Showing 63001 words to 66000 words out of 72389 words
da ta gaisa da ƴan ajin kafin ta fara gudanar da darasin. Kusan rabin awa da fara darasin na su ta jefo wata tambaya wanda Zee Ahmad ta yi saurin ɗaga hannu ta amsa ta sai dai kuma amsar ta ba dai-dai bane, ƴan ajin kaman jira suke su ga ta gaza, sai suka hau dariya ƙasa ƙasa har da masu yin gwalo, sai da Comassie ta dakatar da su kafin su natsu. A maimakon ta gwale Zee sai ta ce "perfect, but we need something better"
Wata mai suna Precious kyangchat ta ɗaga hannu ta sake amsa wannan tambaya sai dai ita ma ɗin ba dai-dai ba ne. Hadiza comassie ta yi murmushi ta ce "Kin yi ƙoƙari Precious"
Ta kalli Zakiyyah da ke gefen Khadijah wacce ke kallon ta amma hankalin ta baya kan ta, ta ɗan kira ta a hankali, sai da Khadijah ta taɓata sannan ta yi saurin ɗago idon ta tana ƙoƙarin ba da nitsuwarta.
Ta sake maimaita ma ta tambayar ko za ta iya amsawa sai kuwa ta ba ta mamaki sosai domin amsar da ta bayar ɗin shi ne dai dai. "Da kyau" ta faɗa sannan ta cigaba da bayanin darasin da ya ke yi.
Zakiyyah kuwa tuni hankalinta ya kauce daga darasin, wani sanyi ne ke shigan ta sosai, zuciyarta na yi ma ta wani nauyi. Ta dafe ƙirjinta tana maimaita hasbunallahu wa ni'imal wakeel, a kowane daƙiƙa ji take kaman ta fashe da kuka ko zata samu sauƙin abin da take ji a zuciyar ta. Bayan lecture ɗin suna da test har biyu, amma bata jin zata iya yin test ɗin. Ta miƙe tare da ɗaukan excuse, ta fice daga ajin.
Ta koma hostel, alwala ta yi ta yi sallah sannan ta hau haɗa kayan ta, ta shirya a gurguje cikin doguwar rigan atamfa wanda ke da kalar blue da ruwan toka (Ash), ta ɗauki babban mayafi ash ta yane jikinta da shi. Chocolate cornflakes kawai ta haɗa da madaran gari na awo ta zauna ta sha kafin ta ɗau jakarta ta fice daga makarantar tana share ƙwallan da ya taru mata a idanu.
Ba ƙaramin kasala take ji a jikin ta ba tana tafiya tana yatsine fuska, damuwa sosai take ji ya har ya hanata walwala. Haka nan take ji a jikin ta wataƙila daga yau sabon shafi na baƙin ciki zai buɗe a rayuwar ta. Idan ta isa gida yau tabbas dole ta roƙi Daddy da ya tsinka igiyar auren ta, idan kuma haka bai yiwu ba zata yi iya ƙoƙarin ta wajen fahimtar da Mohan, fatan ta ya fahimce ta ya yarda ba wani auren gaske aka ɗaura mata ba, idan kuma bai fahimce ta ba tabbas zata rufe ido ta tauya ƙasa koda ba daɗi, zata rabu da shi koda hakan na nufin ɗaukewan farin cikin ta ne, koda hakan na nufin silar ɗaukewan bugun zuciyar ta, ta riga ta ja kan ta a ƙasa da yawa, duk soyayyar da take masa ba zata iya cigaba da bibiyan sa alhalin ba zata samu abin da take nema a wajen sa ba, tunanin da take yi kenan har ta isa Zaria.
A hanya wata baƙuwar number ne ke kiranta ta whatsap. Yadda numban ke kira akan kira ya sa ta yi tunanin ko Mohan ne. Ta dai daure ta ƙi ɗagawa da zimmar tana isa Zaria za ta kira numbar domin ta ji wanene ke kiran, cikin zuciyarta tana ayyana wa ranta ƙila ya karanta saƙonnin ta ne ya kira don ya sake bata dama don ta kare kan ta .
