Showing 12001 words to 15000 words out of 72389 words
much”
Ta wani shagwaɓe kaman zata yi kuka. Alhaji Abdul Azeez ya sake ruɗewa.
'' Cut the call angel, zan kira ki video call and you will show me how you miss me"
Daddy ya faɗa da wani shu'umin murya, babu shiri ta kashe wayar tana dariya.
"Kowa ya sani Ronaldo ya fi Messi sau dubu gaskiya ne bakwa so."
Ɗakin ya kaure da hayaniyan yaranta da ke shigowa.
”ƙarya kake yaa Ammar, idan Ronaldo ya isa ya nuna ƙwarewar sa ya ci world cup mana"
"World cup ɗin banza, shi messin ba penty ya taimaka mai ba?, Skills ɗin Ronaldo ya fi na Messi a wasar da ya sama ma messin naku world cup”
”wane skills?, Ina amfanin skills ma mutum ya kasa saye zuciyar mutanen da ke kewaye da shi?, Sai mutanen social media?"
Don zafin rai ma Ammar switching yayi ya koma surfa bala'in sa da turanci.
"You guys dislike Cristiano because he's not the typical nice guy to cheaters. He's uncompromising, and that's why people around him don't like him, you guys rate Messi higher not because you genuinely prefer him, but we like Ronaldo because he's giving his efforts to gain what he want....."
"Hhhheey wai meye haka?...!"
Siddika ta dakatar da su ganin suna neman maida abin faɗa, shigowan su kenan daga ɗakin Yaa Ammar sun je kallon ƙwallo, gabaki ɗayan su fan ɗin Messi ne, shi kaɗai ne fan ɗin Ronaldo, a gidan gabakidaya kuma daga shi sai Zakiyyah.
"Kuna hauka ne?, Kun wani shigo min gida kuna hauka a kan mutanen da ba su san kuna yi ba, da Ronaldo ɗin da Messi nawa za su baku?"
Tsitt suka yi suna dariya, Ammar ya zagayo ya rungumeta yana dariya da fadin.
"Haba Mum, ba wani abu bane fa... Kin ɗau abin so serious, it's nothing fa, nishaɗi muke,
Yayi maganar cikin son kauda faɗan da Mum ɗin nasu ta fara, Hajiya Siddiƙa ta harare shi tana ture shi.
"Ni matsa min, kun je kun sha gumi zaka shafa min datti"
Ammar ya ja baya yana dariya tare da shinshina kan shi.
"Atleast bana wari... Yawwa Mum you know what?, Can you belive that har office yarinyar nan ta bi ni ta ci min mutunci, a gaban secretary, sannan ta rubuta resignation letter ta wurga min a fuskata, I was shocked"
Waje hajya Siddiƙa ta fiddo kwayar idanunta yanayin ta cike da dumbin mamaki tace
"Bangane ba? Ba dai yarinyar da take claiming ka yi mata fyaɗe ba?"
Tun bata gama rufe bakinta ba Zayn ya tare ta faɗin
"Mum ba da sharri ta yi masa ba fa, ke kan ki kin san halin yaa Ammar, maraban shi da mijin ki kaɗan ne"
Ammar ya harziƙo mishi kaman zai kai masa hannu.
"Shut up, Zayn idan ka sake saka min baki ina magana da Mum sai na ɓaɓɓallaka, ka Sanni"
Yayi magana a zuciye, muryar sa har rawa yake.
