Showing 39001 words to 42000 words out of 72389 words
kike bani farida, ta yadda aka yi kika yi saken da ya sa Siddiƙa ce za ta rinƙa tsara maku rayuwa ke da ƴaƴan ki, idan ta tsara rayuwar mijin ta ba laifi bane, amma haƙƙin yaran ki ya rataya ne a wuyan ki ,wallahi Farida ki san yadda za ki yi ki ƙarfafi zuciyarki ki ƙwatar wa kan ku ƴanci, nan gaba bamu san me za ta sa shi ya aikata ba".
Farida ta sunkuyar da kai idonta ya tara kwalla, tun jiya ake ta mitan zancen nan, babu wanda ya tuna sanda take kawo ƙarar shi tana roƙon su da su raba auren, amma suka dage kan sai ta bi shi kuma ta yi masa biyayya, mahaifiyar ta har da cewa sai ta tsine mata idan har ta sake kawo karar sa. Babu wanda zai fuskanci halin da take ciki, komai take yi don kada ran iyayen ta ya ɓaci ne, kowa sai dai yace mata sallamammiya ko mara wayau, laifin duk ya dawo kan ta, cewa ake ta kasa kwatar yan cin kanta ta sakarwa Kishiya ragamar gidanta, bayan su ne suka zare mata ƙwarin gwiwan suka sa take zaune da shi da haƙurin dole. Haka suka koma gida rayukan su a ɓace, Daddy ya ce ba zai hana su zuwa Maiduguri ba, kaman yadda babu wanda ya isa ya hana shi nuna ikon sa a kan su, saboda su ɗin dukiyar sa ne, sai yadda ya ga dama zai yi da su.
Haka nan suka cigaba da haƙuri, babu abinda ya canza daga halin Daddy, rashin mutunci da nuna isa sai abin da ya ƙaru, Siddiƙa sai zuba mulki take hankali kwance, don gaba ɗaya ta gama samun kan Daddy tun san da ta san weakness din sa a kan ta yake.
Tun da ya sanar wa Zakiyyah an ɗaura mata aure bai sake tada maganar ba, kuma bata ga mijin ba, hakan ya sa hankalin ta ya ɗan kwanta da tunanin ko sun sasanta ne, an biya su kuɗaɗen su ya sasaketa, shi ya sa ta watsar da batun ta cigaba da harkar gaban ta. A zahirin gaskiya kuma batun aure yana nan, duk ƙarshen wata sai an turawa Daddy kuɗin cefanen amarya, haka da Sallah ma za'a aiko da kayan sallah tare da ƙara jaddadawa Daddy cewan a cigaba da haƙuri sun kusa zuwa ɗaukan amaryar su. Amma ko sau ɗaya kayan basu taɓa zuwa hannun Zakiyyah ba, da zarar an kawo yake rabawa ƴaƴan Sidd, a haka har Zakiyyah ta kammala sakandare, ta samu admission a ABU aka bata pharmacy sai dai rashin kuɗin makaranta ya sa ta yi applying FCE, aka bata bio chem. A shekarar farko aka tafi hutun corona, lokacin ta samu kudi ta canza waya, suna tare da Nusaiba lokacin aka tura masu wani link na portal ɗin College of Nursing ta Whatsapp grp, suka yi applying kaman da wasa sai duk suka samu, aka ba Zakiyyah Basic Midwifery yayin da Nusaibah ta samu Basic Nursing. Wannan kaman wani gagarumin dama ne a gare ta ga shi bata da inda za ta samu kuɗin registration, Daddy ne ya biya ma Nusaiba kuɗin, kuɗin da ya haura naira dubu ɗari. Da ta rasa yadda zata yi, dole ta ɗauko kuɗin da ta daɗe tana ajiyan ta wato sadakin ta, ta biya da shi,sannan ta siya wasu abubuwan da zata buƙata.
