Showing 12001 words to 15000 words out of 69951 words
hanna su bayyanuwa, A hankali ta sanya hannunta mai ɗauke da awarwaraye na roba irin masu kyallin nan kwaya biyu pitch color ta shiga mirza saman goshinta irin tana cike dashi ɗinnan.
A hankali ya sake zuba mata ido tun daga yanayin yadda ta zazzaro ido har zuwa sanda ta shiga mirza saman goshinta yadda Idannuwanta suka rinqa sama da ƙasa. Haƙorinsa ya ɗan datse yana ci gaba da mata kallon ƙasar Ido.
"Duk da ance shi ɗin ba kamar sauran mutane bane, amma a yadda nake ji ɗinnan idan har nayi gaba da gaba dashi zan iya kashe shi a matsayina na me kishin ƙasa"
Haka ya riski muryan ta me kama da waƙa take rerawa ba masifa take sirfawa ba, harda irin mutsitstsike hannuwan su bada sautin ɓasss.
Dade beyi niyar jimawa a zaman tattaunawar ba domin akwai manufar shi na yin hakan, akwai saƙon da yake son masu shi su ɗauka. Don haka cikin wani irin jannn hankali da salo me kyau ya ɗaga hannunsa sama tare da mirza shi irin gintsewar nan yace.
"Mutuwa dai kika ce idan kuma ya kasance shi ɗin baya tsoron mutuwar ba fa?"
Zuciyarta ce ta ji ta buga da mugun ƙarfi amma cikin ƙarfafama kanta gwiwa ta mayar masa da amsar daya bata daidai dashi.
"Idan harya kasance baya tsoron mutuwar, ya bayyana kansa mana ga jami'an tsaron da suke fafutukar nemansa ruwa a jallo, nasani dai baifi ƙarfin hukuma ba saidai idan ya kasance shi ɗin matsoraci ne, domin jarumi ba'a san shi da yakin suƙuru ba ya fito ayi na sarari gaba da gaba shida matakan tsaro a gabza yaƙi"
Wani irin ɗan waro mata Idanu yayi, tare da mata alamar jinjina da hannuwansa, kafin cikin hosky voice nashi ya furta.
"Idan kuma ya kasance su jami'an ne da kansu suke tsoron tun karar safa? Mutumin daya Kasan ce baka gane gabansa balle bayansa balle ka gane inda ya dosa, yanzu duk rikicin da tarzomar da ya haɗa a garin nan amma ace yasha, kinga kenan ƙarfinsu yafi ya musu zarrar da basu taɓa iya ja dashi ba, idan kuma sun shirya to Bismillah,
hakan bai hana shi ya shiryawa kansa zuwa mataki na gaba ba kamar yanda ya tsara ma kansa , yana da karfin hali sosai, komai zai aikata yana aikatawa ne cike da kwarin gwiwa ɗari bisa ɗari, tare da yaƙini da kuma sanyawa a ransa tabbas zai yi nasara, Ki sani sawa a rai ne yasa falke baya jin wahalar tafiya,wanda idonsa basa gani sunanshi makaho, Ammah cikakken makaho shine wanda zuciyarsa bata gani kamar dai jami'an tsaron ku.
Haka za Kafin ya sanya kansa cikin harkar sai da ya shiryawa kansa komai da komai, tare da tsara ko wanne mataki!, don haka idan ma da wata manufar suka tsoma zancen zuwa gidan jarida, wannan shine yaƙin sunƙurun da suƙe ikirarin AK EAGLE yana yi, wannan yaƙin iya na filin daga ne bawai na media ba, don haka sojoji, ƴan sanda, wannan yaƙin ba na nan bane, yaƙi ne na iyaka jami'an tsaron da suke ikirarin suna son kare ƙasar su, kana Idan suna jin sunkai sun kuma isa su nuna jajirwarsu, wajen dawo mana da governor da kuma minister ta hanyar nuna jajircewar su a aiki".
