Showing 54001 words to 57000 words out of 69951 words

Chapter 19 - MIKIYA Book One Hausa Novel

18 Nov 2024

8190

ta sake bude idonta.
A take komau daya faru da ita yanzu ya sake dawo mata da rarrafe cikin muryan kuka ta isa gabansa. "Don Allah ka taimakeni! Na rantse batar hanya nayi ne Anne nace ta aikeni gidan gwaggonta"
"Really?"
Ya fada da alamar tambaya yana fiddo da wata yar karamar aba daga cikin aljihun dogon wandon dake jikinsa tare da fadin.
"Kodai kin biyo wannan abar ba ohhh"
Wani irin zaro idonta tayi tare da fara jijjaga kanta zara fara magana yayi saurin katseta cikin dakilalliyar muryan san nan na no nonsense ya furta.
"Shiiiiiiii"
Da alamar zeeping na bakinta sai kuma yace. "Ki sani gidan nan da kika samu damar shigowa duk a cikin target nawa ne, don hatta napep in da kika shigo duk cikin tarko nane domin ni kaina na'ura ne. Motocin na kaiwa inda nake na tabbatar da akwai wannan cctv footage nan"
Ya karasa da jefa mata abarta yana mikewa tare sai kuma yadan juyo kadan yana sake fadin "Ohhhh Ashe bayan arhar da kike da harda jarum ma kin iya na jinjina miki dama nasan ko waye me ita dole yazo weldone ashe ba silly girl ce"
Daga haka ya juya da nufin tafiya ta gudu ta biyo bayansa tana
"Niban fadama kowa ba don allah ka fitar dani na Kar hankalin Anne na ya tashii bata san na fito ba da mij.......
Wani wulakantaccen kallon daya watsa mata ne ya sanya ta shanye sauean maganarta. Cikin tafiyansa na kamar koda yaushe ya fice ai kuwa tayi wuff ra wawuri hannunsa ta kankame a kirji suka fito tare a dakin.
Da wani kyakykyawan lafiyayyan mari ya sauki kyakykyawar fuskanta me kama da atafa don tsananin laushi da haskenta.
Ba karamin gigitata marin yayi ba amma ta gwammaci ta juro ta shanye daya dai barta a wannan killed house ne ma ko die house zatace mane oho. Zuwa lokacin kuma har an fara shiga sallan magrib hannunsa ta samu ta yankama wani azabben cijon da saida ta fasa mar fatar hannu, amma kota kanta be biba saima wurin daya bari cikin sauri don masallacin da za'ashiga.
Ai kuwa kamar yadda ta shigo yanzun ma tanan tayi nasarar fita kasancewar duk security'n sun riga da sun wuce masjid ne, amma duk da wani gudun bala'i tabar gidan tana faman sauke ijiyar zuciya, Kai tsaye ta sami napep ta fada tare da fada masa sunan anguwar data nufa dab da zata shiga suka hada ido ya mata wannan shegiyar alamar tashi, baki ta murguda masa da yimay alamar yanka wuya tana cewa me napeo din suje.....
A lokacin da suka kawo anguwarsu har ana dab da fitowa a masallacin baffanta, da gudu ta fada zauren gidan saida da tsaya ta daidaita numfashinta kana ta shige cikin gidan. Sa'arta daya babu kowa domin duk rashin mutumcin mutan gidan basu wasa da sallarsu, da sauri sauri tayi alwular itama tana fadawa dakinsu a sukwane.......

*By Ammey laylerh*



*🦅 MIKIYA 🦅*


*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*MARYAM NASEER*

~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 41&42

# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# Hope
# courage
# Survival
# Humanity
# Inspiration

