Showing 66001 words to 69000 words out of 72389 words
yayi shi yasa ya haɗa auren.
Anty Saudat ta kasa haƙuri sai da ta zuga Alhaji Naseer ya magantu a kan auren Mohan da Ƴar Zaria, shi ma ya ga dacewan a haɗa su kawai, sai su zauna a sabon gidan sa da ke nan asokoro. Ko kaɗan ran Mohan bai so abin da suke shirin aikatawa ba, ina suke so ya sa ran sa?. Ya fara ji da ƙaddarar da ta haɗa shi da Maryam tukunna kafin a jajibo masa wata wacce ko sunan ta ma bai sani ba.
***
"Alhaji Destiny brought me And Maryam Together, may be we belong to eachother, I appreciate your choice, ƙaddara ce ta sa ka haɗa ni da Maryam, wata ƙila hakan na nufin wata alheri ne, Abba, har abada ina alfahari da zaɓin ka, kuma ko ban fada ba ka san bana son Maryam, Daddy ka san daɗin zama da masoyi, please do not deprive me of my chance to be happy, ka taimakawa rayuwata, ka sama min daman da zan yi farin ciki ko kaɗan ne, help me, a bar batun wancan yarinyar, if you are worried and concerned about me, or about my addiction kar ka damu, i'll be fine eventually, na yi alƙawarin wannan karon na daina shaye shaye, dainawa ta har abada believe me ba zan baka kunya ba"
Alhaji Nasir yace "Muhammad na gaya ma times without number cewa auren ka da yarinyar nan mutu ka raba, yarinyar taka ce, You might think you didn't worth her, wata ƙila za ka yi tunanin ka fi ƙarfin ta, but she'll only hurt you idan halayyan ta basu da kyau, and kai da kake matsayin mijin ta dole ka san yadda za ka bi ka sauya mata halayyan ta, balle ma a binciken da na yi a kan ta ban samu wani aibu nata ba, she's unlike her father, ni kai na ba wani san auren nake yi ba honestly, shi yasa na yi burus da maganar tsawon lokaci, amma baka san dalilin da ya sa na aura maka ita ba, ka sa a ran ka kaine zaka kula min da ita"
Mohan ya ce "Toh Abba...In sha Allah zan yi iya ƙoƙarina wajen ganin na kyautata mata.... Amma ka yi min wata alfarma"
Ya faɗa kan sa a ƙasa, jin Abba bai ce komai ba, sai ya cigaba
"Tun da yarinyar tana na makaranta a kaduna, ni kuma a Abuja zan zauna, ina neman alfarmar ka da a bari sai ta gama makaranta kafin ta tare, kafin nan na yi alƙawarin zan dinga zuwa ina kai mata ziyara a kai a kai don ta san da zaman auren a kan ta"
"Wannan hurumin iyayenta ne ba nawa ba, ka je ki same su ku daidaita idan sun ga za su iya cigaba da ɗawainiya da ita fine, and kuma ina so ka zaɓi ɗaya daga cikin gidajena na asokoro a nan za ku tare"
Mohan ya ɗago kan sa da mamaki, gidajen sa na asokoro ba ƙananun gidaje bane, gini ne masu nauyi, duk gidanjen da suke estate din nan ace sai ya bar gida ya je wani asokoro? Sai kace wata yar zinari?”
“Abba da za'a bi ta shawara na da na ce a zaɓa min gida a estate din nan kawai, ko kuma a gyara min sashena na gidan nan, ba zan iya zama a ƙaton gida irin wannan ba”
Alhaji Naseer ya jinjina kai " Duk wanda ka zaɓa daidai ne, dama duk naka ne., sannan idan an kawo amarya, ka shirya bayan sati ɗaya zaka koma bakin aikin ka, wannan karon zan sa maka matakan tsaro masu tsauri, dan ba zan bar wani hanya da zata sake maidaka ruwa ba"
*Kaduna state College of nursing and midwifery*
Labaran da ke trending a common room a yau
Faifan bidiyon Zakiyyah ya yadu bayan ganin ta da aka yi yau wata tashar da ke Zaria tana tallan soft spot drink.
