Showing 3001 words to 6000 words out of 69951 words

Chapter 2 - MIKIYA Book One Hausa Novel

18 Nov 2024

8171

da kuma aiki da zuciya kamar ABDULMALEEK KUWAIT AK zai iya zama ɗan ta'addar? kamar yadda kuke ƙiransa da shi, dole Akwai dalili ko nace dalilan da suka sa ya zare kansa daga cikinmu”
Ba shi Ajmaal ɗin daya qA@@ maganar ba shi kansa mr. President ɗin yasha jinin jikinsa, wani irin shiru ƙatoton office ɗin ya ɗauka, kowa da abinda yake sakawa acikin zuciyarsa, wani irin shiru ƙaton office ɗin ya ɗauka na kusan second 40.kafin Ajmaal ya magantu "ko tantatama bayana yi kana ɗaya daga cikin ƙashin bayansa"
Ya buɗe baki da shirin sake yin magana keñan mr president ya Wani irin doka table a take komai da yake kai ya tarwatse komai yayi nashi wuri fuuuuu ya fice a office ɗin a fusace, ganin haka ya sa duka soldier's ɗin suma suka mimmiƙe suna barin office ɗin, wani irin kill smile Ajmaal ya saki loƙacin da yake dab da fita.


*ISAH MANU EMPIRE🔥*

Wani katafaren ƙerarre haɗaɗɗen luzary ne iyaka ganinka gini ne Irin na manyan ƙusoshin kasar,wanda suka ci suka sha kai harma suka tada kai, baki ɗaya ginin gidan ya kasance na glass da glasses ne. Duk kuwa irin girman da gidan yake da, amma kewaye yake da uban wasu jibga jigban soldier's.
Kai tsaye katafaren parlourn gidan na kutsa kaina,da wani farin dattijo na fara cin karo wanda keta faman safa da marwa. Hannuwansa goye a gadon bayansa wanda a ƙalla zai iya kaiwa shekaru 80 ko irin da biyar ɗin wani irin sintiri yake famar yi, wanda kallo ɗaya zaka mashi ka kai tsaye ka gane cewar tabbas baya a cikin hayyacin sane, da ƙarfin masifa ya dunkule hannunsa tare da kaima iska naushi.

"Why is everyone afraid of him? Wanene shi yaushe ma aka haife shi dahar zai sanya ni gudun tseran tsira"

Yayi maganar Cikin zallar ɓacin rai da kuma jin ƙona daga cikin tsaƙiyar ƙirginsa.

Da sauri ɗaya daga cikin samudawan mutanen dake zagaye a ɗakin suka haɗa baki wajen furta.
"Ko wa ye izini kawai zaka bamu!, mu kawo maka kansa BOSS"
Idanuwansa da suke rine sosea ya ɗago tare da zuba musu jajayen idanunsa da suka ƙanƙance. Numfashi ya fesar me zafi kamar bazai magana ba, sai kuma ya magantu, Cikin wani irin dakakken sauti ya furta.
"EAGLE, MIKIYA Shi nake da buƙata!"

A razane A ƙiɗime hankali tashe suka ja baya namomin jikinsa na rawa, suka shiga bin boss in nasu da kallon You are smart 😳😱👀

