Showing 18001 words to 21000 words out of 72389 words

Chapter 7 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4948

ki zubawa yaran kaman basu ƙoshi ba"
Bai bari ta kuma cewa komai ba ya kalli namijin yace
"Sadeeq Ameen na nan?"
Ya ce "A'a uncle, ya tafi meeting"

"Auntyn ku fa"
"eh Uncle Morh yana sama"

Mikewa yayi ya hau saman, a falonta ya isketa.

"Barka da Yamma"

Ya gaishe ta, duk da ya bata shekaru sosai, daga ita har mijin ta, amma hakan bai dasa mishi girman kai ba, shi ke fara gaisheta a kodayaushe, a ganin shi wanda ya riga ka aure ya girme maka.
Zarah ta amsa a kunyace da
"Sannu da zuwa Ya Muhammad Sani Batta, CEO tuzuran gidan Alhaji "
Mohan yayi dariya yace

"Kin fara ko?"
Nan suka fara hira irin ta matar ƙani da wan miji cike da aminci, zaman sa babu jimawa Ameen ya dawo, suka dasa da hirar cike da kaunar juna, a duniyar sa bayan Zakiyyah, ƙanin sa Ameen da matar sa Zarah ne kawai yake iya sakewa da su har su yi hira mai tsayi.

Suna cikin firan ne babbar yayar su Hajiya Saudat tayi Sallama ta shigo cikin shigan ta na manyan hajiyoyi, tana kwarkwasa kamar wata yarinya. Morh na ganin ta ya miƙe yana duban agogon hannun sa.

"Ameen, bari na koma"

"Ka koma ina?, Ga maƙiyiyar ka ta shigo ko?"

Ɗan murmushi yayi.
"Allah ya baki haƙuri Anty saude lokacin da Ummie ta ɗiban min ya cika, I have to leave"
Ya faɗa yana kama hanya zai tafi, Muhammad Ameen Naseer Batta ya raka shi da faɗin.

"Allah shi huta gajia Ya Morh".

A parlorn kasa ya iske Maryam, idan idanun sa ba ƙarya suka yi masa ba har wani man baki ta ƙara a lips ɗinta, giran ta ya ƙara shape alaman an gyara shi, tana ganinshi tan nufe shi da sauri.

"Uncle Morh har ka gama da Uncle Ameen?"
Yace "eh"

"Na ga Hajiya Saudat ma ta zo"

Yace "Eh mun gaisa"
Tace "Bari na dafa maka ko indomie ne, mu ɗan yi hira, kafin ya dahu, sai ka tafi da shi"
Yace "sorry Maryam next time" .

Ba haka taso ba sai dai ba yanda za tayi da shi tace "Toh" tana bin bayan sa, tsayawa yayi ya kalleta "Akwai wani abu ne?"

Tace "a'a wai rakiya zan yi maka"
Bai sake cewa komai ba, ya wuceta ta bi bayanshi
"Yaushe zaka sake dawowa Ya Moh?" Yace
"Not soon".
Ta kalle shi a shagwaɓe tana shirin da fashewa da kuka, ya kallle ta da kulawa.

"Me zan dawo in yi miki Maryam?"
kafin yayi rufe baki ta fashe da kuka, ta juya, ta koma ciki da gudu.

Ya bita da kallo, ya shafo lallausar sumar ƙeyan sa da ta sha gyara sannan ya shige motar sa, duban agogon hannun sa yayi, ƙarfe biyar da rabi. Ummie ta ce awa biyu ta ba su, saura minti talatin lokacin ya cika. Hamdala yayi a ran sa, ya ƙara gudun motan sa cikin ƙanƙanin lokaci ya isa ghetto, wurin kaman kasuwa yake, kowa sai hada hadan kasuwancin sa yake, mutane ne da yawa sai kai kawo ake. Ya parka motar sa ya fito yana waige waige cikin tsarguwa, sai da ya tabbatar babu wanda ya lura da shi sannan ya nufi wajen wani mai siyar da kayan marmari, ya ce a haɗa masa fruits na dubu biyar. Mutumin ya haɗa fruits ɗin na dubu biyar ya zuba a leda ya miƙa masa, Morhan ya zare agogon diamond na hannun shi, wanda aka siyo masa last month, ya miƙawa mutumin, ya ce

"Ka yi mata kuɗi"

Mutumin ya kalli agogon, aƙalla a dala zai haura dala dubu sha biyar $15k, a Naira kuma miliyoyin kuɗaɗe ne (25.5M).. Mutumin ya ɗaga agogon a yatsine yana faɗin.

