Showing 6001 words to 9000 words out of 72389 words
rayuwatta.
*Asalin labarin*
Mahaifan sa asalin mutanen Khindar ne, yan hijira, mazaunan cikin dajin Zadraf wanda ya ke arewa moso gabashin Maiduguri da Chad, ahali guda ne suke zaune a wannan yankin, don a yadda labari ya zo masa, cewa aka yi, gabaki 'dayan su matafiya ne, asalin su yan kasar KHINDAAR ne (Wata ƙasa da ke tsaka da wajen Africa). Babu laifi akwai arziki a tattare da ahalin, sana'a suke na bugawa a mujalla kama daga 'danyan gwal, raguna, tumakai da ma wasu dabbobin da ni Bintou ban san sunan su ba. Kasancewan akwai yalwan ruwa da 'yayan itatuwa wadatacce hakan ya sanya su jimawa a dajin. Ba su da wani yare face larabci irin na 'yan Egypt da fulatanci wanda suka koya a iya zaman su da makiyayan da ke yada zango a sansanin su, kaɗan daga cikin jama'ar dajin wanda su ke fita suna cudanya da hausawa ne ke jin Hausa, sai kuma wasun su da suka yadda da boko, suka shiga cikin gari domin neman ilimi, wasu kuma cudanya ta kasuwanci ne yasa suka fara jin yarurruka mabanbanta kama daga shuwa, kanuri har yarbanci, saboda a cikin su, akwai wadanda kasuwanci ya harba su Lagos da Abuja, cikin su har da alhaji Naseer Batta.
Mahaifin Morhan shi ne babban malami a wannan dajin, matan sa hudu, duk a dalilin neman magaji kasancewar duka matan sa 'ya'ya mata su ke haifa masa . Sai da ya haifi 'ya'ya goma sha 'daya duka mata, har ya fitar da rai dan kuwa shekaru sun ja ya bawa arbain baya, sannan Allah ya amsa masa ya azurta matar sa ta hudu wacce dama ita ya'yanta mata basu wuce biyu ba da haihuwar da namiji.
Murna gun Malam Naseer ba a magana dan har kyautar 'danyen zinare mai nauyi yayi wa mahaifiyar Morhan, unguwar zoma da ta karbi haihuwar kuwa ta sha kyaututtuka daga wajen 'dalibai da yan uwa. In da mahaifin Morhan ke murna samun magaji, aminin sa wanda ya fi kowa kusanci da shi, babban abin bakin ciki ya zame masa dan kuwa ya ci burin mallakar komai na malam kama daga mukami har dukiya, ya gama shimfi'da hanyarsa da rashin magajin Malam, tun Morhan na ciki ya so ya ga ya bi kororo amma a duk lokacin da yayi yunkuri sai ya ga kaman ya 'karawa mata lafiya ne.
Kamar yanda Malam Habu ke bakin cikin jaririn da aka haifa, haka ma sauran matan gidan su ka nuna bakin ciki karara. Ranar suna yaro ya ci sunan mahaifin malam wato Muhammad Sani. Bayan haihuwar Muhammad Sani (Morhan) da watanni biyu malam ya koma Abuja da zama saboda harkar kasuwancin sa ya fi ci a can. Ganin ba'kin cikin da suke nunawa mahaifiyar Mohan yasa malam ya yanke hukuncin tafiya da mahaifiyar Mohan ita kadai, da zummar zai dinga dawowa cikin dajin duk karshen wata. Nan ma ba 'karamin ya'ki aka tayar ba, don sai da uwar gidan sa ta yi yaji daga nan har 'kasar Khindar, shi kuwa lamarin da yayi matukar fusata shi, ya aika mata da sakon sakinta biyu, lamarin da yaso tada hatsaniya a tsakanin ahalin, don takalas mahaifinta ya wanko kafa tun daga khindar yayi masa wankin babban bargo, ya kuma ci masa mutunci a gaban 'daliban sa, in da abin da ALHAJI NASEER ya tsana bai wuce ya ga ana kokarin ta'ba masa 'kimar sa ba, shi a rayuwar sa baya ha'da kimar sa da komai, lamarin da yayi matukar bata ran sa, yayi rantsuwar ba zai sake leka kafansa kasar Khindaar ba.