Zuciyar tace taji ta matse da tunanin irin fassarar da yayi ma Maganganun sa
Atake taji tana jin wani abu na narkewa a cikin jikinta kamar ƙarfen da ake ƙonawa a cikin wuta, tabbas yayi maganar gaskiya, wannan yaƙi ne na jami'ai, bawai su kawo media ba, kafin ta ɗago wayammmm taga babu shi babu alamunsa, a wurin da yake zaune, jikinta ne ya shiga wani irin mazari da tsoron masifa, tuni ta gaza sarrafa kanta wajen dawo da nutsuwar ta, tana shirin tashi ne kuma tayi gamo da Katar ɗin ganin ƴar ƙaramar fara tasssss ɗin takarda, wanda take ƙaya ce cikin kyakkyawarn ado, tare da tsarin rubutun daya fi kama da a inji aka zana, cikin manyan harrufa aka yi rubutun kamar haka.
*" FLOWER BERRY PIE, THANKS DA KASANCEWA DA AK EAGLE 🦅 "*
A razane ta tayi cilli da takar dar tana juwo gasu MD, bata tashi aune ba sai ganin Md tayi ƙarƙashin dujuwar office ɗin.
To ai shikenan kooooo saimu gimtse🫰
*By AMMEY LAYLERH ✍️*
🦅 MIKIYA 🦅*
{Mai hangen nesa 👀}
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH
#HOT LOVE
#ROMANCE
#AK FOV
#DEEP ASSUMING FOV
____________________
#*NA MARYAM NASEER*
#~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Page 9&10
🤍🔥✅
__________________
★★★★
Ba md kaɗai ba duk wani ma dake ƙarƙashin zamani hankalin sa idan yayi billions dollars to a tashe yake. Cikin tsananin tashin hankali itama ta shiga zara idonta, bawai don tsoron abinda ka iya zuwa yaje ba. Sai don kawai hangen irin tashin hankalin da Annenta da zata shiga harma da baffan ta.
Hankalin ta bai sake tashi ba saida jiniyar ƴan sanda ta karaɗe gidan jaridar baki ɗaya cikin fitar hankamotar ƴan sanda,wasu zafafan hawayen ta kuma sharewa wanda take jin zafinsa tun daga tsaƙiyar ƙirjinta, me cike da tsantsar tsabar AK me zafin gaske wanda a duniya taji bata taɓa tsabar wani abu ba kai tsaye kamar AK ɗin. Gangan zunzurutun matasan da suka yi zanga-zanga bakin gidan jaridar ne suka yunƙuro da niyar kai hari ga MEERAH tare da Md, wanda zuwa loƙacin yake neman fita a hayyacinsa.
Banda zazzara ba ido babu abinda yake ga uwar zufar data riga ta gama kwaranye masa jiki, na tsabar tashin hankalin da yake ciki, kamar bashi bane mintoci kaɗan yake cikin mafi ƙololuwa a farin ciki, amma gashi komai ya zama shuɗaɗɗe cikin abinda bai wuce 30 mint ba. Zufar dake tsatstsafo masa ya share a karo na ba adadi tare da sauƙe numfashi kaɗan, sai kuma ya ɗan kiwo da dubansa zuwa ga meerah amma ga mamakin sa sam babu wani alamun tashin hankali tattare da ita. Hakan ya jefa zuciyarsa cikin kokwanton ko dai ta samu attack ne koma shock zai ce shidai baima sani ba, bai dawo daga duniyar tunanin daya afka ba yaji tsaiwar motar su a police station GTA ɗin dake babban birnin Lagos ɗin.
Babu ɓata loƙaci akayi ciki dasu wanda suka kuma tadda cincirindon al'ummar dake cike da bakin police ɗin, suna fadin a sudai adalci suke so,mebi ba ai harda haɗin Md ɗin dá yayi fira dashi. Shidai Md ido ne kawai nashi sai kunnuwan sauraren domin tuni gaɓoɓin jikinsa suke tsaya cak da aikin su, wajen iya sarrafuwa, A gaban babban d.p.o aka sune su kai tsaye
Su kuma sauran jami'an sukaji da matasan da suka yi zanga-zangan, kai tsaye dake akan babban criminal ne ake magana yasa sam babu wani jan batu akan jinkirta maganar.
*Army Headquarters*
Suna ganin komi dake wakana amma sukayi biris babu abinda suka furta akan maganar dake ƙara yaɗuwa game da kamen da aka yi. Amma ta ƙasa sune sane da komi ɗin dake wakana a police ɗin, amma a zahiri kam shiru kake ji.