"ka san ni ban san darajar irin waɗannan abubuwan ba. Amma zan biya ka dubu ɗari biy....."

"Menene dubu ɗari biyu?, Agogon?, Ina da receipt ɗin ta, idan baka san kuɗin agogon ba zan kawo maka receipt ka gani, da dala aka siyeta...."

Mutumin ya ce
"A'a malam Muhammad Sani, ba fa dole bane sai in baka agogon ka bani fruits ɗina".....





Ikon Allah🤧
Na yi gabas 🚶🏽‍♀️
Bintou
25th November.
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *007*

Mohan ya ce
"Gaskiya gara ka bani agogona, dama shaiɗan ne ya kawo kawo ni wajen ka, na fasa siya"

Mutumin da idanun sa kaɗai ma abin tsoro ne, ya ɗago baƙar fuskar sa , ya watsa masa wani uban harara. Fuska a murtuƙe ya ce.
"Ɓace min da gani "

Mohan ya ja tsaki, ya ɗau agogon sa, ya maida hannunsa, sannan ya juya yana sake buga wani tsakin.

'' Kai, uban wa kake yi wa tsaki?"

Juyawa mohan yayi, ya kalli mutumin, wanda dauɗa da ƙazanta suka canza masa kamanni, in banda ƙaddara ma me zai kawo shi wajen ƙazami irin shi, har ya nemi ya wulaƙanta shi?
_Ƙaddara_ ya ba ma kan shi amsa. Sannan ya sake doka wani tsakin, zuciyar sa na tafarfasa.

"Mtswww"

Ji yayi an wani fizgo shi ta baya, an wani haɗa kan shi da bango, tare da kashe shi da wasu zafafa kuma tagwayen maruka, akowane side na fuskar sa.
" Kai har ka isa?, Har ka isa ka shigo har cikin masarautata ka ce za ka ci min mutunci?, Ni kake yi wa tsaki?, Me kake taƙama da shi?, Sai in farke cikin ka in ga uban da zai tsaya ma"
Mohan ya ya dafe ƙuncin sa da hannu bibbiyu, yana kallon mutumin da idanun sa da suka kaɗa suka yi jazir, ba yau ya fara shan duka a hannun ƴan area ba, amma wannan shi ne karo na farko da ya ji zafin dukan har cikin zuciyar sa.

Ya haɗiye wani yawu mai ɗaci, ya kalli mutumin wadda ke tsaye yanata faman huci kaman Zaki.
"Saboda tsaki?... Saboda na maka tsaki shi ne ka mare ni?'"

Muryar sa ta fito da sanyi, Ya murmusa yana sake shafa ƙuncin sa, ya ce.

"Ba da niyya na yi haka ba, Allah ya baka haƙuri"

Kaman ya ƙara tunzura mutumin yayi, ya shaƙo kwalar Mohan yana haki.
"Ni za ka ce Allah ya bani haƙuri?, haƙurin ta ci uwatai d**run uwar haƙurin"
Ya faɗa yana sake kai masa wani shaƙar , ya shiga harbin sa da ƙafa yana dukan sa ta ko ina, mutane suka suka rirriƙe shi. Da ƙyar aka kwace Mohan a hannun shi, bayan ya haɗa masa jini da majina, ya kuma ƙarɓe agogon da aka ƙi siyar masa, Mohan ya bar wajen babu kuɗi babu cocaine babu agogo, ga jiki duk tsami.

Da ƙyar yake driving har ya shigo cikin gari. Daga nesa ya hango wata mata mai ciki durƙushe a kan gwiwowinta ga yaran ta biyu, kwance male male a ƙasa sai kuka suke, a gaban su wani mota ce fake a wajen da alama koma me ke faruwa, mutumin suke roƙo da ya yafe masu, amma ko buɗe ƙofar ba'a yi ba, abin takaicin ma shi ne, duk tarin mutanen da ke kai kawo a layin babu wanda ya tsaya balle ya damu da jin ba'asin abin da ke faruwa. Duk da raɗaɗin da yake ji a jikin sa, hakan bai hana shi karya akalar motar sa ba, ya nufe su yana tambayan su mai ya faru?