*Zaria*
Wajajen karfe biyu na rana mai napep ya shigo da Zakiyyah farfajiyan hadadden unguwan su, ya sauke ta a gaban gidan su. Tsabar yadda kanta yake juyawa har jiri take ji, jikinta ya kuma dau zafi, a daddafe ta shiga ciki tana rike kanta cikin sauke numfashi a hankali ba tare da wani cikakken nitsuwa a jikin ta ba.
Ta wuce su Siddika a babban falo ba tareda ta ce da su komai ba. Babban ƙofan ɗakin ta mai kyau mai kalar ruwan ƙasa wanda daga ganin design din sa ka san me tsada ce, kai kusan komi ma cikin gidan wanke hannu ka taɓa ne.
Sosai Daddy yake narka kuɗi wajen ƙawata duk wani abu nasa domin a duniya yana son rayuwa mai tsada. Haƙiƙa Daddy yana son rayuwa, yana son duniya, sosai yake shanawa a duniyar sa kaman ba za'a mutu ba, rayuwan zamani yake baya tunanin lahira.
Tana shiga ɗakin ta sauke jakan ta, amma kuma ƙaran shigowar text zuwa wayarta ya sa ta maida hankalin ta ga wayan domin ta ga wani irin saƙo ne. Video aka tura mata, tun kan ta kaiga taɓawa ya buɗe da kan shi, abin da ta gani ne ya sanya numfashinta ya ɗauke na ƴan daƙiƙu.
Ta miƙe zumɓur tana faɗin
"Wanene wannan?, Wane ne?" hannunta na rawa ta shiga dialing numbar da ta turo saƙon. Aka ɗaga daga ɗayan ɓangaren ana kwashewa da wata mahaukaciyar dariya. Sai da ta saita muryar ta sannan cikin dakewa ta ce
"Wanene kai?"
"aka ce baki son uban ki, ashe duk ƙarya ce"
Huci ta sauke,tana jin ɗaci a maƙoshin ta tamkar ta surɓi maɗi, ba wannan take son ji ba, so take ta san koshi waye shi?, Me yasa ya turo mata hoton tsiraicin mahaifin ta?, Duk da kasancewar ya rufe wani sashe na jikin sa da emoji amma tabbas ta san babu kaya a jikin sa.
"Wanene kai?"
Ta sake furtawa tana jin kan ta kaman zai rabe gida biyu.
Da muryar sa mai kaman dimon girke yake magana
" Babu talakan da ya isa ya wulaƙanta ni ya kwana lafiya, ni ne na yi garkuwa da mahaifin ki, sannan na yi masa tsirara na ɗau hotunan sa na turo miki domin ki shaida, ki shirya ganin hotunan mahaifin ki a kafafen sada zumunta, I heard that shi professor ne, sannan kuma fitaccen ɗan kasuwa, that would be interesting in na yi posting a ending this year, lokacin da zai yi signing babban contract ɗin sa da gwamnati, opportunity ɗin da ya jima yana nema, kuma kin san gwamnati ba ruwan ta da ƙoƙarin ka, ƙimar ta tafi na talakawa, bayan haka sai in waiwayi mahaifiyar ki, sai na yi maganin irin ki marasa kunya, rashin tsoron ki ya sa ba zan yi da ke ba, zan yi amfani da mahaifan ki wajan ɗaukan fansa, amma ke na fi ƙarfin ki har abada "
A daidai wannan lokacin bata san me zata ce ba, bata kuma san ta inda hawayen da ke soya zuciyar ta za su fito ba domin idanauwan ta ƙanana suke tamkar an soya gyada marau, da wanne zata ji?, shi kuma wannan waye shi?, a ina ta san shi?, Me ta yi masa?.
"Malam a ina na san ka?, Me nayi maka?"
Ta tambaya da raunanniyar muryar ta, sai da yayi mata slight narration a kan abin da ya faru ranar sannan ta tuna shi, ta yi shuru har ya dasa aya.
Ta ɗauka wani babban ɗan daba ne, a tunanin ta ma irin manya manyan kidnappers ɗin da suke garkuwa da mutane su yanka wuyan mutum idan sun nemi kudin fansa an hana su ne, ashe shi ne, a kallon farko da ta yi masa kallon sauro ta yi masa, bai bata tsoro ba, kuma bata tunanin zai iya gagararta.
