Showing 66001 words to 69000 words out of 69951 words

Chapter 23 - MIKIYA Book One Hausa Novel

18 Nov 2024

8192

Sai da nayi azumin kwana uku na nuna godiyata ga Allah daya bani ke a matsayin matar aure na, Alfarmar dazan nema daga gareki shine kawai ki SONI!, Ki SONI kada kwatankwacin yadda nake muku ne inason mu rayu cikin aminci bisa jagorancin tsabtatacciyar soyayyar da zamu gudanar a cikin rayuwar zaman aurenmu!"
Sosae ta sake ƙanƙameshi tare da sake shigewa cikin jikinsa tana sakin wani irin kukan da batasan dana me zata ƙirashi ba, kukan farin ciki ko akasin haka?....
"Nasha tazarar dake tsakanin mu irin tazarar sama da kasa ne yaya KAMAAL! Na zata SO be yimin adalci bane dana kamu da son wanda nasan bazan taɓa samu ba har gaban abada a matsayin mijin aurena. Nima INASON KA YAYA KAMAAL! Inaga tun kamin ka kamu da soyayya nina kamu da taka soyayyar yaya KAMAAL. A zatona kamin zarra kafi karfina tako ina Shi yasa na bisne hakan a cikin cannn karshen zuciyata! I LOVE YOU FOR EVERYTHING my Ayh"
Kanta ya dora akan kirjinsa tana jin yadda zuciyarsa ke bugu fat fat. "Da gaske kike? Da gaske kina sona Mrs Ayh?"
Ya fadi kuma yana jefa idonsa cikin tsakiyar idonta, kanta ta gyada mishi tana sake lafewa a jikinsa.....
Bakinsa ya haɗe da nata daga zaunen yana mata wani irin lafiyayyan Romance. Daukarta yayi cilak yana shigewa bedroom nashi, a ƙalla sun ɗauki good 30 minutes kana suka fito hannunsa riƙe da files ɗin daya dawo ɗauka......
Wurin aikinsa ya koma kai tsaye domin kota halin yayane so yake saiya cafke me lefin nan, haka zai ci gaba da zakulo manyan masu laifukan da suke ɓuya ta karkashin kasa. Kai tsaye Lafiyayyen office nashi ya wuce Saida yayi wasu ƴan rubuce rubuce akan file ɗin kafin ya janyo laptop dinsa copying komai yayi ta ciki.
Wayansa da yay ƙara ne ya fidda woyace me muhimmanci dole ya amsa, bayan sun gama ya kunna data da niyar turo sako ta Whatsapp sai abubuwa suka yi ta faɗowa saman screen ɗin woyan musamman ta peonies.
Da niyar share sakonnin Ni yaje amma saiya dakata ganin hoton kamilallar fuskan da bazai taɓa mantawa da ita bane akayi wasu rubutuka akai. Kai tsaye ya gane pisc ɗin na ranar dazai bar kasar ne.
★WANTED?★
Ya sake maimaitawa wani guntun murmushi na kufce masa kaɗan.
"Ya baku baya kuyi duk iya yinku har zuwa makura maza kuyi ta Aman wutarku, don shi idan ya tashi wanka da wutar yake bi ma'ana wankan wuta fire 🔥🔥🔥"
Manna woyar yayi da fuskansa yana sakin ijiyan zuciya bayan yayi wani short rubutu akan fuskan AK ɗin daya juya.


*BY AMMEY LAYLERH*




*🦅 MIKIYA 🦅*


*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 49&50

# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# Hope
# courage
# Survival
# Humanity
# Inspiration
The Beginning of the Beginning
🤍🔥✅✅✔

