Showing 63001 words to 66000 words out of 69951 words

Chapter 22 - MIKIYA Book One Hausa Novel

18 Nov 2024

8187

agogon dake manne a bango wanda yake ƙkawace da zanen pop, tare da pisc na Oum shi tare dame martaba.
⭐10:25am agogon ya buga cire pcarp din kansa yayi yana kallon ƙyakkyawar fuskan Oummey'nshi dake zaune kan caution mug ne a hannunta me dauke da zazzafan ruwan bunu marar madara.
Kallo daya zaka mata kagane ita din mahaifiyarsa ce saboda kamar dake tsakaninsu, lumshe idanunsa yayi hadi da dan sauke numfashin ganin zaune cikin koshin lafiya da yayi.
Cikin amon muryansa mai dadi da nutsuwa yace
"Takabbalallahu minna wamin kum alaina wa'alaiki ya Oummey! ". Shafa tulin sumar kansa tayi wanda yasha gyara mai kyau da sheki yayin da yake durkushe agabanta ya dafa hannayensa duka biyu a ƙkafarta, cike da kulawa tace
"Amin barkan mu da wayewar garin Alhamis lafiya habeebty"

Jesra dake tsaye hannuwanta sarke akan kirjintane ta dan turo baki gaba tare da fadin.
"Aifa shikenan nikam tawa ta kare tun da nakan gaban goshin ya dawo"

Cikin yanayinsa na rashin son magana yayi dan murmushi yana faɗin
"Kina kishi da hakan ne jes?”
ya fadi hakan yana maida kallonsa ga mahaifiyar tasa yana faɗin
"Ya Oummey nah ya saukin jikin ki?".
" Alhamdulillah naji sauki tun da ka dubani HABEEBT?,kaje ga Me martaba ya kamata ka sake auna yanayinsa Garga"
Kansa yayi noding yana mikewa tare sa barin shahin......

*BY AMMEY LAYLERH*



*🦅 MIKIYA 🦅*


*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 47&48

# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# Hope
# courage
# Survival
# Humanity
# Inspiration

🤍🔥✅✅✔

⭐ NIGERIA ⭐

A kullum duniya canjama bawa ajin karatu take yau din kace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙkaddarar jiyanka!. Rayuwa mataki biyu ce Acikin kowacce duniya duk wacce kaddararka ta zabar maka zata kaika ne zuwa makomarta, sabanin shine kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurbatacciya.
A yau dai ga merrah wacce take dab da amsa sunan mrs Salma isa manu, wanda komi da komai ya gama kammala kansa daya danganci bikin aurensu wanda ya rage kwanaki biyu takkk.