Baffa Yusufa, Baffa Habibu da Hajiya Jummai su ne yan uwan Malam Naseer, kuma dukkan su, suna can mahaifan su, wato 'kasar Khindaar wannan lamari da ya auku shi ne silar yankewan zumuncin su a lokacin.
Gata da soyayya karara Malam Naseer yake nunawa Muhammad Sani, hakan ba karamin bakin jini ya jawowa Ummie (Mahaifiyar sa) da shi kan shi ba. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, ana jifa da surkulle domin halaka su, Allah kuma na kare su.
Tun kafin ya cika shekara biyu a duniya ya yaye kan sa ya na kin nono, wanda hakan ya nunawa Ummie ta alamun cikin da ta ke dauke da shi. Murna gun Malam Naseeer wanda a wannan lokacin ya koma Alhaji Nasir ba a cewa komai, shi dai fatan sa Allah ya maimaita a haifa masa 'da namiji. Cikin da Ummie ke dauke da shi ya sanya Nasir ya 'karo ma'aikata a masana'antar sa ya rarraba masu aiki, ya kuma dora amininsa a kan ragamar komai.
Wannan ya ba wa Malam Habu damar yiwa Nasir zagon 'kasa ta hanyar korar wasu ma'aikata da musanya su da wasu don ya kankare dukiyarsa ta yadda ba za'a gane ba.
Da ya ke manyan ma'akatan nasa amintattu ne, kalilan ne su ka bi hanyar malam dan haka ha'kan sa bai cimma ruwa ba.
Nan Abujan yayi mata rijistan awo a wani babban asibitin kudi, kuma da kan shi yake kai ta, ya dawo da ita, ranar wata laraba ta sake haifo dan ta namiji, da mako ya zagayo aka sanya masa Muhammadu Ameen.
Sai da Ameen ya dan yi kwari sannan aka tasanma barin dajin Zadraf gabaki daya, lokacin harkoki sun budewa mazauna dajin da Alhaji, sauran matan sa suka biyo shi cikin garin Abuja, ya ha'da su biyu biyu a gida 'daya.
Har a lokacin yaran Alhaji Nasir basu bar kiwo da sana'ar da ta shigo da su 'kasar ba wato safara da siye da siyar da danyan gwal, kuma Allah ya dafa masu, da sa albarkan sa harkoki suka yi ta bu'dewa, da yardar sa kuma ya gina kamfanin sa na farko a cikin garin Abuja... Cikin shekarun da ba za su haura bakwai ba ya mallaki kamfanunnuwa, Estates hotels da gidajen mai masu taken Naseer batta, ko ina ka gifta a 'kasar nan sai ka ci karo da kamfanin sa Batta...Ya samo sunan batta ne daga gun manager din sa Mr Rogers Smith ya ce sunan shi na kama da sunan wani tsohon amininsa Nasir batta, kaman da wasa sai sunan ya bi shi. Morhan na da shekara goma Alhaji Nasir yayi wani auren, ya auro wata Bayarbiya yar lagos, daya daga cikin ma'aikatan companyn sa na sarrafa taliyan a Lagos sunanta Halimah, makirar mace ce ta 'karshe, ta yi amfani da biyayya da saukar da kai ta lashe zuciyar Alhaji, sannan ta dasa yardarta a zukatan matan sa ta yadda har yanzu babu wanda ya gano boyayyar manufarta na auren Alhajin. Shekarar Halimah 'daya a gidan ta haifi 'yan biyu, a ranar suna Hussaini ya rasu, bayan nan bata sake haihuwa ba, sai mahaifiyar morhan da ta sake haihuwar mata uku, Fatima, Khadijah da Aisha.
Morhan na kammala karatun sa na secondary mahaifin sa ya tura shi Stanford University da ke California US, a nan ya ha'du da 'kaddarar sa, 'kaddarar da ta canza komai. *FATIMAH*
Kasancewan ya taso cikin 'yan uwansa mata, abokansa maza kadan ne, ko a secondary school, ya fi abota da mata. Hakan ya sa koda ya tafi can kawayen sa duk mata ne. Sai dai abotan sa da su ya tsaya a iya makaranta ne, baya bari wata ala'ka ya zarce wacce suke yi a makaranta. Fatimah ita ce mace ta farko da ta fara shiga rayuwarsa.