Da labarin ZEE CHINDOW wacce ta dawo hotel da hot sabuwar motar ta ƙirar Lexus, na yayar ta ne wato mahaifiyar Hassan amma sai ta ce saurayin ta ne ya siya mata.
Akwai wani abu da ke damun mutanen mu, ban sani ba ko ni kaɗai nake nazartan haka, ko kuma saɓanin tunani ne. Idan mutum yayi abin kunya, a wannan lokacin mutane da dama za su nuna ƙyamatar su a kan abin da yayi, a cikin mutanen da ke ƙyamatar shi ba za'a rasa mai tsine masa ba, amma da a ce mutumin zai ɓace na kwana biyu, a daina ganin shi, sannan bayan kwana biyu ya zo da wani abu daban na cigaba wanda ya danganci kuɗi ko wani abin duniya, sai ku ga ana masa kallon wanda rayuwar sa ta cigaba an manta abin kunyan da aka ƙyamace shi da shi. Kaman dai Zee, a ranar da Zakiyyah ta tsige ta a gaban kowa, ta ji kunya, kuma mutane da yawa sun yi Allah wadai da halin ta, har da masu kallon tsabar idon ta suna gaya mata saurayin da take kashewa kudi ya taɓa neman su. Amma a yanzu da ta dawo da babban mota sai aka koma ana mata kallon wacce ta samu ɗaukaka, mutanen da ke ganin kaman ta yi sakarci da har take iya ba wa namiji kudi don ya so ta suka koma suna mata kallon ai ta isa ne, matsayin ta ne yasa take iya bada kuɗi ta nemi soyayya, kuma tana da abin badawa neshi yasa take zuba capacity. Da wannan ƙaryar ta sake kankaro fadan ta a wajen su, ta cusa masu zance cewa Zakiyyahn ƴar talaka ce, hotunan ta da ta sa a ɗauka a ɓoye, da bidiyoyi duk ta yi ta nuna masu, ta ce Zakiyyah bara take yi, kuma sai ta yi aikatau take samu ta ci abinci, shi yasa da ta ga tana ba wa Maleek kuɗi hankalin ta ya tashi ta so a ce ita ake ba kuɗin, shi yasa ta ƙuduri aniyar rabata da shi ta kwashi arziki. Baiwar Allah zakiyyah kina Zaria ana nan ana ƙulla miki sharri.
Kwanan ta uku a Zaria sannan ta dawo, a kwanaki ukun nan bata zauna ba, aiki take yi sosai, so take ta tara kuɗaɗe masu ɗan kauri ta yadda zata jima bata koma Zaria ba, wannan karon ba a iya tasha aikin nata ya tsaya ba, ta yi aiki a restaurant, ta siyar da kifayen ta, sannan har sarin kayan fruits ta yi, ta siyar. A kwanaki ukun nan sosai take iya ƙoƙarin ta wajen ganin ta cire tunanin Mohan a ran ta, duk da tana wahala, dole ya sa ta ajiye wayan ta ta daina amfani da shi tsawon lokacin. Tashin hankali ne a kan ta ƙulli ƙulli, ta rasa wanne zata kama a matsayin zahiri, ga batun auren ta da kullum sai Daddy ya tuna mata, ga tunanin yadda zata yi maganin Hassan don so take ta dakatar da shi daga bibiyan ta da yake, sannan ga Mohan, wanda kewan sa ke takurawa numfashin ta.