Hhhhhhhhhh to ai shikenan 😅🥰 A gimtse 🫰 🙃♥️✅

*BY AMMEY LAYLERH ✍️ ✅*


*🦅 MIKIYA 🦅*

{Mai hangen nesa 👀}

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________


*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Page 3&4

🤍🔥✅

★★★Sosai yasha barci mai lafiya a safiyar ta yau kasancewar a daren jiya ya jima bai kwanta ba. domin bayan ya dawo daga fitar daren da yayi sosea yayi aiki a cikin laptop nashi,wanda ya raba dare yana yi. Sallar asuba ma daƙyar ya fita masjid dake cikin anguwar yayo Ahankali ya soma buɗe lumsassun Idanunsa da har yanxu suke cike da barci, santala santalan fararen sawayensa ya fara zubowa kan tattausan carpet ɗin dake gabansa. A nutse kuma ya miƙe yana nufar haɗaɗɗen bathroom nashi, shower ya sakamar kansa sosai ruwan ya dake shi, kana ya tara ruwa masu ɗumi da daɗin ƙamshi a cikin bathtub,Wanda gefe da bathtub ɗin akwai drawers masu yawa da wata full sized jaccuzi da kuma site din wata striated rectangular glass shower tana wani fidda wani irin ƙyalli, kamar ba'a taɓa amfani da shi ba shima gefen sa da akwai fixtures masu ɗaukar hankali sosai. Yaja tsahon loƙaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe chocolate Colo mai azabar taushin tsiya
dan har wani wani maski-maski take yi tsabar taushi da kuma laushinta,da mini towel ɗin dake a hannunsa ya shiga tsane jiƙaƙƙiyar tulin sumar dake kansa mai tsaho, Fuskar nan a tsuƙe Samm babu alamun rahama a cikinta.
Gaban ƙaton mirror'nsa ya nufa cikin tafiyar jin kai da kuma isa.
Hand dryer dake saman mirror ɗin sabuwa fil ya ɗauka ya jona a socket, ya shiga busar da himilin sumarsa da tafi kama data ƴan India, lotion ɗin dake jere saman mirror'n ya shiga shafa wa jikinsa sama sama. Saida ya mulke jikinsa da spray's nashi masu azabar ƙamshi da tsada, kafin ya nufi gaban wardrobe nashi data kusan cinye bango guda.
Tsabbb yayi shirinsa cikin wasu haɗaɗɗaun track suit baƙaƙe, sai glass ɗin daya sakaye idanunsa a ciki tare da facemask ƴar gadon, phone's nashi kaɗai ya diba yana nufar main Parlour, cikin takun cikakkun mazan dake ji da kansu. Kafin ya fito tuni su milse sun gama shirya komai daya dace, jin takun tafiyarsa da baya taɓa ɓuyane ya sanya su risinar da kansu ƙasa, cikin girmamawa suka haɗe baki wajen furta
"Good morning Boss!"
Saida yaja wasu luƙuta kafin ya amsa "kuna lafiya" iyaka saman laɓbansa.
"So boring Boss"
Wannan karon kammm da ka kawai ya amsa su, yana zama kan ɗaya daga cikin ƙayatattun kujerun dake kewaye da dinin Area ɗin,
A ƙasaitance yaja wata haɗaɗɗiyar kwalba wine Wanda naga ansa with alcohol, zubawa yayi a glass cup ya farasha, bai wani shada yawa ba, yaja plantain chips ya fara cakuta kaɗan yaɗan taɓa ya tashi tare da wine ɗin ya koma kan caution ɗin parlourn ya kafa bakinsa ya fara sha inda saida Ya shanye Kafin ya ajiye bottle ɗin. Laptop ya janyo tare da buɗe mukullan sirrin ya shiga sarrafa abarsa cikin kwarewa.
A rikice a kuma ɗimauce Rooney ya faɗo ɗakin cikin tashin hankali ya nufi ogan nasu kai tsaye, system ɗin dake hannunsa ya dire gaban uban gidan nasu.
