Showing 33001 words to 36000 words out of 72389 words

Chapter 12 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4942

nufa, ta roƙe su da su ɗauke ta aiki ko wanke wanke ne tana masu suna bata abinci, kallon wulaƙanci suka bita da shi, suka ce basu buƙatar ƴar aiki, ta fashe da kuka, ta ce ko goge goge da share share ne, don Allah su taimaketa, yunwa take ji. Shugaban wajen wacce take office ɗin ta a wannan lokacin, ta ji hayaniyan su, ta fito tana tambayan me ke faruwa, Zakiyyah ta faɗi a gaban ta tana roƙonta don Allah su taimaka su bata aiki, yunwa take ji. Matar ta ji tausayin ta, ta miƙar da ita, sannan ta ja ta suka shiga cikin office din ta, ta tambayeta ina iyayenta, Zakiyyah ta tsinci kan ta da cewa Baban ta ya rasu, mahaifiyar ta kuma bata da ƙarfin nema masu abin da za su ci, rabon ta da abinci tun jiya da rana. Abinci aka bata, sannan aka ce gobe ta fara zuwa aiki, zata rinƙa wanke wanke, da serving baƙi daga ƙarfe biyu zuwa ƙarfe biyu tun da tace tana zuwa makaranta. Zakiyyah ta zube tana mata godiya kaman zata mata sujjada.

Sai da ta koma gida ta tuna bata ƙarasa shanyan kayan siddiƙa ba, a hankali take leƙen cikin gidan, gabaki ɗayan ta a firgice take, idonta a zare, ganin babu kowa ya sa ta shigo cikin sanɗa, tana ƙyaftawa mai gadi ido, ya bita da kallo cike da tsananin tausaya wa.

Tana gab da shiga ɗakin ta ji an fizgota da karfi har saida ash hijabi ɗin ta ya yage sosai a wuya, zuciyar ta ta harba da ƙarfi, fitsari ya shiga gangarowa a ƙafarta, Siddiƙa ta murɗa hannunta cikin mugunta, ji kake ƙass, Zakiyyah ta ƙwala ƙaran azaba, bata tausaya mata ba ta wanke ta da wani mahaukacin mari.
Ƙara Zakiyyah ta sake saki ta zame ƙasa tana birgima idanun ta na ambaliyan ruwa. Muryar ta a wahale take cewa

"Don girman Allah Aunty ki yi haƙuri"

Dukan ta Siddiƙa take yi da sanda babu ko digon tausayi a ranta, tana ihu da birgima, amma bata sarara mata ba, ga hannun ta da yayi targaɗe, sai da ta tabbatar ta mata lilissss sannan ta wurga sandar gefe, ta shaƙo wuyar ta tana huci, idanun ta sun yi ja tsabar masifa.

Cikin masifa da mugunta take faɗin
"Keh don kutumar kaza kazan ki har ni zan saki aiki saboda ke tabbatacciyar ƴar iska ce, tsinanniyya, la'ananniya har kina da ƙwarin gwiwar bazar min da kaya a bakin famfo ki yi tafiyan ki?, Tsabar kin mayar da ni ƴar iska ko? to bari kiji in fada miki yasin na rantse da Allah daga yau na sake baki wanki kika bar min a bakin famfo, na rantse sai na sa ki kwana a tsaye, kin ji abin da na faɗa ko?"

eh ta fadi a hankali, idanun ta na fidda ƙwalla jikinta na ciwo sosai, sai dai zafin da takeji a zuciyarta ya fi wanda take ji a jikinta, tana shiga ɗakin ta ta zube ƙasan tiles tana maida numfashi sama sama, idanun ta na fitar da ƙwallan

Shikenan ta zama jaka?, Kenan bata da ƴanci?, yanzu shikenan babu wanda zai kwatar mata yancin ta?, shikenan ita a haka za ta kare rayuwar ta cikin wahala?, Me yasa mahaifin ta ba zai saki mahaifiyar ta ba, ya kore su suje su yi rayuwar su, tun da baya son su?.