🤍🔥✅
_______________________

Koda Anne ta idar da sallah tambaya daya ta mata shine "daga ina kike? Sai after magrib kike dawo bayan kuma tun sanyin la'asari kika fita?"
Dake ita sammm bata iya karya ba inma tayi karyar nan take ake gane tane ya sanya soma inda indar fadar inda taje din.
Uban tsawar da Anne ta daka mata ne ya sanya ta fadin. "Gi gidan su su di sha naje Anne"
Ta fadi mafanar a rarrabe ga rawan da muryanta yake. Wani irin kallon baki da hankali annen ta cilla mata tare da fadin. "Saidai kuma kinyi kuskure domin dishan tazo nemanki itama tama jima anan din, don haka ina kikaje DIDI!?"
Anne ta sake jeho mata wata tambayar. "Zamu fita wani aiki ne dama shine da bata zo na tafi"
"Kuma ita karyar ta miye da kai tsaye kika gaza fadamin?"
Wasu hawaye ta share amma kuma sake zubowa suke yadda annen ta tsareta da ido ma shi kadai firgitata yake. Haka dama anne take zakayi wasa da ita amma kuma bata karbar no nonsense,sai kuma annen ta sake dubanta a nutse cikin tsantsar kulawa domin ba ta lura ba iyaka tsoron tuhamar da tay mata take gani dangane da Didinta ba.
"Ki dauke tamkar babbar aminiyarki, yayarki kan uwarki kana ki dube ni a matsayin mahaifiyar da baki da kamarta, ki fadamin meke damunki?, domin na lura tunda wancan abun ya faru mood naki ya sanja sosae. Idan har bakiji tausayina a matsayina na mahaifiyarki kin fada min damuwarki ba wanne hali kike tunanin nizan shiga? Karkiji tsoron komai ki fadamin komai din da yake faruwa da rayuwarki MARYAMA"
Kife kanta tayi akan kafafun annen domin ta yarda kafff duniya bata da ya mahaifiyarta. Komai na labarinta da Ak bata boye mata har dauketan da yayi da irin yadda take ganinsa ya kwamushe mutane. Har zuwa yau data sake cin karo dashi wanda ita ko a ranta bata taba kawoma ranta cewar shi ne ba....
Kuri Anne tayi da ido tana kallon didin nata kawai tama rasa ta yadda ya kamata ta fara, cannn taja wani numfashi kadan tare da duban meerah din ta fara jeho mata tambayoyi tana bata amsa ita kuma.
Haka harta ta bata shawarwarin dasuka kamata duk da ma ita nata ya kusan xuwa karshe domin suna cikin satin biki ne tsulum tsulum. Dama kuma daga yau din Anne'n tayi niyar hana abarta fita domin killace ta bata gatan da ake bama ko wacce ya idan za'ai aurenta. Duk wasu hidinduminta suna a gidan hajiya ummah na a gidan kuwa yadda Kasan ba biki za'aiba haka gidan yake domin ko tada zancen ba'ayi. Ba danma wannan rikitacciyar tsohuwar kakar tasu tazo ba da itama kanta har mantawa take da wani zancen aurernta.
Amma itama da biyu tazo yau kwanaki uku kenan domin bata kaunar Annenta sammmm acikin duka matan baffanta ita kadai tafi takura mata sa'ar annen ma daya da take da tsare gida bata daukar wargi ko wanne iri ne kuwa daga wurin ko wanne mutum. Shi yasa sau da yawa matan gidan ke shakkarta yadda kasan irin jinjn saurartar nanne ke yawo a jikinta haka take. Ita kanta meerah din wani sa'in kawai kallon annen nata take. Nan anne ta bata shawarwari sosea kuma taji dadinsu tare dajin nutsuwa ta musamman. Don duk wannan tsoron saita nemasa ta rasa Lallai sai yanzu ta yarda da wannan karin maganar ta bature Na *_A problem shared is a problem solved*_ Sai gashi tun ba'aje ko inaba komi yazo mata da sauki.
"ALHAMDULILLAH!"
Meerah ta fadi incheerfully.

★★KANO★★

Yau kwanakin su baffafofin kamal hudu a kuma yaune suke shirin komawa. Amma sai baban mariya yazo da batun kawai su tsaya a daura Auren dansu a gabansu, da sunso kin tsayawar saida kamal din yayi magana kana suka yarda zasu tsaya a daura auren.
Bayan sun sake kiran dangi sun sanar musu wohoho zokaga yadda ake bidiri a dangi nan fa mata da maza suka ringa yowa tururuwa suna dannowa kano gidan kamal. Sunce shima sai sunyi may auren gata irin na ko wanne da, Wasu a gidan kamal din suke wasu kuma a gidan baban mariya aka sauke su. Da yamma kamar yadda baban mariya ya bukata aka daura auren KAMAAL SURAJ RANO da amaryarsa MARIYA USMAN SHEKA akan sadaki dubu dari da hamsin. Akwatuna kuma daga baya zaiyi kwasam saiga abinda ya kusan gigita duniyar kamal domin ga sanarma Ak a kurarren lokacine don besha ma zaiga sakon shiba. Amma sai gashi ya niko gari tun daga lagos zuwa kano dake dama ya taba zuwa sau daya bayan Shi kamal din ak din ya kirashi abujan nan da yaje.. Shi da kansa ya amsawa kamal auren mariyan ya kuma hada musu party dinner a wani katon holll. Ya kuma turama kamal din zunzurutun kudi har million biyu.
A daren yabi girjin dare ya koma wajen sha daya da wani abu yabar kano shida arms, Washe gari aka sake sabon biki kana mazan suka tafi sauran maran kuma sai an gama shagulgulan bikim kafin su tafi. A wata sabuwar anguwa kamal yasai gida yabar wannan baban mariya ya aika a gano gidan don su gane girman gidan saidai abin mamaki kamal ya zuba komai babu abinda bai zuba musu ba. Dade da kayan kitchen ya zuba musu wasu sai yan tsitstsinen da ba'a rasa ba.
Umayma harda kukan ta a lokacin da danjinta dana malam ke sanar dasu abinda kamal din ya musu. Dama yar gudun mawar da yan uwa da aboka nan arziki suka hada musu zasuje su mata kayan dakin, kayan kitchen kuwa dama basa lissafi dashj lallali kamal ya zo busu da wani babban al'amarin da bazasu taba mantawa dashi ba, zuwa yamma aka shiga jibje musu wasu shegun akwatuna masu shegen kyau da tsada. Wannan aikin nabban abokinsa ne ZAYD suraj. Wanda wani aikine ya taba hadasu a wata cout akan shariyar wata yarinya da akayi raping nata kuma kamal ne dan sandan daya jagoranci case din har zuwa sanda yayj winning ta hanyar mikasu ga cout din da anan ne suka hadu da Zayd din wanna shine wanda ga karasa aikin ta hanyar jajircewarsa harka aka yaron senetor na garin kano a prison. Kunsan magana ake ta sarauta a wurin.
Akwatuna saida aka sauke musu set uku ko wacce da kolonta. Yaufa ake yinta dan fulani yaje asibiti dubiya an bashi lemo da kaji akace kado fito yace ahhhhhhh ai nikam naga makwanci. To hakace ta kasance da iyayen mariya Hakika duk wanda yayi hakurin dafa dutsi to asannu zaisha romansa. Sunci wuyar sun shanye dakan da dukan sai gashi sama taka allah ya basu dami a kala.
Duk wasu abubuwan al'ada suma saida sukama kamal suka mika a hannun danginsa. Dare nayi aka mika amarya mariya wa gidan mijinta a yanzu kamaal suraj rano.