A tare miles axton lani da kuma Vincent suka ja baya suna toshe bakunansu, hankali tashe suka juyo baki ɗaya da nufin Boss ya kalla laptop ɗin, amma ga mamakinsu abinda suka kalla ɗin ya tada musu hankali shine Boss ɗin nasu yake kalla hankali kwance tamkar babu abinda ke damunsa ko kuma ya girgiza shi. A baɗini kuwa wata iriyar tsuma namomin jikinsa suka ɗauka.bai motsa da ga zaman da yay a lallausar kujerar ba ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yayinda bayansa ke kishin kiɗe jikin kujerar kansa a sama kaɗan, Yanda yay biris ɗin sai ka ɗauka baima fahimtci kamai dangane da hakan ba, Yaja kusan 10 mint kafin yaja wani irin huci ya furzar yana mai buɗe rinannun idanunsa da suka sake wani irin garai-garai ai nahin suffarsu ta idanun mage na sake bayyana a fili.
Zaune ya tashi da ƙyau sai dai a nutsensa yake Samm babu alamun firgicewa a tare dashi,Sudai baki ɗaya sun gaza samun Nutsuwa sai kai da koma suke famar yi a cikin parlourn, suna a cikin wannan alhinin ne kuma get man na gidan ya faɗo parlourn against.
"Boss da akwai matsala"
Wani irin rumtse idanunsa yayi a duniya kalma mafi muni daya tsani ji itace kalmar yaji an ambaci matsala, ya tsani jin kalmar andaɗe da fice wannan babin, don haka ya kalli get man ɗin tare da ɗunkule hannunsa tamkar wanda zai kai naushi, sai kuma ya kaima iska naushin, yana fesar da wani zazzafan Numfashi, loƙaci kaɗan kamanninsa suka sanja jikinsa ya shiga rawa kana ganinsa zaka san he is not on his mood,musamman yadda yanayin jikinsa ya sanja tare da wani irin tsuma.
Cigarettes ɗin dake jere gabansa ya ɗauka a zuciye da sauri Vincent yazo gaban sa tare da kunna masa lighter ya fara zuƙarta a haukace, cikin ƙankanin loƙaci ya har gitsa parlourn da hayaƙin cigarette.
Saida zuƙe wajen kara biyar kafin yaji zuciyarsa ta ɗan risina, cikin hosky voice nashi ya furta
"A tura saƙon kai tsaye!, Vincent maza a nemo mana biza daga nan zuwa yamma"
"An gama Boss"
Suma suka haɗe baki wajen faɗar hakan suna fita daga parlourn baki ɗaynsu, Shima da ƙyar ya iya miƙewa da ga parlourn ya nufi bedroom ɗinsa.
Zaune yakai saman lafiyayyan gadonsa
         Yanda ya zauna shiru ya dafe kansa zaka ɗauka ciwo yake masa ne. Amma sam ba haka bane Abubuwane kawai suke masa kai-komo a rai da suka wayi gari dasu.
Ba yau ne ya fara cin karo da matsaloli da ƙalubalen rayuwa ba, domin zai iya cewa kusan a haka ya rayu, Amma na yau ɗin sai yafi ƙona zuciyar sa fiye da koda yaushe,dan duk sunzo masa a bazata ne. Hakan na nufin ya sakankance da yawa kenan Sannan dole ne ya sake shiri in har yana buƙatar abubuwa su tafi masa a yanda yake buƙata anan batare da tangarɗa ba.
Goran ruwan dake a Centre table ɗin ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa, Sai da ya shanyesa tas sannan yayi cilli da bottle ɗin. Sake furzar da huci mai zafi yayi a karo na ba adadi yana sake nutsar da kansa. Sosai abubuwa masu yawan gaske suka shiga ƙoƙarin zeroying Brain nashi.
Tamkar kuma wanda aka zabura ya miƙe aɗan zafafe yana yin gaban ƙofan Glass ɗin dake a shafe da Pics manya na emeji me hoton lion, babbar yatsar hannunsa ya sanya a take wurin dake a shafe yayi On tamprint na yatsunsa, zuuuuuuu wata haɗaɗɗiyar ultra door ta baiyana. Wasu manyan Computers ne A ɗakin dasu jojjone ta ko wacce kusurwa dake ɓangaren, akan wani ƙayatacce dogon table saikuma macbook akan wani dogon lumtsatsen kujera, Zama cikin hanzari tare da ɗaukar MacBook ɗin dake kan kujerar, buɗewa yayi yafara aiki cikin ƙwarewarsa da kuma baiwar iya sarrafa ko wanne abu, yakai kusan 40min yana danne danne, wata iriyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya tashi yana barin ɗakin da yafi kama dana bincike.

