Showing 42001 words to 45000 words out of 69951 words

Chapter 15 - MIKIYA Book One Hausa Novel

18 Nov 2024

8176

Gabanta faduwa yake sosae amma haka ta danne ta tunkari kafar room din.
A hankali tamkar wota barauniya ta dan leka kanta cikin room din,Da kafafunsa ta fara cin karo Wanda suke sanye cikin wani sgegen bakin shoe Sandal's. Zara² fararen kafafunsa sunyi wani mugun kyau ta cikin takarmin.
”Boss kamar yadda ka umarta mun dauko shi yana dab da kawowa park din!, ba tare da bodyguards nashi sun ankare ba. Kana kana da zama da misalin 5:35pm da kamal Rano ya sauka shima tun 10:00 am”
Ita dai keyarsa da gashin kansa ke zube kawai take Iya kalla.
Dake shi komi nasa irin na muna fukai da marasa gaskiya yake samm bata ji abinda yacema dayan mugun ba.
Wani irin shegen zaro ido waje tayi ganin Wanda suka zo wurin domin shine wannan mugun yayi kidnapping dinsa.
Sosae jikinta ya shiga rawar tsoro domin taga wannan mutumin da gaske mugu ne, kashe mutane da sacesu kawai ya Iya.
Cikin wani mugun tashin hankali ta juya tana barin word din, tsabar ma ta rikice ta rasa ta wacce hanya suka biyo haka ta ringa sanja hanyoyi amma ta gane inda suka biyo da wannan maid service din.
Gafff taji tayi karo da wani Abu. A tsorace taja baya dake a mugun tsoracen take dama. Ai kuwa bisa tsautsayi kafarya ya zame tayi wani irin baya.
Wani razanannen ihu ta Saki tare da rimtse idonta da karfin bala'i ganin ashe kasa tayi. Baki daya ta gama saddakar da cewar yau saidai wata ba ita ba a cikin wannan duniyar. Shikenan ashe dama sallamar karshe ne tayi da annenta tare da baffanta.
Wani irin fusgota taji anyi babu zata,kai tsaye kan faffadan kirjinsa dake tashin wani irin bala'in kamshi ta fada. Ba tare da tunanin komi ba ganin ta tsirane ya sanya ta wani kankame jikin wanda ta fada da karfin gaske tana sakin wani raunataccen kuka.
”Allah Sarki Anne'na da tuni na mutu yau ba tare da nemo miki koda daya daga cikin ahalinki bane!”
Ta fada tana cikin muryan kuka sosae.
Wani irin fisgeta a jikinsa yayi tare da jifanta da wani shegen kallo yana Jan tsaki.
Tana yin ido hudu dashi a matsayin Wanda ya temaketa ta kwallara kara tare da furta. ”Kai cho na Wllh daka temakeni!, Wllh dana San Kaine kara na fada kasan na mutu, Allah ya Isa ban yafe maka ba! Mugu! Azzalumi!!!”
Tana fadar hakan ta kwasa a guje da gudun masifa tana yin kasa.
Tana dira a gabansu disha da suka haukace a nemanta. Itama a haukacen ta furta. ”Nafsi Nafsi Wllh kowa yayi ta kansa ga mala'ikun duniya nan”
Ta fada da karfin masifa tana kara kwasa a 449, haba tuni sai gashi sun take mata baya ganin yadda take gudu cin karfinta, domin sun San duk abinda ya tsorata MARYAM ABDULLAHI GWANI harya sata gudu to ba karamin abu bane. Da sauri hayatudden daya rigasu Isa gaban motarsu ya bude musu, su kuma suka fada yaja da mugun gudu suna barin wurin. Ai kuwa suna daf da fita a cikin park din idonta ya sauka a kanshi, alama ya mata da saina gimtse miki wannan shegen bakin. Tamakar kuwa tasan abinda ya furta din ta turo dan karamin bakin nata gaba tare da murgudawa.
”wai meerah meya faru?, dasu waye kuma kika hadu bayan mun jiyo ihunki daga can cikin park din, kafin kuma gudunki ya biyo baya?”
Hayatudden ya tambayeta disha kuwa da mardiya in banda faman sauke ajiyar zuciya babu abinda suke aikin yi.
”Hmmmmm kude Ku bari da masu kidnapping mutane na hadu, ihu na kuma da kuka ji kidnapping nawa suka so yi Allah kuma ya kubutar dani”
Da wata kafurar harara mardiyya ta bita tare da furta. ”Dama sun dauke kin Wllh da an rage mugun iri”
Wani Dan banzan kallo meerah ta watsama mardiyya tare da fadin ”Nifa idan na Rena kasuwa ko sautu bana mata, haka idan akace mutum kwakwalwar kifi gare shi to bana tayawa bare nima na samu nawa rabon na toshewar kai!”
Ta fadi tare dajan wani mugun tsaki.
Fadane ya so ballewa tsakanin mardiyya da meerah amma dai Allah yaso be farun fa. Ta hanyar shiga da hayatudden yayi.

