Showing 39001 words to 42000 words out of 69951 words
dake nuna cewar tayi fushi da ita kenan.
Ci gaba tayi da tafiyanta har takai bakin gate din fita daga gidan jaridar, haka ta ringa ratsa manya manyan motocin dake wurin. Tafiya takeyi amma gaba daya duk bata jin dadin yanayinta amma ko a fuska baka Isa gane yanayin da take a ciki ba.
Hango wani me napep yana zuwa ne kuma yasa da sauri ta soma daga hannu tana son tare mai napep din.
Cikin sa'a kuwa ya tsaya cikin yanayin dan hanzarinta ta yunkura da niyar shiga napep din.wata arniyar Rolls *R* Rayce ta danno kanta, wacce kiyastin kudinta a dalar amurka yake daidai $25,000. kamar ance daga idonki sukayi 4 eyes da duk da yau din ma idonsa rude yake da blue shade.
Wani dan banzan kallo ta cilla masa tare da murguda bakinta, kafin can cikin kasan muryarnta irin na tsiwan nan ta furta.
{MARA GASKIYA DAI KO A RUWA GUMI YAKE}.
Fadawa cikin napep din tayi tayi sai kuma ta shiga furta kalmar
”La ilaha illa anta's subhanaka inni kunti minazzalin!”
A bayyane domin zuwa yanxu dai tasan wannan mugun wani abun yake sake nufi da ita....
”Malam nace don Allah kuwa kasan wancen mutumin na cikin motar cennnnnñ?”
Ta fadi da kokarin nuna masa motar, saidai me? Sama, kasa, haka ta nemi motar ta rasa.
”Hajiya wacce motar fa?”
Muryar dan sahun ya farkar da ita.
Ijiyar zuciya ta sauke tana fadin ”muje kawai anguwar dadin kowa zaka sauke ni farkon layi!”
Ta fada tana me sake kallon inda taga motar da yake ciki.
"To Hajiya zaki biya 400"
Me napep din ya fada yana kallonta.
Nooding kanta kawai tayi batare kuma da ta nemi ya rage mata ba, ta bude bag din ta kudin ta bashi yaja suka tafi.
So kawai take taga sunkai gida don Anne'nta tace mata zata aiketa gidan hajiya umma,amma intai dare ba zata aike tan ba ko kafin ma ta dawo ta aika Raiha.
Wani irin kyakykyawan murmushin daya sanya me napep din kallonta ta tayi.Tuno da Anne da tayi Ita kanta batasan iyaka adadin son da takema Annenta ba, Kawai dai tasan Wani irin so takeyi mata na musamman, son da yake tafiya da tausayi mai tsanani bata da kowa aduniyar nan daya wuce mata Anne'nta itane komai nata Garkuwanta haka kuma farinciki agareta ita da Raiha dinta. Hannuwanta da suke hade wuri guda ta sake dunkulewa, tana matukar tausayin Anne'nta sabo da ta tashi ne ba uwa uba Yar uwa Dan uwa wani nata a tare da ita.. Ahankali kuma ta jingina bayanta da jikin kujeran motar.
*{INASONKI ANNE NA}*
Ta fadi hakan acikin zuciyarta tana mejin tsananin shaukin son mahaifiyar nata na ratsata.
Uwar da takejin babu irinta a fadin duk duniya, Uwar da take fatan faranta mata akoda yaushe, Uwar da take matukar son farincikinta fiye da kowa da komi na cikin duniyar.
Aikuwa basu wani debi lokaci ba suka iso gidan kuma babbar sa'arta data ko shirin tada sallah ba'aiba.
Da sallamarta ta shiga kota kan mutanen da suke zazzaune bata biba, Da Anne'nta ta fara cin karo a palo tana duddura humrarta me azabar kamshin gaske. Gaida ta tayi dama kuma al'adar tace hakan, duk idan ta dawo a wurin aiki takan gaida Anne'nta.
Amsata annen tayi da Yar fara'arta tana fadin.