Kuka take da tunani kala kala, har aka kira sallar Magrib ta mike hannun ta na zugin azaba, bayan ta idar ta kwanta tana jin ko ina na jikin ta na yi mata azababben ciwo. Mahaifiyar ta ce ta ɗage labule ta shigo da sallama, ta mike a hankali ta zauna tace

"Sannu Maman mu"
Idanun ta suka ciko da ƙwalla saboda yadda ta ga jikin ta ya tashi ta ce
"Dukan ki ta yi ko?"
Zakiyyah ta fashe da kukan da take boyewa ta kwanta a jikin mahaifiyar ta, ta ji jikin nata zafi rau, ta ce
"Jikin ki da zafi, bari na kawo miki magani ki sha, kin ji?"
Cikin kuka Zakiyyah ta ce
"Maman mu ki bar shi, ba sai na sha komai ba, zan ji sauki"
Mahaifiyar su ta ce
"A'a bari na ɗauko miki, ki sha kin ji?"

Ta faɗa tare da miƙewa, ta nufi ɗakin ta, Zakiyyah ta bita da kallo bata jin za ta iya shan wani magani da ya fito daga gidan nan, bata jima ba ta dawo riƙe da maganin, ta ɓalla ta miƙa mata, Zakiyyah ta juyar da kan ta tana yatsine fuska

"Maman mu ba zan sha ba"
Babu yadda mahaifiyar ta bata yi ba don ganin ta sha maganin amma fir ta ƙi amincewa, daga ƙarshe ma sai ta fashe da matsanancin kuka, ita ma mahaifiyarta sai ta fashe da kuka cike da rauni, da tausayin ƴar ta

"kiyi hakuri Zakiyyah, na san komai ake miki a gidan nan ni ce sanadi, amma babu yadda na iya, babu wanda zai fahimce ni, ki yi haƙuri don Allah, ki yi ta addu'a komai na duniya mai wucewa ne, kuma wata ran sai labari"

Zuciyar Zakiyyah ta kara zafi a ranta tace kullum sai ace mata ta yi haƙuri wata rana sai labari har yanzu babu abin da ya canza, rayuwar ta kara taɓarɓarewa take, shin ba za su iya ɗaukan wani mataki ba dan su kare kan su?.

Ranar da wuri ta kwanta cikin azaba da zazzaɓi, ko chatting ɗin da take yi duk dare bata yi ba.
Da safe ta tashi da matsanancin zazzaɓi, amma haka ta jure ta share gidan kaman yadda ya saba, ta yi wankin da ya zame mata tamkar ibada, yau ba za ta makaranta ba, restaurant zata fara zuwa ta yi aiki, da yamma sai ta tafi islamiyya. Babu yadda maman su bata yi da ita ba don ta ci abinci ko kaɗan ne amma fafur ta ƙi ci, ta ce ta ƙoshi.

Ta fito sanye cikin kayan sanyi na riga da wando , hannayen ta zube a cikin aljiihu, kunnen ta toshe da earpiece tana jin waƙa a tarwatsatten wayar ta, fuskar ta babu walwala ko kadan.

Bamm ta ji an ƙwala mata ƙwallo a kai, ta dafe kan ta da sauri tare da juyawa saboda azaban da ya ratsa ta. Jabir da Zayn ke wasa da ƙwallo, dawowan su kenan daga makaranta, da alama an tashi break, don sun saba dawowa in lokacin break yayi, saboda babu nisa tsakanin gidan da makarantar su.

Maimakon yaran su bata haƙuri sai ma ƙoƙarin tureta suke yi, ko a jikin su, Zayn ya sake bugo ƙwallon saitin ta, Jabeer ya zo da gudu, ya ture ta yana faɗin,
"Ke dallah malama matsa mana..."

Ran Zakiyyah ya ƙara ɓaci, dama yau a zuciye take, jira take a taɓata ta yi spark, ta fizgo shi da ƙarfi ta wanke shi wani lalataccen mari.
"Ni tsarar wasan ka ne?, Yaushe raini ya shiga tsakanin mu da har zaka buga min abu a kai sannan ka nemi ka zage ni?, Am I your mate?, Kada ka ƙara!"