"Little boy, da alama baka san me kake yi ba, domin kuwa ka sa an yanka dabba don biki sannan ka gauraya ruwan inabi da kayan yaji. Hotunan mahaifina da ka ɗauka tamkar ka aiki barorin ka ƴan mata su je su hau wuri mafi tsayi a birni su yi kira ne. A da ban san ka ba, yanzu kuwa da kan ka ka shigo, jahili, kana tunanin zaka iya taɓa iyayena? Ga dolo kuwa! Hmm zo ka ci abincina ka sha ruwan inabin da na gauraya, Ka rabu da ƙungiyar jahilai, ka rayu, ka bi hanyar ilimi... Domin a harkar nan, na fika ilimi"
Tamkar ta sa makami ta daddatse gwiwowin sa haka ya ji, zuciyar sa ta harzuƙa, duk da hausan ta yayi masa nauyi, amma ya san ta ci sa da zance cikin bacin rai da fariya yace
"Wallahi, wallahi sai na durƙusar da sakarcin ki, sai na ɗaiɗaita ahalin ku gabaɗaya, sai na sa iyayen ki sun zubar da hawaye, idan kuɗi na magani sai na yi maganin ki, na fi ƙarfin in yi da ke talaka, da iyayen ki da dangin ki zan yi"
Ta yi murmushi mai ciwo
'"Tabbas ka yi magana, amma batada ma'ana mutane masu fasaha sukan yi magana mai ma'ana, amma wawaye suna bukatar horo. Mutane masu hikima sukan nemi ilimi iyakar iyawarsu, amma sa'ad da wawa ya yi magana, wahala tana kusa. Wadata takan kiyaye attajiri, amma tsiya takan hallaka matalauci, me kake da shi? Ga tsiya ga jahilce. Idan ka isa ka taɓa iyaye na, bai kamata ka tsaya kana faɗa min ba, just go straight, Effort are better than promise, so let me see, the ability of expressing your foolishness is also a wisdom, peace and pieces the option is now yours ɗan halak ka fasa"
Ta ja dogon tsaki, sannan tana sauke wayar ta yatsine fuska a ranta tace "Romon baka bana kwarya bane, da ni kake zancen hmmm mu zuba dai mugani yaro".
Text ta turawa wani lamba dan abinciko mata details din mai numban.
Tuƙi Hassan yake yi a yayin da maganganun ta ke yawo a cikin kan sa, me yasa yarinyar nan ta raina shi haka?, Shi zata kira jahili?, Masters gare shi fa!,. Sau ɗaya ya taɓa ganin ta amma gaba ɗaya ta birkita masa rayuwar sa, Ya rinƙa saƙa da warwara, yana tuna maganar da Zakiyyah ta faɗa masa, sosai zuciyarsa take zafi da tafasa a lokacin, yasha ruwa mai sanyin yafi jarka biyar amma bai ji komi ya ragu a zuciyarsa ba.
Tana sauke wayan ta yi ordern abinci, aka kawo mata ta kira Imam ya ƙarbo mata, ta ci abincin ta tayi nak sanan ta tashi a hankali ta fito babban luxury general falo ɗin su, suna zaune duka a dinning area suna cin abincin dare, suna hira da alama babu abin da ke damun su, a karo na farko bayan wasu shekarun da ita kan ta manta lissafin su, ta ɗaga ƙafa ta taka zuwa dinning area, ta ja kujera ta zauna, duk suka bita da kallon mamaki, fuskanta kaman kullum babu rahama a cikin ta, ga idanun ta da suka kumbura.
"Sannu Daddy.... Siddiƙa sannun ki, sannu Ya Amar"
Ta gaishe su kan ta a ƙasa, tana kallon tarin abincin da ke gaban su, soyayyan dandalin turawa ne da steak, sannan roasted vegetables da kaji, a gaban Daddy kuma salad ne grilled fish kasancewan baya cin kaza, ga kuma roban dakakken yaji a gaban kowanne, dogon flask ɗin da ke ajiye a tsakiyan table ɗin cike yake da ruwan Lipton wanda ya sha kayan ƙamshi kala kala. Ta haɗiye wani yawu idanun ta ya haska abincin da ta yi order a restaurant ɗin da ke kusa da su, tuwon masara ne da manja da yaji.