*AK*

Wuraren 4:30 na yamma yatashi awahale domin samma ya manta da batun ganawar da akace zaiyi da kamal Rano. addu'an tashi daga bacci yayi kafin ahankali ya sauko daga saman clean royal bed nashi. juyawa yayi ya kalli agogen dake bed side nashi yaga karfe nawa ne yanxun, ganin shida saura ne ya sanya shi tashi a hanzarce tare da nufar kofan bathroom ya shiga, wani irin hadadden babban bathroom ne mai hade da closet an raba wajen part biyu bangaren dama wani irin hadadden closet ne komi na wajen blue and white ne, ga kaya kala kala dake jikin hanga ga kuma yar stool a tsakiyar wajen sai bangaren haggun kuma koface wacce bayi ke ciki bude kofan yayi ya shige bayan ya zame kayan jikinsa ya zira bathrobe.

Yay kusan 30 minutes kafin yafito daga bathroom din sanye da wasu lafiyayyun Riga da wando sai yar gadon wato pcarp daya daura gashin nan dake walkiyar kyau da baki ta zuba har kasan keyar.sai nose mark da bakin safa akafanshi sai uban kamshi yake, jinginar da kanshi yay ajikin bangon dakin kafin ya dago kai ya dunkule hannu ya daki bangon dakin da karfin bala'i yana tsaki ganin hoton fuskar wannan fitsaratun a cikin kwayar idonsa tana yimay rashin kunya.
”damn it” ya fada fuskan mace bai taba tsayamai arai kaman na yarinyar nanba but why?! Kiran sallan dayaji daga masallacin anguwar ne yasa ya mike tsaye, wasu tausasan slippers ya zira da sauri ya bude kofa yafita daga dakin, yana sakkowa arms yayi saurin mikewa sauran kuma suka rufa musu baya zuwa masjid danyin sallan magrib. Basu dawo ba saida akayi sallan isha'i dama kuma al'adan shine baya dawowa daga masallaci idan anyi sallan magrib, saida wani kwakwkwaran dalilin. Kai tsaye stairs yahau ya bude kofa ya shiga dakinshi mayar da kofan yayi ya rufe harda saka key ya jingina da kofar yana sauke ajiyan zuciya,ahankali ya daura hannunshi kan heart dinshi da duk single beat remains him of her in his arms, ahankali ya daga kai ya kalli plain sky blue chiffon curtains din dake jikin babban window dakinshi dake kadawa sosai sakamakon iskan da akeyi na hadarin da yama samaniya kawanya ta hanyar yi mata ado da gajimare, garin yay duhu sosai kaman irin tsakar dare din nan sabida hadari sai walkiya sama take, ahankali yatashi daga jikin kofan yafara tafiya kaman kwai yafashe mai aciki yay wurin window ya tsaya ahankali ya mika hannunshi ya taba labulen slowly kafin yakai dayan hanunshi yasa duka hannayen shi ya raba curtains din kowanne yatafi bangare daya hakan ya bayyana window daya ya dan budu kadan, hannu yatura ya bude window duka yadaga kai yana kallon sama, bai damu da ko iskan da ake kadawa ba irin me kurar nan kan iya shigar mai daki ko ido bs, shiru yayi yana kallon sama iska da kamshin kasa dana trees yawani irin blowing suna ratsa duka jikinshi suna karasashi jin wani iri da baitaba jin kanshi aciki ba, ahankali ya mika hanunshi ya fitar dashi waje ta window yana feeling yanda iskan ke dukan hannu dan yayyafin da aka fara na zuba akan soft kyakykyawan hannun shi, hannun ya kafe da ido jikinshi namai wani iri tuno yadda ta rike hannun kafin ahankali ya furta ”what is happening to me?, me zubin kazar mayu”
Inba mayta ba ina ita ina shi ma me hadinsa da ita? Da baya baya ya koma yana kaiwa zaune a bakin bed, sosai Michel dake tsaya daga bakin kofa yana ta famar yimay knowkin don kawo mishi dinner na dare.
Amma haka wannan Dan bawan allan ya share yaki ya tashi ya bude. Dole sai komawa yayi da abincin don yasan ai yana da dangin su snacks da chocolate a cikin deep freeze nashi dake bedroom din....