Tana dawowa Kaduna ƴan ɗakin su (Mutanen Zee) suka fara zuba mata habaici, kowa na faɗin albarkacin bakin sa, da fari bata fahimci inda zancen su ya nufa ba sai da wata Zubaidah ta fito fili ta faɗi abin da ke ran ta, a nan ta gane cewa Zee ta dawo kuma ita ta fesa masu, to ina ruwan su da rayuwar ta?, Me ta tsare wa wani?, Banza ta yi masu kaman bata ji su ba, ta ɗaura ruwan wanka ta yi wanka, har ta dawo basu bar surutan su ba, a lokacin Zee ta shigo ɗakin, ta kalleta tana yatsine fuska
Ta ce
"An dai ji kunya, dama ke matsiyaciya mabaraciya ce kike son haɗa kafaɗa da ni?, a ƙasƙance aka gan ki a tasha kina ɗaga roban fanta kina roƙon fasinjoji su siya, i regret arguing with you you goat, I downgraded my self..."
Habiba ta yi caraf ta ce
"Ko ni bata isa ta ja da ni ba Anty Ze..."
Wani kallo Zakiyyah ta bita da shi wanda ya sa ta yi shiru ba tare da ta shirya Ba.
"Ke ba da ke zan yi ba, da Zee zan yi"
Zakiyyah ta dubi zee cikin takaici
" kin rasa abin da za ki zaga a jikina, shi yasa kika binciko aikin da nake yi...!, so i gave you work, aikin da nake yi shi kike tunanin zaki zageni da shi?, Abege na taɓa cewa ni ƴar wani ce?, neman halal ɗina nake, idan baku sani ba ku sani ni ƴar talla ce"
Zee ta kwashe da dariya
"Very Dirty of you!, A haka kike so ki haɗa kafaɗa da ni?"
''Zainab kenan ai ni na fi ƙarfin innhaɗa kafaɗa da ke, kuma baki isa ki kalleni ki ce min dirty ba, you need to stop forcing yourself to be like a young girl, because kin riga kin tsufa, Zainab bakya wanka, your skin dirty, panties dirty, mind dirty, your armpit look like a pig mouth, because you are a pig, the dirtiest of them all..."
Sosai common room ya ɗau turiri, aka tara yan kallo, Zainab ta manta haɗuwan ta da Zakiyyah na farko bai yi kyau ba, shi yasa ta shafa'a take tunanin wannan zai firgita ta, wa ke kunyar a san sana'ar sa?, daman da ta samu a zaria ne bata samu a Kaduna ba shi yasa bata talla, amma bata kunyar wani ya gan ta tana talla. Da Zee ta ga Zakiyyah na neman ƙona ta da maganganu sai ta canza salon maganar ta, ta ɗauko wata magana na daban, cikin borin kunya take cewa ai dalili kenan da yasa ta fara bibiyan Maleek tana neman sa har gida don ta yi seducing din shi.
Zakiyyah ta kalli Zee da sharp dangerous eyes ɗin ta, Khadijah ta riko hannunta da sauri sanin how dangerous she can be , idanun ta har sun fara tara ƙwalla , hankali tashe Khadijah tace
" noooo..Dan Allah Zakiyyah, ki ƙyaleta haka kar kice mata komai..na rokeki kiyi hakuri.