Da farko karatun yayi mata wahala saboda biyu take haɗawa, da NCE ɗin ta da Midwifery, ga shi shekarar farko dole sai mutum ya maida hankali wajen karatu saboda weeding ɗin da ake yi, duk matsayin uban ka, ko nawa ka kashe a makarantar kafin ka fara karatu, da zarar ka faɗi jarabawan gidan uban ka zaka koma, sosai karatun ya takura mata, sai ya kasance da ƙyar take samun kudin siyan kayan provision, ta sa karantu biyu a gaba, sana'an da take yi ma yanzu ta daina, gaba ɗaya ta rame ta fita a hayyacin ta. Ana haka Nusaiba ta yi aure bayan sun yi weeding kuma cikin ikon Allah duk sun haye, da haka ta samu sauƙin abin, saboda in nusaiba ta kawo kayan abinci tare suke ci, tun da a yanzu ba dukiyar Daddy na haramun bane.
A wannan lokacin tuni sun zama abokai ita da Mohan, sun yi wani shaƙuwa na ban mamaki, kullum sai sun yi chat, ta dinga tura masa hotunan ta shima yana tura mata nasa, phone call da video calls babu wanda basu yi. Ba tare da ta sani ba ta kamu da soyayyar sa tun bata san menene so ba, a lokacin shi kuma hankalinsa na wajen Nihaal ɗin sa, ta kasa furta masa sirrin zuciyar ta, amma tana iya ƙoƙarin ta wajen ganin ta fahimtar da shi, shi kuma baya fahimtar komai sai soyayyar Nihaal.
Daddy Kam likafa ta cigaba ya daina harkar safarar mata, saboda kudin da sirikin shi ke tura mishi ba ƙaramin kudi bane, tuni ya haɗa da na kasuwancin sa ya gina kan sa. Kuma har a baya ganin ƙiman Farida, baya ganin ta a matsayin mata, kuma ya kasa sakin ta, ya rantse sai dai takaicin sa ya kashe ta, tun da har baya so aka aura masa, to kuwa bata da wani mijin bayan shi. Babu irin sharrin da Zakiyyah bata ƙullawa Mahaifiyar ta ba ganin ya gaji da ita ya saketa, amma ya ƙi sakin ta, ita ma Siddiƙa ta buga ta bari. Har tasha Zakiyyah ta je ta biya samarin kan layi ta shigo da su cikin gidan su har uwar ɗakan Farida a lokacin da ta daidaici shigowan daddy ta ce su cire kayan su suyi kaman su kwaratan ta ne, amma koda ya gan su murmushi kawai yayi, yace su fice masa a gida ba tare da ya ɗauki wani mataki ba. Ana haka mahaifiyar sa ta rasu, bai je Maiduguri ba sai bayan kwana uku da yin rasuwar, saboda lokacin da aka yi rasuwan baya ƙasar ya ɗau iyalan sa duka suka tafi. Gabaki ɗayan su suna zaune a tsakar gida sai suka ji ƙarar faɗawan abu cikin rijiya, ji kake tumbul!, Kafin su ankara Zakiyyah ta zo da gudu tana kururuwa da ihu kamar wata zararriya tana faɗin Siddiƙa ta jefa Ayman cikin rijiya....
Toh fah!.
Na yi gabas🚶🏽♀️
Bintou
13th December, 2024.
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *015*
Maganar ta ta ja hankalin Farida da ke tankaɗen garin tuwo, rariyar hannun ta ya suɓuce, ta yi wajen rijiya da gudu, ta leƙa ta ga ruwan na motsi, ta kurma wani ƙara tare da ɗage ƙarafarta za ta faɗa rijiyar, hankali tashe Zakiyyah da matar yayan ta suka yi azamar riƙe ta kafin ta faɗa, kamar ƙiftawar Ido ta ƙwace kan ta, ta dira gaban Siddiƙa wacce a yanzu ta gama jan ruwa a rijiyar, ta cakumeta da ƙarfi tana cewa
"Kashe shi ki kayi?, Kin kashe shi?, Me yayi miki?, Na rantse da girman Allah se kin bishi"
Nan ta shiga kai mata duka kamar an turota kururuwarta da ihun Siddikan ya janyo hankalin sauran mutanen gidan gaba daya, tuni gida ya dauki hayaniya magana ta yi sama kaman hayaƙi, Siddiƙa ta jefa ɗan kishiyar ta a rijiya, ga shi can Farida ta fita a hayyacin ta sai casanta take tace sai ta kashe ta. Dukan Siddiƙa take babu ji babu gani tamkar ma bata hayyacinta, cewa take
"Wlh sai na kasheki, ku bar ni na jefata rijiyar ta bi shi ita ma"
jibgarta take tamkar Mahaukaciya fuskar ta ya sauya daga kamannin ta, da ka gan ta za ka san ba a hayyacin ta take ba, mutanen da ke ƙoƙarin raba su sun fi biyar amma babu wanda ya iya ƙwatar Sidd, Zakiyyah na tsaye daga can gefe tana kallon su daga inda take sai murmushi take..
