Showing 6001 words to 9000 words out of 69951 words

Chapter 3 - MIKIYA Book One Hausa Novel

18 Nov 2024

8169

YA FECE kamar yadda ya saba dai, kamar kwanaki da labaransa suka game media kan ta'adda cin ɗaya shiga cikin babban hotel ɗin yayi fashin sa ya fice salin alin. Masha yi, maci amanar ƙasa ɗan ta'adda, We want an end to oppression💪. Musaso a kawo ƙarshen zalunci, cin amana, ya kamata jami'anmu su farka daga nannauyar barcin daya ɗaukesu kodan sharen fa gen da wannan babban criminal ɗin ya soma ɗauki ɗai ɗai a cikin al'umma, donjin ra'ayoyin ku zaku iya na ƙara faɗa We want an end to oppression💪
tuntuɓarmu akan wannan number 081----------- ko kuma shafin mu na Instagram, Facebook, dadai sauran tasho shinmu a gimtse 🫰 "

Tana kammala shirin ta miƙe jiki a mace tare da barin ɗakin baki ɗaya, Tafi su su majeedah dasu Sairah ɗauka da shewa shi kuwa me girma MD sai faman washe baƙinsa yake domin dai yasan wannan karon zasu shahara,
Daga cikin garin Lagos kuwa harda ma ƙetare a take mutane daban daban suka shiga turo saƙonnin jinjina da ƙara buɗaɗama jami'ai hanya, na suna tare da su 100 percent.

Kamar yadda al'umma suka saurari wannan labaran na yau haka ma babbar headquarters ta Lagos ta saurara, Cikin ƙanƙan da da ido mr.presiden ya ɗago kansa tare da duban Ajmaal, ƙasss masa da ido, nan suka suka shiga tattauanawa akan wannan batu me girma, cikin ƙankanin loƙaci kuwa duk inda ka gaza labarin KIDNAPPING ɗin ake, saiga ZAMANI TV a sama tana shawagi.

A gimtse 🫰
To ai shikenan kooooo ⁉️🚯
Sai na ce sai mun haɗe a next page kanan. Laaaaaa na manta shegun sunyi bannet numbern WhatsApp nawa nefa


Shi yasa kuka jini ɗifffff taku ce *AMMEY LAYLERH ✍️*


*🦅 MIKIYA 🦅*
{Mai hangen nesa 👀}

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH

____________________


*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Page 5&6

🤍🔥✅

" Ita yarinyar da tai labaran lallai ina son sanin wacece ita"
Ya faɗa cikin dakakken sauti tare da ɗaukar kwalbar Win yana kafata a baki, bai dire kwalbar ba Saida ya shanye tasss.
"Sunanta MARYAM ABDULLAHI GWANI wacce akafi saninta da MEERAH, haifaffiyar garin nan ce suna zaune a unguwar GATAN KOWA. Mahaifinta malami ne sananne wanda daƙyar ya bar yabar yarinyar ta fara aiki da gidan jaridar, acewar aure shine kaɗai rufin asirin dukk wata mace ta gari, Md ɗin ne yaje har gida ya roƙi alfarmar malam Abdullahi don ganin loƙacin da suka je pratical cikin tashar, bayan sun gabatar da pratical ɗinne yarinyar ta ringa samun viaw na jama'a, hakan ya haukata Md, shine dalilin da yasa yaje har wurin mahaifinta neman alfarma ta fara aiki da tashar, nashi kona ɗan loƙaci ne.yana da mata uku tayi karatun ta tun daga kan primary nata har zuwa high school ɗinta ji duka anan cikin garin Lagos, ta fara aiki da gidan jaridar zamani tv watanni shida da suka wuce, tana da tsayayyen saurayin ta wanda za'a yi bikin su nan ba da jimawa, tun ranar da rahotannin ya fita na bibiyi ita kanta yarinyar, don nasan dole zaka buƙaci sanin wacece ita, yanxu haka md ɗin yana ƙoƙarin buga jaridu akan hakan, umarnin ka kaɗai muke jira wajen daƙile faruwar hakan, A yadda nayi kyakkyawarn bincike game da Md ɗin yana da masifar son kuɗin masifa, shi ba ruwansa da inganci abu burinsa kawai kuɗi ɗaukaka sune kaɗai yaren daya fi fashimta"
Axton ne duka me wannan maganar kuma tun a ranar da rahotannin suka fita yabibiyeta, harya samu cikakken tarihin ta.
Saida ya kuma zuƙar cigarettes ɗin dake hannunsa, kafin ya ɗago rikitattun idonsa ya zuba su akan axton, shi yasa ahar kullum yake kuma alfahari dashi acikin yaran nasa, duk abinda ya kamata kafin yace shi kuma ya aikata.
Miles ne ya kuma daidai ta nutsuwar sa cikin gurɓatacciyar hausar sa da baya fita ya furta.
"Boss ni kuma bayan na bibiyi rahotannin ta na shiga duka kafofin sadarwarta, kamar yadda ta umarta tabbas tauraronta na haskawa a wannan tashar dama duniya baki ɗaya, duba da yadda take da tarin masoya tako ta ina hakan yasa cikin ƙanƙanin loƙaci wannan ruhotannin ya baza garin Lagos harma da ƙetare, a yadda ma na samu cikakken bayani daga cikin headquarters na A F S, aka bama shi MD ɗin bayanin dukkan abinda ya faru a safiyar juma'ar, kana Saida suka yi duba da yanda tauraron yarinyar yake haskawa kana sukayi amfani da hakan don son cika burinsu, zasuna amfani da ita ne kawai don.....