"Me yasa kuke haka ne?, Maganar da yayi har yayi zafin da kake wannan harunton?, So kake yi kuma ku zama kamar dabbobi ace babi jituwa a tsakanin ku?, ba za ku hada kai da baki shawarar ku ta zama daya ku rufawa kawunan ku asiri ba? Idan kuna haka suma ƙannenku abinda za su ɗauka kenan, ni kuwa fatana ku haɗe kai ko bayan ran Baby babu wanda zai tantance akwai ɗan haram a cikin ku, so nake a ce duk abin da za ku zartar a tsakanin ku sai kun shawarci juna, sannan ku rufawa kan ku asiri, koda kisa aka kama wanin ku yayi, ku zama kuma babu babba ko yaro in har daya ya yi laifi ku haɗu ku rufawa juna asiri, ni kai na na san Amaar ya yi wa yarinyar fyaɗe amma ai ita ta ja wa ya ce ta rinƙa saka matattsun kaya tana kawo kan ta office ɗin shi, Sauran da suka kame kan su me yasa bai neme su ba?, In ban da iyayi da kwaɗayi irin na talaka ma, ina messenger da ina CEO?, ni kaina tunanin hakan ya sa na tsaya kai da fata na rufa masa asiri, ba zan so maganar nan ta fita ba, ko za mu reni shege ba za ta hannun ƴar talaka ba"
Ta ƙarasa da isa tana sake ƙurɓan lemun ta
Zayn yayi shiru, har ga Allah baya jin dadin yanda Siddiƙa take goyon bayan duk wani sakarcin da yayan su yake aiwatarwa. Matan da yayi wa ciki a office ɗin nan sun fi ashirin, har kotu an kai shi, amma kuɗi da rashin shaida ke sawa a yi watsi da case ɗin. Ya zurfafa cikin tunani, a yayin da su kuma suka kamo wani hiran.
"Mum, kin san wa na gani yau a tasha?"
Ammar ya faɗa yana ƙoƙarin gyarawa Hajiya Siddiqah karamin ɗan kunnenta da ya karkace a kunnenta.
"A'a sai ka fa'da"
"Black devil..., na ganta a tasha ɗazu da zan je Kano".
Lemu take sha babu shiri ta ƙware nan ta shiga tuttula tari kamar zata amayo kayan cikinta Jabeer da Zayn na jera mata sannu. Sai da ya lafa mata ido da fuska sun yi jajir sai sauke numfashi take yi dan ta shaƙu amma bata daddara ba ta kalli Ammar tana zaro ido tace
"'Aljanan yarinyar nan ce ce ta dawo?,me ta dawo yi? kwananta nawa da tafiya?"
"Ni ɗin ma I was shocked, na gan ta a tasha tana talla, a wajen ta na siya Fanta da breadi don na tabbatar ko ita 'din ce" Ya sake bata amsa. Jabeer ya dafe 'kirji
"Mun shiga uku"
Ammar ya ce
"Wallahi na tsaneta"
Ran Mum ya ɓaci, ta tsani yadda suke jin tsoron yarinyar, duk da cewa ita ɗin ma shakkar yarinyar take, don bayan kisisina da iya makirci akwai wani kwantaccen kwarjini a tattare da ita wanda ke sa a ji shakkan ta har uban ta Alhaji Abdul Azeeez Yabo, a fusace tace
"Mala'ika ce da zaku tsorata don an ambaci sunanta?"
Jabeer ya ce
"Mum, kin san alheri baya kawo yarinyar nan Zaria, ni wallahi tun da ta ƙullawa wa Uwar ta tuggu, ta sa Daddy ya sake ta na ƙara tsorata da lamarin ta, har yau idan na gan ta sai gabana ya faɗi"
Hajiya siddiƙa ta yi ƙwafa
"Wallahi sai ta bar gidan nan, ba zata kwana a gidan nan ba, sai na sa Baby ya kaɗata inda ta fito... "
"Assalamu alaikum...."
Sallamar da aka yi ne ya sa su duban ƙofa a tare, gaban su ya faɗi a tare lokacin da ta sako ƙafanta a falon.
Wani irin kallo mai dauke da mutsamutsan tsana da kishi ne ya chaki zuciyoyin su . She's very captivating tun daga yanayin fuskart a da a kullum yake a cunkushe, yadda take takunta cikin isa sai ka ɗauka jinin Siddiƙa ce. Ko dage ido bata yi ta kalli inda suke ba ta wuce su tana fa'din.
"Sannu Siddi'ka"
Ta gaisheta ciki ciki, bata jira amsarta ba ta wuce ɗakinta, ba'kin ciki ya rufe su na yadda bata shakkar kiran sunan mahaifiyar su gatsal babu ko sakayawa, kaman wata tsarar ta.
Zakiyyah kuwa dawowanta gidan ya ƙara dagula mata zuciya, abubuwa dayawa ta ji na damun zuciyar ta amma haka nan take ƙoƙarinin danne su dan ita kan ta bata son ganin kanta a cikin damuwa ko kadan.