Ihun Siddiƙa na neman ceto, da kururuwan Farida tana fadin sai ta jefata a rijiya ne ya janyo hankalin mutanen waje, aka shigo wasu samari suka fara ƙoƙarin shiga rijiyan don ceto yaron. Hankali tashe Daddy da ƴan uwan sa suka taho shi kaɗai ya iya danne Faridan har Siddiƙa ta samu ta kubuta daga hannun ta, shi ma sai da ya samu nasa rabon marin, ita kuma siddika an yi mata jina jina, fuska ta kumbura dan duka tasha ba ta wasa ba.
"Meye haka? Kin yi hauka ne Farida zaki kama ta da duka?"
Daddy ya faɗa yana dafe kuncin sa cikin tashin hankali.
"Wlh ban gama dukanta ba, idan an ga na haƙura to na jefata a rijiya kamar yanda ta jefa min ɗa a rijiya, wayyo Allah.... Aymaaaaaaan!"
Farida ta ƙarasa cikin kururuwa na kuka, da zaburowa yan uwanta suka riƙeta. Cikin rashin fahimta Daddy yace
"Wace magana kikeyi haka? Wane Ayman ɗin aka jefa a rijiya?"
Zakiyyah da ke tsaye a bayan su har yanzu ta dubi fuskar Sidd, duk ta sha yaƙushi da duka ta ko ina, dariya ya taho mata, ta yi saurin toshe baki tana murmushi.
"Ke nake tambaya wane Ayman ɗin aka jefa rijiya"
Farida ta kasa magana don takaici, sai kuka. Jama'an wurin suka yi masa bayanin komai. Ihun kuka da hargowar Farida kawai ake ji a gidan
"Na rantse da girman Allah yanda ta saka min yaro a rijiya itama sai ta bishi babu uban daya isa ya hanani daukar mataki akan wannan abun, ba zan yadda ba"
Taci gaba da sheƙa kuka, Zakiyyah na daga nesa tausayin mahaifiyar ta da dariya na cin ta, amma babu daman nunawa. Mutanen da suka faɗa rijiyan suka fito suka ce ba su ga kowa a cikin rijiya ba, ba ƙaramin hauka Farida ta tayar ba ta shaƙo wuyar Ahmad gam, Siddika na ɓoyewa a bayan shi cikin matsanancin tashin hankali, Ahmad ya janyota jikinsa ya rungume da ƙyar tun tana fizge fizge, har yi luf tana shessheƙar kuka. Zakiyyah ta ja tsaki cikin takaici, ba haka ta so ba.
Yana rungume da ita ya dubi Siddiƙa da kamannin ta suka sauya ya ce me ya faru, Babu tsoron Allah Zakiyyah ta yi karaf ta ce.
"Daddy saboda ta ce Ayman ya jawo mata ruwa a rijiya, shi ne ya ce ba zai iya ba, sai ta kama shi da duka, ta kuma cakumo shi ta jefa shi cikin rijiyar"
Nan kowa na gurin ya fara ɗaɗɗaga kai da cewa tabbas an ji ƙarar jefa abu mai nauyi a cikin rijiya, kuma tabbas yaron na cikin rijiyar, gabaki ɗaya daɗa firgita Sidd suka yi, ta tsure da tashin hankali.
Nusaiba dai ta yi shiru, har ranta bata ji daɗin abin da ƙanwar nata ta yi ba, magana ta gaskiya tun san da Siddiƙa ta fara dukan Ayman suka shiga faɗan, suka janye shi, Zakiyyah ta ce ya gudu ɗakin da ake kiwon awaki, sai Nana ta jefa wani katon dutse a cikin rijiyar, zakiyyah ta shige ciki tana kurrruwan an jefa yaro cikin rijiya.
