Showing 60001 words to 63000 words out of 72389 words
gama sharar ta ɗau bokiti, ta tara ruwan famfo ta je ta yi wanka da sanyin shi , kasancewan gas ɗin ta ya kusa ƙarewa, lokacin Khadijah na kwance kan gadon ta tana danne danne a wayan ta..
Da ta dawo sai ta ga wayan ta a kan gadonta, babu kowa a ɗakin, irin wannan lokacin ƴan ɗakin suke fita karatu, bata kawo komai a ran ta ba, amma ta ji haushin yadda Khadijah ta ajiye mata waya saman gado ta yi tafiyan ta. Tana tsaka da shafa maii Khadijah ta dawo, ta harareta
"Sannu ƙawata uwar kasada, shi ne kika bar min waya a kan gado salon a shigo a sace min ko?"
Khadijah ta ce
"Wai saman gado kika iske wayar?,ai kuwa da zan fita na ba Mrs Morh ta baki"
"Ina kika je?"
Zakiyyah ta faɗa tana kallon roban hannun ta.
"Ɗakin Rakiya na je, ta dafa tuwo shi ne nace ta ɗeba min, dan na ga alama idan na ce zan biye wa mutumiyar ki yunwa ce zata kashe ni"
Zakiyyah ta yi murmushi tuno draman su sa Mrs Moh, tun da suka zo makarantar suka haɗa kayan abincin su Mrs Moh da Khadijah, tare suke girki, wasu lokutan ma har wasu kayan suke sharing a tsakankanin su, toh yau Mrs Moh ce da girki, tun da ta tashi take video call da samarin ta taƙi tashi ta ɗora masu girki, itama Khadijah ta ƙi tashi ta ɗora abincin, haka breakfast ya wuce basu ci komai ba, da rana ma wanka ta ɗauka suka fita da saurayin ta, tana fita Khadijah ta dafa indomie nata ita kadai ta cinye ta wanke kwano, tun suna shara take mitan yunwa take ji, Allah Allah take ta gama ta tafi maula wajen Rakiya, kuma ta yi sa'a ta bata abincin.
Tare suka ci tuwon sannan suka fita karatu, test gare su har biyu a gobe dan haka tun da suka fita karatu a silent ta saka wayar ta shiyasa bata ji kiran Daddy, Mohan da Mahaifiyar ta ba, da suka je sallar Magriba kuma ta ga missed calls kaman haɗin baki, da suka je sallar isha ma Mohan ya sake kira tace she will call back amma ta manta bata kirashi ba.
Ƙarfe tara ake kulle hostel, don haka takwas da arba'in suka dawo, Koda ta dawo numban Daddy ta fara kira
"Ke har kin yi girman da zan kira ki ki ƙi ɗaukan wayata?..."
Ta ɗan yamutse fuska kaman yana gaban ta, murya can ƙasa ta ce
"ka yi haƙuri Daddy mun je karatu ne, wayar na silent"
Ya ja tsaki yana cewa
"Okayyy!, da kyau, na gode Zakiyyah, na gode sosai, na gode da sakayyan da kika yi min a matsayina na mahaifin ki, tabbas ba zan ce haihuwan ki bai yi min rana ba, haihuwan ki ta yi min baƙar ranar da ba zan taɓa mantawa ba, kin sa an zo har gida an ɗauke ni a, ni mahaifin ki, kin sa an azabtar da ni, mutanen da suka ɗauke ni basu bar ni a haka ba sai da suka yaye min sutura suka yi min video tsirara, kullum cikin fargaba da taraddadi nake kwana nake tashi, sun yi rantsuwa cewan sai sun yaɗa faifan a duniya, tun da suka kama ni ban sake wani farin ciki ba har yau, kullum bacci nake cikin taraddadi da tsoron ranar da tsiraici na zai fito duniya su gan ni, na yi nadamar haih....."
"Daddy, Daddy, ka ɗan dakata ka saurare ni Please,.... me kake so?, Me na yi maka?"