Misalin sha biyu da kusan rabi na dare wasu motoci guda uku suke tafiya akan shimfideden titin inda motocin suka fiti daga wajejen daji dajin gefen hanya, kai tsaye suka yanki hanyar dazai sada su da airport.
titin shiru sosai yake babu wasu motoci dake wucewa banda su haka babu motsin ko wanne rai me numfashi a cikin tsakiyar wannan dare, benz guda biyu ne suka saka wata black din jeep a tsakiyan su me tinted windows. kaman daga sama power bike din Ak ya yanko daga cikin wata siririyar hanya da wani irin fitinannen gudu, gaban wadan nan motoci ukun yasha rike hanun bike din yay da hannu daya ya janye dayan hanunshi daga dayan hanun bike din yakai hanun tabayan wandonshi ya ciro karaman bindigar shi daya saka mata silencer abakin sabida kar dai kara. A kuma daidai lokacin motocin su arms suka kayo wurin suma, domin satar hanya yayi su kuma dake ankare suke da duk wani motsin uban gidan nasu ne, ya sanya suka rufo mai baya ta cikin budaddiyar hanya.
Kallo daya yama motocin su arms ya dauke kai, be fasa ba ya saita bindigarshi tare da harbe tayan jeep din tsakiyar,
ya harbe na jeep.
Wani irin juyi motocin motan ta shiga yi sakamakon fashewan tayan a guje mutanen dake sauran motocin suka bubbude motocin suna fitowa a rude domin bama yan uwansu dauki.

Kai tsaye wajen motar Farouq audu bashasha suka nufa da suke protecting suna gyara bindigar su batare dasun damu da jinin da jikinsu ke yiba. Koda suka karasa gaban motar saidai me?, wayammmm ba farouq a cikin motar babu dalilinsa daga shi har yarinyar da zasu bar kasar da ita bisa umarnin mahaifinsa audu bashasha. Daya bukaci da yaron nasa ya taho masa da RIYYA din cennn kasar India inda yake jinyar kansa.wannan shine makasudin fitiwar su kenan a cikin motocin.

”wat is happening?” daya daga cikin yaran ya tambaya ya tambayi sauran waima me yake faruwa?. Hhhhhhh Ashe her boss in naku sleeping powder ya bade shegu dasu a lokacin da suka yunkuro da niyar kaima ogansu dauki. Kowa sai ya shiga waige waige sai kuma dukansu kusan a tare suka hade baki wajen furta
”WHAT?”
Da karfin masifa ganin hasken rana a akan idonsu, saurin kara mutsitstsike idanunsu suka shiga ganin dai tabbas hasken rana ne ya sanya daya daga cikin yaran furta.
”Impossible”
Da karfin gaske, in banda rainin hankalima taya za'a ce haka ta faru dash to waye ya musu wannan aikin?, *ÊÀGLÉ ÆK* Idon Sa yakai kan kan dan note din dake dauke da sunan ak din cikin salon burgewa akayi shi akansa rubutun.
Wani ihu ya sanya yana wawuro Dan sauran note din tare da kukuruwa yana matse note din akan tsakiyar kirjinsa.
Sai kuma ya ware ma yan uwansa note din Yana furta *ÆK* da karfin gaske.
Duka a tare suka dune shi ”Yeah wannan aikin bana kowa bane sai tantirin tantirai, nifa Wllh da zanyi ido hudu da wannan ak din ba abunda zai hanani rungumesa harma na furta masa *I LOBE YOU*”
Ya fadi yana kara nade note din a cikin duka hannuwansa biyun.