Yana fitowa daga wannan ɗakin ya ciro iphone XR ɗin sa, NO na Vincent yayi dialing NO In, cikin ƙanƙanin loƙaci daga ɗaya ɓangaren ya cira wayar yana faɗin
"Boss"
"Get ready to go out operations!"

Da wannan ƙasaitar nashi yayi maganar yana zare farar Morocco ta mazan dake jikinsa, cikin sauri sauri ya shirya kansa cikin straight leg trim trouser sai black Versace greco hoodie, ƙafafunsa sanye cikin wasu haɗaɗɗaun black hermes cover shoe, sai hannunshi sanye cikin wasu haɗaɗɗun safan hannu, ga kuma facemask ɗin dake saman fuskarsa dake saye cikin sun glasses ɓaki wuliƙ dashi.
Yana fitowa coumpaund ɗin tuni wannan samudawan sukayi shiri na musamman sun ɗane cikin rantsatstun baƙaƙen motocin su. Suna ganinsa suka hau fito da shewa suna faɗin "BOSS! BOSS!! BOSS!!!" Cikin wani irin salo da ƙwarewa Miles ya yayi tsalle ya diro yana shirin buɗewa Boss In nasu car, hannunsa dake a rufe ruff ya ɗaga masa yana mashi nuni da power bike ride ɗin da zai hau, sara masa yayi yana komawa cikin motar, shi kuma cikin wani irin taku ya nufi power bike ɗin tare da daura hannunsa akan key na machine ɗin, wani irin tsalle yayi cikin salon daya zam ɗabi'arsa ya haye saman machine ɗin, tare da masa key wani irin kuka yayi machine ɗin ya ɗauka. Kasancewar shine a gaba ya sake daidaita machine ɗin Cikin sallon ƙasaitarsa ya ɗaga hannunsa sama ƙaramin yatsansa ya fara musu wata alamar dasu kaɗai suka san ma'anar kayansu. Suna gama fashimtar haka
yaja machine ɗin da wani irin azababben gudu ya fita a gidan baki ɗaya, suuuuuu motocin suma suka rufa masa baya Sosai motocin ke sheƙ uban gudu a titi tamkar suna a jerin gasar tsere, bakajin komai sai ƙara ƙainarsu,
Da yawan sauran motocin dake a kan titin sauƙa suke gefen hanya domin basu fili, ganin yadda suke zuga uban gudu na tashin hankali, dan duk mai hankalin da yaga wannan gudun yasan bana lafiya bane ba. Kai tsaye Lekki suka nufa daidai wani mahaukacin ƙaton luzary suka kutsa kansu, tuni jami'an tsaron gidan suka soma sakar musu wata.
Wani irin sakin kan machine ɗin yayi tare da Ciro wasu bindigogi guda biyu kirar berreta M9, tsalle ɗaya yayi ya diro akan power bike ɗin ya fara tafiya kamar irin fusataccen zakin nan,
Saida yayi pulling trigger Kafin cikin wani ƙayatacce salo ya soma harba bindigar.
A gigice Governor Ibrahim Khaleel Nasara dake zaune irishe irishe acikin mahaukacin parlourn sa yayi wani tsalle kamar mage ya haye saman lumtsememiyar kujerar jikinsa na kerma, minister Zubairu tanbuwal kuwa rasa ma yadda zai yi yayi sai kawai yayi knell down a tsakar parlourn.
Acen coumpaund na gidan kuwa Sosae jami'an tsaron suke neman gagararsu su, tuni AK ya fusata kafin kace mene saiga wannan kattin jami'an a ƙasa shi kaɗai ya kutsa kansa cikin ƙaton parlourn, duk wani lungu da saƙo dazai shige saiya haɗu da jami'ai haka yake harbesu. Harse daya danganta kansa da rantsatstsen parlourn minister'n. Fuskarnan yawa kunu haka ya tisa ƙewarsu su duka biyun. Bayan na jakin da suka sha.
Tuni suka bama wurin iska suna barin cikin anguwar, suna barin unguwar manyan sojoji da jami'an tsaro harsun ƙaraso, hakan yasa suma jami'an tsaron a fusace suka mara musu baya, nan fa aka shiga fafatawa tsakanin ƴan ta'addar da kuma jami'an tsaro, suna dab dacim musu suka suka saki hayaƙi tuni wurin ya gauraye dama titin baki ɗaya suka harba motocin su tamkar walƙiya haka suka ɓacema jami'an Nan.

       Cikin wani mugun jin haushi Ajmaal ya taka birki tare da jan wani mugun tsaƙi tare da cije saman laɓbansa.
       Rai ɓace suma sauran jami'an tsaron ke yarfar da hannaye, kowa yanajin takaici da ƙunar rai cikin zuciyarsa.
"AK!"
Wani zazzafan numfashi ajmaal yaja tare da komawa cikin motarsa yana yin reverse, a 370 yaja motar tamkar wanda zai tashi sama.