”Ai kuwa da baki zo ba saidai ki tarar Raiha ta tafi!”
Anne ta fadi da dariya a saman kyakykyawar fuskarta me kama da bata yan Nigeria ba.
”Ai kuwa da kuka zanta miki Allah Anne!, kinsan na dan kwana biyu rabo na da gidan hajiya umma ”
Ta fadi cikin muryan shigoba tamkar wota baby.
”Crying Mumu gurl ey kuwa da har videoing dinki zanyi na dora a media with caption ”
Dan micilon bakinta ta turo gaba tare da fara Mirza kafa a palon.
”Yowwa Anne dakko min eyken kinga gudu na tayi, daga gidan su maman Mujaheed din. Aysha CE ma ta tsayar dani na mata wasa, badon haka ba Ina ba mummy Hafsah aikar zan dawo!”
Duk Raiha CE me Wannan maganar ba tare data bari ko numfashi tashaka ba.
Da sauri Meerah ta mike tana ma Raihan hararan wasa.
”Anne dakko saimu tafi tare kafin a shiga sallah”
Da to Anne ta amsa tana shigewa uwar dakan ta babu jimawa ta fito hannunta rike da laida. Harta mikama meerah ta tuna ko abinci bata Ciba.
Dauke wani wargi a idon ta tayi cikin kamewa ta furta.
”Zauna sai kinyi dinner tukunna”
Fada fuska tayi kadan sai kuma ta furta. ”Ayya Anne kinga fa naci tare da disha”
Gyara zaman ta Anne tayi cikin no nonsense ta furta ”Ashe baki shirya fita ba kenan okay?”
Tana gama fadar ta mike tayi tayo tsakar gidansu.
Haka ba don taso ta janwo plask din abincin gabanta, washe baki tayi ganin dan waken fulawa ne.
Ai a tamanin ta janyo gabanta Raiha tace suci tace mata ta koshi. Sai kuma ta dan matso kusa da meerah din tana fadin.
”Kwai da Kwai Maman Mujaheed ta bani, Ashshalle kuma ta bani rufaida yoguht”
Ta fada tana kyafkyafta ido kamar wata mara gaskiya,domin tasan idan Anne taji kashinta ya bushe.
Dan dole suka tsaya sukayi sallar magriba kana suka amshi sakon suka tafi....
Tana fitowa tafiya kadan sukayi ta hadu da Fatima kawarta da suke layi daya, A cikin wata hadaddiyar motar ta prado. rashin kyawawan halin da fatiman bata da shine ya sanyata meerah din yakice ta a jikinta, Amma ita fatiman sosae take kaunar kwayancensu da meerah din, rashin fuska ya sanya itama janye mata amma duk inda suka hadu tamkar tasa zani ta goye meerah din haka takeji.
Tun kamin su karaso tayi parking motar ta.
Fitowa tayi cikin fara'arta ta fito tana ma meerah din magana.
”A ahhh kawata wannan fa ba girmanki bane kina tafiya da qafa zuwa wani wuri, gaskia bakyama kanki daidai ace kina mace cikakkiya da acikin matan make Ishasshiya ce meji da tashen kyau da cikar zatin halitta da haiba fara kyakyawa ga diri son kowa qin maqiyin Allah zaki zauna kina yawo a kafa,Dubeni koni da banbkaiki kyauba dubi irin motar da nake hawa bare ace 500 hundred ta gagareni na hawa napep. bareke kyakykya son kowa kin wanda ya rasa kullum ke fuska kwakume da niqab kina cutar kanki, wllh meerah kullum bazan gaji da gaya miki gaskiya ba akan kiyiwa kanki fada, yanxu dai shigo na rage miki hanya”
Ta fada tana wani iyayi ita nan ga me mota.
Wani dan iskan kallo meerah ta watsa mata kafin kuma ta saki murmushin takaici ta furta.
”Ai dana shigar da aka sameta ta haram kwara na shekara ban kai inda nake son kaiwar ba, dadai na shiga motar da ake sameta ta kyazamtacciyar hanya maras kyau!”
