Showing 57001 words to 60000 words out of 69951 words
muke samu dake. Shi kuma daddy so tari ra'ayinmu kanzo daidai dashi so shiyasa zakina ganin kamar bana bin umarnin, pls my mommanah kimin afwa Ina matukar son Meerah ne har zuciyata wllh"
Wani irin rumtse idonta tayi tare da zare hannunta dake cikin nashi zuciyarta na mata daci kalamansa na kona zuciyarta. Ya zama dole tayi wani abu akan wannan auren da har cikin zuciyarta taji bata kaunarsa kwata². Tashi tayi tana barin parlon da kallo ya bita domin tsaff ya gama sanin so take taga ta dakatar da auren nan kota halin kaka, ficewarsa shima yayi a parking space ya dauke daya daga cikin manyan motocin dake shake da wurin ya cilla saman kwalta tare da daukar hanyar hotel din Asas rayallerh.
★★KUWAIT★★
Duk inda ka wulga bayine da kuyangi bila adadin akowace kusurwa ta cikin babbar masarautar. kowanne da aikin daya duqufa yanayi wasunsu kuma a kakkame suna gadin hanyoyin wucewa da kowace qofa ta cikin masarautar. Musamman entrance din da sashin me martaba sarki HASSAN AL-HASSAN EMAAR KUWAIT yake, Wasu mahaukatan Samudawane kewaye da sashen baki daya.
Kallo daya zakama dukkaninsu ka gane ko wannensu yana cikin yanayi na tashin hankali ne.
Wani irin shiru ne ya ziyarci wurin tamkar wanda mutuwa ta gimla ta wajen.Kowa a take ya shiga nutsuwarsa Wanda suke a daidai hanyarta suna rabewa gefe tareda sunkuyarda kai kasa don bata hanya saboda takun tahowar gimbiya ADEENERH.
Wanda sautin anklets din zinarin dake kafarta shine yake ankarar ma duk wani hadimi isowarta ko tahowartar tundaga nesa.
Wannan sautin sarkar shine ke sanarda tahowartatahowarta tun daga yarinta harzuwa yanxu data manyanta saboda mulki a jinin jikinta yake. Macece me takukar izza dajin kai kagata yar zafin kaice ba komi ake mata ya burgeta.
Tana da wani irin boyayyen hali na tsananin jin dausayi, idan akace kowa ya tsani abu to ita kuma zai kasance tana yi ma wannan abun ko maye wala mutum wala sabanin hakan. Idan kuma aka daukaki abu to kuwa zaka tarar ne sammm wannan abun beyi mata ba koda kuwa kyansa ace yakai zinare kyaune.
Tana karasowa hanyar dazata shigarda ita bangaren mai martaba sarki ta tsaya cak batare da tace kala ba saima juyowa da tayi ahankali tadan kalli gefenta.
jakadiyar dake gefen tace tayi saurin matsowa tareda juyawa takalli kuyangin dake take musu baya kusan su shida, kallo daya tayi musu suka ja baya ahankali suna tsaya tareda sunkuyarda kai domin sun san ma'anar hakan...
*BY AMMEY LAYLERH*
*🦅 MIKIYA 🦅*
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________
*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*
Page 43&44
# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# Hope
# courage
# Survival
# Humanity
# Inspiration
🤍🔥✅✅✔✴✳❇
Boyayyar ijiyar zuciya tasauke ahankali saida nu'ura ta tantanceta kana ta sanya kanta zuwa kayataccen parlon.
jakadiyart na mara mata baya Parlour ne mai wani irin girma da tsari dayaji adon royal chairs gold and golden kamar zinari sai kyalli da daukar ido suke. sai komai daya kawata parlourn yazamto shima gold and golden colour dinne splits aircon kusan guda biyar sai aiki suke sanyi yakama parlourn tako ina sabida wata irin dukiyace ta musamman aka narkar a parlourn. Wanda tsabar haduwa da girman parlourn yasan ya sammm alkalamina yayi kankanta daya rubuta muku irin kayatuwar parlour kuyi emaging kawai aranku yadda parlourn zai kasance.
