Showing 48001 words to 51000 words out of 72389 words
da ta gani a tare da shi ita ce matar sa, idanun ta ya ƙara hasko mata yanda take ƙoƙarin shiga jikin sa tana ba shi tea, zuciyarta ta matse da wani irin kishin mai tsanani, ,tsanar Maryam ta cika mata zuciya lokaci guda.
Ficewa daga ward ɗin shi ne daidai a kan ta koma ciki, don a yadda take jin kan ta komai zai iya faruwa idan har ta sake haɗa ido da Maryam, idan na ce komai ina nufin komai, zuciya zai iya diban ta ta shaƙe Maryam har sai ta daina numfashi, ko kuma ta rufeta da duka har sai ta nakasata, tunanin ta ya tsaya a lokacin da ta ji sautin takun ƙafafu ta bayan ta, sautin da ya taho tare da bugun zuciyar ta, ta shaƙi daddaɗar ƙamshin da take da tabbacin ba na Ibrahim bane, kafin ta gama tantance irin tasirin da ƙamshin ke dasawa a cikin jinin jikin ta, ta ji an dafe kafaɗun ta duka biyun, ana ƙoƙarin juyo da ita.
Jikin ta ya shiga rawa a take lokacin da yayi nasaran juyo da fuskan ta suka fuskanci juna, duk wata jijiya ta jikinta ya shiga juyawa a take, tunanin ta ya ɗauke sannan wani abu ya shiga hurawa a jinin jikinta, yadda hannayen sa ke dafe da kafaɗun ta kaɗai yasa tunaninta hargitsewa, zuciyarta ta shiga bugawa a cikin ƙirjin ta sannan ƙafafunta suka shiga rawa ta yadda duk da yana riƙe da ita, ya dinga jin kamar zata faɗi ta baya ya sake riƙeta sosai yana kallon yadda taƙi yadda ta haɗa ido da shi, kuma hawayen ta basu bar sauka ba.
"Ina glasses ɗin ki?"
Ya furta da murya mai taushin da shi kan sa bai san yana da shi ba.
"Yana hostel"
Ta ba shi amsa kan ta a ƙasa tana share hawayen ta.
"Why are you crying?
Ya faɗa a hankali yayin da hannun sa ke ƙoƙarin share mata hawayen, ta yi shuru tana jin kaman za ta ɓace saboda emotions ɗin da ke circulating a cikin jikin ta. Ya riƙo hannunta yana faɗin.
"Mu je ki gaisa da amaryata...."
Ji ta yi tamkar ya soka mata _*Wuƙa a zuciya_ sai tayi ƙarfin halin girgiza kanta tare da ƙwace hannun ta, kaman ƙiftawan ido ta fice daga ward ɗin tana kuka sosai, ya bi bayan ta da sauri. Ibrahim da Maryam suka tsaya kallon ikon Allah, inda Ibrahim ya faka motar sa ta ja ta tsaya, ta kifa kan ta a jikin motar tana share ƙwallan da ya kasa tsayuwa a fuskar ta. Kamar a mafarki, sai kawai ta ji ya jawota ya wani rungume ta, tun da take a rayuwa namiji bai taɓa rike koda hannun ta ne da sanin ta ba, ko ɗazu da Ibrahim yayi ƙoƙarin taɓata sai da ta yi masa kallon gargaɗin da ta san ko gobe ba zai ƙara kwatanta hakan a gare ta ba.
Ta kwantar da kan ta a jikin sa tare da lunshe idanun ta sakamakon shaƙar daddaɗan turaren sa da ta ke, zuciyarta ta matse a take, wata irin matsewa da taji kamar ansa igiya ne an daure zuciyar, ta manta da komai, ta manta a inda suke, ta manta kamewan ta da zamowan shi ba muharramin ta ba, ta sa hannu ta rungume shi da kyau tana sakin kuka mai sauti, nauyin da take ji a zuciyar ta na raguwa, shi kuma ya shiga rarrashin ta, yana bubbuga bayanta a hankali, bai san dalilin kukan ta ba amma ya san shi ne sila
Murya kasa kasa yace
"I'm sorry Problem...., My candy....., My crush, share stop crying.... If you keep crying you are not the strong girl I have been crushing on, yarinyar da na sani bata kuka, ko ni ma so kike na yi kukan uhm?"