"Ranka ya daɗe, mun fito bara ni da ƴaƴana, sai na shiga wancan gidan abincin don na samo mana abin da za mu ci, na bar yarona a waje, ban sani ba, shi ne yarona ya ɗau ƙarfe yayi masa rubuce rubuce a jikin motarsa, da ya fito sai ya kama yaron yayi ta jibgan shi, ya ce sai mun biya shi motar sa, yanzu haka ma ya kira ƴan sanda suna hanya...."

Mohan ya dubi Matar, tausayin ta ya cika shi, ba wata babba bace don ba za ta haura shekara ashirin da biyar ba, talauci da haihuwa su ne suka maidata kaman tsohuwa. Ya ce

"Da ya ce haka me yasa baku gudu ba?, Ina ne gidan ku?"

"Mu gudu fa ka ce?, Idan mun gudu ma ina za mu ranka ya daɗe?, Ba mu da gida, mu ƴan gudun hijira ne...."

"Ya Moh?"

Ya jiyo muryar Hassan ta bayan sa, ya juya ya kalle shi da mamaki. Yace
"Dama kai ne kake ƙoƙarin azabtar da waɗannan bayin Alllahn?, Wai kai wane irin azzalumi ne?"

"Motata fa aka lalata ya Muhammad, for God sake don na nemi a bi min haƙƙina shi ne kake ganin laifi na?, Bari ƴan sandan su ƙaraso ma tukunna, wallahi sai na yi amfani da dukiyata ɗaure su, sai sun ɗanɗani azaba da raɗaɗin d...."

Tassss, cikin rufewar idon Mohan ya sauke masa lafiyayye marin da ya saka matar da ke durƙushe ta razani. Maruwa dai kam Hassan ya maru, dan har sai da ya buga kan sa da jikin motar sa.

"Shashashan banza!, Da kai da ita meye banbancin ku?, Kana da ido, hannu kunne da ƙafa biyu itama biyu gareta, kana ji da kunneka ita ma haka numfashin da kake shaƙa shi take shaƙa, banbancin shi ne suturar da ke jikin ka!, Da duniyar nan tsirara muke yawo da babu abin da zai banbanta ka da ita sai banbancin jinsi, jinsin da bai banbanta da na uwarka ba!"
Hassan ya shafa kuncin sa, wani abu kaman shock yana haskawa cikin idon sa, ya kalli Mohan, ya kalli matar, sai ya ji kaman ƙasa ta tsage ya nitse a cikin ta tsabar kunya, iya ƙasƙantarwa Mohan ya gama da shi, ya ciji lips ɗin sa tare da gyaɗa kan sa, wani ruwa mai kama da hawaye na taruwa a idanun sa, ya shiga motar da ya ja ya fice a layin da wani uban gudu.

A natse ya ƙarasa inda matar ke duƙe, ta rungumo yaranta, gabaki ɗaya ta gama tsorata, jikinta har rawa yake yi.

" Kun ci abincin?"
Matar ta ce "A'a''
Ya ce

"Ba ni da kudi a hannuna, amma zan kai ku gidan mu za'a baku abinci, kin ji"

Matar ta sake rungumo yaranta, tana fashewa da wani sabon kuka a tsorace
"A'a .... Mun gode, da ka kuɓutar da mu a hannun wannan azzalumin, amma ba zan iya bin ka ba"

Mohan yayi murmushi
"Ga katangar gidan mu can, babu abin da zan yi miki, ki yadda da ni"

Da ƙyar ya lallaɓa matar har ta amince, ya buɗe masu motar da suka shiga, har a lokacin kuka yaran ke yi, tausayin su na sake ratsa shi, ga tsamin da jikin shi ke yi, yana ji kaman yanzu ake dukan sa.

Tun da suka shigo gidan kowa yake ta bin su da kallo, yayin da matar ke biye da shi tana waige waige zuciyar ta cike da fargaba. Kai tsaye main parlor ya kai su, duk suka zauna a ƙasa, suna waige waige cike da tsananin tsoro. Ya kira Sa'a ya ce ta basu abinci, sannan ya haye falon Ummie don ya sanar da ita garajen da yayi, duk da yana da tabbacin har ya gama zantukan sa ba za ta ce komai ba z haka kuwa aka yi koda ya shiga ɗakin ta ya sanar da ita, tana jin shi amma ko ɗago kai bata yi ba, hakan ya sa ya sauko ƙasa zuciyar sa babu daɗi.