Daddy ya kalli Masoyiyar sa wacce zama abar tausayi, fuskarta a kumbure ga duka ga uban kukan da ta sha. Cikin tausayawa yana kallonta yace
"Honey I want to hear from you"
Cikin shessheƙa ta fara magana, bakin nan ya ƙara faɗi da tsawo, ko da can ƙatoto ne, kwalliya da yawan zama da make up ne ya hana shi fitowa sai yau da ya ji azaba.
"Baby na rantse Wallahi Allah shi ne shaidata ban yi mishi komai ba. Ni ban ma san ya aka yi ya fada ba, ni wallahi ban san komai ba"
Siddiƙan ta fada cikin firgicewa da dasashshiyar murya me ban tausayi da ka gan ta za ka san ba a hayyacin ta take ba.
"Daddy me ya sami Anty?"
Muryan Ayman ya dakatar da Alhaji Ahmad da ke shirin yin magana. Gabaki ɗaya suka ɗago suna duban sa, har da Farida da ke kwance jikin mijin ta har a lokacin, ta ƙwace da sauri ta rungume shi tana kuka, kowa ya cika da mamaki aka rasa wanda zai yi magana, Ahmad yayi ƙarfin halin fadin
"Siyam daga ina ka fito?"
Ayman cikin rainin hankali ya ce
"Nima ban sani ba... Kawai dai na gan ku a gabana ne"
Maganar ta sa ta fi kama da rainin hankali, ran Daddy a ɓace ya daka masa tsawan da ta firgita shi, ya ƙanƙame Farida da sauri tare da fashewa da kuka
"Daga ina ka fito?"
Cikin kuka ya ce
"Daddy ban sani ba"
Takaici ya cika Daddy, ya ji kaman ya kama yaron da uwar sa Farida wacce ta dakan masa annurin zuciyar sa yayi ta duka har sai ya samu sassaucin abin da ya ke ji a cikin zuciyar sa. Duban Siddika yayi, gaba ɗaya halittar ta ya sauya, ta firgice, ta daku ga fuska duk yaƙushi, ya ciji lips ɗin sa. Ya kama hannun ta yana rarrashin ta, ran sa a ɓace ya ce
"Dama ni tun da na ji na san setup ne, Baby ba zata iya aiwatar da wannan muguntar ba, Farida yaushe kika zama muguwa me baƙar zuciya haka? Meye riban ki don kin ƙuntata mata?, Ji yadda kika ɓata mata fuska fisabilillah?"
Shiru ne ya gifta gurin kallon abin ake kaman Film babu wanda yayi magana, dama babu me son Sidd a gidan, Zuciyar Daddy ya sake harzuƙowa ganin babu wanda ya yi yunƙurin ya bashi haƙuri, ko ya nuna tausayawan sa a kan abin da ya faru, hasali ma kallon Allah ya ƙara duk suke masa shi da Sidd, don haka ya cigaba da magana yana cewa
"Na gaji da wadannan mugayen halayen naki Farida, daman ba son ki nake ba... Kuma kin rantse sai kin rabu da ni''
Yayi murmushi wanda bai da alaƙa da nishaɗi
"Darajar ƙwarya tana ragaya, idan ta sauko ƙasa ta canza suna, kin yi wa kan ki, na ruguza bangona da kika jingina da shi, igiyar da take tsakanin mu, na warware ta"
Ba tare da ya sake furta komai ba ya ja hannun Siddiƙa suka fice, ya bar su da salati da salllallami, Zakiyyah ta ji kaman ta yi tsalle ta girgije don murna....
Tana kaiwa nan a tunanin ta, ta murmusa, ba tare da ta ba shi amsar da yake jira ba, ta kashe datan ta, ta saka wayar ta a Flight mode.
Tunowa ta yi shi ɗin a yanzu mijin wata ne, Zakiyyah sai taji kishi mai yawa ya dabaibayeta musamman ma da ta tuna yadda ta ji muryar sa, babu alaman damuwa a cikin ta.
Hawayen da ya soma gangaro mata ne ta share da sauri ta ɗauko abokin hiran ta, ta soma rubutu kaman yadda ta saba, a duk lokacin da ta tsinci kan ta cikin ƙadaici.