Ta yi saurin katse shi ganin yana shirin yi mata baki, ko kaɗan zuciyar ta bata motsa ba da jin kalaman sa ba, hasalima bata so a sako shi da wuri haka ba, ta fi so su hora shi da kyau har sai duniya da abin da ke cikin ta ya fita a ran sa, tana so ta ga ya rage son duniya, don shagalar tasa ta yi yawa sam baya tuna mutuwa. Muryar ta a raunane ta cigaba da cewa
"Daddy me yasa?, Me yasa zaka rinka min irin wannan maganun?, na taɓa yi maka wani laifi ne?, Kullum ƙoƙarina in kyautata mu'amalana da kai, ban taɓa bijirewa umurnin ka ba koda zuciyata bata so, ina ganin ganin girman ka, ban taɓa saɓawa umurnin ka ba ko hakan ya ya saɓa da ra'ayina , amma baka taɓa faɗin alheri a kai na ba, a ina na taɓa gazawa?"
"Yi min shuru Zakiyyah, yi min shiru, baki min komai ba kika ce?, kin min abubuwa da yawa Zakiyyah, kullum cikin gazawa kike, Ko sau ɗaya baki ɗaukeni a matsayin uba ba, ina iya ƙoƙarina iya gwargwado wajen ganin na yi covering duka buƙatun ku, amma ke kin zaɓi ki yi talla ki biya wa kan ki buƙata da kan ki, You choose to be independent over seeing me as a man, kin ɗauka ina jin daɗi ne?, Zuciyata zafi take yi a duk lokacin da na ga kin nufi tasha da niyyar yin talla, wata ran haka kike kwana da yunwa don ki yi malejin kudin ki, baki cin abinci sau uku a rana saboda maleji, idan baki da lafiya da kan ki kike kai kan ki asibiti, a baki magani, da kan ki kike siyan maganin duk tsadan shi, ga ƙannen ki nan a gida me suka nema suka rasa?, kullum in na kalle ki sai na ga tsananin tsanan da kike min a cikin ƙwayar idon ki, me na yi miki a rayuwa da za ki tsane ni haka?,Saboda ke na daina harkar safarar mata, amma duk da haka baki yadda da ni ba."
Daddy kenan, idan ka ji yana irin wannnan maganganun wani abu yake nema a wajen ta, amma har Daddy ne zai kalli tsabar idon ta ya ce yana tausayin ta?, Mafarki ma kenan.
"Hmm Daddy kenan, a duniyan nan bayan ni, kana ganin akwai wanda zai iya faɗanhalayyan ka ne?, kai ma ka sani, na san ka kaman yunwar cikina, don haka go straight to the point what did you want?, Me kake so?"
Daddy ya sauke ajiyan zuciya yana sosa gemu
"Check your SMS na tura miki saƙo, ina so ki dawo gida gobe"
Ta ce "Tou" tana murmushi, Dadddy kenan, Mahaifin Zakiyyah, Uban shegu, Mijin Hajiya Siddiƙa, ta riga ta san halin shi kawai a bar mata kayan ta. Message ta buɗe, ta ga duk babu unread message, ta duba na saman tana mamakin yaushe yana buɗe su?, message ɗin Daddy ne da na Mohan, na Mohan ta fara karantawa. *Ina ɗan kwalin ki?* , Sai yanzu ta tuna, lokacin da za su taho ta cire ɗankwalin ta ta haɗa mai da jakar ta tace ya riƙe mata, da za su rabu har gaban gate ɗin makarantar su ya rakota, ya miƙa mata jakar kadai, kuma bata tuna ba sai yanzu da ya tunasar da ita. Murmushi kawai ta yi sannan ta fita ta shiga message ɗin Daddy.
"Ina fatan kina sane da auren dake kan ki, ya kamata ki faɗa ma mahaifiyar ki, ku san yadda za ku yi, nan ba da daɗewa ba zan miƙa ki gare su"
Tsabar takaici ma kasa karance sakon ta yi, ta ja dogon tsaki. "Dole ma in je Zarian gobe, in ji wane aure yake nufi?, don ba zai yiwu a ce auren da aka ɗaura shekara uku da suka gabata yana da rai har yanzu ba".
*MOHAN*
Wajajen takwas na dare suka iso estate ɗin su, kaman kodayaushe masu aiki ne ke shawagi a harabar gidan kowa da kalar abun da yake yi.