A guje ya shigo da tasa motar, ta abokin sa Salman ya bi bayansa yana jin wani sabon ɓacin rai na shigarsa, tsanar Mohan na sake azarzala a cikin ƙoƙon ran sa, a tare suka shigo falon babu ko sallama
Daidai lokacin Mohan ke saukowa daga saman stairs, fuskar sa cike da rauni, rauni irin na wanda ya rasa gata da kulawa na uwa.
Kwalar rigarsa ya ji an cakuma kaman daga sama, an kuma ƙwala masa wani abu a tsakar kai.

"Ni zaka wulaƙanta??"
Hassan ya faɗa yana huci kamar mahaukaci yana shaƙe wuyan Mohan, abokin sa Salman riƙe da wani sharɓeɓen bulala sai uban huci yake. (Ko me zai yi da ita ojo)
Hannun Hassan da ke wuyan sa ya bi da gani sannan ya ɗago da kallonsa ga gare shi, ya kuma juya ya kalli Salman da ke shirin kai masa duka da bulalan hannun sa a karo na biyu.
"Don't try it"

Ya furta muryar sa a kausashe, hakan ya sa Salman ya sauke bulalan babu shiri, don ba karamin kwarjini Muryar tasa ta yi masa ba. Duban Hassan yayi
"Sakar min kwalar riga malam."
Ya faɗa da haɗaɗɗiyar muryarsa kai kace koyar magana ya ke, yana kai hannu ya dafe na Hassan da ke riƙe da wuyan sa.

"Idan na ƙi fa me zaka yi Muhammad?.."

Sauƙar marin da ya ji akan kuncinsa ya sa shi runtse idanuwansa da ƙarfi.
"Kar ka taɓa min ɗa dan ubanka."
Mom Halima ta faɗa da buɗaɗiyar muryarta, cikin sanyin jiki ya sauke hannun sa, idanuwansa sun sauya kala zuwa ja. Hassan ya sake maƙure shi.

"Kai ma ka sake shi, ko so kake ka ja min zagi?"

Mom ta faɗa tana hararar Hassan, Hassan ya sake shi yana huci, Mohan ya kalli uwa da ɗan, ya ciji lips ɗin sa, yana ƙoƙarin hana zuban hawayen da ke neman bada shi, ya kaɗa kai ya fice daga sashen. Halima ta ja hannun ɗan nata cikin zafin rai za su bar sashen, surutan da suka ji a falo ya sa duk suka dakata, suna duban yaran da ke zaune bisa dinning suna cin abincin da aka kawo masu hannu baka hannu ƙwarya.

"Kai...!, Uban wa ya kawo ku gidan nan?"

Hassan ya furta a fusace tare da ɗumbin mamaki yana nufarsu, Mom ta riƙe shi.

"Ina zaka kuma?, Kana nufin taɓa waɗannan ƙazaman za ka yi?"

"Mum kin san ko su waye?, Lalata min mota suka yi, da na nemi na hukunta su shi ne uban nawa da yake ji kaman ya isa da ni ya hau ni da duka a titi, a gaban talakawan nan, tsabar mamaki ma na rasa mai zan yi, shi ya sa na kira Salman ya zo ya taya ni cin uban sa..."

Halimah ta rungumo kafaɗar sa tana shafa ƙeyar sa

"Ka ƙyale shi, ya isa da kai ne... You need to respect your self, ya kamata ka san ka fi ƙarfin rigima da talakawa, You win, ƙaruwar ka ne, saboda ka fi su komai dukkan su, daga yayan naka har waɗan nan ƙasƙantattun talakawan, tarbiyyan ka cikakkiya ce ɗa na, saboda baka shaye shaye, shi kuwa har gobe ya kasa barin shaye shaye...''

Halima ta faɗa cikin ɗaga murya, duk don Ummie ta ji ran ta ya ɓaci.