*ZAMANI TV*

"MEERAH! MEERAH!! MEERAH!!!"
Sunan da suke ta famar ƙira kenan tare da juyi da matashiyar budurwar a tsaƙiyarsu. Ita kuwa wannan matashiyar da suke ƙira da MEERAH, murmushi kawai take saki baƙar doguwar riga ce a jikinta wadda ta yane kanta da baƙin mayafin doguwar rigar sosae tayi wani irin fitinannen ƙyau cikin shigar.
"MEERAH ABDULLAHI GWANI!, ana son ganin ki a sashen MD"
Aka faɗa daga cenñnn ɗan nesa dasu.
Ahanzarce wannan matashiyar budurwar da zatayi irin shekaru sha taran nan, ta juyo tare da nufar office ɗin MD ɗin harda ƴar sassarfarta.
Da sallama ta shiga cikin fuska kaɗan kadaran kada han, bakinsa ya baje ba ki ɗaya yana amsa sallamar nata,
"Stay here"
Ya faɗi cikin ɗan saurin bakin da yake da, zama tayi bayan ta gaida shi, amsata yayi sauri sauri kafin kai tsaye ya shiga rattaɓo mata bayanai. "Amm MEERAH aduk faɗin wannan tasha tamu kusan zan iya bugar kirgi wajen faɗin kece haskenmu, kana Nasarar mu, ɗaukakarmu, yanxu nake samun labarai daga majiya me ƙarbi kan cewa yanzu yanxu wannan babban criminal ɗin ya ƙwamishe gwamna da kuma ministan gida!, SO shine nake son ki haskaka ki faɗaɗa ki ninki maganganun ta yacce wannan tasha tamu zata ƙarayin popular fiye da da, duba da cewa duk wani abu daya danganci wannan babban me laifin son shi mutane suke kamar hauka. Tuntuni nake son samun ɗan firit news akansa ko yayane, saidai sammm babu wata hanya to yanxu ga dama ta samu mezai hana a yanxu kafin wasu gidan jaridun labarain suje musu ke ki fara fitarwa daga wannan tasha tamu ta ZAMANI TV!"
(Ɗan azabar son kuɗi dason suna)
Ta faɗa a cikin ranta
Jin tayi shiru ne yasan MD dan takar teburin dake gabanta cikin marairaice murya yace.
"Wannan labari zai jawo hankalin Mutane zuwa wannan tashar tamu uwa uba yanda kowa ke ƙage dason jin sabon News daga AK EAGLE babban ɗan ta'addar da duk duniya sunansa ya kewa ye ko ina"
"Pls MD naji!, naji!! Naji!!!"
Suna kawai kalaman data furta cikin ƙosawa dajin harmutsatsan zancen MD ɗin.
A take aka tattaro duk wasu ƙananun ma'aikata dama manya, cikin 5 mints kowa ya gama halarta a inda ake gudanar da shirin a ɗaki na musamman. Dama tuni Md ya bata doguwar takardar da duk wasu maganganun suka ƙunsa.
Murya ta gyara bayan ta maƙala headphone tare da sanya ƴar ƙaramar loudspeaker a bakin ta, Cikin zaƙin Muryarta sautin maganarta ya fara fita kamar haka cikin amsa kuwwa.

"_Assalamu alaikum masoya barkanmu da kasancewa damu ayau safiyar juma'a, wacce akema laƙabi da juma'atu babbar rana , karku manta kuna tare da tauraruwar tasharku mai farin Jini wato ZAMANI TV!, Wanda muke tafe muku da zazzafan labari akan wannan babban criminal ɗin nan wato EAGLE, wannan Ni! MEERAH ABDULLAHI GWANI Ni ce jagoranci shirin.
A yau safiyar juma'a mun tashi ne da alhinin labarin ƙwamishe governor da kuma ministan gida, da wannan tantirin ɗan ƙunar ɓakar waker ɗan. Ta'adda wato AK EAGLE yayi wanda ahar kullum tazara kaɗan ce tsakanin sa da jami'an tsaro.
Bayan karkashe masu tsaron gidan gwamnatin, shin ku a tunaninku miye wannan criminal ɗin yake nufi ne?, yana nufin yafi ƙarfin jami'ainmu kenan, domin dai kunsa tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login