Direct sashen mahaifiyar sa ya nufa yana amsa gaisuwan masu aiki, a hadadden dakin ta dake kama da aljannar duniya ya iske ta, kaman kullum suna zaune a babban falo suna hira da su Aisha, ya durƙusa a gaban ta yana gaishe ta, ta kau da kan ta tana amsawa ciki ciki, gwiwa a sace ya baro sashen, ya nufi sashen Halima, ya gaisheta ita ma, ta amsa babu yabo babu fallasa, zuciyar sa ta cika da ƙunci, ya tsani gidan nan sosai, asibiti ma ya fi gidan daɗin zama so dubu, a yanzu zai dawo rayuwar ƙunci da kaɗaici.
Ya jera tsaki ya fi a ƙirga, yana isa sashen sa ya hau rage kayan jikin sa ya haɗa ruwan wanka, ran sa duk a jagule, ga wancan yarinya da ta kira shi a waya ta jagula masa lissafi.
Ɗaure da lallausan white towel ya shige hadadden bathrum din sa wanda tsabar haduwar sa sai ka yi tsammanin dakin hutawa ne bana wanka ba.
Ya jima yana wanka kamin ya fito, ya wuce gaban madubi yayi night routine ɗin sa. Sannan ya dawo babban falon sa.
Kaman koda yaushe looking breathtaking duk da ran sa babu daɗi fuskar sa bai ɓoye murmushin sa mai ɗaukan hankali ba.
sanye yake da armless shirt Ash da three quarter shot na kamfanin adidas, fararen ƙafafun sa sun yi wani irin fresh a cikin lallausar Clogs roam sleepers din da ya zura a kafafunsa. A center table ya ga an ajiye masa abincin sa, ya zauna sannan ya shiga bubbuɗewa, cappuccino a bottle flask and some pancake, sannan taliya mai zafi da miya ya ji kifi. Yayi murmushi, favorite ɗin da kenan kuma ya san Ummie ce ta dafa masa, ya kunna TV yana kallo har ya cinye, ya ɗauko wayar sa ya kunna Data ya hau online.
"Ka aiko min da ɗankwalina"
Saƙon ta ya fara shigowa,
_"A yadda na samu labari ma har ciki gare ta, sannan mijin ta matafiyi ne shi yasa take zaune a hostel, amma tana komawa Zaria duk bayan sati biyu"_
kalaman matan ɗazu ya faɗo mata, ta ya zai fara yadda da total stranger over his girl, yarinyar da yake kyautata zaton ko mahaifiyar ta bata fi shi sanin halin ta ba. Sai dai duk yadda ya so ture maganar kasawa yayi, dan tsaye yayi masa a maƙogoro, furta shi gare ta shi ne sauƙin sa, don haka sai ya kirata video call da niyyar tambayan ta. Tana kwance sanye cikin kayan sanyi, kaman kullum yau ma kan ta babu ɗan kwali ya harareta.
"Rufe min ƙazamin gashin nan naki"
Ta turo baki, ƙasa ƙasa ta ce
"Ƙazantar ta kashe ka"
Ya yi murmushi
"Wato kin fara raina ni ko?"
Ɗan marairaice murya ta yi, tace "I'm sorry"
"To ki rufe gashin ki" Tun kan ya rufe baki ya ga ta ja hulan rigan hoody ɗin jikin ta ta rufe gashin.
"Good girl"
Ta lumshe idanun ta, sannan ta yi shuru, hakan ya ba shi daman ƙare mata kallo, baƙar fatanta sai daukar masa hankali take yana son bakar mace, bayan baƙar fatarta baya gajiya da kallon fararen hakoranta da idanun ta masu kaifi da kama da ana wanke su da ruwan madara a kullum.
Jin yayi shiru sai ta buɗe idanun ta, ta yi rolling nasu a kan sa.
_Ya ilahi_
Ya furta a ransa yana kallon idanuwanta da farin yayi fari kamar watsa ruwan madara a ciki.
"Problem..."
“Uhmm mmm”
Ya amsa irin amsar dake nuna ta fito ne daga kasan zuciyarsa.
“Ina son na tambaye ka wani abu...”