*MORH*
Yana shiga, yayi wanka, sannan ya fara jera nafila kafin lokacin sallah ya ƙarasa, bayan ya idar ne ya fara addu'an Allah ya raba shi da wannan ƙaddarar da ke bibiyar rayuwar sa, Allah ya sa ya daina shaye shaye, idan ba zai daina ba Allah ya sa yan uwan sa su fahimci yadda yake ji idan yayi yunƙurin dainawa sosai tsabar ruɗewa ma wasu addu'oin bai san yana furtawa ba. Bayan ya gama ya yi Sallah sannan ya kwanta, yana jin hayaniya na damun sa a cikin kan sa, kamar yana filin ball, surutai yake ji da yawa, kan nasa yayi masa wani irin nauyi, ya riƙe kan nasa yana jin hawaye na zubo masa daga cikin idon sa. Sosai ya riƙe kan sa yana tunanin abubuwan da shaye shaye ya jawo masa daga lokacin da ya fara shaye shaye kawo yanzu. Ya tuna ciwon a da Athma ɗin sa ba mai yawan tashi bane, amma shaye shaye ya sa a yanzu baya sati biyu ba tare da ya ziyarci asibiti ba, bayan lafiyan sa ga farin cikin sa da ya rasa, ya rasa soyayyar iyayen sa da ƴan uwansa, ya rasa Nihal a kan shaye shaye, ya rasa respect daga wajen mutane, ƙaramin yaro baya shakkar gaya masa magana, ga aikin sa da ya rasa, ga rashin kuɗi da tattali, duk wani abin da ya samu burin sa ya siyar ya ƙona kuɗaɗen a shaye shaye, sau biyu yana shiga ɗakin Abba a ɓoye yana masa sata, tsabar masifa da bala'i, a haka har barci ya ɗauke shi.

Washe gari juma'a Mum ta tari Alhaji Naseer da wata magana, wai tana so a haɗa auren Mohan da ƙanwar ta Zainab saboda ta ga rashin dacewar zaman sa a gida, kuma ko ba komai auren zai sa ya natsu, idan aka masa auren zai fara tunanin tara iyali, kuma hakan zai sa ya daina shaye shayen ko don kada ƴaƴan sa su taso su gan shi yana shaye shaye. Sosai Alhaji ya ji daɗin wannan shawarar kuma ya ga dacewar haɗin don ba laifi Zainab mace ce mai natsuwa, cikin ƙanƙanin lokaci har ya sanar da aminin sa cewa a shirya bayan juma'a zai je gidan nasu da yayyin sa domin nemo izini.

Hassan yana office dinsa Ameen ya tura masa saƙo cewa za su je nemawa Mohan auren ƙanwar Mum ɗin sa bayan sallan juma'a. A mugun fusace ya ɗau wayar sa ya fara dudduba wasu lambobi., Bakin sa na furta.

"Noo...No way .ba zai yiwu ba, Aunty Zee ba za ta auri mashayi ba"

1:40
A tare suka yi sallan juma'a da Alhaji Naseer, sun ɗan jima sosai a masallaci kafin suka jero shi da Hassan kaman abokai suna hira cikin natsuwa.

"Daddy ya kamata mu shiga sashen Ya Morh, mu sanar da shi, sai mu je tare da shi, daga nan ma sai ya ga amaryar ta sa"

Hassan ya faɗa yana fatan Allah ya sa Alhaji ya amince da roƙon sa . Bai ce komai ba, ya dai sauya akalar tafiyar tasa izuwa hanyar da zai kai shi sashen Mohan. Farin ciki ya lulluɓe zuciyar Hassan, har sai da ya murmusa ya ɗauko wayar sa yana dannawa, yana amsa hiran da mahaifinsa ke jan shi da shi a hankali.

Ƴan aikin gidan da basu jima a gidan ba sai abin ya zame masu kaman almara, ganin Alhaji Naseer da kan sa a hanyar sashen Mohan... kowa ya zura masa ido kaman sun ga wani baƙo, suna kallon cikakken gwarzon gidan mai kamala da tsoratarwa ga duk wanda zai iya jure kallonsa. Karasa takowa yayi sashen cikin takun nan nasa ɗaidaya, Hassan na biye da shi da tashi kalan tafiyar da yau ya kara zama cikin izzar da wani ɓoyayyen farin ciki da ban san na meye ba.

*Mohan*
Dawowan shi kenan daga sallan juma'a, ya rage kayan jikin sa ya shige bathrum a mugun gajiye ya wuce bathroom, ganin duk towels din sa sun yi datti ya saka ya dawo dakin sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login