Zakiyyah ta mike tsaye a masife tana cewa
"C'mon Khadijah, that's crab... akan me bazan ci uban ta ba?,da namiji na gabana kina tunanin Small boys irin maleek zan bi? Shi asuwa tsinken goge tsuliya? Mtswwww"
Khadijah tace no Zakiyyah,
"Are we not talking about her fooling boyfriend wey him dey beg me to be his fiancé?, Zainab did I told you that the man you are dying to be with wanted me to be his peace but I declined?, I declined a man you cannot buy with money for survival, I'm not thirsty, anytime wey you want dey Comot you go dey wear borrow borrow shoe kill them with lies say you be minister daughter... Hello!,. I don't want cast you, but still that shoe wey you dey borrow if I wan show up I for buy it ×10, or make i show You my shoes, borrowed shoe na wetin person dey use dey show off?, Borrowed car too saboda ina da tabbacin bakida mota ko ɗaya, duk na aro ne And you say you get level, mutanen da ke bayan ki sun ɗauka ke wata shegiya ce, you dey smell, ƙazamiya wari kike kaman takashin kunkuru, ki ji da ciyayin da suka yi gini a hammatan ki tukunna, with your dirty armpit wey pass 1yr you no shave, maƙaryaciyar banza da hofi, You lie any how!, Ranar da kika fara zuwa makarantar nan you come dey say na your papa be the minister for Abuja, ba wanda ya tambaye ki, idan da gaske baban ki minister ne Allah ya tsine min, idan ya kai matsayin da za'a ba shi counsellor ma make i bend , na Zakiyyah You wan dey lie give duk wacce bata yadda Zee ƴar ƙarya bace ta ɗau wayan ta ta bincika jerin ministocin Nigeria, idan akwai something cindo a ciki ku fille ni"
Kunya, tozarci da ƙasƙanci sun rufe mutumiyar, ta ji kaman ƙasa ta tsage ta shige ciki, ta kasa buɗan bakinta ta kare kan ta, kallon ta Zakiyyah take yadda ta yi sululu kaman balam balam ɗin da ya sha wuta.
"Zainab kafin ki taɓa ni ya kamata ki san banbancin da ke tsakanin ƴar tasha da ƴar minister, shekarun ki ashirin da bakwai amma kina nan kina dragging boyfriend talk da 21yrs old child, what a shame, idan ni namiji ne, say you naked Infront of me, I swr I go pursue you go outside, god create you well you turn your self like when person make mistake come cancel am, like rubbish, abege go and hide your self in shammmeeee. "
"Kar ki manta ke ɗin ba kowa ba ce Zakiyyah, rashin ƙaunar ki da ake yi ne yasa aka badake sadaka ga stranger ɗin da ba'a san asalin shi ba"
Maganar ta ƙwala ƙara a kan Zakiyyah, ta yi shiru j in shock najin abin da Habibah take faɗa, ta ina maganar auren ta ya fito?, Ya aka yi suka sani?, Duk yadda aka yi su ne suka gaya ma Mohan, ta tuno ranar da ta iske saƙon Daddy, kafin ta buɗe har an buɗe, kallon Habibah ta yi da mamaki ta ce
"A ina kika ji wannan labarin?" Habiba ta yi shuru tana jan tsaki. Zee ta yi amfani da wannan daman ta fice a hostel ɗin tana kuka
****
Ƙaramin walima aka haɗa don bikin tarewan amarya, duk da ba wani gayyata aka yi ba, iya family ne da abokan arziki wanda ya haɗa har da dangin amarya. An ci an sha, an yi hotuna kala kala, abinci ma sai kalar wanda kake ra'ayi zaka ci, just simple taro ne ba'a yi rawa ba.
Da yawa sun zo daga dangin Ummie da Halima sun zo, saboda Alhaji Batta ya sanar musu da kan shi, hakan ya nuna yana son zuwansu bikin kenan, ciki har da Zainab Cindo, mutumiyar Zakityah da wasu daga cikin yayyin ta, amman daga bangaren sauran matan Alhaji babu su babu yayansu haka kuma babu a wani na su da ya zo. Amma ban yi mamaki ba daman na san ba za su zo ba saboda Alhaji ba saka su cikin lamurran da ya shafi harkan ƴaƴan sa maza yake yi ba.
Misalin karfe takwas na dare aka jera manyan motoci na alfarma a kofar gidan su Maryam kai kana ganin motocin da manyan matan da suka zo bikon amarya ka san gidan ango sun shirya. Haka aka barota da gidan iyayen ta bayan ta sha nasihohi kala kala
A babban falon Ummie aka shiga da ita aka zauna da ita tana sanye da lifaya an rufe kanta da fuskarta.
