Showing 3001 words to 6000 words out of 72389 words

Chapter 2 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4952

A takaice dai Zakiyyah mace ce iya mace, sai dai kayan da ke jikinta sun banbanta da na sauran mata asalima riga da wando ne a jikinta, Tana sanye cikin farar Longline T Shirt mai fadi da kuma tsawo sai bakar wandonta Cargo kanta yane cikin siririyar ba'kar mayafi, a saman mayafin ta 'dora wani katon hulan sanyi, bayanta goye da jakar makaranta, don tun da ta dawo daga kaduna ta yada zango a tasha, ko gida bata le'ka ba. A tsaftace take ta yanda kana iya ganin karin gugan kayan dake jikinta.

'Karar wayarta ne ya katse mata sautin da take sauraro, ta 'daga ba tare da ta damu da duba wanda ke kira ba, don ta san babu mai kiranta a wannan wayar in ba Khadijah ba.
"Kawata ina kika tafi?, na duba 'dakinku ban ganki ba, ki sauko mu je karatu"

Muryar Khadijan ta fito ta cikin wayar a lokacin da take 'kokarin saukowa daga stairs din da ya kaita 'dakin su Zakiyyah,a nan hostel din makarantar su.

"Ke na tafi weekend"
Zakiyyah ta fa'da a takaice.
"Weekend....?, Bura'uba ne, muna da test fa, ko kin manta ne?, kodai wasa kike yi 'kawata?"

"Ba wasa bane ina Zaria"
Wannan karon a dake ta yi maganar, wanda hakan ya tabbatar da gaskiyar da ke cikin muryarta.
"Kin san muna da test din Foundation, kuma kin san Malama Bilkisu bata makeup, ga Rubben ma ya bada note shi ma ran tuesday za mu yi test na part din shi, ga littafinki a hannuna sai ki kama hanya ki tafi Zaria?"
Fatar goshin Zakiyyah ta ɗan tattare cikin layi biyu.
"Ina ruwanki da rayuwata?, Ina ruwanki?, Ke kike biya min kudin makaranta?, ki 'kyale ni in na fadi ba ke zaki maimaita min ba, ki yi karatunki ki bar ni please"
Cewar Zakiyyah, muryarta a dan zafafe don har ga Allah ji tayi Khadijan da neman shiga rayuwarta, da yike khadijan ma ba kanwar lasa bace tuni ta hau nata layin ta hau surfa masifa.
"Wa ya damu da rayuwar ki?, ke kin dauka kina da rayuwa ma?, Ina rayuwar taki take? in kin ga dama ki tare a zarian kada ki dawo , shegiya mai ba'kin hali"
Cewar Khadijan, muryarta na shaida 'bacin rai, kuma bata jira ta 'kara jin cewarta ba ta katse wayar. Itama Zakiyyan tsaki ta ja, ta yi resuming track dinta, ha'di da 'kure volume, ta cigaba da tafiyarta a gefen titi.
Ba zata wata mota ƙirar Bugatti Centodieci baƙa wuluk mai baƙin tinted ta fallatsa mata ruwan da ke ƙasan kwaltar, nan take farar shirt din jikinta ya ɓaci, har fuskarta sai da ruwan ya fallatsa mata, dagowan da zata yi, sai 'kasa ya shige mata cikin idanu.

   "Wayyo Allah nah!" Ta faɗa cikin raunanniyar muryarta hannayenta saman fuskarta tana goge idon da tafin hannunta.

