Showing 33001 words to 36000 words out of 69951 words
Wani matsiyacin kallo Ajmaal ya jefawa arms.
”Ta Yaya yasan kana a wannan boyayyen wajen?”
Ya fada yana shakar arms din.
Wata shegiyar dariya arms ya saki tare da furta.
”Ku a dakikin tunaninku da kunyi haka ne don boye ni daga BOSS?”
Ya fada cikin wannan dangerous voice din nashi.
”ANSWER MEE ARMS!”
Ajmaal ya sake maimaitama arms tambayarsa.
Dariya ya shiga yi kafin ya furta ”footage”
”Karya kake arms babu camera a jikinka nida kaina nayi check out naka!, don haka ka bani amsana a karo na karshe”
”Shi yasa na CE duk cikin Ku babu Wanda Zan kira da *JAN WUYA, duk kaninku ”KOLAYE NE”
Ya fada yana daga harshen Sa tare da sanya shi tsakanin seen da tongue nashi ya turo musu Yar karamar camerar.
Duk cikin su babu Wanda be razana da wannan basirar tasu ak ba. Ehhhh dole suce basira mana amma sai suka waske abinsu....
Few minutes
Zaune yake zama irin na harde kafar nan. Akan kujerar da Isa manu ke kanta a da a yanxu kuma ta dawo da ak din.
Fuskarnan tamkar tayi aman Wuta tsabar tsananin fusata,A fusace Ajmaal yayo kan ak duk kuwa da yadda Mr President ke kokarin hana shi amma be hanu ba.
”Kaida kazo da sunan kwatar yaronka to kasani kazo nan da sunan mutuwarka ne!,, A wannan rana a kuma nan wurin idan har ban dagarzaga kasusuwanka to na rantse ni ba namijine”
Wani Dan iskan kallo da ak ya watsawa Ajmaal ne ya sanya jikin Isa manu ya soma karkarwa,shi da ba shi aka ma kallonba.
Wani irin gyara zamansa yayi ya sakko da kafarsa daya dayar kuma ta na kan kujerar da yake kai. Ya dora hannunsa saman kafar like irin kasaitaccen basaraken nan.
”Ko wane mafarauci gwarzone har sai sanda ya fuskanci ingarman zaki. Ba kamar kai da rundunar jami'anku ba!, bana da runduna bana da tsoro a jikina bare naji tsoron mutuwa.
*TUN A HAIHUWATA NACI GALABA AKAN MUTUWATA_*”
Ak ya furta kalaman tare da wani iriin doka hannunsa akan kujerar da yake zaune a kai. Kalaman da suka kusan zauta yar karamar kwanyar duka jama'ar dake setrest din.....
A zuciye wani da suke kira da tonfal babban yaron su Isa manu yayo kan ak, da wani irin salon daukar hankali ak dake zaune ya sanya kafarsa tun kafin mutumin ya karasa ya sarke kafarsa. Ji kake rigifff mutumin ya zube kasa ba tare da ya ko motsa ba.
Cikin kankanin lokaci ak ya sissince arms dake daddaure ya tafi dashi a gaban idonsu ba tare da sun Iya dakatar dashi ba haka suna ji suna gani ya sabi arms a kan shoulder nashi yabar wurin dashi.cikin wannan takun NASA me cike da bajinta,hadi da mazan taka Wanda kallo daya idan kai masa sai hantar cikin ka ta kada.....
”Kai wannan yaro anyi dan tsinanne, kasa sai kace ta uwarka kazo ka zame mana fitina tare da hana mu rawar gaban hantsi”
Isa manu ya fada bayan daya tabbatar ak dade da barin wurin.
Ajmaal da gefen kunnansa ke digar jini ne Wanda ak ya bashi rabon shi. Cikin tsanin bacin ran ya furta.
”Stoppp”
Da karfin masifa ”Na gaji dajin koda me irin sunan sane”
Sai kuma ya dago ya kalli Mr President ya furta.