“Maraba Maraba Maraba”
Shi ne abun da Ummue take ta fada har ta zauna tana kallon inda Maryam ke zaune, hakan ba ƙaramin mamaki ya ba wa mutane ba, don babu wanda yayi tsammanin ganin haske a fuskar Ummie a lokacin da za ta yi arba da fuskar matar Mohan, basu san cewa wannan shi ne dadadden burin ta akan Mohan ba
“ Na gode Allah da ya nuna min wannan ranar Alhamdulillah, welcome to Batta's family....Na damƙa miki amanar ɗana, ki kular min da shi, Ki ji tsoro Allah a kan dukan lamurranki, ki yi biyaya ga mijinki domin shi ne abokin rayuwarki a yanzu kuma shi ne jigonki, ki bi shi sau da kafa neman aljannarki ya tashi daga karkashin kafafuwanmu ya koma gurin mijinki, farin cikin da Mohan ya sani a rayuwa kaɗan ne, ki taimaka ki zame masa farin ciki koda kaɗan ne, na tabbata ko baya son ki ba zai wulaƙanta ki ba, zai baki farin ciki daidai gwargwado.”
Ɓangaren ango kuwa, yanda Abba ya gayyato abokan sa, da yanda yake nuna shi a wajen kowa, hakan ya taka rawa wajen rage masa dakon damuwan da yake yi a kwana biyun nan.
Sai a lokacin yake jin wani kalar farin ciki da be san a muhalin da zai aje shi ba, a lokacin ne wani shaukin auren da annashuwa da zumudi suka same shi. Yayi fatali da lamuran Zakiyyah ganin babu abin da tunanin ta zai haifar masa face damuwa. Duk da kasancewar yana jin motsin wani abu da be san menene ba a bangon zuciyar sa dangane da ita, amma ya zaɓi ya danne ya rungumi zahiri. Haɗuwar sa da Zakiyyah, da tarayyan su duk mafarki ne. Hmm mafarki!☹️😩
Idan fa ka ji namiji na cewa baya son mace ba'a aura masa ita bane, idan ma baya son ta da gaske a ranar angwanci dole sai yayi zumuɗi, barin ma idan hakan ya haɗa da yawan shekarun da ango ya ɗauka bai yi aure ba kaman dai Mohan ɗin mu na gargajiya.
(Malama Fatee, Maman Mukarram, da sister Safiyyah soyayyar da kuke ma auren sa da Zakiyyah ba shi zai hana shi murna da zaɓin mahaifin sa ba, duk da ƙaddara ce ta haɗa su da Maryam, Amma there's a fact that duk wani ango yana ɗokin ranar angwancin sa, i'll not deceive you farin cikin da yake ciki baya misaltuwa)
#TeamMohan anyways💪
Hanyar da dakinsa yake ya nufa yana tafe yana gyara babbar rigar abun ka da wanda bai saba saka manya kaya irin wannan ba. Sai da ya ƙara feshe jikin sa da tutare wani irin yanayi yake jin kansa da bai taba samun kan sa a ciki ba, yanayi ne dabam da yake zuwa sau daya a rayuwar ko wane saurayi da budurwa, mu manta yanda tsarin auren su ya zo, Mohan ba mai riƙo bane, tun da ta kira shi ta bashi haƙuri ya haƙura, sannan ya yafe mata, sannan ganin yadda mahaifin sa ke farin cikin auren ya sa yana farinciki shi ma, har hakan ya saka mishi shauki da ɗokin auren, ya tsinci kan sa a yanayin da kan canja yanayin ango da Amarya tun daga yanayin gari har zuwa na hallita da mu'amala da kuma na iskar da aka shaka, ya kuma haskaka rayuwar su da wani haske wanda babu duhu a cikin ta.
Duk wacce ta ji haushin farin cikin da Mohan yake yi, ta zo ta dakeni ina Zaria 😜🏃🏽♀️
*LITTAFIN MOHAN NA KUƊI NE*
Mutane talatin da za su fara siyan littafin za su siye shi a kan farashin #300, duk