Kan ta na jikin sa ta girgiza masa kai. Ya ɗago fuskar ta yana kallon yanda ta ƙi yadda ta haɗa fuska da shi ya ce
"Kin fi kyau a hoto problem..."
Ta turo baki haɗi da ture shi tana yatsine fuska dramatically
"Ni ka sake ni...warin taba ma kake"
Yayi saurin shinshinan kan sa, ya ce
"Ƙarya kike wallahi.., turaren da na mannna miki har kayan ki su tsofe ba zaki daina jin ƙamshina ba"
Ta harare shi
"Sai ka ce turaren aljanna?"
"Turaren aljannan duniya mana"
Ya faɗa yana ɗage mata gira ɗaya, itama ta kwatanta yin haka amma ta kasa, suka yi dariya a tare, yasa hannu ya gyara mata ɗankwalin ta da ke neman zamewa
"Mai ƙaton goshi, you need to go to the hospital for the forehead reduction"
Ta dafe goshin tana ɓata fuska
"Is it that big?"
"Meye haka Muhammad?"
Da sauri Mohan ya juyo, ganin Ibrahim ya sa wani sahihin murmushi ya bayyana a fuskanshi yace
"Khalilullah, ashe tare kuka zo, ban ma lura da kai ba fa..Bismillah. mu koma ciki"
Ya faɗa yana nufar Ibrahim that is Looking sad and frustrated, idanun sa sun kaɗa ga kishi da ya tokare shi, duk yanda ya so yayi maintaining mood din shi ya kasa, sai da ya yi loosing temper din sa dan sosai ran sa ya baci, ya ga lokacin da Mohan ya rungume ta da kuma irin dariyan da suke yi, shekaran su ɗaya da watanni yana soyayya da Zakiyyah amma zai iya ƙirga so nawa ta taɓa yi masa dariya, sai dai murmushin yake da take yawan yi kaman ana mata dole.
"Mtswwww..." Ya dubi Zakiyyah wacce kunya ya dabaibaye ta "Ke, shiga mota mu tafi", Mohan ya dube shi da mamaki, kafin yayi magana har Ibrahim ya bude motar sa Zakiyyah ta shiga, dama itama daman da take jira kenan don Allah ya ji ya gani, ba ta jin zata iya haɗa ido da matar Mohan, Mohan bai ankara ba ya ji tashin motar Ibrahim a fusace ya bar harabar, yana baɗe shi da ƙura. Da ƙyar ya ɗaga ƙafan sa ya shige ciki zuciyar sa cike da tambayoyi da dama, me yasa Ibrahim zai yi masa haka?, daga zuwa ko zama bai yi ba sai ya koma?, ya zauna gefen gadon sa ya kama kan shi cikin damuwa, muryar Maryam ta dawo da ahi duniyar da yake inda take cewa
"Baby...Wacece yarinyar nan?"
Ba tare da ya dubeta ba ya ce
"Maryam ki tafi don Allah..."
Maryam ta dube shi da rinannun Idanun ta tace
"Babu inda zan tafi sai ka gaya min wacece wannan yarinyar"
Ta faɗa a ɗan tsawace, ya harareta
"Kin ga Please don't shout here, ba'a ɗaga murya a nan ɗakin... Just go Out of here"
Maimakon ta fita kaman yadda yace sai ta yi tsaye a kan sa tana zage zage da ɗaga murya.
"Keh..kin haukace ne?"