”Sorry sir. Duk ba laifinka bane da alokacin da na d'ana kunamar bindigata baka tsayar dani ba ai da tuni saida wani bashi ba!, amma ka dakatar dani”
”Babu dai kai ba shiba!”
Tonfal ya fada Wanda babu jimawa ya farfado daga mutuwar wucin gadin da yayi.
”More bit never get one choice but if we take a maximum change we get a big choice”
Mr President ya fada yana gama fadar hakan ya fice a wurin...
A lokacin da akai wannan darbarwar salman yana kasar India yawan shakatawa tare da wayayyun yan matansa.
★★★
”Mommy Wllh duk inda yake a fadin duniyar nan saina dau fansar Jinin mahaifina da yayi, sai nayi sanadiyar barin numfashinsa da gangar jikinsa kamar yadda yaso raba nawa mahaifin da nashi!”
*FAROUQ AUDU BASHASHA*
kenan da ga audu bashasha shi kadai ya haifa a duniya.Shi yasa yaron ya taso cikin wani irin sangarta da tabara, Duk inda ake neman wani teteros to in akace maka Farouq fakat kenan. A yanxu haka Audu bashasha yana kasar India wurin kwararrun likitoci don kula dashi.
Ashe be mutu ba da sauran ranshi lokacin da ak ya fasha kansa, Sun boye hakan ne domain gudun bacin sunan Sa, shi da kansa shine ya dauke RIYYA, ya mata wani irin mugun boye mahaifiyarsa kuma irin muta nan ne da sammmm babu ruwansu da duniya. Itace ma dalilin daya sanya ta hana.
Cikin muryar da yake cike da tsantsan sarauta Hajiya Khadija suraj sunusu shureim ta dubi Dan nata Tare da furta.
„Idan har Jinin dake gudana a cikin naka Jinin nawa to ban amince maka ba”
Ta furta hakan tare da bar masa palon, shi kuma ya bi bayanta da kallo domin duk wani Iya shegensa da ji da samartaka da zafin kansa jinsa yake shiba komai bane a gaban hajiya Khadija.
Ya ta biyu kenan ga me martaba sarki suraj sunusu shureim.
*BY AMMEY LAYLERH*
*🦅 MIKIYA 🦅*
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________
*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*
Page 27&28
# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# BEST LOVE
🤍🔥✅
★★★★
2 months ago
Haka dai al'amurra suka ci gaba da wakana. Tuni baffa ya kashe waccen maganar haka kwanaki suka ci gaba da juyewa zuwa satikai satikai sukaci gaba da juyewa zuwa watanni.
Cikin iko na Ubangiji meerah ta koma bakin aikin da ko a mafarki ba tayi tunanin komawa ba, Bisa matsawar MD da kuma wasu manyan anguwanni ta koma bakin aikin ta.
Haka kuma maganar aurensu da Salman yake neman kan kama, Wannan abu shi yafi komai ɗaya hankalin meerah matuƙa saidai tana danne hakan a ranta.
Kusan kullum yanzu shike zuwa har ƙofar gida ya ɗauke ta zuwa wurin aikinta saidai ta dakatar dashi first.
A tacen ɓangaren su Salman kuwa wasu irin abubuwa suke ma shirye shirye shida mahaifinsa Isa Manu.
*******
Yamma ci ne mai daɗi haka kuma yau din rana ne da ya kasance na musamman wato Jumma'a, ranan da yake ɗauke da albarka da kuma rahamar Ubangiji kala kala.
Wannan dalilin yasa sassanyar iska mai cike da tsananin daɗi da kuma sanya shauƙi ke busawa, a gaba daya ko wani lungu da saƙo dake cikin gidan jaridar zamani TV
Kowa ka kalla harkar gabansa yake cikin tarin nutsuwa, amma banda meerah da tayi zurfi a cikin duniyar tunanin data jima ta faɗawa.