Ji take kamar she cant just waste her time on abunda ba zai amfane ta ba, shi yasa a koda yaushe ka ganta za ka ga she's too busy da kasuwanci, day and night. Wanka ta yi, ta ci abincin da ta siyo, don tun tana ƴar shekara goma sha biyar ta daina cin abincin gidan da ma duk wani abin da ya fito daga hannun mahaifin ta, saboda wani dalili da ta bar wa kan ta.
Tana gamawa ta yi sallah, ta haye gado, ta jawo system ɗin ta ta ɗan yi danne danne, sannan ta ɗauko wayarta, saƙon shi ta fara gani.
"Babe fushi kike da ni dan jiya kare ya biyo mu na gudu na bar ki?"
Turo baki tayi kaman yana gabanta
"Waye kai?, Wa ya baka numbana?"
Ta mayar masa tana sake turo baki.
"Babe what's this abege"
"Ni ban san da wa nake chatting ba"
Maimakon ya mata reply, wannan karon kiranta yayi, tana ganin kiran ta 'ki dagawa har ya katse.
"Babe please, zan miki kuka fa"
A fili ta ja tsaki bata son lalaci, shagwaɓar sa ba ƙaramin ɓata mata rai yake ba, ita fa a tsarin rayuwan ta bata son namiji da ya cika lallaɓa mace don tana fushi da shi, ta fi son wadda zai yi laifi ta yi fushi ya yi banza da ita, har sai idan ta sauko ta yi masa magana don kan ta za su sasanta. Wani tsaki ta sake ja sanda saƙon shi ya sake shigowa da emoji ɗin kuka, ta maida masa martani fuska a murtuƙe.
"Ka ƙara himma, babu mai rarrashinka"
Tana typing tana jan tsaki
"Katon banza, ga kuka ga tsoron kare"
"Eh din, ai gudun kare ma Sunnah ne, saboda duk gun da kare yake annabi baya gun kin ga bai kamata ki ga laifina don na gudu ba"
Haushi da takaici ma sun kasa barin ta ta yi reply, ta sauka ta koma facebook, tana kai message ɗin Mohan ya shigo, ta miƙe daga kwancen da take tana zabga murmushi. Shi ma ta yi masa typing
"Solver ɗina...."
Comment and share please 🥺😩
21 November 2024
Na yi gabas🚶🏽♀️🚶🏽♀️
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *005*
Tuni ta manta da chat ɗin da suke yi da Ibrahim, ta mai da hankalinta kan Mohan.
"Solver... Ka ci abinci?"
Murmushi yayi, damuwarta kenan a kullum, tana ganin shi online abin da take fara tambayan sa kenan. Yadda ta damu da shi da kuma yadda take nuna damuwar ta a kan duk wani abin da ya shafe shi, shi ya ƙara ƙarfin shaƙuwar su a kowane lokaci.Ya yadda da ita fiye da yanda ya yadda da kan sa, babu wani sirri nasa da bata sani ba.
Ta san yana shaye shaye, amma bata taɓa ƙyamatar sa ba, akasin ƴan uwansa da suke ƙyamatar sa saboda ƙaddarar da ninke rayuwar sa, hasali ma, hasali ma ita kaɗai ce wacce take iya fahimtar yadda yake ji har ta fahimci dalilin da ya sa ya kasa daina shaye shaye. Wasu lokuta ma idan yana cikin damuwa, da kan ta take cewa ya sha, ta kan ce "Problem shaye shaye yana da illa ga lafiyar mu, amma ta kan zama waraka ga wanda zuciyarsa bata da ƙarfin jure damuwa, ka riga ka saba, idan baka sha ba za ka yi wa lafiyar ka wata illa na daban, gara ka sha ko zaka samu ka yi bacci, tun da lafiyar ka ya riga da ya samu giɓi ta wannan fannin, ka sha ka ji?"
"Baka ci ba ko?"
Message ɗin ta ya sake shigowa a karo na biyu, wannan karon ma murnushi yayi.
“Ke ni fa ba yaro bane"
"Ƙalya ne, kai yaro na ne”
"To mamana na ci abinci"
"Me ka ci?, yaron kirki"
"Tuwo da miyan egusi"
"Kai da baka son swallow da daddare?"