Gudu take sosae akan Pawer bike ride dinsa motocin su arms na mara mishi baya suma a mugun gujen. Suna kaiwa cikin hadadden mention dinsu kai tsaye samansa ya haura.
Arms ne da yake dauke da Riyya ya shimfideta akan sopar Palon tare da furta
”RIYYA? RIYYA!!! Weak off”
Shiru babu alamun ma tana jinsa ganin ko motsi taki yine ya arms yakai zaune kan sopar shima dago kanta yayi tare da tapping fuskarta adan rude yace
”RIYYA! Hey Riyya”
Sai kuma yayi saurin kallon axton tare da furta
”get me the water pleaseee”
Ya fada da karfi domin shi kadai yasan irin halin da yake ciki na tashin hankali.
Fesa mata ruwan sanyin da axton ya kawo masa yayi. Wani gauron numfashi ta kawo a wahale tare da bude kyawawan eyes nata.
Akan Armstrong ta fara sauke ganinta.
Ai da mugun gudu ta rungumeshi tare da fashewa da kuka tana fadin.
”YAYA!!!”
Da sauti me karfin gaske tana sake cusa kanta cikin kirjinsa.....

*BY AMMEY LAYLERH*


*🦅 MIKIYA 🦅*


*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 35&36

#AK POV
#MEERAH RIYYA join
#kamal R
#Curruption
#POVERTY's
#Deep friendship
#playful


_______________

*Kano*

____”Baban Mariya har yanzu ba'a dace ba ko?”
Yar matsakaiciyar matar ta jefawa mijinta tambayar cikin nuna alhini karara. Ijiyar zuciya ya sauke tare da fadin.
”Ban samu ba su'ada” ya fada cikin rashin jin dadi da mutuwar jiki. Kallonshi tayi cikin tsananin tausayawa itama, kallonta yayi ganin yadda take kokarin maida kwallar da suka mata ido. Cikin tsananin tausayinta dake cike a ranshi ya furta.
”Na tambayi duk wanda na sani amma ga baki daya kowa yaki taimakona!, damuwata itace abinda ka Iya faruwa da kuma me gobenmu zata haifar mana”
Hannuwanta da suke manne a cikin juna ta matse sosai tana son hana rauninta bayyanuwa a gaban adalin mijinta, domin karya ga rauninta hankalinsa ya sake tashi fiye da yanxun. Sama ta kalla cikin raunin murya da nuna jarumta tace.
”Àduk lokacin da Ubangi ya jarabceka ka mika al'amurranka gareshi kawai. Anan ne zaka gane cewa lallai da akwai dalilin daya sanya ya jarabcekan”
Wasu hawayene masu zafin gaske suka sakkomai
"makomar mariya shine abinda yafi komi tsaya min a cikin rai da rayuwana!, ina tsoron a karo na uku aurenta ya fasu akan rashin kayan daki umayma"
malam yusufa ya fadi cikin nasa hawayen daya gaza boyuwa a garesa.
murya a tausashe wacce ya kira da umayma ta furta . "kada ka samu damuwa malam insha allah allah shine zai kayo mana dauki lokacin da bamuyi zata ko tsammata ba bi'izinillahi"