Jabeer ya dafe kuncin sa sannan ya fashe da matsanancin kuka yana zagin ta, cikeda rashin kunya yana cewa

"Allah ya isa muguwa azzaluma, algunguma"
Taji zafin zagin da ya yi mata, ran ta a mugun ɓace take kai masa duka ta ko ina, yana kuka yana surfa mata duk zagin da ya zo bakin sa, ita kuma bata bar dukan shi ba da iya ƙarfin ta, tana bubbuge bakin, cikin ƙanƙanin lokaci bakin ya fashe, ya fara jini amma bata daina


Zayn da tuni hankalin shi ya tashi ya shige sashen su da gudu, yana ƙwala kiran Mummy, kusan a tare suka nufo su shi da siddiƙa


Please share😩😩
Comment please.

9th Disamba 2024
Nayi gabas 😎.
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *013*
Zayn da tuni hankalin shi ya tashi ya shige sashen su da gudu, yana ƙwala kiran Mummy, kusan a tare suka nufo su shi da siddiƙa. Siddiƙa na zuwa ta daga hannu ta faska ma Zakiyyah mari har kala biyu tace
"how dare you Black witch?, dama ke jaka ce ban sani ba? Ke ƴar iska ce ban sani ba? Yaushe siddiƙa ta yi lalacewan da Zakiyyah za ta ɗaga yatsa ta daki ɗan ta, ashe ke ƴar iska ce..?"

Cikin huci da jin raɗaɗin marin da Siddika ta yi mata ta katseta da faɗin
"Ni ba ƴar iska bace, kada ki ƙara ki kira ni da ƴar iska, ban yi kala da irin ki ba!"

Mamaki, tsoro, fargaba da firgici haɗi da razana da kalaman da ke fitowa daga bakin Zakiyyah suka sake fusata sidd, jikin ta sai rawa yake gana wani kame kame cikin kamkamba ta sake ɗaga hannu ta wanke fuskar Zakiyyah da mari.
"Ina faɗa kina faɗa?, Ni sa'ar ki ce?"

Izuwa yanzu wasu sabbin hawaye ne suka sauko ma Zakiyyah tana jin kamar ta wanka fuskar Siddiƙa da kyakkwan mari, ta kafata da rinannun idanun

''Siddiƙa wannan ya zama karo na ƙarshe da za ki ɗaga hannu ki mare ni, ni ba jaka bace, tsaf zan rama don na lura ke akuya ce baki gane kawaici ake maki..."

Ta faɗa ranta na tafasa kamar ruwan da aka jona shi a wuta mai 100°c.
Tabbas wanda yake cikin kuttu da zarar ya samu kuttu zai miƙe kafa har ya kishingiɗa, Siddiƙa bata san kawaici Zakiyyah take mata ba a matsayin ta na matar uban ta, shi yasa ta yi amfani da damar fiye da yadda ya kamata, har ta kai ta bango, ta kuma yi forcing ɗayan fuskar ta wanda take ɓoyewa a kullum, ta sa ta rikiɗe ta koma tamkar wata zakanya, tsoro da al'ajabi suka dabaibaye Siddiƙa, ta kasa magana, ita Zakiyyah take ma tsawa? Yarinyar da ko haɗa ido da ita bata yi saboda tsoron ta da take ji?

Tana tsaye da mamaki zuciyar ta na lugude har bata san lokacin da ta fice ba, ta bar ta da mamaki da al'ajabi. Farida da ta ji hayaniyar su tun a ɗakin ta ta fito don ta ba Siddiƙa haƙuri, tana riƙe da autan ta Siyam, tsawar da ta buga mata ya sa ta ƙasa ƙarasowa, Siyam ya fashe da kuka. Kan ta ta nuna da yatsa jikin ta har wani rawa yake yi