Kaman da gangan take juya masa idanu, don yayi loosing control nasa, Wani shaukin kallon ta ne ya dauke shi ya lulashi a wata duniyar da ya haddasa bugawar zuciyar sa a mabanbantan dakiku, natsuwarta na neman bukata a gurin sa a karo na farko ya saukar masa nishadi da ya samu kan sa da lumshe ido ya bude yana kallon ta kamar mai jin bachi.
“Name what ever you want girl...”
Gyara kwanciyan ta tayi, tarankwafar da kai, da wata murya da ta fi kama da tausayi da shagwaba ta ce.
"Promise me.. you won't leave me, ko na yi aure"
"Ko kin yi aure fa kika ce fa?"
Kwaryar idanunta ya fara tara ruwan da aka sirka da gishiri (Hawaye), ta gyaɗa masa kai, sannan ta ƙanƙame jikin ta cikin kayan sanyin da take sanye da shi.
"Kina nufin idan kin yi aure?, Wa za ki aura to?"
"Nima ban sani ba, kawai bana so na rabu da kai ne"
Ta furta muryarta can kasa sosai. Zuciyar sa ta buga da mugun karfi, kodai maganar yarinyar ɗazu gaskiya ne?. Zuciyarsa ta sake bugawa da karfi tana raba tunanin sa ga sauran sassan jikinsa da suka kasa yadda da maganar.
"Zakiyyah, kina da aure ne?"
Tambayar ta faɗo daga bakin sa a take, kuma a take ya ga idanun ta sun wani zare da mamaki, mamakin abu biyu, yadda ya ambaci sunan ta kai tsaye a karo na farko a rayuwar sa, da kuma tambayan da yayi mata everything just happened so fast, ta rasa me zata ce, ƙarya ba nata bane.
Reaction ɗin ta ya ƙara tsorata shi sai ya ji duniyar na neman juya masa wani sashi na zuciyar sa na neman yadda da cewan tana da aure.
"Da gaske... Ne?, Kina da aure?"
Ta gyaɗa kan ta a hankali, hawaye suka suɓuce mata.
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un''
Yake ta ambato a zuciyar sa, bakin sa na neman ƙaryata zahirin abin da yake zaton gaskiya ne.
"Ki buɗe baki ki min magana Please... Da gaske kina da aure?"
"Ina da aure...amma... Amma, wallahi"
Sai kuka Minti ɗaya... Biyu, uku, kuka da take yi sosai, gabaki ɗaya ta rasa me zata ce masa, ta jika screen din wayarta da hawayen dake zuba a idonta.
Kenan da gaske ne, tana da aure...,
"For how many years?"
Ya tambaya bayan ya saita kan sa, Yatsun ta uku ta ɗaga masa tana toshe bakin ta da ɗayan hannun.
"3years...!"
Ya furta, ta gyaɗa masa kai tana kuka, ya kawar da ƙwayar idanun sa daga kallon ta.
“Problem... dan Allah kar ka guje ni, ina buƙatar ka a rayuwata, ina son ka.... Ina.... Matuƙar son ka, dan Allah ka fahimta”
Ta furta cikin matsanancin tashin hankali, a yayin da pride ɗinta, girman kan ta, da jiji da kan ta suka yi fiffike suka tashi daga gangar jikin ta, abin da take hangowa shi ne rabuwa da Mohan, wanda take ganin muddin ya rabu da ita jin daɗin ta ya ƙare a duniyar nan.
"Me yasa kika ɓoye min ke matar aure ce?"
Ta ƙara share hawayen idonta, sannan a tace.
"Saboda ina son ka, bana son rasaka Mohan"
“A haka kake so na Zakiyyah?, Can i say Kin munafurce ni ?...!, Idan na ce Kin ci amanar yardan da na yi miki ban yi kuskure ba ko?, Bana so na alaƙanta ki da kalman munafunci, amma You did it, kin munafurce ni"
Zakiyyah ta buɗe idanunwata da ƙyar ƙwalla wata na bin wata, ta shiga girgiza masa kai.
"Ka fahimce ni...."