    "Malam baka da hankali ne?!"
Ta ji muryar wani dattijo ya faɗa da ƙarfi, da alama lamarin da ya sameta makamancin shi ne ya same shi shima. wanda hakan ya sa mamallakin motar ya taka wani wawan burki, kana yayi reverse ya dawo da motar sa baya, ya mur'da sitiyarin motar da ƙarfinsa ya sake fantsala musu wani ruwan, sanan ya daɗa yin gaba yana ƙara juya bakaken tayoyinsa a cikin ta'balin ruwan, ta yadda zai 'bata su da kyau. Ruwan ya jiƙe musu kaya sosai ya kuma ɓata musu jikin su gaba ɗaya, farar shirt din Zakiyyah har ya fice a kamarsa, ya koma kamar ta yi birgima a ƙasan ruwan. Dattijon nan wanda a 'kalla zai haura shekara sittin da biyu ya shiga surfa masa ashar cikin'bacin rai.
    "Amma wannan yaron an yi tsinanne daga gani ba gidan tarbiyya ka fito ba, Allah ya tsinewa iyayenka da basu yi addu'an saduwa ba suka yi tsiron tofin alatsine suka haifo mana masifa da bala'i, ina amfanin haihuwar asara?."
Har a lokacin Zakiyyah na tsaye inda take kaman an dasata kuma bata daina goge idonta ba, don dama tana fama da ciwon ido tsautsayi ya aa ta baro gilashin ta a hostel.
   A hankali mammalakin motar ya buɗe murfin motar, sai da ya ɗauki tsawon wasu daƙiƙai sanan ya zuro da kyakkyawar farar ƙafarsa, da ke ɗauke da baƙin takalmi rufaffe a cikinta, a hankali ya fito gaba ɗayansa, cikin farar T shirt din da ta bi jikinshi , sai baƙar P,cap da ke kansa, da kuma agogon da ya ke saƙale a hannunsa shima baƙi ne.
  Fuskarsa na sanye da farin gilashin da ya ƙawata mata kyau. Duk inda ake kiran abu mai kyau to wanan matashin saurayin ya kai har ya wuce.
  Fuskarsa a ɗaure tamau babu alaman annuri a cikin sa, da izzarsa ya tako inda dattijon yake tsaye har a lokacin bakinsa bai bar furta duk munanan maganganun da ya fado masa ba, gaba daya kaff dangin matashin babu wanda ya bari, sai da ya zage su tasss.
A gaban dattijon ya tsaya yana bin SA da kallon 'kyama, ya tattaro yawun bakinsa ya tofa masa a fuska. Fuskar dattijon ya yamutsa cikin gigita.
  "Kai wanene a garin nan da zaki min 'daga min murya?, Ka san su waye iyayena?, me suka yi maka da zaka zage su?, in banda iyayi ma me ya kai talaka bin hanyar mota,?"
Ya faɗa cikin dakakkiyar muryar sa da ba kowane namiji yake mallakan irinta ba, tsabar kaushi da gar'di. Shiga sabgar da bai shafeta ba banata bane, haka ko kashe dattijon zai yi a gabanta, matukar ba zai shiga harkarta ba, ba zata tanka ba, amma ya ta'bota ne, kuma ya nuna kaman bai san da wanzuwar ta a wajen ba, hakan ya sa ta magantu.
"Bawan Allah meye haka?"
Sai a sannan ya lura tana tsaye a wurin hannunta na sosa idanunta har yanzu, yanda ruwan ya 'bata mata kaya, ba'kar fatarta da kuma yadda take sosa idanunta suka ha'du suka saka mata matsanancin tsana da kyankyaminta a lokaci guda, zuciyarsa ya tashk tsabar kyan'kyami ya ji kaman zai yi amai, wani irin gigitaccen tsawa ya daka mata.
"What the fuck...Keh...!, 'bace min da gani!, karki sa in yi ama..."
   Difff sautin bakin sa, da amon da ke shiga kunnuwansa suka dakata, domin shifidan yatsunta da ya ji a dakalin fuskar sa, ha'di da gilmawan wuta ta idanunsa. Da ace 'kafafunsa dasu rike shi ba, babu abin da zai yi masa shamaki hantsilawa.
   Bin fuskarsa ta yi da kallo da fararen hannunsa ke riƙe akan kuncinsa, mamakin da ta gani da kuma furgici bayyane a fuskar sa.

  "kwaltan titin na ubanka ne?, idan na ubanka ne ya zo ya hanamu bi, ba sai ya aikoka ka wulakanta masu bin hanyarba, ka gayawa uban naka ya zo ya liƙa allon sanarwa akan hanyar ya tantance ku ku iyalansa ku kaɗai zaku bi ta kanta.... Baka da tarbiyya samm wlhy, baka da shi."
  Taja dogon tsaki, tayi gaba tana dafe jakar bayanta ran ta a jagule, shi kuma kaman an dasa shi, ya kasa 'kwa'kwarar motsi, ya bita da idanu zuciyarsa na tiriri. Dattijon kuwa babu abin da yake fadi sai hamdala yana Kara da cewa, Allah ya saka min, ya ha'daka da daidai da kai''

Tayi taku goma, sai ta ja ta tsaya tana Kallon farar shirt 'din jikinta yanda ya 'baci da ruwan dau'da, ba zata iya 'karasawa cikin gari da wannan kayan ba, duk da ba damuwarta bane ko an ganta da jikakken kaya, ba damuwarta bane maganar mutane baya ta'ba damunta, sai dai kuma ita kanta kyamar kanta take dan har tsikar jikinta tashi yake, idan ta tafi ta bar shi a haka ya ci banza kenan. Ta rintse idanunta da 'karfi ta furzar da huci, sannan ta dawo da baya da baya, yana tsaye a wurin, ya kasa ko motsin kirki.