Ɗaga masa hannun da Boss In nasu yayi ne ya sanya shi dakatawa, wani irin killet murmushin gefen baki ya saki tare da faɗin.
"A barta taci gaba da buga wasan da dukkan alama zai yi armashi, zai kuma kawo nishaɗi, Nazari muke da ƙwaƙwalwa karku manta!, Sadaukai ne mu tamkar mafarauta!, ba'a taɓa nasarar yaƙi sai in da mayaƙa, don haka ina son a buga wannan game ɗin tare dani"
   Wani mugun waro idanu sukayi suna bin boss in nasu da kallo
Lallai Boss rigimarka yawa gare ta da ɗaukar abu me muhimmanci da rashin muhimmanci.
Kai komai da zuciyarka ta raya maka sai kace ayi baka tuna abinda zai iya zuwa ya dawo,in banda taryan Aradu da ka taya ma zakace a bari a buga jaridu akan ka, kana kace a barsu kana son buga wasa akan mutanen dake farautar rayuwarka. Sune kalaman da da axton ya shiga nanatasu cikin zuciyar.

Tsammm ya miƙe cikin tafiyar nan na ƙasaita da kuma izzar da yake da yabar main Parlourn tare da nufar upstairs nashi, yana barin su da wasuwasai falll zuciyarsu.
Shi kuma Boss In saman sa ya nufa zaune yakai gefen bed nashi tare, da janyo system nashi me ƙirar campanyn apple, engine machine ɗin sa ya jona tare da jan glass cup yana siyanyar coffee tare da fara dan sipping nashi a Ahankali, kana ya shiga wasu ƴan sarrafe sarrafe kafin ya janye ta tare da ɗaukar wani ɗan kit box,, buɗeta yayi a take wata ƙaramar waya ta bayyana irin nokia ɗin nan ta da.
A take ya shiga loda Numbern daya gama haddace abarsa ya lodata tare da shiga ɓangaren messages, ya koma yana ajje wasu short mess tare da switch na wayar yana jefata cikin wannan kid box ɗin.