Bashir mutumin da gadon sa ke nan kusa da na Mohan ya faɗa cikin fusata yana tasowa kaman zai hau ta da duka
"Are u insane?.... An gaya miki nan wurin gurin hayaniya ne?, Get out"
Yayi maganar yana ƙoƙarin tureta, da karfi Maryam ta ture shi , gaban ta na faɗuwa dama an ce mata duk mutanen ward din mahaukata ne, ga shi ta yi gamo da ɗaya, cikin ƙarfin hali itama ta birkice masa da masifa a tsawace ta ce
"i am not mad, kai ne mahaukaci, "
"Nurse...!,, Doctor!, Two fighting"
Ƙaramin cikin su Abdullahi wanda shi ma gadon sa ke gefen na mohan ɗin ya ƙwala kiran Nurse cikin neman agaji, kuma ba tare da ɓata lokaci ba mutanen ɗakin suka taru a kan su suna kallon drama, Maryam ta wanke Abdullahi da mari mai zafi cikin jin tsananin takaicinta hade da wani irin tsananin bakinciki ta cakumo shi masifa na cin ta.
"Na fi ƙarfin in yi faɗa da ku...!, Wai kun manta a inda kuke ne?, Psychiatric aka kawo ku fa, asibitin mahaukata, saboda shaye shayen da kuke yi, ku mahaukata ne"
Abdullah ya dafe kuncin sa, Bashir ya ce
"Kika mare shi?, Kin san ko shi waye? You re calling troubling upon urself, kina kiran ma kanki bala'i!"
Basu gama rufe baki ba, Abdullahi ya yi tsalle ya wanketa da mari, kuma nan take faɗa ya kaure a tsakanin su, Mohan na kwace ko ɗagowa bai yi ba, baƙin ciki da takaicin halin Maryam ya cika sho ya rantse ko kashe ta za su yi ba zai ɗago ba, ko ma me suka yi mata ai ita ta ja, wata ƙila in sun gyara mata zama za ta koyi kame kai ta daina shisshigi.
Mutanen ɗakin da dama ƙiris suke jira su hau mutum da duka, ko shi da yake kwana a cikin su takatsantsan yake da su, sosai yake gudun fitina, da ƙyar likitocin wajen suka ƙwaceta bayan sun kumbura mata fuska, ta bar asibitin tana kuka da ɗaukan alwashi kala kala a kan Mohan da mahaukatan patients ɗin.
***
Gudu yake yi a mota fuskan sa a murtuƙe, Ba ba karamin tsorata Zakiyyah tayi ba kam, dan wutar bala"i ta gano kuru-kuru cikin idanunsa da kan fuskarsa. Tun da ta shiga motar bai ce da ita komai ba, sai ma hucin bala'i da yake fitarwa. Haka kawai sai ta ji ba daɗi, dole ya ji wani iri ko ita da Mohan ya rungume sai da ta ji wani iri ballantana shi, ya kamata ta ba shi haƙuri ta wanke kan ta ko kadan ne , cikin rarrashi kira sunan sa a sanyaye ta ce
"Babe. .. ka yi haƙuri, it's not what you are thinking"
"Zakiyyah....!"
Ya fada cikin karajin da ya sakata zabura. Ya taka burki, cikin wata irin birkicewa da bata taba fuskanta da ga gare shi ba ya ce
"Fita min a mota...."
Cikin tsoron da bata bari ya bayyana a fuskan ta ba tace
"Babe please kada ka min haka, ban fito da jaka ba..."
"Wihy idan baki fita min ba sai na kwashe fuskarki da maruka. Ƴar iska kawai, ki barni na ji da abinda ya isheni out please".
Ba karamin tsorata Zakiyyah ta yi ba, ta buɗe motar ta fice, ya ja wani shegen wawan tsaki da raka bayanta da harara ya ce,
"Tinkiya kawai, munafuka"
Ta ji zafin zagin har cikin ran ta, a kan me zai dinga ɗirka mata wannan munanan zagin sai ka ce ya kamata tana aikata wani abin?, Just because ya hug gan su sun yi hug ba shi zai sa ya zageta ba, Don ta rungume Mohan ma sai me?, Idan ma wani abu ya kamata tana yi da Mohan ɗin bai kamata ya ɗau zafi haka ba. Mohan ne wanda a sanadiyar sa ya gan ta har soyayya ta ƙullu a tsakanin su. Don haka bata ga laifin abin da ta yi ba, tafe take ita kaɗai sai jera tsaki take yi, tafiya take a gefen titi ko juyowa bata yi ba, ta yi nisa sosai ta ji ana danna horn a bayan ta, da fari ta yi tunanin ko Ibrahim ne, hakan ya sa bata juya ba, don ita ma yanzu haushin sa take ji, sai da mai motar ya sha gaban ta, ya fito sannan ta dakata tana duban sa da mamaki.