Bai ankara ba ya ji shi timmm cikin ruwan dattin, ta tura shi da iya 'karfin ta, yana 'kokarin mikewa idanunsa suka haska masa sanda ta shige motarsa, bai ankara ba ya ji tana kokarin tadata, ta taka motar da 'karfi ta yi gaba, ta kuma dawowa tana yawo cikin ruwan, tayi masa kwatankwacin yadda yayi maya, har sai da ta tabbatar ruwan yayi mugun 'bata masa farar kayan da ke jikinsa. Ta kashe motar, ta cire makullin sannan ta fito da makullin motar a hannunta tana karka'dawa. Ko'ina a jikinsa rawa yake zuciyarsa na bugawa kamar zata faso daga k'irjinta idanunsa har sun rine tsabar bacin rai sai wani huci yake kaman wanda ya ha'diyi garwashi. Jefa masa makullin tayi, cikin rashin sa'a ya fada cikin ramin da ke bayan sa. Ta yi murmushi mai zurfi zuciyarta dada yin haske, ta san a yanzu babu abin da yake tunani sai yadda zai karairayata idan ya kamata, idan ma tunaninsa kenan ya kamata ya san ko ita wacece, ya san gidan su, don in ya tashi nemanta ma kada ya wahala, zata zauna ta jirayi zuwansa, yayi kadan ta ji tsoron sa..

"Sunana Zakiyyah, Cima Ahmad Abdul'azeeez Yabo, gidan babana yana nan bayan layi kowa ka tambaya a layin wanene professor Ahmad yabo, za'a kai ka har kabarinsa dake gine a tsakar gidan mu lokaci kawai yake jira, Sunan mamana iyabo mai amala tana sana'ar siyar da abinci a bakin kasuwa, idan ka je kan hanyar da zata kai ka layin masu hijabai ka tambayi wacece Maman Blaky za'a kaita har wajen sana'arta, don Allah idan ka tashi zuwa ka taho da 'yan sanda da dakarun gwamnati 'karshen ta'kama 'dan marasa tarbiyyah"
*******
_Naseer Batta street 10am:Abuja_

A cikin nitsuwa yake driving, a hankali yake bin 'kira'ar Abdullahi Abba da ke tashi a motar cikin sanyayyar muryar sa.
Tayoyin motar suka yi kwana zuwa cikin gate d'in wani katafaren guri mai mutuk'ar kyau, a samansa an rubuta 'Nas World'.... Duniyar da Ahalin Naseer Yabo Batta ke ciki.

A cikin parking lot d'in, ya saka motar tsakanin wasu motoci biyu..

Morhan bai fito ba har sai da karatun ya kai 'karshe, sannan ya kashe motar ya d'auki wayar dake gefensa ya fito, zuciyarsa a cunkushe taf da al'amura kala-kala.

"Barka da zuwa yallab'ai."

Jimoh security ya fad'a cikin harshen turanci, ya amsa fuskarsa a washe yana tsokanar sa, sannan ya taka zuwa cikin gidan.
Sanye da navy blue jersey designer ta companyn FLUXO mai dauke da cap da dogon wando alaman daga street warming execise yake, mur'dadden jikin shi yayi matukar kyau cikin kayan kaman kullum.

Hayaniyar shigowar motar Hassan da Horn din da yake dannnawa ne ya dakatar da shi, ya maida dubansa kan motar da ke kokarin shigowa . ...