*Zamani tv*

Jikin MD har mazari yake wajen amsa saƙonnin dake ta famar shigo musu, tun a daren shekaranjiya da da suka bayyana rahotannin babban criminal ɗin, kamar daga sama kuma yaga wani ɗan short mess ya faɗa masa, cikin rawar takashi ya shiga cikin message ɗin,
_ Amatsayina na babban masoyin wannan tasha ina so ayi fira dani da misalin 11:15Am na safiyar gobe tare da
MEERAH ABDULLAHI GWANI🫨_

"Yesss!"
MD ya faɗa da masifar ƙarfin daya sanya sauran ma'aikatan dake dab da Ofishin sa fitowa, dama abinda yake fata da kuma buri kenan ayi ta jan maganar wannan AK ɗin, gashi Alkhairuka suna ta samunsa a sanadiyar iyaka yaɗa labaran sa kawai. Loƙaci ɗaya tashar sa ta kara zama shahararriya kuma yasan duk ata sanadiyyar MEERAH ne.
"Kai wannan ƴa kin zama Alkhairi na iyayenki sun iya farar haihuwar ƴar baiwa!"
Haka dai Md yaci gaba da zabga surutunsa kafin yasa a ƙira masa mera ɗin.
Zaune take gaban me girma Md wanda ya shiga koɗa ta da mata kirari kala daban daban, kafin ya shiga sanar mata da buƙatarsa na wannan bawan Allahn da yake son yin fira da ita.
nooding kanta kawai ta yi tare da zuba masa ido tana binshi da wani irin kallo wanda kai tsaye zamu iya ƙiransa da najin haushi. Ganin ba haƙura zai yi bane ya sanya ta miƙewa dare da barin office ɗin, kai tsaye coumpaund na gidan jaridar ta nufa tare da barin gidan baki ɗaya. tana fita kuwa taci Sa'a ta haɗu da me napen, shigewa kawai tayi shi kuma yaja kanta ta kife saman cinyarta, tsananin ciwon kan da take ji na ƙara tsananta, "Hajiya ina muka nufa?" Ɗan adedeta sahun ya tambaye ta.
"Daɗin kowa" ta bashi amsa ba tare da ta ɗago kanta ba, babu wata tafiya me zurfi sai gasu har sun ƙaraso, handbag ɗinta ta buɗe bayan ta fita tare da zaro dari biyar ta bashi, canjin ɗari da hamsin ya bata tace ya barshi tana faɗawa cikin gidan nasu.

________★★★________


Cikin wasu haɗaɗɗun riga da wando na campanyn Dior saddle Brook yafito brown se ɗaukar ido yake baƙaramun amsar jikinsa kayan suka yi ba, abinka da cikakken namiji me jini a jika da ɗan sassarfa yake saƙƙowa daga stair ɗin, Zazzaune ya samu su axton suna ƴar firan su , ganin sakkowa Boss In nasu ne ya sanya suka miƙe zumbur tare da rusunar da kansu.
Kai tsaye motocinsu suka nufa suna mata key dake dama already sun riga da sun san da fitar.
katafaren unguwar Banana Island suka nufa wadda take nan da manya manyan ƙerarrun gine gine na zamani
duk inda ka kalla zaka so kara kallar wurin, tamkar ba'a nigeriyarmu ba, ko ina ka ɗaga idanu ka kallah sai ka ji baka son kawar da kanka daga wannan wajen, tsaruwa iya tsurwa, haɗuwa iya haɗuwa kammm anguwar ta gama haɗuwa.
Tun da motocin suka hau saman titin babu abinda kakeji sai suuuuuu suuuuuu suuuuuu shine kaɗai sautin dake tashi, har suka nufi wani ƙayatacce fitaccen gini na alfarma, da remote suka yi amfani wurin buɗe ƙaton jibgegen get ɗin. Kai tsaye suka danna hancin motocin nasu zuwa cikin gidan a jere, nan suka ci gaba da tafiya a jere a saman kwaltar, a ƙalla dai Saida suka wuce wajen get huɗu kamin su isa gaban wani ƙaton parking space ɗin da ya gaji da haɗuwa, wasu shegun tsadaddun motoci ne maƙare a parking space ɗin, tamkar companyn kera motoci , kowani mota ka ɗaga idanu ka kallah sai ka sake kallah saboda tsabar tsananin kyau da tsadar motar, kallo ɗaya zaka ma dogon ginin da yafi kama da masarrafin kera motoci.
A jere waje guda motocin nasu suka yi parking, ɗaya daga cikin manyan samudawan sane ya fito tare da buɗe masa ƙofar motar, cikin zallar izza ya fito yana ƙara gyara zaman p-carp ɗin dake saman kansa, wanda lallausar sumar kansa ta fito ta ƙasar ƙeyarsa. Ya Ilahi wannan gida kacokam ɗinsa saidai mu ƙirashi da aljannar duniya, ga wasu haɗaɗɗun beneye wajen hawa ashirin da wani abu.
Su dukka daga nan suka dakata shi kuma ya soma tafiya cikin tsananin zallar iya sarrafa tafiya, wata rantsatstsiyar ƙofa ya dosa tare da seta ƙofar da ƙwayar tsaƙiyar idanunsa, wanda suke nan exctly irin na mage a take kofar ta buɗe sai gashi cikin wani irin azababben narkakkun parlour, wanda ya linka na gidansa dake Victoria island sau goma a haɗuwa da tsaruwa.
Baki ɗaya parlourn ɗauke yake da wasu uban lumtsuma lumtsuman kujeru wajen set huɗu, ga ta ko ina na parlourn kewaye da na'u'rorin sarrafa abubuwa, gaban wata kerarriyar ƙofar glass ya nufa, bayan ya shiga cikin lifter ɗin ya danna Black B Parlour 3 zuuuuuuu lifter ɗin tayi ƙasa dashi idanunsa Lumshe a haka har ta kawo shi parlourn, still wasu kofofin da suka kusa kwance min kai na kuma cin karo dasu, nan ya ringa ratsa parlouna yana wucewa har ya isa gaban wani ɗaki da yafi kama dana masu bada horo.
Nan ma Saida yayi amfani da ƙwayar idonsa kafin kofar ta buɗe ya sanya ƙansa cikin ɗakin, tare da ɗan yin baya da blue jacket ɗin dake saman shigar sa, mutane biyun dake a galabaice ne suka yi saurin dago kansu domin tun da aka kawo su wurin ko sau ɗaya babu wani mahalukin da suka kuma gani.