"Ƴan mata kaman na so na ganeki ko?"
Ta yi murmushi, idanuwanta na yawatawa a kan kyakkyawar fuskarsa.
"Ban san ka ba"
Ya ce
"Ni kuma na san ki, room mate ɗin Girlfriend ɗina Zee Chindo"
Ta gane shi dama, saurayin Zee ne wanda take matuƙar ƙauna, ba wani mai kuɗi bane, in fact ita take masa spending, hatta motar da yake hawa ita ta siya masa, layin yayi shuru kuma bata fito da kuɗi ba, hakan ya sa ko da yayi mata tayin hawa motar da bata musa ba, ta hau ya kai ta har gaban hostel yana jan ta da hiran Zee, yana sauketa ta yi masa godiya ta shige hostel, hankulan mutanen da ke kai kawo ya koma kan su, duk makarantar babu wanda bai san cewa Abdul Maleek saurayin Zee bane, saurayin da aka yi wa ƴan mata da yawa jan kunne a kan sa, saurayin da a dalilin shi aka yi faɗan da ya girgiza Admin ya gagare su har ta kai ga nursing council sun saka baki....
Tana shiga ɗakin su ta tarar har ƴan ɗakin sun dawo, alwala ta yi, ta yi sallah sannan ta ɗora girki ta dafa taliya, tana jin suna maganganu ƙasa ƙasa amma bai dameta ba, saboda magana in har ba'a sakota a ciki ba, bai cika damun ta ba, ta soya mangyaɗa, ta ɗebi taliyan ta ɗauko yaji ta haye gado zata fara ci Zee ta shigo kaman an jefota tana masifa kaman zata haɗiye ɗakin, tana poly aka kirata a waya aka ce an ga saurayin ta ya sauke wata yarinya a hostel, babu shiri ta dawo..
"Na rantse da girman Allah yau sai an ga tashin hankalin da ba'a taɓa gani ba a makarantar nan, sai na kashe ƴar iskan in ya so nima a kai ni prison, Mabaruka mu je ki nuna min wace shegiyar ce ke wasa da rayuwar ta, mu je ki nuna min asararriyar da ta zaɓi ta kashe rayuwar ta a kan a zauna lafiya...."
Zakiyyah na jin ta, amma ko a fuska bata nuna ta san tana yi ba, abincinta take ci hankalin ta a kwance, tana shaƙar daddaɗar ƙamshin turaren Mohan da ke manne da jikin ta, tana tuna kyakkyawan fuskan sa a lokacin da yake mata daddaɗar murmushin sa mai tsada. Can ƙasa Habibah ta ce "Hmm Zee ai ba sai kin tada hankalin ki ba, yarinyar da kike nema na nan ɗakin don ko nima na gani da idona"
Zakiyyah na shirin kai loma baki ta ji an kwaɓe shi, ya zube a kan katifarta, ta ɗago da mamaki murnushin fuskar ta na ɓacewa, Zeee ta sakar mata ruwan sanyi a fuska
Zakiyyah ta miƙe a zabure, numfashin ta na sama sama, saboda tsananin sanyin ruwan.. Sama sama take jin muryar Zee a cikin kunnen ta tana masifa, amma bata iya tantance me take cewa ba, sai lokacin da ta hango ɗagawar hannun Zeee da niyyar sharara mata mari, ta riƙe hannun kafin ya sauka a fuskar ta,, ta sa ɗayan hannun ta share ruwan da ke fuskar ta. Ta sarke fararen idanun ta a cikin na zee wanda ya sauya kala zuwa dangerous red.
Zakiyyah bata ta cika magana ba, koda zaka zageta idan har baka taɓata ba ba zata tanka maka ba, don ta riga ta yi experiencing cin mutuncin da ya fi kowane irin zagin da wani zai yi mata, rashin son maganar ta ya sa ake cewa she is rude, amma rudeness ɗin ta baya fitowa sai ta buɗe bakin ta after a thousand silent ta yi magana. Da ƙarfi ta wancakalar da hannun Zee da ke huci kaman wata kumurci...