Sosae tasha amarya mariya tasha kukanta kasancewarta mutum bame hayaniya bane ya sanya sammm babu wani batun tada hankali akan maganar auren.
Haka dai al'amura ke wakana cikin kwanciyar hankali komai yaci gana da tafiya.

★★Lagos★★

Gidansu salman kuwa mahaifiyarsa da yayar mahaifiyarsa ganin dai tabbas auren na shirin tabbata ya sanya hankalinsh tashi matuka, yanzuma zaune suke itada yayarta me suna Aunty mariya sai kuma yarta sury idon nan yay hulu hulu dashi nashan kuka. Ran kowa a wurin a bace yake, cikin kuka sury ta rarrafa gaban mom salman ta kama kafafunta fadi take.
"Mom don allah ki taimaki rayuwana wllh ni salman nake so shi kadai nake kauna a matsayin abokin rayuwata! Mom taya kuka min haka bayan kunsan cewar ni shi kadai nake so"
Ta fadi tana sake rushewa da wani kukan Salman da shigowarsa kenan yaja tsaki "Mtsss ni kuma uban wa yace miki zanso mace kamarki babu baya babu gaba, ki sani rayuwar ma da kikai dani costa risca ba ason raina bane. Don dai kawai muna gida daya ne kuma babu wata beb din a kusa shi yasa ma har na nemaki nayi maleg dake".
Yana fadin hakan yay haurawansa upstsaid nashi.da wani mugun kallo umma mariya ta bishi kafin da dubi mam ta mike a fusace tace aidai kina jin abinda wannan watsatstsan yaron naki yake fadi a gabana, amma kikai shiru to wllh idan har ina numfashj a duniya babu wanj shegen daya isa daura wannan auren alkawarinane wannnan kuuma kinfi kowa sanin daukan alkawarina daidai yake da bi takan kowanne shege ne, koda kuwa za'a zan bada da kisa ne to kuwa saina cika wannan alkawarin.....

Fuuuuuuhhh taja hannun yarta suna fucewa a gidan Zeey dake kitchen a lafe ta share wasu hawaye tana jizar labbanta. Tare da fadin "ai wallh inda numfashina na gangar jikina ahalin wannan gida kuda kwanciyar hankali kuma kunyi sallama". Tana fadan maganar tabar kitchen din tare da laluben wata number a wayar da kawai wata jar alama ta mata babu suna.
Woyar na shiga ta zube akan gwawowinta tare dayin sujjada daga inda take.ta furta "Ran uwar gijiyata ya dade". Daga cikin woyar kuw wata kakkarfar tsohuwa ta wagaje wargajejen bakinta ta hakwaran sukayi tsatsa ta kwashe da wata dariya me kama da kukan jaki.
Kafin ta shiga fadin "An gaida kura me dauke da fatar akuya Birinya baki jelen banza kedin kamar hadari kike malafar duniya ba shirgi maganin bari ta wajena, meke tafe da wushuwatu na?"