⭐⭐⭐⭐

Akace salati baya hana ɗaukar rai kowani rayuwar ɗan Adam akwai salon ƙaddarori masu tarin yawa, akowacce duniya akuma koda yaushe kaddara tana tafiya ne daidai da rayuwa, haka kuma tana rayuwa da mune cikin farinciki ko akasin haka.
Sannan kuma babu wani bawa wanda ka iya gujema tarin ƙaddarorinsa lallai ƙaddararmu tana gudana ajikinmu ne kamar jini, akowace rana abubuwa mabanbanta suna faruwa to haka itama ƙaddara takan iya sanjama bawa ako da yaushe, haka kuma babu bawan da yake iya sanja tarin ƙalubalen yadda ƙaddararsa tazo mai ayau gani a daren juma'a wanda wayewar garin azabar itace zata zamo ranar da ALƘALAMIN ✍️ ƘADDARATA zai ci gaba daga ranar daurin aurena. Ko wacce ƙaddara tana zuwarma ko wanne Muminine feji bayan feji haka ko wanne feji yana dauke ne da nashi salon rubutun.

♡✩❤♡♡ ✩


♡NIGHT IN THE MORNING♡

Du inda ka gimla ta cikin shilton hotel ɗin sautin Night music ne ke tashi. Wata iriyar badakalar rawa ake gudanarwa a cikin hotel ɗin. Duk wasu ƴaƴan manya kuwa wanda basu samu halartar sauran shagulan dasu Salman suka shirya ba to ayau kammm sun sami isowa, domin na daren yau din shine shakundum.
Wadan da manyan yara suka shirya ma Salman ɗin ♡BACHELOR's NIGHT✩ duk wasu ƴan gang bang nasu masu ji da fatu da tsantsar wayewa suna cike a wurin. Kallo ɗaya zaka ma wurin ka gane Are not my kind of people domin bana kowa da kowa bane.
Kowa ka kallo yana tare ne da Ben ɗinsa suna kwalɓewa a tare wasu kuma Romance na junansu suke. Kamar yadda uban gayyar da yake tare da dolly ɗinsa da suka shirya tun daren jiya, yanzu ma rungume suke da juna daga shi se wata shegiyar fit out ɗin riga da wani guntun wando, gaba ɗaya gaban rigar a bude yake sai sake shigar da kanta da babu ko wula take. Kwalbar wine ce a hannunta idan tasha saita bashi.
Daga nan surar ta yayi suka faɗa wani bedroom wa'iya zubillah, babu ruwandu da jama'ar dake dakin wanda suke aikata masha'arsu. Suma wani wurin daban suka faɗa........