A police station kuwa dake Md shine namiji shi suka fi tsananta bincikensu a kansa, amma amsar ɗaya ce sam baya da masaniya akan Ak ɗin. Hakan yasa jami'an ganin kamar raina musu hankali yake son yi, shi kuwa Md tsoro ne me tsanani tattare da zuciyarsa na irin uban gargaɗin da yasha wurin wanda suka bashi batun kai tsaye, don haka baya da yacce ya iya dole ne yayi gum da bakinsa, tunda yasan idan allurar sojoji ta tashi sunfi Mahaukacin kare iya hauka, bare ma wanda ya bashi bayanan kai da ganinsa kasan ba ɗan ƙaramin mugu akayi ba.
*********Gidan su meerah kuwa idan hankalin Annenta yayi dubu to a tashe yake, Raiha kam zuwa wannan lokacin duk da ƙananun shekarun tayi kukan rashin kwanan meerah ba'a gida ba, amma haka anne ta danni zuciyarta ta hana nata tashin hankalin bayyanuwa, ko washe gari kuwa mutan gidan tamkar sabuwar kasuwa haka suka tashi da hada hadarsu, tamkar basu san abinda yake faruwa da meerah ba. Baffa kuwa tun bayan da akayi sallar isha'i babu wanda ya sake jin motsin sa daga mutanen gidan, domin kuwa kai tsaye meerah itace raunin sa, haka za itace sanyin idaniyarsa. A loƙacin da wannan mummunan labarin ya riskeshi, saida yaji numfashinsa ya tsaya cak da aiki, duk wata hanya saida yabi a sirrance don ganin al'amarin bai girma har haka ba, amma akace idan wani sammako yayi to wani kwanan tsaye yayi inji masu iya magana.
Shi ɗin babban malami ne na addinin musulunci amma sai gashi ya rasa duk wata ta ganin meerah ɗin ma kawai, wannan shine dalilin hana bayyana kansa da yayi, domin sam bazai iya kallar tsakiyar idon Anne ya faɗa mata an hana shi ganin meerah ɗin ba.
Sosai bakar Ralls Rayce ɗin ke shahara uban gudun fitar hayyaci a shimfiɗeɗen kwaltan, babban burin Isha Manu bai wuce ace ya ganshi cikin police station ɗin ba, domin tun jiya daya sami zancen hankalin sa yaƙi kwanciya, bacci ma ɓarawo gwanin iya sata kasa sace sa yayi, haka ya kwana cingirgir a zaune domin gani yake ai kamar ma Ak ɗin ne aka kama, don gani yake shine mutum na farko da ak ɗin ya fara illatawa mafi muni a cikin rayuwa.
*AK*
Tunda ya riga da yabar baya da ƙura bai sake bi ta kan kowa ba, duk kuwa irin fifigen da jama'a harma da jami'an tsaron suke famar yi a kans, amma yayi shiru yayi biris da dasu yaƙi magantuwa akan komi. Badan baya da yacce zai yi ba a'a sai don kawai yana son ganin gudun ruwansu ne, ya dai manna musu bajon haukane kawai ya fisge abin sa, burin sa dama saƙon nashi ya Isa duk wuraren da yake son isar kuma sun isa, don haka yaci gaba da shimfiɗa life ɗin sa yadda yake so.
Zaune yake akan ƴar ƙaramar couch ɗin dake dining room, cikin hadaddiyar shigarsa da mafi yawanci yafi amfani dasu, fararen Dior sweet shirt ne sanye a jikinsa, sai kuma dogon wandon trouser kansa sanye cikin luxury fcap ɗin daya sanya cikin natsuwa yake breakfast nashi da ƙayatattun dinner ɗin da Vincent ya musu odar daga wani tsadadde kuma Hadadden eatary luxury
Chips pepper soup na zallar tsoka sam babu ƙashi ko kaɗan a jiki, sai kuma ketchup
Hankali kwance yaci gaba da yin ɗinner gefe guda kuma yana sarrafa laptop ɗin dake gabansa. Kamar koda yaushe yauma zagaye samudawamsa suke dashi tamkar wasu masu gadin gidan wuta, a kasaitance yaci gaba da dakilar laptop ɗin bayan ya kammala breakfast in da kamar 20 minute ya kunna cigarettes yana busa hayaƙin. Almost 30 minutes ya miƙe cikin yana nufar upstairs cikin takun mazan taka.