"Ban san cewa zuciyata tana aiki ba sai da na haɗu da kai, ban san cewa ina da zafin kishi ba sai da na fahimci na faɗa tarkon soyayyar ka, ka fahimtar da ni me ake nufi da soyayya, sannan ka sa zuciyata ta fahimci ɗacin in kana so ba'a son ka, kai ɗin jigo ne a gare ni, kuma madubi, ka zame min bangon da idan na jingina a jikin ka ba zan taɓa faɗuwa ba, kai ne mafarin soyayyata, sannan ina fatan in ƙare rayuwata da kai, ina son ka problem ɗina".
****
Idanuwan sa ya shiga kokawar buɗewa, duhu dinɗim wurin yake ta yadda ko tafin hannuwan sa baya iya gani, zuciyar sa ta hau biye salati amma bakin sa ya kasa furtawa. Bumm ya ji ƙara gami da haske a lokaci guda sun mamaye ɗakin.
Kafin ya ari mayafin natsuwa ya saka ya ji ana kwance kakkaurar igiyan da aka ɗaure shi da shi
"Me nayi maku?, Don Allah ku mayar da ni gida"
cikin amo sautin muryar sa ya fito
Bai ɗago ya kalle shi ba kaman yadda bai dakata daga abin da yake yi ba, har sai da ya gama kwance shi, ya ja shi zuwa gaban shugaban sa, ya gurfanar da shi a kan gwiwowin sa.
Kyakkyawar farar fuskar sa mai ɗauke da murmushi ya haska cikin yalwataccen hasken ɗakin. Bakin Daddy ya mutu, ya kasa cigaba da ihun da yake yi, gabaki ɗaya ya sauya daga kamannin sa, sai wari da zarnin fitsari yake yi wuya ta yi wuya firfita da tsinken kwakwa, ya tsotse ba shi da wani kuzari, tamkar matacce ɗaure da riga da wando haka ya kasance, baya ko iya motsawa.
"Professor Ahmad Babban Zakiyyah"
Mutumin ya faɗa da sanyayyar muryar sa yana murmushi.
"Su wanene ku?, Sannan me kuke buƙata a wajena"
Daddy ya furta cikin ƙarfin hali, cikin muryar sa mai kaman dimon girke ya dube shi, fuskar sa rufe cikin face mask yana yatsine fuska, saboda zarnin fitsarin da ke buso masa. Ya nuna kan sa cikin isa da taƙama ya ce
"Na yi maka kama da wanda zai nemi abu a wajen ka!?..."
Daddy ya girgiza kan sa jikin sa na karkarwa, cikin son taƙaita maganar, saboda zarnin fitsarin da ya addabe shi ya ce
"Sunana Dr Hassan,ƴar ka ce ta shiga gonata, na ɗauko ka ne don in nuna mata bata isa ta ja da ni ta zauna lafiya ba, na fi ƙarfin na rama abin da ta yi min a kan ta, sai dai na rama a kan uban ta''
Cikin Daddy ya ɗuri ruwa, tun ranar da ƴan sanda suka dire shi a gidan bai sake ganin haske ba, ɗakin baƙi ƙirin yake kaman cikin kabari tsabar dubu baya iya ganin komai, bai taɓa ganin fuskar kowa ba sai yau, ko abinci za'a ba shi sai dai a buɗe ƙofar a turo masa, a nan yake fitsari da ba haka, duk tashin hankalin da ya shiga a wannan lokacin bai kai wanda ya shiga a yanzu da ya ji kalaman da ke fitowa daga bakin Hassan ba, duk da bai san waccece a cikin yaran nasa ba, amma ya tabbata babu wanda zai iya saka shi cikin wannan mummunar yanayin idan ba Zakiyyah ko Nana ba. Bai gama tunanin ba ya jiyo muryar Hassan ya cigaba da magana, tun da ya ji ya ya ambaci sunan Zakiyyah ya ji komai nasa ya tsaya!
A daidai wannan lokacin bI san me zai ce ba, bai kuma san ta inda hawayen da ke soye zuciyar sa za su fito ba, domin kuwa tun da Hassan ya ambaci sunan Zakiyyahi, ya tabbata dai alƙiyaman sa ne ya tsaya, ko kashe shi zai yi ba zata damu ba, sai a yanzu hawayen da ke soya zuciyar sa suka fara zubowa saman dakalin fuskar