Kamar kullum yanzu ma zaune take a palon Annenta tana danna wayarta wajen karfe biyar da rabi na yammacin ranan alhamis.
A zahiri danna wayar take amma a badinin ta ita kanta bazatace ga abinda take aikatawa a cikin wayar ba. Abinda kawai ta sani shine tana lallatsa wayar ne.
Sallamar da aka yine ya sanyata dagota da kanga. Hajiya ummace ta shigo da sallama rataye da jaka a hannunta.
Mikewa tayi ta nufeta tana murmushi ta amshi jakar tana fadin "Hajiya sannu da zuwa"
Zama tayi akan kujerar palon kana ta amsa da cewar "Yauwa Merrah na biyo sahun kine dama kwana biyu shiru bakya zuwa. Ni na rasa wacce iriyar amaryace wannan ace gyaran jikinka ma gudunsa kake?' Kyaje gidan ne mijin ya koroki astagfiroullah Allah na tuba. Wllh tsaya kiji wannan bikin da naje Ikaja. Bayan kai amaryar da kwana biyu mijin nan ga daho kaza a dafe rigijff tasha kayan miyarta sharr. Ai wllh nake baki labari yakai gidan su amaryar nan bayan uwarta taci taji salam babu komi tace wannnan ai kunyi mantuwa babu komi a ciki na kayan hadi. Kinsan me yace ce musu yayi yanda sukaji kazar nan haka yaji yar su, to yanzu dan Allah me amfanin hakan? Wllh babban gata nake miki yar nan"
Wani murmushin da baikai zuci ba meerah ta saki tana sunkuyar da kanta kasa. Acen kasar zuciyarta tana furta
(Ni wllh da yamin daidai kuwa amma fa ni bama yarda zanyi wannan me kama da birin ya taba niba, bare ya hada jiki dani nevermine wllh)
Fitowar Anne shine ya katse meerah daga duniyar tunanin data fada. Kallo daya Anne ta mata ta dauke kai tana karasawa inda hajiya umma ke zaune. Gaisawa sukai nan suka fada wata maganar daban ba wacce hajiya umman keta kokarin ganin ta kawota ba.
Jakar kayan Anne ta turama meerah tana fadin taje tayi amfani dasu kafin ta shigo dakin itama. Hayaniyar data kaure a cikin gidan ne ya sanya su umma fita.
Wata matashiyar mata ce wacce taci wani ubansun ado jikin farin leshin daya sha doguwar riga half bubu, sai farar siririyar yarinyar dake gefenta cin mutumci take zuwaba a cikin gidan tana fadin sai an nuna mata uwar data haifi amaryar da ake shirin likama dansu, dan son zuciya da bakar zalama anga gidan arziki shine za'a likema dansu...
Kallo daya Anne ta watsama matar ta dauke kanta tana komawa inda ta fito, shunenta maman affan ta mata ai kuwa ta tafi zata fusgo Anne.
Wani irin juyowa Anne tayi tare da watsa mata wani mugun kallon daya sanya maman sury jan burki daga shirin fusgar da taso yima Annen.
Tsananin kwarjinin da idanuwan annen suka mata ne ya sanya ta hadiye sauran maganganunta, tana kama kanta cikin muryan da baya daukar wargi ko wanne ta furta.
"Idan har kun isa da danku kuje gida ki hana a daure aurensa da DIDI!, jinina yafi karfin a wulakanta shi haka jinin Ayshatul humaira ba daskararren jini bane jinin dake gudana a jikinta tafarfasa yake ya tafashensa yake. Tafi karfin ta hada zuriya da gurbat.....
Maganar ce ta yanke mata sakamakon rufe bakinta da hajiya umna tayi. Ita kuwa sury tuni ta makale jikin mummynta haka nan ta tsinci kanta da shakkun matar ba karamin kwarji ta mata ba.
Daya bayan daya matan gidan suka fara zamewa domin su kansu ba karamin gwarjini Annen ke musu ba barin ma idan halinta najin kai ya tashi.
Su kansu yayanta wani bin sai su wuni ba tare da kalma daya ta shiga tsakaninsu ba, wannan halin nata kuma ba karamin tayarma da malam abdullahi hankali yake ba.
Jan hannunta umma tayi suna komawa parlournta. Nan ta shiga bata baki amma samm taki tanka mata ita kanta tasan wannan gwamutsen hadin auren ba son shi take ba, to amma ya ta iya.
Ta kasance matar da bata jayayya da hukincin ubanhiji in banda haka ko ita da tuni ta farke wannan auren da take ganinsa kamar ba tabbatacce ba har waye war garin yau din. Har yamma hajiya umma na gidan....
Bangaren meerah kuwa haka tayi wunin sukuku gashi ba damar fita bare ta dan fita ko ta samu full energy nata ya dawo. Ta hanyar shakar iskar wage, abincin da tun dazu Anne ta tura mata take ta faman jagwalgwalawa, ita bata ci ita bata dena jujjuya shiba. Har saida hajiya umma ta fasu ta furta.