”Nifa abu mafi bani takaici dake befi yanda kike cewa wai bazaki shiga motana ba abu kadan kice haram, ina zinar bajikinki nake kaiwa ba nawa ne kuma bake kikai ba, amma ace kina kawata kina tafiya da kafa gaskia Impossible shigo mu tafi”
”Fatima kenan koke fatana Allah ya shiryar dake babu wani kalar kaddarar da zai Sa Insha Allahu na aikata zina. musamman irin wacce kukeyi fatima karuwa tsirara babu ko sakayawa shine sunan da kike amsawa. Kina wofintar da darajarki ta ya mace kina wulakanta suturar da Allah yai miki kina kaiwa mazajen bariki jikinki,suna amfana da ni'imomin jikinki suna halllakar dake! suna amfani da dan abinda Allah ya basu na dukiya suna dulmiyar dake suna rudar dake!, yayinda su nasu yayayen suna cen a killace a nasu gidajen a garkame.
Auren da ze gagareki nan baba su nasu yayan na gata suke zasu musu wanda dan gwamna se yar gwamna! Yar minister kuma se dan chiaman, Dan shugaban qasa kuma se yar minister'n kudi ko mimister'n fetur!!! Yayinda ke kuwa aure ze gagareki koda dame daukar ruwan layin kune sabida wanda suke batancin dake sune dai zasu koma su zageki!!!”
Wani numfashin bacin rai ta fesar kafin taci gaba da fadin.
”Koda yaron abokanansu sukaji zasu aureki zasuce ke yar bariki ce! Yar Bariki shine sunan dazaki samu daga bakunansu amaimakon Fatima ko *TESTY* din da suke kiranki dashi!!! Ya kamata zuwa yanzu Kima kanki fada fatima ki saisaita nustuwarki da rayuwarki”
Dan tabe baki fatima tayi tace
”Bari kiji ko annabi dakanshi yace mu nemi tsari da talauci daga wurin mahaliccin bayi!, Sanin kanki ne kin rigada kinsan irin kuncin rayuwar da muke a ciki. Duniya taki kowa kanshi kadai ya sani, Masu kudi basa bada taimako domin Allah talaka yana cikin wani irin hali na kani kayi, da qyar da sidin goshi kake samun na break, wani kuma saiya kwana ya wuni be ciba alhalin ga masu kudin cennn sun tara sun rasa yadda zasu dashi. Ba dole muje su amfanu da albarkatun jikinmu su bamu mu kashe wutar gaban mu. yanzu kuma Allah yamun hanyar kasuwanci bazan cuci kaina ba allah ma ya gani”
Fatima ta fadi cikin kwarin gwiwwarta.
girgiza kai kawai meerah tayi wato kudi masifane kuma daudar duniya. ta furta a cikin ranta tare da duban fatiman ta furta.
”Karuwanci yanzu shine sana'ar? dan Allah fatima ki dawo madaidaiciyar hanya duk wani mutum indai masoyinki ne na gaskiya fatan shiryar ubangiji zai nemar miki, bawai ya famfa kiba wllh zina masifa ce fatima, Annabi bafa cewa yai muyi zina ba cewa yayi karmuyi zina mu kuma nesanta kanmu daga duk hanyar da zata hada mu da zina!. ma'ana karmu kusanceta mezesa ki kira wannan da sana'a?”
yatsine fuskarta tayi alamun gajiyawa da qosawa da zancen ta furta
”Meerah banida wani zabin daya wuce wannan idan na dena neman kudi da jikina ke zaki ciyar damu nida mahaifiyata da yan uwana? Ki sani wllh meerah ina sane sosai da haramcin aikata zina amma wllh bazan bari mu rayu da yunwa ba nida yan uwana”
Dan lumshe idonta tai tana me qoqarin hana qwallan idonta zubowa.