Fatimah Haysam jerril haifaffiyar 'kasar Sudan ce, itama karatu ne ya kawota California, duk cikin kawayen sa ita kadai ce musulma, kuma tasu ta fi zuwa 'daya, saboda shi mutum ne mai barkwanci, yana da tsokana da wasa da dariya ga kyauta da son kyautata mu'amala. Itama kusan haka ne. Tana da saukin kai ga barkwanci da shigar kamala, fannin kyautatawa kuwa har ta kere shi. Yadda yake kashe mata kudi, itama haka, bata 'kyashin kashe masa ko nawa ne, idan suna makaranta in sun gama lectures da kanta take kai su wajen abinci su ci ta biya ba tare da ta damu ba. Haka in zata kai wankin kayanta, sai ta kira shi ko ta aika a hado da nashi a wanke, ta biya.
Please share😩😩
Comment please.
16th November 2024
Nayi gabas 😎.
[12/21, 6:52 AM] Zakiyyah Bintou Ishaq🌚: *003*
Fatimah mutumiyar kirki ce, tana da tarbiyya daidai gwargwado, amma Allah ya jarrabeta da matsalar shaƙar cocaine, lokacin da take yarinya Allah ya yi ta da ƙiriniya da kukan dare, sosai kukan ta ke hana iyayen ta sakewa da daddarre hakan ya sa mahaifin ta ya yanke shawarar ya fara ɗura mata maganin bacci, tun da ya fara bata maganin suka samu salama, har ta kai Fatimah bata iya barci sai an bata magani, a haka har ta girma, ta fara siya da kan ta. Da tafiya ta yi tafiya sai maganin baccin ya daina mata aiki, ta koma siyan su cocaine, tramadol da sauran ababen maye. Tun iyayen ta na ganin abin kaman ba komai ba, har abin ya fi ƙarfin su, suka bar mata kayan ta. Suka bar shi a matsayin hakan shi ne ƙaddarar ta.
Babu wanda bai san Fatimah tana shaye shaye ba, don ta riga ta saba, bata iya ɓoyewa. Mohan shi ke rakata inda take siyowa kasancewar ba a ko ina ake samun masu siyar da abin ba, kuma akwai matakan tsaron da suka hana ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a ƙasar, yasa sai sun yi cikin ɓadda kama suke samun in da za su saya. Idan ya rakata shi ke biyan kuɗin ko nawa ne, so tari ma a nan wajen take fasawa ta shakka jikinta na rawa. Shi kuma sai ya tsaya yana kallonta da mamaki, ya kan tambaye ta
"Wai ke Fatee, me kike ji a wannan abin?, Powder ne fa"
Sai ta yi dariya ta ce
"Morh kenan, wannan abin ya fi battery iya charji.... Akwai surutan da nake yawan ji a cikin kai na, kai na yana yawan yin nauyi, in kasa gane me ke damuna, da zarar na sha'ki wannan abin.... Shi kenan komai yayi disappear... In koma kaman jinjira, ba damuwa, ba tunani, my soul will be empty.. hmm .duk yadda zan maka bayani ba zaka fahimta ba".
Sai ya ce "Fatee ki riƙe bayanin ki, don ba fahimta zan yi ba".
Loko da lungu kwararo kwararo, duk inda ake siyar da cocaine a California Fatee ta san shi, kuma ta yi nasarar zagaye wurin tare da Morhan, tun suna zuwa cikin ɓad da kama, saboda gudun jami'ai har ta kai wasu lokutan ma jami'an da kan su suke zuwa su karɓi kudin su, su siyo masu, saboda gurɓacewa.