"ya abincin gabanki tun dazun kinki ci sai famar jagwalgwalashi kike?. Meye haka kike yi da abincin nan meerah?" dago kanta tayi ta kalleta Itama Anne sai ta maida attention dinta kan meerah din. Wani dan murmushi ta saki irin me ciwon nan kafin a hankali tace.
"Umma kinsan dazu da yamma na ci
Wannan abin sam bana wani jin cin abincinne kawai na ji yanzu bana jin yunwar ma"
"Toh idan baza ki ci ba ki rufe anjima kyaci" tashi tayi sai kuma jiri ya dibeta ba tare da kowa ya lura da hakan ba Kawai sai faduwarta suka ji. Da sauri Anne ta nufeta tana jijjigata, dakatawa tayi sai kuma ta juyoo da kallonta zuwa ga hajiya umma tare da furta "Bata numfashi"
"Subhallah dama ba jiri bane ya dibeta?". Hajiya umma ta fadi tana yin kan meerah din " Maza kira malam ki sanar dashi Ayshatu" hajiya umma ta fadi cikin kidima domin ba karamin tashi hankalita yayi ba.
Cikin kankanin lokaci saiga malam tare da Ibrahim babban dansa. Fito da ita sukai suka sanya a mota suna nufar hospital drektly....
A hankali take bude idanunta da sukaimara masifar nauyi, dan motsa idanunta tai tare da dan cije leɓe kadan.
kafin ta samu nasarar bude ido da ƙkyau. "Asibiti kuma?" Ta ambata a hankali tana dan waige-waige da kallon dakin data bude ido ta ganta cikin bazata.
Nan komai ya shiga dawo mata sai kawai ta koma tana jingina da jikin gadon, lokacin wajen goman dare.
"Meerah ashe kin tashi ma?"
Hajiya umma ta fadi tana komawa don yin magana da dactor. Tunda Anne tana gida babu jimawa hajiya umman tace taje. Ba don taso ba ta tafi tana tunanin damuwar da ake taima didinya yawa da kuma yawan tunani.
Sai gasu ita da nurse ta dawo sake aunata nurse din tayi nan tace ma da umman babu wata damuwa insha allah zuwa safe ma zasu basu sallama. "Zanyi sallah ummah"
Meerah ta fadi cikin muryan da yayi low sosae.
Da taimakon Umma ta sakko a gadon sai yanzune ta kuma fahimtar a daki na musamman take, kuma ita kadaice a ciki hakan ya sanyata kallon umman da alamun tambaha.
"Bamusan wanda ya sanar masa ba muma kawai ganinsa mukayi yazo ya sanya an sanja miki daki" dan lumshe ido tayi tana jin ma sam.. Bata son ci gaba da zaman hospital din. Sallan magrib da isha'i ta kawo tana koma ta jin gina kanta da karfen gadon.
Sallamar salman din itane ta katse mata rufe idon da take niyar yi. Hannuwansa rike da manyan ledojin shopping ya shigo. Gaida umma yayi ts amsa tana tsokanarsa da angon kwana biyu. Dan murmushi yayi yana shafar sumar kansa yana jin wani irin madararn dadi na lullebeshi. Don ji yake tamkar ya jawo wannan kwanan biyun su dawo yau, kamar ya janwo nesa kusa haka yake ji da yana da damar hakan da tuni ya dawo da nesansa kusan sa. Kodan muradin wannan lafiyayyan jikin da yake ya kwadaitu sosae da sosae da tsarin halitta da kuma surar jikinta.
Kallo daya ta masa ta dauke kanta shine ya gaida ta tare da mata ya jiki ciki² ta amsa. Nan ya shiga yar firarsa da umma domin gwanar tamu taki ko saurarensa.
Kiran wayar sa friend's nashi suka yine akan sun sauka lafiya suna airport yazo ya dauke su, shine ya san yashi masu sallama yana cema umman abokanan sane suka zo domin tun gobe juma'a zasu fara shagwalgulan bikin. Yama so ace tun laraba suka fara amma malam da kanshi ya dakatar da hakan. Domin ya kawoma meerah katunan shagulgulan ne d nufin ta rabama friendies nata, wannan shine dalilin dakile maganar da malam abdullahi yay, ba tare daya sani ba kuwa haka salman da manyan abokanansa suka kama manya manyan hotels dake garin lagos dim suke abinda suka ga dama.
Ta hilton hotel yabi ya taho da wasu domin debo manyan friends dinsa. Ajeborters na waje sa sauran garuruwa, a lokacin dayay ido biyu da dolly ba karamin baci ransa yayi ba domin idan ya tsani abu ya tsane shi kenan. Haka idan yaso tofa ya so shi kenan da dukkan zuciya da ruhinsa. Cikin kaushin murya ya kalli moussa yana fadin.
"Kaine kazo da wannan abin ko?"
Ya fadi yana masa nuni da dolly wani kafurin murmushi dolly ta saki tana " hey beb baka happy da zowa na ba kenan?"
Tana shirin rungume shi ya ture ta a jikinsa yana fadawa motarsa yana fadin.
"Le's go guys ku muje ko?"
Sauran motocin suka shishshiga suna barin airport din tare da kama hanyar hilton hotel dasu..