Nayi gabas⛹️
Zakiyyah Bintou Ishaq
13th November 2024.
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *002*
Hayaniyar shigowar motar Hassan da Horn din da yake dannnawa ne ya dakatar da shi, ya bi motar da kallo yana mamakin rabon da ya gan shi da motar nan, tun da Hassan yayi sabuwar mota ya daina ganin motar a gidan, a tunanin sa ma Hassan din ya siyar da motar ne. Tunanin sa ya katse lokacin da ya ji muryar Hassan din yana 'kwalawa Aminu Driver kira, Aminu ya taho da gudu ya gurfana a gaban Hassan yana kokarin gaidashi, saukan wani zazzafar mari a kuncinsa ya dakatar da yunkurinsa.
Jikin Hassan har rawa yake, ya nuna shi da yatsa.
"Aminu ni zaka tozarta?, Har ni zan kiraka a waya ka 'ki daukan min waya?"
Sai a yanzu Morhan ya lura da shigar da ke jikin Hasssan din, daga shi sai singlet dai boxers, ga shi jiki ba ka'dan ba, a mur'de yake kaman autan samudawa. Aminu ya dafe kuncinsa kan sa a 'kasa.
"Ka yi hakuri yalla'bai, wayar ne ba charji, nnn...na saka charji a sashen Hajiya 'karama..."
Bai 'karasa ba ya sake jin saukan wasu tagwayen maruka wannan karon a both sides na fuskar sa, zai sake kai masa wani ya ji an rike hannunsa.

""You are very stupid Hasssan, Malam Aminun kake 'dagawa hannu? saboda baka da hankali?"
Morhan da karasowan sa saukan marukan suka zo a tare ya fada yana rike da hannun sa, Hassan ya kwace hannunsa, ya kada 'keyarsa ya juya yana cewa
"Ko kai baka fi karfin in 'daukeka da tafi ba Ya Morhan, da ni ka kira na 'ki 'dagawa ba bugu ba da yanzu ka hada ni da Ya Ameen an ce min mara tarbiyya, saboda kawai ana ciyar da ni, shi kuwa yana aiki 'kar'kashin mu, muna ciyar da shi da iyalan sa, mu masa sutura mu tallafi rayuwarsa amma aikin ya gagara yin aikin da muka daukesa ya mana, yanzu saboda rashin adalci marin sa da na yi har ya juye ya zama laifi, wallahi yau a gidan nan babu wanda zai hana ni hukunta Aminu ko waye shi, sai Aminu ya zagaye garin Abuja da 'dan kamfai babu riga tun da har ya bari sakacin sa ya sa wata 'kazama ta min rashin mutunci "

Daga haka ya barshi tsaye kamar soko saboda mamaki. Yayi maganar a kunnen ALHAJI Naseer lokacin da yake fitowa drivern sa na biye da shi, amma kallo 'daya yayi masa daga nan bai kara ba. Morhan ya gaishe shi, ya amsa ciki ciki.
Ya bi bayan mahaifin nasa da idanu, sai da ya ga fitar mahaifin nasa sannan ya shige cikin gida, daf da ze shiga falon Hajiya kunnuwansa suka jiyo masa maganganun laure da sa'a, masu girkin hajiya
"Nidai Sa'adatu ban ga amfanin Alhaji a gidan nan ba, shi fa babu ruwan sa da lamurran kowa a gidan nan, rayuwar sa kawai yake yi... Fisabilillahi ji uban damben da Fatimah da Aisha suka yi, abin ya kai sai da aka kai su asibiti jiki jina jina, amma bai ce uffan ba?, Tun suna dambace dambace ana kai su asibiti, wallahi wata ran gawargwakin su za'a kai mutuary, tun da babu mai kwa'abr su, duk abin da 'ya'yan gidan nan za su aikata daidai ne, shi fa bai san abin kunya ba. Abin kunya a wajen sa shi ne a ce za'a tauye kimar sa ko kuma ya ga 'dan sa na shaye shaye, idan fa kinga Alhaji ya saka baki a lamuran da ya shafi gidan nan to Morhan ne yayi laifi, ya tsani yaron nan kaman ba shi ne Ubansa ba, kuma uwar sa na gani, itama kaman ba 'dan ta ba , ga shi duk cikin 'ya'yan sa shi ne natsatte, babu ruwan sa ga kyauta da sanin darajar dan Adam...wlh Alhaji bai yi wa gidan sa tanadi na kwarai ba, Allah ya baka arzikin ilimin arabi, ga arkikin uban dukiya da na zuri'a amma ka tarwatsasu da hannunka? babu kwa'ba sai fariya da nuna an fi uban kowa ilimi?, to ina amfanin ilimin da ba'a aiki da shi?, Yanzu fa da ace a 'kasar nan za'a yi taron da ya ha'da da Malaman addini, yana cikin sahu na farko, don tabbas Alhaji ya 'koshi da ilimin islama yaransa ma duka a kananun shekarun su suke sauke al'kur'ani, amma idan ka ga yadda yaransa ke yahudanci wlh ba zaka taba yarda uban su ne babban malamin da duniya ke alfahari da shi ba, wani wula'kancin ma idan suka yi maka ko ahlulkitabi ba za su yi maka irin wannan tozarcin ba ballantana dan uwanka muslmi."
Sa'a tace
"Uhm kedai bari Laure kin san Alhajin ya yadda da tarbiyyan su ne shi yasa baya tanka masu, shi kuma Morhan tun da 'kaddara ta sauke shi daga turban tarbiyyan da alhaji yayi masu, shikenan ya kafa masa kahon zu'ka, shi ma ban san 'kaddarar da ta kai shi ga shaye shaye ba, Allah duk cikin yaran Alhaji babu kamar sa, bawan Allah ga sakin fuska da yawan murmushi, abin duniya sam bai dame shi ba, idan Alhaji ya bar duniya bai gyara kan gidansa ba to kuwa kangarun yaran nan nasa ba za su bari yayi kwanciyar rahama ba"