*"MEERAH!"*
*"MEERAH!!"*
Disha dake tsaye kanta ta shiga ambata tana me ƙoƙarin rataya handbag ɗin dake hannunta, Wanda kuma ahankali ta ɗan ranƙwafowa da kanta, tana me kallon Meerah.
"MEERAH wake up kodai bacci kikeyi ne?."
Disha ta faɗi tana me gyara tsayuwanta, tare kuma dasa hannu ta zunguri meerah ɗin.
Ahankali ta ɗago kanta wanda ta kifashi akan desk almost 15mn ago.
Sam ba bacci takeyi ba hasalima duk abunda ƙawar nata ke faɗa tana jinta.
Numfashi ta ɗan sauke Ahankali tare da ɗago manya manyan eyes nata me kama dana mashaya masu matukar kyau, Wanda hakan ya sake bayyana tsananin kyawun dake kwance akan fuskarta, Idanunta da suka ɗanyi blue ta lumshe tare kuma da buɗe su aloƙaci guda.
Cikin unique voice ɗin ta mai daɗin amo da sanyin sauti, tamkar ana busa sarewa tace.
"What happen DISHA? ba bacci fa na keyi ba, just I'm tired."
Ta ƙare maganan tana ɗan kwantar da wuyanta gefe.
"What happening kike tambaya? time ɗin tashi a aiki yayi, kalla ki gani babu kowa ya watse sai nidake kawai, oya tashi mu tafi kodai zaman wurin ne bai isheki ba?."
Disha ta faɗi tana ɗan hararanta tare da yin gaba.
Fuska meerah ta ɗan kwaɓe kana cikin yanayin gajiya da kuma tsananin damuwar dake cinkushe a cikin ranta ta miƙe itama. cikin sauri ta rufa mata baya tana me ƙoƙarin rataya jakanta bisa shoulder nata.
Atare suka fito compound ɗin, tafe suke suna fira sama sama abinsu.
"Disha a raina inajin ina gab da ajje wannan aikin nake ga"
Meerah ta furta cikin cushewar yanayi.
Dafa kafaɗarta disha tayi cikin sanyin jiki ta furta.
”Haba meerah komai yayi zafi maganinsa Allah, ki barwa Allah komai Insha Allah shine maganin komai”
"Hmmmmmm!"
Ta sauƙe ijiyar zuciya me ɗan ƙarfi haka suka ci gaba da tafiya har suka fito gefen titin. Napep suka tara suka hau suna mai kwatancen anguwar da zai kai su.
Ko a cikin napep ɗin ma wata sabuwar duniyar tunanin ta ƙara faɗawa. Na irin daskararriyar K'addarar dake kwance acikin jininta wacce ta fara motsawa kanta.
Haƙiƙa akoda yaushe rayuwa tana tafiya ne tare da tarin ƙalubale.Haka kuma kowa da salon nashi Kalon ƙaddarar amma nata ƙaddarar gani take yafi na kowa, domin daga ta fita daga wannan sai kuma wannan ya kutso kai.
Kamar kuma yanda yake a bayan kowani baƙin ciki akwai farin ciki, haka kuma a bayan kowani kunci akwai sassauci. rayuwa mai juyawa ce farinciki ko akasin haka mummunan ƙaddara ko akasin haka, wayewar garin yau sun waye shine da maganar kawo kuɗin aurenta da iyayen Salman sukai har Naira miliyan ɗaya. Wanda ya tashi hankalin jama'ar gidansu, suka wuni zazzaga ruwan bala'i da masifu kala daban daban.
Ita kuwa wacce ake yi ɗin dan ita sammm ba abinda ke gabanta kenan ba. Wani abu ne daban ke damun rayuwarta wanda da tayi ƙoƙarin zurfafa kanta yake neman juyewa zuwa wani ɓigiren na daban......