Tun da suka shigo harabar hotel din suka soma jiyo tashin sautin Wakar da aka sanya din. Irinta shegen nan wanda suka rike a harkar tantiranci.

Tab katon harabar inda suke yake da wayayyun matasa da yan mata 'yan bana bakwai,wadanda rayuwa da kuma duniya ke musu dadi suke cashewarsu cikin kwarewa, wasu babu kayan arziki a jikinsu mafi yawan mazan kuma gajerun wanduna ne a jikinsu.
Hannuwansu dauke da manyan kwalaben giya wasu cigarette's ce a hannunsu suna busa hayaki. Wasu kuwa pep na shisha ne a ganansu suna zuka su fesar da hayakin cikin wani dan iskan salo.
Tun kamin motarsu ta gama parking dolly dake sanye cikin wasu shegun outfit riga da wanda na baxon ta balle murfin motar fa fito. Akan inda giya, shisha, cigarette's coc suke ta fara nufa kai tsaye. Shishar ta dauka ta mata wata kafurar zuka tana baza hayakinta daya hada hoton love. Zaune takai akan almurun kujera. Tana zare wawakeken shade din daya kusan cinye rabin fuskarta.
Mafi hankalunan yayan ajebor din dake zagaye da wurin ne ya dawo kanta, Nanfa suka mata caaa aka har wasun su na kakarin kama hannuta donsu shakata tare da ita. Kai tsaye club dancing din ta shige ya soma wata kalar rawar daya sanya manyan yaran daukar ihuuuuuuu suna sowa.
Nan fa kowa ga fara kokarin isa ga dolly saidai taki ba kowa damar hakan. Har suka karaci shedancinsu suka tashi wajajen karfe biyun dare.