"Don't even dare try it...!, Ban yi lalacewan da wata ƙazama zata ɗaga hannu ta mare ni ba, ba minister ba, ko President ne uban ki baki isa ki mare ni ina kallo ba!"
Ta taɓe baki tana kallon Zee da ke huci, gabaɗaya ta firgice don jaraba da tashin hankalin da ta sa wa kan ta,cikin takaici ta ce.
"A kan namiji kike wannan haukan? Namijin da ma ba son ki yake ba?"
Idanun Zee suka zare cikin firgici, Zakiyyah bata bata daman furta komai ya cigaba da faɗin
"Eh...Hope say you know say na pity make this guy date you, da fatan dai kin san tausayi ne ya sa yake son ki?, Abdul Malik ba son ki yake yi ba, tausayin ki yake ji, kuma ke ma kina sane da hakan, don kina ba namiji kudi a lokacin da ba shi da shi ba shi yake nufin zai tursasawa kan sa soyayyar ki ba, likeee today wey your guy carry me for him moto this guy dey look me lostfully, he loose focus, I come dey shame for una, yanda mutumin nan yake kallona a lokacin da ya ɗaukeni a motar ki har tausayin ki na ji kodai bai san ni course mate din ki bane?, at least koda a ce shi mara kunya ne shi ya kamata a ce ya baki girman ki kodan ne, atleast he should give you that little respect!, Seee ehn, I hate way woman dey disgrace her self, I hate am, it irritates me, na tsani yadda wasu matan suke zubar da mutuncin su a kan namiji, abin na matuƙar bani takaici, saurayin ki ya ɗauke ni a mota, maimakon ki tare shi ki tambaye shi me yasa?, Kin zo nan kina neman fitina, You come here come dey find trouble with me, ɗaukana a mota da yayi babu wani sirri naki ki bai buɗe min ba, ina gaya miki ne don a yanzu na san wacece ke...!"
Ta faɗa tana kafe idanunta a cikin na Zee with a dangerous smile on her face
"This is what happens when you have given up on yourself as a lady, maganin ku kenan, You feel say if this man leave you no man can love you the same, gani kike kaman idan ya bar ki ba zaki iya samun kamar sa ba, kin yi tarayya da mazaje kala kala kafin ki tsamo irin sa, how can you defend a cheat man like that!, Are you not ashame of yourself? Baki ji kunya ba?, Can you imagine!,
Yau na yi longest chapter, na jiya na haɗa da na yau😎😎
*A zo a siya Littafi kafin farashi ya tashi*
*A zo a siya littafi kafin farashi ya tashi!😒*
*LITTAFIN MOHAN NA KUƊI NE*
Mutane talatin da za su fara siyan littafin za su siye shi a kan farashin #300, duk wanda zai siya daga baya zai biya normal Price #500
*Za'a biya ta wannan lambar 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*
Sai a tura receipt ko shaida ta wannan lambar *09125491597*
Haka zalika zaka iya biya a matsayin katin MTN a wannan lambar *07046627683*
MOHAN IS AN INTRIQUIENG EMOTIONAL STORY OF ADDICTION INTO AFFECTION.
KINDLY SUBCRIBE @ *500 NAIRA*
FIRST 30 SUBSCRIBERS WILL BE GOING FOR #300
Pay
*VIA 9122107940*
*ZAKIYYAH ISHAQ OPAY*
EVIDENCE TO *09125491597*
YOU CAN SEND MTN CARD SEND To *07046627683*
Be the first subscriber ❤️
NB _Part one is free_
©BINTOU.
Na yi gabas 🚶🏽♀️.
16th December.
[12/21, 6:52 AM] Star: *019*
Da an yi magana ki ce kin dogara da kuɗin da kike ba shi, shi namiji idan manemin mata ne ko ke uwar sa ce sai ya ci amanar ki, kin damƙa yaddan duniya kin ɗaura a kan sa, kin ɗauka ke kaɗai yake kulawa, kina bin shi duk inda za shi ne?, a yanzu da na