Gashi yau wajen kwanaki shidda ake magana, komai na amfan da aka tana jar musu ga ɗan madaidaicin stoor nan a cikin dakin wanda abubuwan da suka shafi rayuwa aka tanajar a cikin sa irin su kayan girki ne, maƙulashe ne kayan tea ne, chocolate cake recipe with milk duka dai abubuwa ne da akayi tanajinsu dama, farar kujera yaja irin da ƴan ɗaurin auren nan yana zama akai tare da fuskantar su.
A take suka sha jinin jikinsu sai suka ji duk wani hope na ƙwarin gwiwar dake garesu ya gudu nashi wuri,
Cikin haɗiye miyan wahalta governor Aminu Bello ya dubi AK tare da faɗin.
"Mine hurumin ka na sacemu?,
Wani irin ɗan jujjuya kyawawan ƙwayar idonsa yayi tare da furta.
"Kar kayi magana a loƙacin da babu abin faɗa, koda da abin fadanma kasani shuru bai taba zama illaba, rayuwar duniya kamar series film take, episode episode take zuwa amma duk yawan film ɗin dole ne ya ƙare wata rana"

Ministan gida ne ya ɗan zunguri Aminu Bello, tare da fara kifkifta masa ido ga jikinsa dake tsuma
Shi kuwa cikin aro wata jarumtar ya kuma furta. "Yaro A wasu loƙutan kana ganin kayi nasara shine faɗuwa, haka ma wasu loƙutan ka yadda ka faɗi shine nasara"
"Ka sani sawa a rai ne yasa falke baya jin wahalar tafiya,wanda idonsa basa gani sunanshi makaho, Ammah cikakken makaho shine wanda zuciyarsa bata gani kamar dai ku ɗin nan"
"Ita fa Duniya kamar jirgin ruwa take,
Zata iya kaika inda kake so, kuma zata iya kaika inda take so. don haka be careful respect your mouse ba lallai a wannan karon ta kaika inda kake so ɗin ba"