"Hmm ke dai bari lamarin alhaji akwai sake... na 'dora girki, bari in duba kada ya kone"
"Uhum... dai ya kyauta"
Morhan ya daga 'kafa dakyar ya karasa shigowa bakin sa dauke da sallama. Tunanin maganganunsu ya keyi a ransa, ba su yi 'karya ba. Alhajin su ba shi da matsantawa mutum, yana iya kokarin sa wajen ba su tarbiyya tun suna 'kanana, da zarar 'dan sa ya haura shekara sha takwas zai zame hannun sa a lamurran da ya shafe shi, kudi ba matsalar su bane don duk wata suna samun kason su a kowane companyn Alhaji da ke fadin 'kasar nan.
Dakin Ummie Mahaifiyarsa ya nufa, ya gaisheta ta amsa itama ciki ciki, ko kallon sa bata yi ba, in da sabo ya kamata a ce ya sabawa, zuciyarsa ta matse da wani irin kaɗaici mai nauyi. Da wannan ƙunar ya koma sashensa.
Sanyin AC ya doki tsakar fresh hair make up din sa, simple low cut ce wanda ba'kar suman sa da hasken fatar kansa suka 'kara kawata askin. Ga carve din askin da yabi shatin kayattacen bakar shiny saje da beard line din sa wanda ya daɗa bashi irresitable look, yayi looking very cool and young. Ba shakka Morhan ya hadu kyakkyawa ne, ruwan fulani da kabilar Khindar (wata ƙasa can tsakiyar Africa). Kasar da ta kwashe kyawawan Africa gaba'daya, ta rarraba kanzon kyawu ga raguwan kasashen Africa. (😏🙄)

Fuskar sa babu walwala ya sauya zuwa comfy white towels ya shiga batrum, ya dade a nan jingine da glass wall din shower sanyi na ratsa ɓargo da duk wani' bangare na jikin sa.

Rayuwar ta ishe shi, ji yake kaman shi kaɗai yake rayuwa a duniyar sa, a kowane fitan hasken rana ji yake kaɗaici na daɗa mamaye ragowar ƙwarin gwiwan sa. Rayuwar sa babu wani jin dadi, sai matsantawa da kaɗaici, wanda ke daɗa ingiza shi zuwa rayuwar da ya zama silar tauyewan farin cikin sa.
Ya rufe fuskarsa da duka tafukan hannayensa sannan ya fitar da iska ta bakin sa.
Ya Allah! , Ya Rabbi! Ka taimake ni, ka sama min natsuwa, i'm confused, rayuwata a rikice take, ya Allah..!, Ka karb'i addu'o'ina, rayuwata ta hargitse.
Ya Allah ka tserar da zuciyata daga sharrin wannan ƙalubalen, ka azurta ni da ni'ima a rayuwata ka raba ni da jarabtar da ke lulluɓe da baƙar tabon da ke nisanta farin ciki daga rayuwata...

Ya ilahi, ka bani wani sabon fata a rayuwata ko da na wucin gadi ne ya Allah..!, a firgice nake ya Allah, Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login