Babu kowa parlourn kasancewarsa parlourn farkone dazai sadaka da palon sarauta harzuwa turakar sarki. Saima wani irin shiru da parlourn ya dauke.
Sake tsayawa cak tayi tareda sake sakin wata nannauyar ijiyar zuciya akaro na uku zuciyarta na harbawa batareda tajuyo bangaren da jakadiyar ke binta ta mata alama data dakata.
Ajiyar zuciya ta sauke a karo na ba adadi kwawan idonta sun rikide sun koma jajaye. Hakan na sake bata tabbacin jikin Mahaifin nata ya matsa kenan da gasken?.
Adeenerh ta fada acen kasan makoshinta kafin ta tattaro duka jarumta da karfin gwiwanta.
Ratsa dogon palon tayi kai tsaye kofar da zata kaita ainihin parlourn mahaifin nata ta tunkara zuciyarta na neman karyewa. Saida ta runtse jajayen idonta kana tayi kundunbalar tura kofar bedroom din.
Wani bedroom ne na alfarma babu kowa sai qarar ac dake tashi ahankali.
Zaune yake cikin shiga ta alfarma saidai Kallo daya zaka masa kasan bama ya a hayyacin sane, jin motsin shigowane ya sanya Zaid dago da kansa kallo daya yayi mata da idanuwansa masu tsananin kwarjini da firgitarwa ya dauke kansa.
Duk da taso rudewa tayi saurin daidaita kanta ta tattaro nutsuwa da karfin halinta baki daya. Duk da kasancewar Zaid kani yake gareta amma ba karamin kwarjini yake mata, kasancewar kwarjin mahaifinsa ne ya dauka reality shida Biyuninsa Maleek.
Karasowa tayi cikin sanyin jiki da fargaba ta kallesa ta rufe idanuwanta dasuka fara canxawa tana durkushewa gaban zaid din. murya na rawa tace "Me martaba! Paapana zaid Ya abana"
Idanuwan daya sake watso matane yasan ya jikinta sake daukan mazari ga shirun daya mata shi kansa babban tashin hankali da azabtarwane wa zuciyarta.
Sake dukar da kanta tayi saboda gudun ganin yanayinsa. ko dagajin yanda ya dauke wuta yaki ya magantu ya sanyata rushewa da kuka wai ko zai magantun, domin ita wllh tsoro take! Tsoron dunkarar dakin sirrin me martaba take gudun abinda ka iya zuwa yaje. Gudun kar tayi gamo da abinda zai sanya zuciyarta bugawar lokaci guda.
A kalla sai da dauki tsawan wani lokaci tana rairai kukanta nan ma shiru yaki kulata.
Kamar daga sama taji dakakkiyar muryarsa cikin ikon mulki yace.
"Me martaba me mutuwa paah yana nan da ransa, domin mikiyansa ba zasu taba iya kaishi kasa ba. Kimin shiru anan domin wannan kukan naki sake fusata zuciyana yake, ki sani Sarki HASSAN AL-HASSAN EMAAR dashen Allah ne hadari ne shi malafar duniya duk wanda yace zaiyi dashi yaja da ikon Allah ki shiga idonki ya kalla miki shi. Dole wannan karon dan zaki ya bayyana akan mikiyansa. Lokacin dawowarsa yayi Masu gudu su gudu domin kowa yasan karon ba dadi!!!"
Ya karasa fadar maganan nashi a fusace.
Dagowa tayi takallesa idanuwanta na canxawa zuwa kalar tausayin dan uwan nata. Tare da zubo da wasu kwallar zafin da zuciyarta ke mata, tana jin tsananin kaunar yan uwanta a ranta duk da kasancewar ba uwa dayace ta haifesu ba. Adeenerh itace babbar yar me martaba mahaifiyarta ta rasune a lokacin tana yar shekaru shida xuwa bakwai. Ba tare data sake kallon inda zaid din yake ba ta mike tana nufar daking room din data tabbar anan me martaba yake. Tamkar yadda ya bata umarni haka ta ratsa ta shige cikin parlourn.
Duka wadanda suka dace ne a cike tare da dakin kowa rannan bace babu me alamar sassauci. Kowa ta shiha bi da ido anan ta itama nata idon suka kallar mata
Mutanen dake ma paah dinta kallon ka mutu kawai muhuta din nan.