"Ni... Ni za'a ci wa mutunci?, Wallahi ba'a isa ba, baki haifi ƴan banzar da zata wulaƙanta ni a gidan mijina ba, ina jiran ƴar taki, duk inda ta tafi za ta dawo ta same ni, koma me ta sha a yau ɗin nan sai ta gane banbancin ruwa da kalanzir, sai ta san ta taɓa wacce ta fi ƙarfin ta, wato kin zugata ta fara jin kan ta kaman wata shegiya ko? har da dakan min ɗa ko?, Hmmm... Hmmm, Wallahi wallahi ina jiran ta sai na banbance mata tsakanin aya da tsakuwa"
Ta qarasa cikin isa da nuna tsananin ɓacin ran ta. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki Farida ta juya ta koma ɗakin ta. Daddy na dawowa ta fesa masa ƙarya da gaskiya, shi kuma ya hau kai ya zauna, sai gab da isha'i Zakiyyah ta dawo gidan, ya kamata da bugu kaman ya samu jaka, amma taurin zuciya irin na Zakiyyah ya hanata ko motsawa balle ta yi ihu, yadda ka san ba mutum ake duka ba, hakan kuma ba ƙaramin tunzura zuciyar sa yayi ba, ya fizge igiyar charger ya shiga dukan ta da shi, duk zafi da azaban da take ji a jikin ta, bata motsa daga inda take ba, idanuwan ta ƙamas suke kaman ƙafaffen rijiya, Farida ta zo ta rungume ta tana kuka bulalan na sauka a jikin ta, sai da ya gaji don kan sa sannan ya ƙyale su, ya fice yana huci. (Kun san dai babu abin da ya kai a ce kana dukan mutum amma ya ƙi yin kuka, hakan ba ƙaramin tunzura zuciyar mutum yake yi ba). Dukan da ta sha a wajen Daddy babu abin da ya sa mata sai ma tanƙwarar da zuciyar ta da yayi a kan Siddika da mahaifin nata, sam ta daina ganin girman su, ko aiki ta sa ta bata yi, kuma bata isa ta mata maganar banza ba, sai ta rama, hakan ya sa ta yi baƙin jini wajen Daddy. Duka da zagin Daddy babu abin da ya ƙara mata sai daɗa busar da mata da zuciya da yayi. Shima Daddy tun yana dukan har ya gaji don kan sa ya daina bugun ta, ko Siddika ta kawo masa ƙararta, sai dai ya bita da addu'ar Allah ya shirya.


Haka al'amura suka cigaba da gudana a gidan, bata yarda ta ci sisin Daddy, kullum sai ta fita ta yi aiki take cin abinci, duk da irin kyawun ciman da ake ci a gidan su, idan weekend ne kuma da sassafe take fita, ta dawo bayan isha'i, neman kudi take ido rufe, ɗan kuɗin da take samu a restaurant din shi take haɗawa ta siya ledar pure water sai ta kai tasha ta siyar, in ya ƙare ta sake siyowa ta siyar, da haka ta tara kuɗi ta fara siyar da lemun gora, ta rinƙa haɗawa da pure water, duk aikin da ta san zata samu kuɗi shi take yi, wata ran ta samu wata ran ta yi asara koda a ce ta fita bata samu ko sisi ba hakan ba zai sa ta dawo gida ta ci abincin da aka dafa ba, komin yunwar da take ji. Zakiyyah tana da wani irin taurin kai irin wanda idan ta kafe a kan abu ko duniya za su taru a kan ta domin sauya mata ra'ayi ba zata canza komai ba, wani irin murɗaɗɗen zuciya gareta, ko mahaifiyar ta ta kan shafa mata lafiya saboda zuciyar su ɗaya da mahaifin ta Ahmad Abdul azeez, duk wahalar nan da take yi ta fita neman abin da zata tun safe ta dawo da yamma babu wanda ya sani, bata bada ƙofan da wani zai fahimci abin da take yi ba, Farida ta ɗauka itama fitan ta fara irin yadda su Imam suke yi don ta guje ma masifan Siddiƙa, ita ko dawowa cin abinci bata yi kaman yadda sauran suke yi, da zaran ta fita sai an gan ta. Da ta dawo take iske an kai mata abincin ta ɗaki ko buɗe abincin bata yi da ta fita take bawa almajirai. In takaice maku, ba abincin gidan kaɗai ne bata ci ba, hatta sutura da takalmanta duk ta kyautar, kafin Daddy ya biya mata kuɗin school fees take biya, idan ya zo biya sai a ce masa ta biya, yayi ta mamaki, koda ya tambaye ta bata ɓoye mai komai ba, ta ce sana'ar sa haramun ne, idan bai sauya ba ba zata cigaba cin abinci a ƙasan sa ba, ba Zata gina rayuwar ta da haram ba, ya duddungure mata kai tsabar haushi da takaici yace
"Shegiyar yarinya mai baƙin hali, kin yi wa kan ki"