Cikin nisan da tayi a duniyar tunani har suka isa ƙofar gidansu bata ma san sunzo ba, Saida disha ta mata magana da ɗan ƙarfi kana tayi firgigit ta dawo hayyacinta Cikin duniyar mutane bata tunani.
*AK*
Msalin ƙarfe biyar na yamma manyan motocin Ak dake cikin garin Abuja suka ma airport ɗin tsinke.
Wasu irin zafafan motocin kusan goma sha biyar irin su Range Rover, Bugatti Veyron, Toyota Highlander, Toyota Tacoma, Ferrari California,gefe ga wasu mahaukatan manyan jifa jifai har guda biyar da aka ware su baƙaƙe wulik dasu. motocine a wurin babu colourn da babu shi kansa airport ɗin kewaye yake da tsaro na musamman.
Ahankali cikin takun izza dajin kai ya fara tako matakalar benen.
Su kuma samudawan sa na aikin su na take mai baya, cikin sauri manyan security'n dake zagaye da airport ɗin suka shiga bashi kariya wa kallon da jama'ar airport ɗin ke binsa dashi. Don kuwa kallo ɗaya zaka masa ka kasa ɗauke idonka a kanshi. Sanye yake cikin Wani arnen cashmere valley wanda kallo ɗaya zaka ma yadin ka tabbatar da ba karamin kuɗi aka narka wurin siyen shiba...
Ahankali yake taka Fararen sawayensa da tamkar wanda bai taɓa takasu ba haka suke, don tsananin taushi da kuma yadda suke sumil luwai.
Wata kafurar Black blue ɗin Mota ƙirar Mercedez Benz aka buɗe masa Armstrong kuma ya faɗa cikin wata narkakkiyar bakar jeep Wrangler . Suka ɗauki hanyar wannan haɗaɗɗen Hotel ɗin na da sukayi booking tun a daren jiya.
Dake babu wata tazara tsakanin support ɗin da kuma Hotel ɗin babu nisa cikin 25 minute suka isa ƙaryataccen hotel ɗin.
A room me lamba 105 AK ya ɗauka su kuma duk suka rarrabu daban daban.
Kwance yake acikin bathtub dayake cike da ruwa masu tashin qamshi na musamman, Iyaka kanshi ne a waje ya lumshe idanuwan sa ya faɗa duniyar tunani me zurfi, wanda nake da tabbacin ya mantar dashi a duniyar dayake yanzu haka.
ya jima sosai acikin ruwan wankan daga bisani ya wanke jikinsa ya fito towel blue ɗaure a jikinsa.ga kuma wani mini qarami a hannunsa shi kuma kalar light blue yana tsane gashin kansa dake cike sosai baqa wuluk! lotion ya shiga shafe jikinsa dashi tsadadde ya gyara tulin gashinsa da mayuka masu kyau da tsada.
Kayan da aka rigada aka ciro masa ya ɗan kalla a takaice dogon wandon jeans ne blue da shirt fara qal me asalin kyau an mata zanen Lion ajiki da blue din colours, sanya kayansa yayi kafin ya fito zuwa balcony na room ɗin. Hannuwansa zube jikin wandon jeans ɗin. Wurin ba hayani sai sassanyar iskan dake kaɗawa mai cike da tarin ni'ima sakamakon hadarin da yayima sararin samaniya ƙawanya.Hakan yasa garin ya yi luf ga dukkan alamu akoda yaushe a ko wanne loƙaci ruwan sama kan iya sauƙa.
Yana zaune kan Chiar silinder caution ɗin dake cikin balconyn Wata ƙatuwar Toyota land cruiser Prado ta shigo harabar wurin fara ce kal sai faman kyalli da ɗaukar ido take yi.Wurin da aka tanada dan adana motoci motar ta parker,cikin slow mamallakin motar ya yi parking.
Kasancewar glass ɗin motar tinted
ne yasa ba'a iya hangen mai mamallakin motar har saida ya fito.An ɗauki tsawon 10 minutes kafin matashin dake draving motar ya fito. Back sit ɗin motar ya buɗe nan kuwa sai da aka kusan 20 kafin wani siririn matashin saurayi ya fito izza.