★★KANO★★

Idan muka koma kano kuwa sosae rayuwar kamal da mariya ke gudana cikin kanciyar hankali, akwai girmama juna a tsakanunsu sosae suna zamansu lafiya yau kimanin kwanakj tara kenan da aurensu. Amma babu abinda ya taba shiga tsakaninsu. Hasalima kowa daki daban yake kwana abinsa. Sammm daga shi har ita babu abinda ya dame su kowa ya harkan gabansa. A kullum zata shiga dakinsa ta gyaro masa ta kuma wanke masa ƙananan kayansa a washing machine. Kamar kullum yanzu ma aikin gyaran ɗakin take hankalinta kwance, ɗomin dama sauya fita take shigowa ta gama masa Aiyukansa ta tafiyarta. Riga da wando ne a jikinta na palazzo ride vizzon ruwan kasa inda rigar ta kasance baka irin me kamar robar nan. Kanta babu ɗan kwali sai fakin gashinta da tayi a ƙasan ƙeyarta. Bluetooth ne a kunne ya tanaji latest waƙar Hamisu Breaker me taken mu daina TSORO. Wanda wakar yake ratsa zuciyanta kai tsaye, domin tabbas talakan kasa shine a wahale babu tsoron Allah a zuciyoyin shuagabannin mu. Kana babu tsoron Allah a wajen wasu jami'an kasar.
Tun ɗazu yake tsaye yana kallonta a ƙalla ya mata sallama sama da sau uku amma shiru bama ta jishi ba. Wani kakan shagaltar yayi a kallonta yadda take motsa ƙananun laɓɓanta shi yafi komai tafiya da imaninsa, aikinta take cikin nishadi da nutsuwa harta kammala ta juyo da biyar tafiya, Nan sukayi hudu dashi saurin ja baya tayi tana sunkuyar da kanta kasa tare da faɗin.
"Kayi mantuwa ne yaya?"
Ta tambaye shi,shiru ya mata yana sake kureta da mayen kallonsa. Jikinta ne ya ɗan soma rawa kaɗan Idanunta na cikowa da kwalla. Gudun ko ganinta a dakin sane ya ɓata ransa, "Don Allah kayi hakuri!" Ta fadi muryanta na karyewar sansomin kuka. Komai baice mata ba haka ta raba gefensa ta wuce....
Taku ɗaya tayi a na biyu taji lallausan hannunsa cikin tafin hannunta, cak ta tsaya zuciyanta na bugawa domin duk tsawon zamansu ko yatsarta be taɓa kwatankwacin kamawaba.
Juyowa tayi Idanunta na zube da hawayen da take ta kokarin ganin boyewa. Ta buɗe baki kenan da biyar sake bashi hakuri ya taryi nata numfashin ta faɗin.
★I LOVE YOU★
Wani irin yankar kirjinta taji yayi numfashin na kokarin barin gangar jikinta. Dagowa tayi a tsorace hakan ne ya bashi daman tallafar fuskanta yana jefa idanunsa cikin tsakiyar nata idanun. Wani kalan mamular baki tayi Idanunta na far far. ★And I really love you 2 appreciate my love★
Kalamansa suka dade mata dirar MIKIYA a tsakar kanta. "I lOBE YHU MARRIYERTOU" ya sake faɗi yana janyo ta zuwa cikin jikinsa. Xuwa lokacin kuwa ƙafafun kariya sun soma rawa tana dab da kaiwa kasa ya rigata yana dorata a kan ƙafafunsa.
Ji da ganinta ne suka dauke na wuccin gadi, {KAMAAL?} Ta tambayi zuciyarta ta hanyar furta sunan sa a cikin zuciyar. Hannuwansa dake cikin nata har loƙacin ta damke da karfin daya sanya kamal ɗago kansa yana me sake dubanta kaɗan. (KAMAAL!) ba tare data sake fargaba zuciyanta ya ƙara ambatar sunan. "Yeah KAMAAL SURAJ RANO na tsananin ƙaunar MARRIYERTOU fiye da duk yadda zaki zata"
"Kasan kuwa da wace kake tare?. Tare kake da Mariya Mariyan da sau uku anasa bikinta ana fasawa, wannan mara sa'ar! Wannan wacce ba kowa bace ita fa ce wacce ta tashi cikin tsananin rayuwa? Sammm Ni banyi zubi da kalan matar auren kaba yaya KAMAAL, A nawa tunanin ka aure nine domin cire mahaifina daga cikin damuwa. Ka aure ni domin kana tausayinmu wacce zaka iya sak........
Bata karasa ba ya rufe bakinta da nashi tsawon minti uku. Sai kuma ya ɗago idanunsa na tara ruwa.
"Na aurekine don ina sonki MARRIYERTOU! Na aureki bisa jagorancin zuciyata domin tun baki kai haka ba nake jinki har cikin raina!, Yanayin nutsuwarki, kamalarki haɗi da kyawawan halayenki ban bayyana miki bane gudun kada na ɓata alaƙarki da tsofaffin samarinki. Amma sai gashi Allah ya bani ke ta inda banyi zata ko tsammata ba!.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login