"To Problem ya na iya...?Abin da aka bani kenan, kuma ina jin yunwa"
Sosai suke hirar su cikin nishaɗi, ko fita daga chat ɗin shi bata yi ba ballantana ta ga jerin tarin message ɗin Ibrahim. Wanda yayi ta turowa ganin tana online, a tunanin sa tana gani ta ƙi reply ne saboda fushin da take yi da shi. Ita kuwa tuni ta mance da batun sa ma. Idan tana tare da Morhan bata chatting da kowa, iya shakuwa sun shaku dashi sosai ta san kusan komai na rayuwar sa, da duk wani motsin sa tana sane, baya iya buɗe cikin sa ga kowa, amma idan suna tare da Zakiyyah, sai ya tsinci kan sa da fige mata komai har da wanda bai dace da ya gayawa kowa ba, jin ta yake kaman safety ɗin sa, privacy, kuma abokiyar kuka mai fahimtar sa fiye da kowa a rayuwar sa, idan na ce kowa, ina nufin kowa har da mahaifiyar sa. Hakan ya sa ta san abubuwa sosai a rayuwar sa, waɗanda babu wanda ya sani hatta Ummie da ke mahaifiyarsa. Cikin abin da ta sani wanda ba kowa ya sani ba har da mutuwar auren Nihaal da kuma soyayyar da suka sake ƙullawa, da kuma shirye-shiryen auren ta da yake yi.
Suna cikin hira aka banko kofar dakinta aka shigo, Juyowa ta yi don ganin mai shigowa. Gaban ta ya faɗi ganin mahaifinta ne, wayar hannun ta ya suɓuce ya faɗi ƙasa, ta miƙe a razane ilahirin jikinta na rawa, tana ƙoƙarin gaida shi ya dakatar da yunƙurin ta.
"Me kika dawo yi?"
Girgiza kai ta shiga yi bakin ta na rawa.
"Ba komai"
A zahiri in ka gan ta zaka rantse cewan ba karamin tsoron mahaifin nata take ji ba don har fuskar ta ya nuna hakan, a zuciyarta kuwa dariya take yi, don ba ƙaramin dariya mahaifin nata yake bata ba, musamman in ta kalli fuskantar sa, yadda yayi dyeing farar gemun sa zuwa peach irin ga gayen nan a dole ba'a so a tsufa, ga wani ƙaton tumbin sa da ya turo ta farar singlet ɗin sa, a hakan ma don siddiƙa na takura masa wajen zuwa gym ne.
" Ka ga Alhaji, daga dawowanta ɗazu ɗazun nan har ta fara takalar yarana da faɗa tana zagi na, don kawai sun nuna rashin jin daɗin su a yadda take kiran sunana babu sakayawa..."
Zakiyyah ta tsinkayo muryan Siddiƙa cikin kissa da kisisina ta ɗaga kai ta kalleta, har a lokacin da tsoro a fuskar ta.
"Ki yi shuru sweetheart, dole ta bar gidan nan, kina ji na ko?, bana so in tashi in tarar da ke a gidan nan, you have two options, ko ki tattara tarkacen ki ki kama hanyar Kaduna cikin daren nan, ko kuma gobe da sassafe kada ki bari in rigaki tashi, bana son sake ganin ugly face ɗinki in my house anymore, in ba hutu kuka yi ba, kina ji na"
Ta ɗago ta hade kwayar ido da na mahaifin ta a take yasa taji tsananin rauni ya lu'llumeta. Duk dama ta tsaneshi a ranta amma da ciwo a ce mahaifin ka shi ke furta baya son ganin ka a gidan sa, ba tare da ka yi masa laifin komai ba, duk don kawai ya burge mace. Har ya gama bambamin bala'in sa bata fahimci abin da yake cewa ba, ya fice yana huci kaman wanda ya haɗiye transformer. Ƙarar rufe ƙofa ne ya ankarar da ita fitan su, ta bi bayan su da kallo, yana gaba siddiƙa na biye da shi kaman raƙumi da alaka.