Ƙafa ɗaya ya fara zirowa ƙasa sanye da halp cover shoe white color mai adon Stone a jiki irin na sarakuna.Cikin loƙaci ƙalilan ya fito da gangar jikinsa,Dogo ne sosai amma yana da ɗan kauri jikin shi a murje yake alamu na yana cikin hutu da jin daɗi,yana da hasken fata amma ba sosai ba.Farin yadin boyal ne a jikin shi mai ɗauke da ƙananun zane,wanda ya sha ɗinki irin na samarin zamani,sai Black agogo daya ɗaure a tsintsiyar hannun shi na dama dashi,a jikin siraran fararan yatsun shi kuwa ya saka white ring mai kyau a karamar yatsa.kanshi bai saka hula ba sai baƙar sumar shi data sha gyara gwanin sha'awa kamar ɗan India. kyakkyawar face na mai ɗauke da manyan dara-daran eyes balls ɗin da suke kamar madara.
A hankali ya rufe manya eyes ɗin shi yana sauke ajiyar zuciya.Tare da furzar da iskar bakin shi.Manyan wayoyin shi dake riƙe a hannu ya kalla ga dukkan alamu ƙira ne ya shigo.
Ɗan siririn tsaki ya ja wanda idan ba kana gaf da shi ba ba lallai ka ji ba. A kunne ya manna woyar cikin fusata murya a daƙile ya furta.
"Zanci ubanka Wllh Najeeb akan takura min da kayi!, Wllh idan ka tunzirani zan fasa maka visa'n naga uban da zakay ok”
Datse woyar yayi Cike da taku irin na zaratan maza ya fara taku yana nufar cikin hotels ɗin.da sauri driver'n ya mara masa biya da system nashi da dayar woyarsa.
A room na daban shima ya sauƙa tare da kayayyakinsa suka zube akan lafiyayyan gado. ZAYD SURAJ kenan ɗa ga Sarkin kano mai martaba SURAJ SUNUSU SHUREIM.
*AK*
Cikin bacci yaji ya soma jin vebration na woyarsa, da ƙyar ya iya buɗe lumsassun idonsa. Idanu ya tsurawa screen ɗin wayar dake ta faman ruri, tamkar me nazartar wani abu haka ya tsira wa woyar kaifafan idon shi.
Duk da cewar yasan ZAID bazai ƙirasa haka kawai ba, lallai dole saida wani abu haka nan ya tsinci kansa da faɗuwar gaba. Hannunsa ya miƙa da niyar ɗaukar wayar saidai kafin yakai ga ɗauka ƙiran ya katse.
Ɗin Jim yayi yana me tunanin bin ƙiran saidai sanin da yayi cewar mai ƙiran nasa zai sake ƙira ne yasa shi sauƙe ajiyar zuciya tare da fesar da numfashi.
Anutse ya tashi zaune yana me tunani acikin zuciyarsa, haka nan Idanunsa da suka dan ɗan tara ruwa ya lumshe saboda tunowa da PAAH tare da Momma'n shi da yayi.
”ZAID EMAAR KUWAIT”
Ya furta a saman laɓɓansa woyar ya jawo tare da mannata da kunnensa. Daga cennnnn Zaid cikin yanayin sanyin jiki ya furta.
” ABDOUL-MALEEK PAPA?”
Zaune ya tashi da sauri amma a zahiri ba saurin yayi ba shine a ganinsa yayi saurin.
Cikin fitar sautin da yayi low sosae ya furta.
”Why? Where is my PAAH”
Shiru daga cennn Zaid yayi, Ak kuma jin shirun Zaid shine ya sanya shi furta.
”Ina PAAH yake you will die ko? ka buɗe baki kamin magana Zaid”
Ya ƙarashe cikin sautin tsawa
“Ko ɗaya bai mutu