"Fatima ki barwa haramcin nan don Allah na rokeki, Kuma fa karki manta na gari basa taba karewa a cikin duniya duk kuwa irin lalacewar da zamani yayi”
”Fatima muje wata maganar kinga ma wani ana kirana wani alhaji ne yake son tear leather a ledar ta, da zaki yarda ai dana jonaku Wllh ki kwashi rabonki kema”
Shiru kawai meerah tayi domin fatima tayi nisan da batajin kira,wannan ya sanya ta Jan hannun Raiha sukayi gaba abinsu. Ganin lokaci na tafiya har Isha'i na shirin kawo kai.
Tafiya suke amma gaba daya cikin kunan rai take tana mamakin wannan rayuwar da wasu suke ganin hanyarsuce madaidaiciya.Tasan a yanzu haka da za'a kasa Mata kashi dari da kyar a samu kwararan talatin na gari, towai meye matsalar? Daga kuma ina abun ya samo tushe?, Rashin hakurinmu?, Rashin kai zuciya nesa da kuma son zuciyoyinmu.
A fili ta furta
”Ya Allah ka mana maganin dukkan matsalolin da suke kewaye da rayuwarmu, ka Zama gatan Mara gata, ka sanyaya zukatan bayinka ya Allah ka kuma nesan tamu daga cikin gurbatattun bayinka”
Haka da taci gaba da tafiya cikin wani irin sanyin da jikinta yayi. Haka sukayi tafiyan babu armashin komai, Ko a gidan hajiya umman ma sama sama suka gaisa suka bata sakon suka dawo gida.
*🦅 MIKIYA 🦅*
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________
*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*
Page 33&34
Bayan dawowansu dake lokacin anyi isha'i sallar tayi kana daga baya kuma tayi wanka. Shirin bacci tayi bayan tayi nafilanta kamar ko yaushe,kwanciya tayi tare da daukar wayanta Deta'nta ta kunna ta shiga WhatsApp nata, sama sama tadan galli status na mutane, sai itama ta koma wurin status din tare da rubuta.
*_BEAUTY IS NOTHING WHEN BRAIN IS EMPTY_*
Tare da sanya emoji na hamma. Har zata sauka sai kuma taga anyi tagged nata a group nasu na *Jonalist empire's*
Shiga tayi hayatudden taga yana tuna mata da fitan da zasuyi gobe da hantsi zuwa wani park. Da _OKay don't worry Allah ya kaimu_
Ta bashi amsa tana sauka.
*district Abuja*
Yana kwance akan irin wannan doguwar kujerar me kama da gadon nan. Lallai sai yau na sake tabbatar da kamannin AK da dirin jikinsa da wannan actor'n Indian film din suke tasananin kama wato *PRABHAS* Sai naga fuskan shin ma kusan nace a ga nina ma yafi *PRABHAS* din ma
haduwa da hasken fata the guy is faultless and flawlesss and very cleaning skin.
Sanye yake cikin wata Riga Latvia Lithuania Luxembourg da wando na kamfanin dior hormes white shirt and a very soft white, masu tsananin taushi da kuma laushi.
Suman kanshi is silky black and shining gashin nan kwance har keyarsa inda ya masa wani dan iskan aski. A hankali ya shiga ware lumsassun idonsa dogayen eye lashes dinsa me suka shiga motsawa, harya samu ya bude idon a kasalance.
He loves keeping straight face din na a matse kamar kullum, Nikam zan iya rantsewa ban taba ganin mutun mai son bata rai kamar AK ba.
well pampered yatsun hannun shi da suka ji gyaran manicure ya lankwasa su suka bada sautin *BASSs* kai Wllh duk inda ake Neman cikakken namiji Ak shine katt kuma babansu, don he's goddam porschy sosai yaji wankan aji da Hutu hadi da haduwa.
Door bell daga taba ne ya sanya shi dakatawa daga niyan nufan bedroom da yake, cikin muryan nan kasa sosai ya furta ”come here"
Arms ne ya shigo shima cikin nashi shigan na bakaken suit, zama yayi tare da kaida ak din a takaice.