"Bani da loƙacin ɓatawa loƙaci loƙacinsa,don ba zamane ya kawo niba, a cikin mutanen ku duk mutumin da ya kuskure ya kuma yarda ya haɗa hanyar sa da nawa, saidai uwarsa ta haifi wani badai shiba rayuwata rayuwa tace, haka za rayuwarku rayuwar kuce, kowa ya rufe idanuwansa akan mahaukacin zakin daya fito domin yin farauta, ya kuma toshe kunnuwansa daga hargaginsa"
Sosae suka sake rikicewa ba kuma su sake rikicewar ba Saida ya danna wani ɗan abu mai kama da elevator kyawawan kwalaben wine suka bayyana tare da dasu cocaine cigarettes. Wannan cocaine ɗin ya ɗauka tare da walwale ledar yana matso da ita dab da hancinsa, wani irin kyawawan shaƙa ya mata tare da Ciro kwalin cigarette yana zarar guɗa daya lighter ya ɗauka a cikin abun kana ya karsta ya mata zuƙa ɗaya tare da faso musu hayaƙi Sigarin, zuƙa biyu ya mata ya gama da ita kai da ganin yadda yake zuƙar cigarettes kasan ehhhhhhhhh lalle wannan ubanta ne.
A take yanayin idanunsa suka jirkice zuwa wasu colourn daban, wannan blue In tuni ya kau yana dawo wa jaaaa sosae ga kuma ƙwayar idon ta tayi wani irin fari tasssss tamkar wanda aka ɗura madara a cikin su. Haka ya tashi yana tafiya irin ta wanda ya bugu har yaje bakin kofar sai kuma ya waiwayosu cikin muryarn maye ya furta.
"Duk lalacewan kura a dawa to tabbas tafi ƙarfin kare, haka duk lalacewan mafaraucin zaki yafi karfin alade"
Zuuuuuuu kofar ta koma bayan ya gama fita , directly ya hau lifter ta komar dashi har zuwa asalin wannan narkakken parlourn.
Cikin mayen daya fara ɗibarsa ya nufi kofar yana fita bayan ya loda mata security. Suna ganin yanayin her boss ln nasu suka tabbatar ba'a cikin hayyacin sa yake ba, axton ne yayi saurin buɗe masa murfin motar, shiga yayi suka ja motocin nasu a guje tare barin anguwar baki ɗaya.
Wayar sane ya hau vibrating ring a fusge ya shi ƙoƙarin zaro wayar, *first love* sunan daya bayyana kenan saman screen In wayar, manna wayar yayi a kunnensa bayan yayi picking call ɗin,
"My Boy!"
Shine sautin daya fita cikin wata irin kamalalliyar murya me sanyi, a take yaji jikinsa yaji ya yi wani irin sanyi rauninsa na ƙoƙarin bayyana.
Shirun da taji yamata ne yasanyata ta furta *"William"*
 gaban sa ne yaji yayi mummunr faɗuwa jin sunan data ƙira shi dashi. yanzun ma shirun yamata dama tasan abunda zai faru kenan ɗin, dama tasan hakan ce zata kasance duk loƙacin da zata ƙira shi da wannan sunan na William bakin sa yana masa nauyin ne wajen amsata.
Da dai taga alamun bazai amsa tan ba ya sanya ta furta "ABDOUL-MALEEK KUWAIT! har yanzu kana nan kan bakarnka na ƙim amincewa na dawowarka gida?, rayuwar da ka zaɓarma kankayanxun William.
takai ƙarshen maganar cikin yanayin
Sanyin murya da kuma raunin da muryar ta samu, domin maganar harya fara fita da sautin rawa rawa na rarrabe wa.
A hankali yaji  jikin sa na ƙara yin sanyi sanyi, ita kuma cikin muryarn dake dab da fara zubar hawaye taci gaba da faɗin. "Kasan irin mikin dake cikin zuciyarmu kuwa William?, kasan irin tsananin ciwon dake galabaitar damu aduk loƙacin da duniya zata haskaka a matsayin criminal kuwa?, do on hey ta yes'ka'rev'nvu ka dawo ƙasarka me ƴanci, Onoyin na nan na maraba da dawowarka tare da sauran ƴan uwanka, harda ma jesra, twin yafi kowa missing naka. MOH tana buƙatar ganin ka William.......
Sammmm bazai juri waɗannan maganganun ba hakan yasa hannunsa har rawa yake wajen datse qiran, wayar ya tsura ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login