Maimakon abin ya ɓata mata rai, dariya ma ya bata, ta faɗa kan gado tana dariyan, in da sabo ya ci a ce ta saba da wulaƙancin mahaifin ta, ko ciyar da ita baya yi, ita take biyan kuɗin makarantanta da komai nata, ita ke hidimta wa kan ta, tun tana da shekara goma sha ɗaya, har yau, kuma bata jin har abada akwai wani abin da mahaifin nata zai bata ta sake ƙarba. Tun lokacin da ta gane aikin mahaifin ta shi ne safarar yara mata yana kaiwa masu kudi da ƴan siyasa suna lalata da su suna biyan sa, lokacin yana lecturer a ABU Zaria kafin ya zama professor. Tun daga lokacin ta ƙuduri aniyar daina ƙarɓar duk abin da ya fito daga hannun sa. Gidan da suke zaune ma don tana da tabbacin na gadon sa ne ya gyara masu da babu abin da zai hanata kama hayar gida a waje ta rinƙa zama ita da ƙannenta Nabeela, Imam, Ayman da Aaman. Lokacin da maman su ke tare da mahaifinta ma ta sha ƙulla mata tuggun da zai fitar da mahaifiyar ta daga gidan, don ta tsiratar da ita daga haram, da ƙyar ta yi nasarar raba su.
Wayar ta ta ɗauko, ta cigaba da chatting ɗin ta hankali kwance, sai ƙarfe ɗayan dare ta kashe data ta yi sallaah sannan ta yi bacci, tun asuba ta haɗa kayanta, har zata fita sai ta dawo
Ta ɗauko wani pink takarda ta yi rubutu a kai kaman haka.
*Stop looking for happiness in the same place you lost it*
_Ki daina neman farin ciki a inda kika rasa shi_ ..
Ta ɗauko pin, ta liƙa a jikin ƙaramin bord ɗin ta, wanda ke ɗauke da takardun rubuce rubucen kalmomi mabanbanta.
Ko da Daddy ya dawo daga masallaci direct ɗakinta ya nufa, har hamdala yayi sadda ya ga ɗakin nata a kulle, don a zahiri idan yana tare da ita za ka ce ita ke tsoron sa, amma a ƙasan ran shi tsoron yarinyar yake kaman ranar mutuwan sa, saboda bayan kwarjini da take masa, zuwanta gidan baya taɓa zama alheri a gare shi yanzu ma gaban sa faɗuwa yake yi, ya san dole wani mummunan abu na shirin faruwa da shi.
Ƙarfe bakwai da rabi, iyalan gidan Alhaji Ahmed Abdulazeez suka zauna a dining area suna breakfast, hankalin su kwance, da zarar ka gan su zaka gane basu da wata damuwa, karyawa suke da haɗaɗɗen chicken wings,burgers da salads da mashed potatoes da kakkaurar tea, haɗin ƴan gayu. Lafiyayyen abinci ne mai rai da lafiya, idan ka gan su ba zaka ɗauka akwai wani ɗan Alhaji wanda ya kwana da yunwa ba. Su bakwai ne a table ɗin, ƴaƴanta shida, da ƙannen Zakiyyah biyu, (Ammar, Zayn, Jabeer, Safaana, Layla da Bilal) su ne ƴaƴanta (Imam da Julaybeeb) kuma ƙannen Zakiyyah, su ba'a cika nuna masu bambanci ba kaman ƴar uwar su, saboda suna saukar da kai su mata biyayya iya gwargwado, ita ma Zakiyyahn taurin kai da girman kai ne ya haddasa tsanar ta a zukatan ƴan gidan, da zata sauke jijji da kai, ta kwanta a wulaƙance tana masu bauta babu abin da zai sa su tsane ta.
Yadda suke cin abinci cikin kwanciyar hankali, ba za kace akwai ƴar Alhaji da sai fita cikin rana tana talla kafin ta samu ta ci abinci ba. A gidan kusan ƴan aiki ma sun fi Zakiyyah gata a wurin Alhajin, don in za ka tambayi Daddy, ka ce yaushe rabon da sisin sa su shiga hannun Zakiyyah, sai ya kwana yana ƙirga shekaru.
Mai gadi ne ya shigo da sallama a bakin shi, jikin shi na rawa ya zube yana miƙo gaisuwa cikin matsanancin firgici da girmamawa amma ko kallo bai ishe su bare su amsashi, ballantana su fahimci yanayin da ya shigo da shi.
Bakin Haruna maigadi har rawa yace
"Ran ka shi