Ta kauda idanta daga kallon abincin, ta dubi Daddy tace
"Daddy na ga message ɗin ka, amma ina roƙon ka da ka yi magana a kashe auren nan, don ban ga amfanin shi ba"
Siddiƙa da Daddy suka kalli juna, Daddy yace "Zakiyyah why are you so Stubborn, ban san ki da haka ba, i'm sorry i cannot do this, auren nan babu fashi, wannann kaman alfarma ce a waje na, ki daure ki min, do this for me, na shirya tsab domin in miƙa ki gare su"
Zakiyyah tace "Sorry, Dad ask for anything but not This"
Siddiƙa da dama baƙin cikin auren take yi, jiya ma ƙaramin hauka ta tayar, karara ta nuna baƙin cikin ta da auren ta ce a raba auren kawai, auren ba shi da maraba da auren jeka na yi ka, da ƙyar Daddy ya shawo kan ta ɗazun suka ɗinke, dama faɗan su baya wuce awa goma. Tace
" Ni ban ma san me suka gani a jikin ƙazamiyar yarinyar nan ba, sun wani jajibowa kan su ƙazanta da masifa, alfarma aka miki, idan baki sani ba alfarma aka miki, tun da su sun amince ke waye da ba zaki amince ba?"
Zakiyyah ta ce
"Akwai waɗansu mutane da suke ganin kansu tsarkaka ne, alhali kuwa ƙazamai ne su, ƙazantar taki ma mai dalili ne, har abada ni mai tsafta ce ... Ni fa ko sun amince ni ba zan amince ba, ba zan taba yarda da wannan auren ba
cikin bacin rai Daddy yace "Don't disrespect my wife!, And who is asking for your opinion?, shut the hell up girl, babu abin da zai raba auren nan sai dai in kashe kan ki zaki yi"
Zakiyyah ta ji hawaye a kuncin ta da sauri ya goge murya a raunane ta ce
"Daddy ya batun karatu na?"
"Wannan ba matsalata bane, idan an kai ki sai ki nemi izinin mijin naki"
Idonta ya kawo ruwa ba tare da saninta ba hawaye suka fara zuba daga idanuwan ta
"Daddy in aka min auren dole sai na sha piya piya na mutu kowa ya huta"
Daddy ya ce "Wannan kuma ai ke da Allah"
Wasu hawayen suka ƙara zubo mata, zuciyar ta ta ɗau zafi, ta ɗau spoon ɗin gaban ta, ta yi dipping ɗin shi a roban yajin da ke gaban ta, ta ɗibo da yawa ta kai bakin ta, idanun na zubar ƙwalla, ta haɗiye yajin duk zafin shi, Sai kowa ya dakatar da abin da yake yi yana kallon ta, shan yajin take yi sosai tana hawaye, zafin da take ji a bakin ta bai kai wanda take ji a zuciyar ta ba. Babu wanda ya habata.
Daddy ganin tana neman illata kan ta da yaji sai ya yagi tissue ya goge bakin sa, gaba ɗaya ya tsarguwa, ya miƙe ya bar wajen. Hakan kuma be yi ma Sidd dadi ba domin ta san shakkar Zakiyyahn ne ya sa, ta so ya zauna har sai ta shanye, sannan ya yi convincing ɗin ta ta sha fiya fiyan ko zata mutu kowa ya huta . Ta dauke plates din ta fita ba tare da ta ce komai ba, Ammar da yan uwan sa sai tsaki suke ja. Ganin Daddy ya fita sai ita ma ta tashi ta bar wajen tana share hawayen ta.
Ammar ya bi bayan ta dogon tsaki
“Mummy kina jin yarinyar nan?”