Ƴan sanda sun sha kama su, amma Morh shi ke belin su tun kan a kai ga zuwa station. Akwai ranar da aka kama su Mohan ya yi belin su, ɗaya daga cikin mutanen da aka kama tare da su Mohan ya ce "Mohan da baka biya ba wallahi, su kai mu station ɗin, za su ga hauka wallahi, zan nuna masu ni ɗan ƙwaya ne kuma ɗan Africa, sai na tona asirin su, cin hancin da suke ƙarɓa a hannun mu duk sai na tona, ina da hujja"
ƴan sandan da jin haka sai hankalin su ya tashi, don California ba kaman ƙasar mu bane, karɓan cin hancin a wajen su babban laifi ne. Ba ƙaramin ƙura aka tayar ba kafin a sake su, kuma daga wannan rana sai rashin mutuncin ƴan sandan ya ya ƙaru, suka fara kame na tsakani da Allah, cin hancin ma sun daina ƙarba, masu siyar da kayan maye duk suka gudu, wasu suka sauya salo. (Morhan yana da Athma amma ba mai yawan tashi bane).
Rashin masu siyar da ƙwaya ba ƙaramin takurawa Fatee yayi ba, ta kasa sukuni, cikin ƙanƙanin lokaci ta rasa walwalarta, ta daina samun isasshen bacci, da ta kwanta take farkawa, ta yi ta mutsu mutsu tana soshe soshe z wani lokaci ma cikin dare take kiran Morhan a waya da ya ɗauka sai ta fashe mai da kuka, tausayin ta yake ji matuƙa. Wata rana ya haɗu da wani mutumi da ya suka taɓa yin karo a wajen siyan cocaine, mutumin ne ya kwatanta masa yadda zai haɗu da su a cikin gari, idan a wajen gari yake son haɗuwa da su ma akwai su, a take a wurin ya kira wayar Fatimah, ta taho suka garzaya bayan gari, sun yi sa'a suna wajen, tun kafin a basu cocaine din jikin Fatee har ya fara rawa, ana bata ta farka takardar ta yi masa wani dogon shaƙa. A take a nan ta faɗi a nan tana wani nishi, da birgima. Shi dai Morhan yayi tsaye yana kallon ta, tsawon minti goma, sannan ta tashi tana kakkaɓe jikin ta, fuskanta fayau, sai yanzu ya lura da wani irin rama da ta yi. Ya girgiza kai. A karo na farko wani tunani ya yi crossing mind ɗin sa, ya fara tunanin gwada shaƙar wannan abin shi ma ya ji yadda ake ji. Washe gari da suka koma wajen, bayan Fatima ta ƙarɓi nata, sai ya sake miƙa kuɗi, ya ce shi ma a ba shi zai gwada ya ji abin da ake ji. Sai dai ko da aka ba shi ya shaƙa bai ji komai ba, ya ja tsaki, yana sake kai abin cikin hancin sa ..
"Meye a abin nan da har yake sa ki wannnan harguwwan?, hoda ce fa, common face powder, wallahi babu abin da na ji"
Duk da a wannan lokacin ta yi charji, amma hakan bai hana maganganun Morhan girgizata ba, ta ware idanunta da ƙyar.
“Ƙarya kake Morhan ƙyarrr..ya ne, wannnan da kake gani original charger ce, zallar hoda ce babu mix"
"Ke..!, Wallahi ban ji komai ba... Kin gani?, Nothing change"
Ya fada yana sake kaiwa hancin sa, da gaske bai ji komai ba, shi kan shi mamaki yake don yana ganin mutanen da suke shaƙar sa, kuma suna yin charji iya gwargwado, iya mamaki ya gama shayar da fatee, amma ta ɗauke shi a ɗan baiwa, mutum na musamman.
Washe gari da suka koma, sai ya ce a ba shi wanda ya fi na jiya ƙarfi ya kwatanta, mutumin mai siyarwa sai ya yi tunanin ya ba shi babban dan ya ƙure alfaharin sa. Mohan na shaƙar shi yaji kan shi ya wani nauyi tare da juyawa na fitan hankali, a take a nan ya yanke jiki ya suma. Mutumin na ganin haka ya arce a guje, Fatee ta ƙwala ihun neman taimako, da taimakon wasu mutane aka kai shi asibiti. Athma ɗin shi ne yayi mugun tashi da ƙyar aka samo numfashin sa, satin sa ɗaya a asibiti yana jinya, Fatee ce mai kula da shi, saboda a halin yanzu ba shi da kowa bayan ita. Ko da aka sallame shi bai bar raka Fatee yana siya mata ba, a duk lokacin da ya rakata, sai ya dinga ji kaman ana tsungulinsa da ya sake kwatanta shaƙar abin, amma idan ya tuna azabar da ya sha sai ya fasa, har ta kai ga wata rana zuciyarsa ta fi ƙarfin sa, ya sake kwatanta shaƙa, sai dai a wannan lokacin ba kaman wancan karon ba, a wannan karon ya ji irin charjin da Fatee take so ta fahimtar da shi... Wannan shi ne mafarin ƙaddarar da ta jefa Morhan a harkar shaye shaye tun yana shaƙar cocaine kaɗai har yazo yana haɗawa da wasu ƙwayoyin, har da sigari.