"Na baki dama Problem, ki faɗi min menene, ki kare kan ki kin ji?, say it, ki kare kan ki"
Kuka take yi sosai kaman ran ta zai fita
"Ba komai ya sa na ɓoye maka komai ba sai dan ina son ka. Zan je Zaria gobe, zan gaya masu ban ƙarbi auren ba. Ina buƙatar ka a rayuwata problem, Zuciyar ka kawai nake buƙata, da zarar ka mallakamin ita zan nuna maka so. Zan nuna maka yanda ake so. Zan koyar da kai so. Zan nuna maka yanda fasasshiyar zuciya kan haɗe ta dawo me kyau fiye da sabuwa. Zan tabbatar da na ƙawata duniyar ka da ƙauna mara gushewa, ni ce farin cikin ka. Ka yadda da ni ko da sau ɗaya ne, ba wani auren gaske bane ka gwada mallakamin zuciyarka ka mu rayu mu kaɗai. Na roƙe ka, Please!”
Gabaki ɗaya ta birkice, ta fita a hayyacin ta, ita kan ta bata san maganganun da ke fita daga bakin ta ba, Mohan ya girgiza kai cike da takaici.
"Na ɗauka ke mutumiyar kirki ce, but fine... Na gode, kin nuna min asalin halin ki, daga yau ba za ki sake ganina ba"
Diff siffar sa ta ɗauke daga fuskar wayar.
*LITTAFIN MOHAN NA KUƊI NE*
Mutane talatin da za su fara siyan littafin za su siye shi a kan farashin #300, duk wanda zai siya daga baya zai biya normal Price #500
*Za'a biya ta wannan lambar 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*
Sai a tura receipt ko shaida ta wannan lambar *09125491597*
Haka zalika zaka iya biya a matsayin katin MTN a wannan lambar *07046627683*
MOHAN IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF ADDICTION INTO AFFECTION.
KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA*
FIRST 30 SUBSCRIBERS WILL BE GOING FOR #300
Pay
*VIA 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*
EVIDENCE TO *09125491597*
YOU CAN SEND MTN CARD SEND To *07046627683*
Be the first subscriber ❤️
NB _Part one is free_
©BINTOU.
Na yi gabas 🚶🏽♀️.
25th december.
[12/26, 6:37 PM] Star: *023*
Ta bi wayar da kallo zuciyar ta na bugawa da sauri. Ya yanke wayar, ya ce ba zata sake ganin shi ba, ita ya zata yi da ran ta.
Hannun ta ya ɗauki rawa kafin ta ɗaga wayar ta tura masa saƙo, hawaye na bin fuskar ta.
"Problem Dan Allah ka saurare ni, ka ɗaga wayata zan maka bayanin komai"
Ta tura masa, kuma a take ta sake kiran sa, sai dai har wayan ya yanke bai ɗaga ba, bata gaji ba ta sake tura masa wani saƙon. Bai duba ba balle ta sa ran samun amsa daga gare shi.
A wannan daren ta tura masa saƙonni sun fi talatin amma babu wanda ya buɗe. Sai dai sanin ta ƙarar da gishirin ta a dahuwar ƙaho, sai ta kifa kan ta a katifan ta, tana jin kamar ta yi tsuntsu ta same shi a inda yake, sai dai ba daman zuwa makka da kare
Yana ganin shigowan kowane saƙo amma me zai ce mata?, me take so ta faɗa masa?, me yasa ta ɓoye masa tana da aure?, duk friendly chats ɗin da suke yi kenan da matar aure yake tare?, ya tuno yanda ya rungume ta a asibiti, not knowing that she belongs to someone else.
Haznunallahu wani'imal wakeel.
Daren ranar yanda suka ga rana haka suka ga dare, musamman Zakiyyah da ta kwana tana kuka, zuciyar ta ɗauke da baƙin ciki that comes in waves, gruelling, stealing appetite and sleep alike. Ta tashi da safe feeling so weak and restless, ba za ta ce zazzaɓi take ji ba, amma sam jikin ta babu ƙwari, sannan bakin ta babu ɗanɗano, idanun ta sun mata nauyi kaman yadda zuciyar ta ta kasance da nauyi. Daga asubah zuwa wayewar gari ta kira wayan Mohan yafi sau goma, amma baya ɗagawa daga ƙarshe ma kashe wayar yayi. Haka suka je class idanun ta a kumbure.
Ajin na su yai tsit saboda shigowar Miss Comassie . Kamar yadda ta saba sai