"Alfarmar kamar ba alfarma bace a badini da za'a juwa gabansu zuwa bayansu bayansu ya koma gabansu nake ga hakan kawai zaifi, domin naga kamar ba masu ganewa da fahimtar bane"
"Hhhhhhhhhhhhh
Hhhhhhhhhhhhhhh
Hhhhhhhhhhhhhhhhh
Rainon shegu karki damu dumuwasi na tare dake yar shegiya uwar tsinannun, jaraba a cikin jarababbu makata a cikin makatattu annoba a cikin al'umma hinge kike babu me iyawa dake wushuwatu, dan daukar fansa aka yiki"
Wata iriyar dariga zeey data koma wushuwatu ta barke dashi tana saisaita yanayinta ya koma normal daga na mummunar halittar data koma zuwa zeey din asalin da muka sani..
Shi kuwa salman saman lafiyayyan gadonsa ya fada tare da fiddo wayarsa kai tsaye data ya kunna tare da kiran dolly video call. Fitowarta daga wanka kenan tana daure da wani guntun towel ga wani bature kwance akan lafiyayyen gadon hotel din, ya tukun kune jikinsa da tattausan farin duvet daga shi sai wani transpared pyjamas. Woyanta da dama alread datanta yake a bude ta dauka, ganin me kiran saida ya sanya tadan bata fuska kana ta dauki woyar zama tayi akan stool na mirror'n. Kallonshi tayi yana kwance daga shi sai longsleev pant sleek wani irin numfashi ta sauke cikin muryan yar shogwaba ta furta.
"Ohhhh my babyna I miss you somuch mua" ta bashi wani kyakykyawan kisses ta cikin woyar. "I miss you so much dee" ya fada yana gyara kwanciyarsa yana dan lumshe ido domin tunda ya baro poland bai sake mu'amulantar wata mace ba, domin shi ba da kowacce mace yaje iya mu'amularsa shi ne ma dalilin daya sanya ya ware dolly ita kadai dinta.
A hankali ya shiga bude idonsa sai ya hango wani kakkarfan bature yana nufo dolly'nshi, Wani irin shafarta baturen yayi wanda hakan ya zoma dolly a bazata domin ita har tama manta cewar tare take da wani.da karfin masifa ya rumtse idonsa yana jin jijiyoyin jikinsa na tashi na tsantsan bacin rai. Me kenan?Amananshi dolly taci kenan kome? Meye wannan yake yi a tare da bai karasa maganar zucin saba wannan baturen ya finciki mitsil towel din dake jikin dollyn tare da wani irin hugging nata.
Wata kara salman ya saki cikin tsawa ya mike tsaye a fusace tare da ambatar.
"Dolly!!!"
Wani irin mikewa tsaye dolly tayi babu wata² ta dauke fuskan baturen nan da mari cikin tsawa tace "I hate yhu Vham I hate that"
Salman kuwa tuni ya datse kiransa wani irin dafe kansa da hannuwansa yayi kansa na wani irin sara masa lokaci guda, bathroom ya fada ya sakarma kansa ruwa kozaiji dan sausauci jin zuciyarsa yake tamkar yankar naman kirjinsa take tana zazzabowa kasa.
Da bathrobe ya fito sanye a jikinsa sai kamshin shower gel yake da sauri sauri ya shirya ya fito da nufin xuwa club haka ko park,don ragema kansa takaicin dolly.....

Mom nashi ce zaune a parlon har lokacin laptop ne a gabanta dana famar sarrata cikin kwarewa, sai zeey dake dan matsa mata kafafunta sama sama. Har yakai gab bakin kofa mom bashi ta tsayar dashi ta hanyar ambatar sunan shi.
Cakk kuwa ya tsaya tare da juyowa yana kallonta "Dawo inason magana dakai ne" ta fada cikin rashin wargi.
Dan yamutsa fuskarsa yayi yana fadin ta jira yanzu zai dawo cikin muryan no nonsense ta furta "Dawo nace"
Dan dole ya dawo yana zama tare da tankwashe kafafunsa a gabanta yana fuskantar cikin yanayin jin haushi.
Kallan shi mom nashi tayi tana ajje laptop din dake kan cinyart zuciyarta na quna tace.

"Se yaushe ne zaka daina kuntamin da rashin daukan maganar mahaifinka fiye da nawa, sai yaushe zaka me amfanin dazanyi alfahari dakai amatsayin dana Salman? Kullum mahaifinka shine a samana akan dukkan wasu lamuranka!. Menene yake faruwa acikin kanka ne da kwata kwata babu ranan da zakasa nayi alfari dakai a matsayin dana? Ban isa dakai ba ban isa sakaka abu ka yimin shi ba cikin dadin rai....
Hannuwanta ya kama yana hadewa cikin nasa tafin sai kuma yadan rausayar da kansa yana sakar mata murmushi. " Mommah me yasa kullum kike ganin tamkar baki isa sani abu nayi ba? Kullum maganar kenan sabanin ra'ayine kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login