Ƙalubalen da ya fara fuskanta shi ne rashin sallah a kan lokaci, don idan yayi charji yana jimawa bai sauka ba, ƙalubale na biyu, rashin tanadi, kafin ya fara shaye shaye ya kan manta rabon da ya duba account balance ɗin shi, don ko ya duba ba ya iya ƙidaya adadin kudaden da ke cikin accounts ɗin sa, amma a yanzu shi kan shi tsoron duba balance yake yi, don ba ƙaramin kuɗi yake narkawa a harkar ba, ƙalubale na uku kuwa lafiyar sa ce, sosai cocaine ke barazanar datse masa jin daɗin da ke tattare da fitar numfashin sa, Athma ɗin sa yana yawan tashi.
Bayan shaye shaye baya aikata wani fasadi, mata basu gaban sa, bai damu da mu'amala da abokai ba, daga shi sai ƴan matan kwaleji suke rayuwar su. Sai kuma Fati wacce alaƙar shan ƙwaya ya daɗa ƙulla zumuncin su, shaƙuwar su ta zama tamkar ta yaya da ƙanwar sa. A haka suka kammala karatun, suka rabu suna kewan juna, ta koma ƙasar su, shi kuma ya dawo Nigeria, nan ma bai sha wahalar neman joint ɗin masu siyar da kayan maye ba, don ya san masu harkar tun kafin ya bar ƙasar. Ana haka Alhaji Naseer ya sake tura shi ƙasar Egypt don ya ƙarasa masters ɗin sa. Ƙasar Egypt ba kaman ƙasar mu ba, kuma ba kaman California ba, akwai tsauraran matakan tsaro sosai. Duk inda ya zagaya babu masu siyar da kayan maye, hakan ya sa duk nacinsa da ƙwaɗayin sa sai da ya haƙura ya rungumi karatun da ya kawo shi, a lokacin ba ƙaramin wahala ya sha ba, da fari ko barcin kirki baya iya yi, jikin ya tsira wani irin ƙyaiƙayi na fitan hankali, hannayen sa da ƙafafunsa basu iya zama waje ɗaya, sai su rinƙa shaking kaman an dasa musu lartarki, ƙwaƙwalwarsa ta zama kaman a birkice, ko tafiya yake yi sai ya dinga surutai yana soshe soshe, ga kaɗaici da matsanancin kewan gida da ya dame shi, ba zan iya kamanta wahala da azaban da Mohan ya sha ba, kafin ya tsallake wannan yanayi.
Da ƙyar ya tsallake wannan yanayi, tun da ya dawo normal sai ya koma shuru shuru, kullum in zaka gan shi bakin sa na motsawa yana istigfari, ƙur'ani da salatin annabi suka bi jikin sa. Ya maida masallaci wajen zuwan sa a kowane lokaci, a nan ne ya haɗu Ibrahim da Ahmad su ma ƴan Nigeria ne suna cikin mutanen da gwamnatin jihar Kaduna ta basu scholarship a makarantar su. Abotansa da su shi ya ƙara nisanta zuciyarsa da ƙwaɗayin shan ƙwaya, idan ya tuna rayuwar da yayi a baya ta silar ƙwaya sai ƙyamar kan sa ya kama shi. Cikin yardar Allah har ya kammala karatun sa bai sake yunƙurin kwatanta shan ƙwaya ba.
Dawowar sa Nigeria shi ya sauya komai. Jirgin su na sauka a airport weather ɗin ƙasar ya tayar masa da kwantacciyar