★RANA BATA ƘARYA

Masu iya magana suka ce wai Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya.
Ni Meerah Ayau nafi kowa yarda da batun domin kuwa nima da kaina na yarda wannan rana tawace kam. Domin A yau gidanmu cike yake taff Yan uwa na kusa dana nesa duk sun gama hallara kansu. Ta ko ta ina hayaniyar ƴan bikice kawai ke tashi masu farin ciki nayi haka basu baƙin cikin ma duk nayi. Ga tarin abinci kala-kala da ake ta hidimar yi saidai kash! Babu dangin Anne'nmu ko ɗaya. Sai Hajiya umma kawai wanda za'a ƙira da dangin Anne'n sai kuma mutanen da ake mutunci dasu.
Zai wasu ƴan ƙananun gulmace gulmacen dake tashi wai babu abinda Anne tayi tanadi na biki. Tanaji tayi shiru ta share su domin ita sammm wannan ba matsalar ta bace, Ni kuwa Ina cannn kuryar ɗakin Anne'n zaune cikin shigar wani mayen leshi maroon color's.
  Wanda yay masifar fitowa dani sai na tashi tamkar wata irin jinin larabawan nan ko kasashen ketare, ga gyaran da aka min ya sake tsatstsafo da zallar kyawuna na asali sosae dan ba ƙarya Anne tayi ƙoƙari ba lefi ita da Hajj umma. Acan ƙasan zuciyata kuwa jina nake duk wata iri kamar yanda aka san duk wata amarya da shiga irin wannan yanayin a irin ranar Ranan. gefe.Shigowar Disha da wasu kawayena suna rangada min guda aka shine ya sake sanyaya jikina sai kace ba wannan meerah'ɗinba ƴar zafin kai. "Allah yayi an daura amarya a gidan Salman, Ni zaki fara Bama wannnan kwallelen farin goran albishir ɗin"
Ban sake tsinkewa da lamarin ba Saida naji shigowar babban yayanmu yaya Ibrahim. hakan shiya sake tabbatar min cewar shikenan an ɗauro auren. gabana sai ya shiga wani irin luguden daka da sauri-sauri wani irin tsoro da fargaba na ratsa min cikin ɓargo da duk wata magudanar jini ta jikina. Shikiyancin da su disha sukaci gaba da min tare da guɗa a saman kai shine ya sake tattare duk wata nutsuwa data saura wa jikina. Sai na samu kaina da sakin hawaye masu zafin gaske da ban san dalilin yinsu ba, domin na gagara banbance komai a yanda ya dace na fahimcesa wanda kai tsaye Ni zan iya kiransa dana baƙin cikin zama mallakin Salman da nayi a wannan rana. Bugun da zuciyata taci gaba yine ya sanya ni lumshe idona a take wasu hawayen suka sake sakkomin. Shewa da dariya suka shiga min suna cewa duk hawayen farin cikin mallakar Salman ne ai hawayen. Ni kuwa ni kaɗai nasan kalan yanayin da nake ciki. Ya tabbata kenan ƙaddarar wani sabon fejin ta sake buɗe min? Ganin kuma yanayin sanyin nawa yayi yawane ya sanya su disha kyaleni, batare da sun fahimci kamar akwai abinda ke damuna ba don sun dauka ƴan izzar ne a kusa.
Daga can tsakar gida kuwa taro yay taro gida ya sake kacamewa da hayaniya irin ta biki, Wasu na hotuna wasu na kwalliya wasu na hirarsu haka ma masu aikin abinci nayi. Bayan daura Aure da kamar mintina ashirin baffanmu ya ƙira Anne, bata ɓata loƙaci sosae ba ta dawo fuskanta da ɗan sassauci ba kamar kwanakin bikin ba. Nan abokan zamanta suka shiga kus kus a tsakanin su bayan sun gama gulmar wanne irin sulun bikine da babu dangin mahaifiyar amarya, a loƙacin ma Saida Aunty labiba babbar ƴar Hajiya umma ta taka musu birki kana suka shiga nutsensu. Domin kowa ya san labiba bata da mutunci kona miskana zarra.
Nan akaci gaba da shagalin biki kowa be tsinke da lamarin ba Saida Anne ta fito cikin wata rantsatstsiyar shigar farin less. Howowo zanso ku hango yadda Anne ke walainiya cikin danyen leshin data dautsa.
Mu kuwa muna can uwar ɗakan Anne wajajen lassar la'asr Aunty labiba ta shiga tare da aunty adawiyya da baby autar Hajiya umma suka shiga niki niki hannuwansu dauke da wasu shegun bags har guda uku. Badan kar ace na fiya kyauyanci ba dana rantse ban taba ganin kome kala da bags ɗin ba. Zama suka yi fuskar ko wannensu dauke da murmushi a fuskarsa.