“Ba laifin ta ba ne Ammar, laifin Baby ne yana mugun tsoron yarinyar nan, ya fi shakkar ta da ni , dubi yadda ya kiɗime saboda tana shan yaji, dan ta ce zata kashe kan ta, kuma ƙarya take shegiyar ciccika baki ne kawai”
Ammar ya ce
“Hmmm
Ta cigaba da cewa
"ai ni ganin nake kamar ba banza uwar yaran nan ta bar Daddy ba, ita kanta ai ba a banza ta aure shi ba, shi yasa ya gana mata azaba ai, yanzu kuma saboda iƙirarin da ta yi za ki ce na faɗa maki, yasin ba zai fita aiki ba gobe, zama zai yi yana gadin ta sakarai a haka yana nuna bai damu da ita ba, amma tsoron makircin ta yake”
“Wallahi sai na kai mata fiyafiyan, idan ta isa ta sha ta mutu"
“Toh ka dai yi a hankali, in ba haka ba hukuma ta shigo zancen ka san babu mai fitar da kai”
Ta tashi ta fice dakin tana wani zakuɗa ita ga hana tsufa.
*Mohan*
Kafin dawowan sa sun gama shiri tsaf har sun tsaida ranar da za'a kawo amarya ranar juma'a wato ƙarshen sati, Abba ya ba Hajiya saudat ta haɗo masa lefe.
Akwati Set1 (Guda 6) Anty Saudat ta hada, komai ya ji, Anty Saudat tace
"Da Abba zai yi maganin yaron nan da ya haɗa lefen nan da yarinyar can ƴar Zaria, in ya so sai su tare a tare"
*LITTAFIN MOHAN NA KUƊI NE*
Mutane talatin da za su fara siyan littafin za su siye shi a kan farashin #300, duk wanda zai siya daga baya zai biya normal Price #500
*Za'a biya ta wannan lambar 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*
Sai a tura receipt ko shaida ta wannan lambar *09125491597*
Haka zalika zaka iya biya a matsayin katin MTN a wannan lambar *07046627683*
MOHAN IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF ADDICTION INTO AFFECTION.
KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA*
FIRST 30 SUBSCRIBERS WILL BE GOING FOR #300
Pay
*VIA 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*
EVIDENCE TO *09125491597*
YOU CAN SEND MTN CARD SEND To *07046627683*
Be the first subscriber ❤️
NB _Part one is free_
©BINTOU.
Na yi gabas 🚶🏽♀️.
26th december.
[12/27, 2:00 PM] Star: *024*
Assalamualaikum ƴan uwa da abokan arziki, zan yi amfani da wannan lokaci wajen miƙa saƙon godiya a bisa goyon bayan ku a Gaskiya bazan boye muku ba inajin dadin comments da goyon bayan da kuke bani Allah ya barmu tare. You guys are amazing, na gode sosai. Kuma ina mai sanar da ku cewa daga gobe In sha Allah free pages zai tsaya, za mu cigaba da posting a paid group ɗin mu da iyaka mutanen da suka biya kuɗin littafin. Mai buƙata zai iya tunatuɓana ta whatsapp a wannan numban 09122107940
Let's go....
Ummie tace "Ni in zai bi ta tawa da na ce a raba auren nan kawai, shi kan shi Abban naku na lura baya son auren, kawai don alƙawarin da ya ɗauka ne don sun yi zaman amana da Ahmad a baya, kafin halayyan sa su tarwatsa komai"
Anty Saudat tace "a'a ke kuwa Ummie, a bar masa kayan sa kawai, wlhy in an haɗa masa biyun zai yi hankali, dole ya manta yadda ake shaye shaye".
Sosai mutane suke zuwa ganin lefe, suna ta murna don Mero ta yi Goshi, kaya sai sambarka, uban gayyan kuwa ko fitowa baya yi, yana nan ƙuryar ɗakin sa, in da yayi ma laƙabi da kurkukun sa, Maryam ta kira shi a waya tana kuka ta roƙi ya yafe mata a kan abin da ta yi masa, ya ce ya yafe mata, amma ta sami mahaifin ta ta gaya masa gaskiyan abin da ya faru, shi kuma ya fahimtar da Alhaji Naseer, baya so ya cigaba da kallon sa a matsayin mazinaci, haka kuwa aka yi, Alhaji Naseer ya ce yana sane babu abinda ya shiga tsakanin su, kawai ganin dacewan su