A police station kuwa duk yadda kuke tunanin wannan abu da sauki toya zarta haka, domin kuwa ta ko ta ina ƙara rura wannan wannan maganar ake. Abin kamar wata alamara saiga labarin kama su meerah ya zama lates a yanzu musamman media da gidajen rediyo a cikin kwana guda kawai. Kusan dai ko ina ba'a rasa ƴan adawa tuni labaran ya gama karaɗe media dama kusan duka duniyar zance baki ɗaya.
Md kuwa cikin kwana ɗaya takk ya fita a hayyacinsa sa, gogar tamu kuwa da ido ne kawai take bin kowa take kuma kallon duk wani abu dake wakana a tsakan kanin su, zuciyarta ta bushe ta ƙekashe taƙi kuma ta magantu duk kuwa uban jaddagadeden da d.p.o yake a kanta zuwa sauran jami'ai tun a yammacin har zuwa wayewar garin ranar.tana zaune ta kafe wuri guda da idonta daya yayi jaaaaa, a hankali wata police ta Turi ɗakin tsananin hasken daya haske mata idone ya sanyata ɗago da kanta, plate ɗin robar dake hannun ta dake shirin ajje mata a gaba, amma kuma ga mamakin ta sai taga meerah ɗin ta ɗaga mata hannu alamar bata da buƙata. ”ma'am Ina buƙatar text book da pen idan ba dmw pls”
Tayi maganar ba tare data motsa daga yadda take ba, ɗan jim police ɗin tayi alamar tunani kome ta tuna kuma sai tayi saurin juyawa tana barin ɗan suƙurƙurin ɗakin ajje masu laifin baya ta rufe. 10 minute sai gata ta dawo ɗauke da text book ɗin da kuma pen tsaye tayi akanta, ba tare data damu da tsaiwar data mata a kai ba ya ta fara aiwatar da abin da zuciyarta ta gama tsara mata, kyawawan idaniyarsa masu kama dana mage ta shiga zanawa a pepper ɗin, exactly tayi zanen full face nashi sai dai iyaka eye nashi ne a bayyana ne. Ita kuwa wannan police ɗin har wani sake karkatar da kai take wajen hango zanen.
Tana kammala zanen ta miƙa ma police ɗin text book in, jiki na mazara ta fice ta text book in a hannun ta kai tsaye babban office ɗin d.p.o RT Atya ta nufa. A lokacin d.p.o na tare da Isa Manu Atya ta ajje text book in gabansa.
”What are you doing to say?"
"Sir. Meryam yebdullahi goni meerah!"
"What?"
D.p.o ya faɗa a zabure tare da miƙewa yana nufar hanyar woje, har da ƴar sassarfa yake haɗawa ganin ya cimma ɗakin da take. Hasken daya sake haske idonta a karo na biyu ne ya sanya ta sakin wani lalataccen kill smile dama tasan za'a rina, samm ta rasa mine ma ya hanata aiwatar da hakan tun a juya.
Zanen fuskar da tayi aka d.p.o ya tura gabanta, "muna buƙatar ƙarin haske akan zanen da kika bamu!"
(Anzo wajen) ta faɗa a cennn ƙasar zuciyarta.
A zahiri kam ɗan duban wanda ake da d.p.o tayi a kai kaice ba tare da shakkar komi ba ta furta.
"AK kenan! Inda har da gaske kuna kan aikin ku, ga Ak nan ku baza yaranku su fara farauta iyaka idonsa ne kawai nima na sama gani"
jikin d.p.o har tsuma yake ya furta "da gaske kina da tabbacin wannan face ɗin na Ak ne?" Noding kanta tayi alamar tabbatar wa.
A 380 suka bar ɗakin tsabar sauri hular d.p.o har faduwa take. Cikin ƙanƙanin loƙaci aka baza fuskar Ak da ake nema ruwa a jallo. Kanka ce me matasa sunyi caaaa a media game da fuskar Ak da aka ɗora.