Shima zaunen ya koma tare da daukar woyansa yana latsawa.
”Already flight namu zai tashi ne da 4:00pm”
”okay alright”
Ya fada tare barin palon zuwa bedroom, shower ya sakarma kansa.
After 45 minutes sai gashi ya fito Sanye da bathrobe sky blue a jikinsa, daya soft hannunsa kuma dauke da wani towel yana sharce gashin kansa.
Soft fatar Jikinsa sai digar ruwa take, jikin nan yadda kasan kwai da madara don santsi da daukar I do.
Cikin be ko wanne lokaci lokacinsa ya soma shirya kansa, babu jimawa ya fito zuwa harabar hotel din kai tsaye parking space ya nufa. Domin yana da wata fitane kafin jirginsu yabar Abuja.
*Meerah POV*
Dake yau suna ta fita baccinta tasha sai sha biyu saura kana ta fito sanye cikin Arabian jallabiya ta mata. Anne tama sallama 1k ta bata tunda tasan inda suka nufa yau. Adda'ar samun nasara ta data da kuma binta da fatan alkhairi.
Haka ma saida ta shiga wurin baffanta shima sallamar tamay. 1k ya kuma bata sai ta fada masa anne ta bata. Shima adda'ar ya mata ta fito kai tsaye gidan jaridarsu ta nufa.
A bakin gate din gidan jaridar suka hadu da disha da hayatudden sai mardiyya, wacce take faman banka mata harara.
Ita kuwa disha tama manda da batun woni fada da suka yi jiya, da gudu ta karasa suna rungume juna.
”kai masha Allah dear yau kinyi kyau sosae"
Murmushin gefen baki meerah ta saki tana furta ”zaki farako”
”Kar dai Ku sanya mu yi leet oya Ku shiga muje”
Hayatudden ya fadi yana bude musu motar. Da sauri mardiyya ta bude gidan gaba ta shige.
Oho itakam ma merrah batasan abinda take ba.
12:00 suka Isa park din da zasuy aikin ranar akan wani kusa.
Shiga ciki sukayi bayin sun nuna I d card nasu. A inda ake faka motoci suka ajje nasu, kai tsaye A cafeteria suka yada zango order juice sukayi tamkar a gaske. juyar da kanta tayi tana kallon reception din park din yanda iska ke kadawa kaman za'ayi ruwan sama, flowers din reception din sai kadawa suke suna making sounds, wani iri taji zuciyarta namata da bazata iya cewa exactly ga yanda yake mataba. wani iri iri dai haka takeji kamar ana kallonta hakan yasa ta juyo dakanta adan hankali
Duk da yadda take da dakakkiyar zuciya hakan be hana gabanta faduwa ba. Wai me wannan mutumin yake nema da itane da yake ta faman bibiyar rayuwarta haka.
”Naga kinata kallon waje meerah ko wani abune yake damunki, gashi ko juice din baki shaba”
Hayatudden ya katse mata tunani.
Saurin dawo da nutsuwanta tayi tana furta
”babu komi kawai banajin sha ne”
Sai kuma kamar wadda aka tsikara ta mike tana ce dasu ”pls ina dan zuwa”
Ta fadi tare da mikewa tsaye kai tsaye cikin park din ta numa, Ahankali take binsa tamkar me sanda. Woyane a kunnensa cikin yaren labarcin da tamkar a bakinsa aka ruwaito shi yake wayar. Kafin daga karshe taji ya ambaci room 0035 3rd floor. Ganin kamar zai juye ne ya sanya ta saurin komawa baya a haka ya bace mata.
Rasa ma yadda zatayi takai kanta room din tayi, cennnn wota dabara ya fado mata wata maid service CE tazo zata wuce ta gefenta. Ai kuwa cikin sauri tasha gaban wannan maid service din tare da furta.
”please go to room 0035 a 3rd floor ”
”okey biyoni”
Wannan maid din ta mata jagora har xuwa gaban room din.