"amma ke ina iya ganin damuwa akan fuskarki umaymatu, kuma kinsan bazan iya juriyar hakan ba"
da sauri ta juya tana barin wurin domin kada ta raunatawa mijin nata zuciya.....
kanta ta hade da jikin bakin kofar da take tsaye hawaye masu zafin gaske na zubo mata. tana tsananin umminta da babanta, wai sai zuwa yaushe rayuwa zataji kansu su fita a halin kani kayin da suke a ciki na halin rayuwa? sai zuwa yaushe suma zasu dandani irin yadda zakin rayuwa yake?.
"Ya Allah!"
mariya ta furta cikin wata iriyar raunatacciyar murya. sallan magriba da aka kira ne ya fitar da baban mariya cikin tawakkali da karfin zuciya.
Cikin sanyin halinta kamar koda yaushe anutse ta mike kanta duke a kasa, saidai ahankali take matse lips dinta da kyawawan teeth dinta. kai tsaye gaban dan karamin fanfom dake gaban bishiyar mangoron gidan ta nufa....alwala ta daura tana jin duk ma yanayin baya mata dadi baki daya.

shi kuwa malam auwalu da mutanen anguwa ke kiransa da baban mariya bayan idar da sallar isha'i, dake shine lilaman masallacin anguwar yana zaune har saida kowa ya gama fita kana ya mike da zimmar fita. wata farar embulons ce ta fado daga saman jikinsa cikin rawar jiki ya shiga waige2 saidai baiga kowa ba....
saurin fitowa yayi a masallacin da shi ya fara cin karo,wani irin dafe kansa malam yusufa yay. me yasa aduk lokacin da yake da bukatar taimako sai shine kadai me taimakonsa.
jiki a sanyaye ya karasa xuwa gaban farar motarshi da yake tsaye, sanye yake cikin kakin yan sandan shi kamar kullum. "Na rasa wanda zai taimakeni amma ba wanda ya taimakamin, duka na tambaya haka ban samuba! amma kai bamma tambayeka!" ya kasa karasa maganar shi sabo da kukan da yaci karfinsa.
"Aina riga na fashimci komai dana kalli cikin idanuwanka. wannan ba komai bane"
inspector KAMAL RANO ya fadi
"bansan ta yayene zanyi wani abu game da yata ba. ban kuma san da wanne irin idon zan dubesu ita da mahaifiyarta na fada musu cewar auren ya fasaya!. bayan fitowana daga cikin gida zuwa masaaci. KAMAAL?"
Malam yusufa ya kurayi sunan shi cikin karyewar zuciya. cikin tsananin.zafin dake narka kirjinsa ya furta.
"A yau da kai danane dana zartar maka da wani hukunci kai tsaye! ko kuma in baka umarnin aikata min wani abu"
idonsa daya tara kwalla ya dago yana kallom baban mariyan. kafin cikin muryan da kai tsaye ba zaka iya tantance taba yace.

"Ya kuma zakace haka baba? kenan niba danka bane kome?. matsayinka a wurina ya wuce makwabtaka ni KAMAAL IDREES RANO A MATSAYIN MAHAIFI NAKE KALLONKA, ka bani ko wanne irin umarnine ni kuma in aiwatar maka shi cikin sauri da tsananin biyayya"
hawaye da kuka ne suka zowa baban mariya lokaci daya, cikin jin yakini da kuma karfin zuciya ya furta..............

"KAMAAL A MATSAYINA NA MAHAIFINKA NA BAKA UMARNIN AUREN MARIYA!"
wani irin dokawa kirjin kamaal yayi amma saiya danne hakan cikin cikakken bin umarnin nashi kamar yadda ya daukar masa alkawarin ya furta.
"A MATSAYINA NA DANKA NA AMSHI AUREN MARIYA, AMANA SAI DAN AMANA! HALACCI SAI DAN HALAK, zan amshi wannan auren bisa wakilcin waliyina ABDOUL-MALEEK"
Da karfin gaske ya rungume kamaal din yana fadin "nagode na gode nagade kwarai da gaske bana da haufi akan baka auren mariya da nayi kamaludden uban daraja uban kamala"
..........Umayma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login