Bayan wannan rana ya haɗu da ita a titi tana tallan ruwa cikin shigar maza, babu takalmi a ƙafarta gabaki ɗaya ta jigata, tsakanin uba da ƴa, wani irin tausayin ta ya ji ya kamata from no where, ya fito daga cikin motar sa ya nufota, tana ganin shi ta arce a guje ta bar wajen, daddare bayan ya isa gida ya kira ta yana tambaya ta dalilin da ya sa take talla a titi, bayan babu abin da ta rasa a gida, sai ta ce in dai da haramun zai cigaba da ciyar da su, ita ta tsame kan ta daga cikin iyalan sa, ta yafe ko me zai yi masu, nan ma takaici ne ya kama shi, ya duddungure mata kai yace

"Kya ji da shi, baƙa mai baƙar zuciya"
Abin da Zakiyyah take yi ba karamin ɓata ran Daddy yake yi ba, sosai hakan ke taɓa ƙima da mutuncin sa, ga shi babu yadda zai yi ya hanata, yarinya ce mai shegen kwarjinin tsiya, ga taurin kai, ga shi ba'a isa a hanata abu ta hanu ba, in ka ga ta yi abu to da san ran ta tayi, halayyan Zakiyyah yasa ya ƙara tsanar uwar ta Farida.
A shekaru biyar da auran Sidd Farida da yaran ta sun fita hayyacin su sai ka dauka jinyar shekaramu goma suka yi saboda rama, barin ma Zakiyyah wacce wahalar gidan ya ƙare a kan ta, ta yi baƙi duk da dama ita maƙa ce, amma ta ƙara munancewa, ƙafafun ta sun yi ƙauje hannun ta yayi kanta. Idan ka gan ta dole ta baka tausayi.

Wani irin zama suke yi a gidan mara kan gado, Daddy gaba daya kamar wanda aka sakawa hannu baya shiga sabgar su tsakanin su da shi idan yana dakin Farida gaisuwa ce kuma baya leƙa sashen ta sai ranar da yayi sha'awar kulata a shimfida, kuma yana biyan buƙatan sa yake ficewa, dangin sa da nata sun ɗauke ƙafafun su a gidan tun bayan rasuwar mahaifin Ahmad, tsakanin Farida da iyayen ta sai a waya, ko idan ya ga dama yace su je.

Baya ga wannan idan ka ji yayi magana da ita ko yaran ta to ƙorafin ta Sidd ta kai masa, sai ya zo yayi ta mata fada da faɗan magangani ita kuma bata iya ce masa komai illah ta bashi haƙuri, koda a ce ɗaya daga cikin ƴaƴan ta ne ya aikata laifi faɗan a kan ta yake ƙarewa. Wata irin manafukar matace Siddiƙa, rashin mutunchi da tijara a wajen ta kaman wacce aka zaunar a aji aka koyar da ita. A yanzu da Zakiyyah ta fi ƙarfin ta, da zarar Daddy ya fita, sai ta tasa Imam a gaba ta tara mai kayan wanki, idan ya wanke bai fita ba sai ta sa ya sake wankewa, tun Farida na zuba ido har ta fara magantuwa, ta ce Imamu ba zai sake wanke mata kaya ba, ranar kuwa zagi da tijara babu wanda Farida ba zata ji ba, Daddy na dawowa kuma ta sheƙa masa wata ƙaryar ya zauna a kai a hakan kuma ze zo ya rufeta da fadan Siddiƙa tace tayi mata kaza ko tace mata kaza babu bin ba'asi babu tambayar ya akayi yanda kasan wanda Siddiƙan ta wanke al'adarta ta bashi yasha haka yake shakkarta yake jin maganarta.

Ita kuwa Siddiƙa daman a shirye ta shigo gidan Ahmad, tun kan ya aureta take takun ta, bata tsara wa kan ta zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login