"Amarya ya kamata ki sanjà shiga ga sabbin kayanki da Anne'nki ta sai miki na fitar biki su zaki sanya"
Ijiyar zuciya na ɗan sauke inajin yanayin bugun zuciyana ya sanjawa tare da cinkushewar yanayin dana tsinci kaina a ciki.
"Amma aunty adawiyya wannan shigan na jikina ma ai babu laifi nake ga, nifa bana gayyar kayan zafin nan!"
Meerah ta fadi tana miƙewa tsaye banɗakin cikin dakin ta shiga alwula ta dauro kamar yadda aunty labiba ta faɗa. Nan kowa ya shiga yin alwular muka gabatar da sallar la'asr. Bayan mun idar aunty baby ta shiga tsara min kwalliya a fuskana duk da banso hakan ba. Gashin kaina da shi kansa nasa gyaran na daban ne aunty baby tama wani irin style. Ta raba shi biyu ta kai har karshen ƙeyata wanda ya sauka har gadon bayana wasu shegun style ta shiga yi da gashin. Saida ta kammala kana ta sake nado shi da ribom's. Wata fitinanniyar riga da sket half bubu na wani shegen luxury catton less, irin me haɗe da jakar nan ta tamarmi sai mayafinsa. Wasu shegun barima me kama da diamond ta sanya min tare da zobenta da agogon hannu. Ya subhanallah a take wani irin kyalkyali ya shiga tashi a jikina. Ga wasu Mayun turarukan da ban taɓa jin koda irin ƙamshin su ta shige ɓarinsu a jikina. A take dakin ya ɗauki sowar kawayena jan hannuna aunty labiba tayi tana faɗin ALHAMDULILLAH sai gaban Anne da baffa har dama wanda basu so ganin wannan babban rana ba, namu ba irin nasu bane.
Ina sanyo kafata tun bai kai ga fitowa ba duk wata jama'a dake tsakar gidan suka zubo idanuwansu a kan bakin kunshin daya wani irin sake fidda kyawun kaɗana. Kwallace take kokarin zubo min ganin tabbas waɗan nan mutanen sun taru ne a yau domin ni, hannuna aunty labiba ta janyo tana karasa fiddo ni zuwa tsakar gidan. Wani irin tsitt duk hayaniyar data kacame gidan a ɗazun sukayi. Ko wanne idonsa na kaina, harda masu sake mitsirtsike idanuwansu.
Wata babbar guda Hajiya umma ta saki tana cira hannuwana sama tare da sake ranbada gudarta tana faɗin.
"ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! Yarinya tayi goshi Ubangiji ya baki zaman lafiya tabbatacciya a gidan aurenki MEERAH, Allah ya kare ki daga dukkan sharrin masu sharri. Allah ya tsoka ne idon makiya akan wannan auren da Allah ne ya hada shi, bawai mutum ba saidai Allah Wllh kuwa mutum din zaija da ikon Allah to bismilla!"
Duk wannan abin ciki daga murya Hajj umma tayi nan fa wasu suka sha jinin jikinsu domin kaff ya'yan baffa mata babu wanda yaba Anne ko gudun mawar nera biyar. A cewarsu a gudun mawa karin ƙarfin biki.
Nan marasa kunyar cikin su suka shiga amshe Hajj umma suna shiga tare da jeruwa da meerah ɗin aka fara buga photuna na garari. Babu kunya Anne ta rungume DIDI'ƊINTA aka musu photos da yawa. Nan manyan yayye maza ma suka shigo akaci gaba da hotunan Raiha ce nanuke da meerah duk inda ta yi cikin tata shigar na cotton less.
Nan fa gida ya sake ɗaukar hayaniyar data fi ta ko yaushe kawayena kuwa sunyi cannn ta bayan kewayen gidan sun kafa party tare da shan disko harda mardiyya da bama shiri, dake dama rashin shirin akan hayatuddeen ne saita sauke ta shigo ake shan shagalin da ita. Wajajen sallar magariba kawaye suka fara mitar basu ga ango yazo ba bare ayi zancen photo dake baby na tare dasu sai tace musu ai suma suna da party'n da suke yine da an daura auren shi yasa bai zoba.
OHO nidai bansan abinda ake ba domin ina cennn ɓangaren baffa wani zazzafan zazzabi ya rufe ni tun ina dauriya har Saida ya kaini ga kwanciya. Nan baffa kuwa ya sameni da nasiharsa na komai naga ni a lamarin aurena tabbacecce ne tun daga rabbi izzati, karna yadda nayi jayayya da hukuncin da Allah yay min. Kana karna taɓa butulcema zabinsa na zama mace mai tsananin haƙuri da biyayya a gidan aure na Insha Allah zanga sakamakon auren nan ko bayan babu ransa. Abinda ya sake sanyaya jikina kenan sai kaina ma ya soma sara min.