★★★
Wani irin kafirin murmushi Ajmaal ya saki a lokacin daya kalla zanen fuskar Ak ɗin shishar daya ke zuka ya feso da hayaƙin matashiyar budurwr ko nace ƙaruwar da yake tare da ita ya sake mannata da jikinsa, a bayyane ya furta. "AK muje zuwa da dukkan alamu wannan wasan me zafi ne!, Lallai na yarda da tauraron ki yana haske ƴar jarida meerah, kece tsanin Ni! Kuma nine mahayin" sai kuma ya sheƙe da wata iriyar dariya ta marasa hankali. Tare da hade bakinsa dana wannan budurwar, ita kuma cikin kwarewa a fannin ta wani shiga sarrafa gangar jikinsa tana karasa fitar dashi daga ɗan hankalin daya saura a gareshi.
★★★
Safa da marwa kawai yake famanyi a karo na ba adadi ke nan sai yana dab da cimma burin sa. Sai wannan ɗan gaba da fatihar yazo ya rugaza masa aiki. Baki ɗaya ya gama jigata kansa gumi sai kwaranye masa jiki yake. Idan bai manta ba governor da kuma minister suna hannunsa,kenan target ɗin Ak na gama dole shine.
"Inaaaaaaa hakan ma bazai taba yiyuwa sammmm" ya faɗa da ƙarfin masifa haɗi da kaima bango iska nashi, sai huci yake saukewa. (Kai wannan yaro uwarka ta haifo mana masifa da bala'i wllh) ya faɗa a cikin zuciyarsa. "Dole na dakile duk wata hanyar da nasan wannan ɗan shegiyar yaron da nasan zai ganni, kafin na gama samun mafita"
★★★
A bazata murmushin ya subce daga fuskar Ajmaal (dole na fara nuna maka ba kai kaɗai ne teterors ba Ak) ya ayyana hakan a cikin zuciyarsa tare da ciro wayar sa yana dialing wata number.
"AK! AK!! AK!!!, Da kyau tsohon abokina sheɗanin sheɗanu, kuma tsuntsu me wayo"
"Kwarai kuwa haka ne sabo da mun saba sheƙe sheɗanu tare da kai ba Ajmaal"
"Uyummmm naji daɗi dake fashimce haka Ak baban shadanu a yanzu haka dai nasan ka girgiza ba?"
Jin Sautin lalataccen murmushin Ak ɗin da yafi natsa a kaff cikin duniyar ne ak ya sakar masa. Ɗan zame wayar yayi tare da kallon screen ɗin sai kuma ya sake manna wayar da kunnunsa, still Sautin fitar murmushin ya kuma ji daga Ak ɗin. dip dip dip yaji sautin katse ƙiran da akayi ba tare da an sake furta masa komi ba. Shima murmushin ya saki domin wannan loƙacin yaci alwashi akan Ak ɗin sosai, shi kaɗai yasan shirin daya danajama hakan ciki kuwa harda ziro meerah acikin tafiyar.
To ai shikenan kooooo saimu gimtse🫰
*By AMMEY LAYLERH ✍️*
*🦅 MIKIYA 🦅*
{Mai hangen nesa 👀}
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH
*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Page 11&12
#KIDNAPPING
*DRUG TRAFFICKING
#AGGRAVATED ROBBERY
🤍🔥✅
__________________
★★★
*Police station*
Zaune farin dattijon yake gaban d.c.o bayan gama koro masa jawaban sa akan meerah ɗin,duba da uban kuɗaɗen daya zube masa wanda dama already yau za'a sallames, ganin tsuntsu daga sama gashashshe ne yasa jikin d.p.o har mazari yake wajen bada umarnin a kawo meerah ɗin. Cikin ƙankanin loƙaci sai gasu da meerah ɗin, shi kuma ya miƙata ga wannan dattijon. A kamilance ya musu sallama yana ma Meerah nuni da suke, saida ta ɗan yi dammm na alamar mi hakan ke nufi.kana dai tayi gaban, bata sani ba ko duk cikin aikin ne hakan.
Gaban wata arniyar bakar mota suka tsaya shi da kansa ya buɗema meerah ɗin ta shiga domin kuma zuwa yanzu ta fuskanci kamar gida ne za'a maida