
*LITTAFIN MOHAN NA KUƊI NE*
Mutane talatin da za su fara siyan littafin za su siye shi a kan farashin #300, duk wanda zai siya daga baya zai biya normal Price #500
*Za'a biya ta wannan lambar 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*
Sai a tura receipt ko shaida ta wannan lambar *09125491597*
Haka zalika zaka iya biya a matsayin katin MTN a wannan lambar *07046627683*
MOHAN IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF ADDICTION INTO AFFECTION.
KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA*
FIRST 30 SUBSCRIBERS WILL BE GOING FOR #300
Pay
*VIA 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*
EVIDENCE TO *09125491597*
YOU CAN SEND MTN CARD SEND To *07046627683*
Be the first subscriber ❤️
NB _Part one is free_
©BINTOU.
Na yi gabas 🚶🏽♀️.
16th December.
[12/21, 6:52 AM] Star: *018*
"Problem....!"
Kakkaurar muryar sa mai zurfi ya dakatar da ita, cak ta tsaya, ta rufe idanunta da sauri yayin da hawayen da suka tarun mata suka samu daman gangarowa, wani sanyi ya shiga ratsawa cikin jijiyoyinta.
"Problem....?"
Ya sake kiran ta a karo na biyu, bata juyo ba kuma ta kasa motsawa daga inda take...
"Problem....shigo mana"
Wannan karon sai ta ji fitan muryar sa na shiga cikin jikin ta, tana ji kaman yana tsittsinka mata jijiyoyin jikin ta, ta lumshe ido, hawayen ta suka ƙara gangarowa kan fuskan ta kaman ruwa, ko ba'a gaya mata ba ta san yarinyar