Ana idar da sallar magariba ƴan daukar amarya suka zo, tun kamin suzo nake wani irin kukan daya sanyaya jikin kowa dake gidan, kira nake Ni Wllh nama fasa wannan Auren dama ai banaso don karnama baffa musu ne ya sanya ni amincewa toni Wllh na fasa. Nan na tayar da hankalin Anne'na da baffa dama duk wani masoyina, wata irin nasihar dahar nabar duniya bazan taɓa mancewa ba Anne na tamin haka ma baga Hajiya umma ba, domin nasihace irin me ragargaza zuciya harma da ratsa gangar jiki. Nidai kuka na nake a haka har dangin ango suka zo tafiya dani.
Nan fa na ce bansan zance ba na rike hannun Anne na kakam ina risgar kuka.
"Ki sani wannan tafiyar itace mabuɗin bude abubuwa da yawa meerah! Bawai kuka nace kimin ba jarum taka yaka mata ki nuna, yanxu an dena kuka dan anyi aure. Bare ma ki sani naki auren yasha banban da saura, Ki nuna musu ke kibiyar ajali ce wacce sulke baya iya ratsata! Ki nuna musu kedin jinin da...........

Wata farar dattijuwoce tayi saurin damkar hannuna da nata lallausan hannun, wanda ya hanani karasa jin me Anne na take nufi a gaban da ɗin nan?, Motocin da baka ganin iyakarsu wanda tsadarsu kaɗai kan iya juyarma dame ƙaramar ƙwaƙwalwa kai. Cikin kuka nake don haka ban tantace ya kamanni da kalansu yake ba nadai san ban iya hangar iyakarsu. Kar kuce wai bana lura a ah ina lura da komai domin idan naji ana magana har wani sake leƙo da kaina nake. Da bismilla wannan matar ta sanya na shiga cikin wata narkakkiyar Toyota Highlander 2024/2025 bugun American.
Ido a rufe yake amma sanda kamshi da sanyin daya ratsa ko ina na jikina ne ya tilas tamin buɗe jajayen idona da sukaci kuka.kallo ɗaya nama motar na furta.
"Allah ya isanmu" na faɗa kasa kasa ɗan nasan da kukaden mu talakawan kasa aka siya wadan nan shegun motocin.

★SALMAN POV★

Sabo da tsabar farin cikin da yake a ciki jinsa yake tamkar an yimay bishara da gidan aljanna, wai yau shine ya mallaki meerah a matsayin matar sa shi kuwa me yafi wannan daɗi a duka cikin tarihin rayuwar sa.
"BABU!"
Ya fadi a fili lokacin da jerin abokan sa suka yo masa rajiyar angwaye. Haka ya kemashe idanunsa yace babu me shigar masa gida wai shi a matse yake don haka kowa ya kama gabansa. Nan fa suka shiga masa tsiya suna cewa zasu rama ne. Shi dai bai damu ba kansa ya mayar da get ɗin gidan ya rufe dan yasan zuwa yanzun kowa ya kama gabansa.
Har wani sassarfa yake haɗawa da ita wajen isa ga muradinsa meerah wacce kullum sai yayi mafarkinta suna sheka soyayyar su...
Jiki har mazari yake sanda ya ƙarasa shigowa palon gidan da yaji wasu shegen kujeru na alfarma. Da dai yaga saurin kamar bazai masa ba sai kawai ya kwasa da gudu sama kai bedroom ɗin daya tabbar da anan aka ajje masa amaryarsa ya tura.
Tana zaune cikin lullubinta har yanzun kuwa ga wani kamshi dake tashi daga jikinta, wata kakkaurar ijiyar zuciya ya saki yana jingina da jikin kofa domin gani yake kamar bazai zo yagan taba. Amma yanzu ALHAMDULILLAH hankalin sa ya kwanta. Ajje ledar da abokanan sa suka bashi yayi saman stool.
Zama yayi kusa da ita ba tare dako sallama ya mata ba, kai tsaye ya sanya hannunsa yana janye lullufin fuskarta zuwa kan shoulder nata.
Wani irin zabura yayi yanaja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login