Zaune takai ta bangaren da Oummey ke zaune, shiru ne yaci gaba da wakana a dakin zamanta da kamar mintuna biyar MOH JIDDOH ta dubi Oummey tare da furta.
"Wannan karon saiki kira lalataccen dayan dan naki, dan wannnan jinyar tasha banban da sauran, mebi ta ajalinsa ne tazo kuma ta gaskiya da gaskiyar kenan.
Wani irin mikewa tsaye Adeenerh tayi cikin furyar fusatar zuciya da dacin murya ta furta.
"Wannan kalmar marar kan gado fa JIDDOH! Ki sani gudun hatsaniya ne ya sanya mutanen da suka kasance mugwaye a cikin zuriyarki ya sanya mutumin daya kasance shiru shiru ya fusata!. Inason ki sanarma azzaluman cikinku cewar idan har akaci gaba da fusata shi to ki sani tarwatsa masarautar zaiyi kinsan da hakan?. Uwa uba kuma Zakin da kika dade kina ikirarin ya dawo to ki sani yau sai adda'arki ta karbu dole ya dawoooo........
Kowa da yake daking room din babu wanda jinsa da ganinsa basu tafi hutun wucin gadi ba. Kai tsaye Adeenarh ta zari wayar Oummey directly numbern da tayi lakabi da *Willion gargalion* ta dokama kira tare da manna woyar da kunnen oummeyn "kima danki magana a gaban kowa ki sanar dashi ya isa haka paah dinsa da kasar shi na bukatarsa suma, har wadan da ba'a gayyata bama na muradi da dawowarsa mahaifarsa EMAAR's kai tsaye ABDOUL-MALEEK HASSAN AL-HASSAN EMAAR's take da bukata!”
Tana fadar hakan ta juya a fusace tabar dakin.
★★NIGERIAN/ LAGOS★★
Fitowarsa kenan wayarsa ta fara ringing ransa adagule yacirota da nufin kashewa gaba daya. Domin tunda yayi waya da zaid komai ya gama kwance masa. Saiya sami kansa da tsurama woyan nashi ido ganin sunan dake yawo akan screen na woyan *_Sweet Oummey_* wani iri rintse idanunsa yayi ransa nakuma dakulewa. Saida woyar ya katse kana ya sake calling nata againt.
"*GARGALION*"
Kai tsaye sunan ya tafi ya ratsa har cikin tsakiyar zuciyarsa.
"Paah! Dinka EMAAR's na bukatar Tsayayyen matashin zaki majinginarsu. Ka sani shi marar jin magana sai ammasa hukuncin jaki yake ganewa. domin kawo gyara acikin al'umma kuwa dole sai wasu sunsha duka dole wasu sai sunsha jijjiga, maza ka dawo GARGA!!! Kai kadai ne mafaraucin da zaiyi wannan farautar”
Wani irin fesar zazzafan numfashi yayi tabbas duk Wanda yake da hannu a poisoning na paah dinsa sai yayi dana sanin saninsa arayuwa. Babu ruwansa da wani yar uwa, dan uwa, dangi domin babu tsoro ba fifitawa ba kara ba alfarma ,zai hukunta duk wanda yake da hannu akan paisoning na paah dinsa. cikin suyar zuciya data ruhi ya Wani irin kaima glass di car din da yake shirin shiga naushi. nan take glass ya tarwatse. bai damu da ciwon dayajiba.
Cikin dakakken sautinsa ya furta, “tabbas kafin suga bayan paah ni zanga nasu bayan oummu!!! rayuwar mahaifina bazata salwanta abanzaba! Saina wulakanta dukkan masu hannu aciki kosu waye su wlhy oummey numfashina fansa ne akan mahaifina!!”.
Dole saida oum tacire wayar daga kunnenta saboda yanda Ak ke magana cikin matsananciyar tsawa.
Buga wayar yayi da kasa batareda ya katse kiranba. Nan take ta tarwatse wata uwar tsawa ya dakama security'n akan suje.
Gaba dayansu cikin rawar jiki suka nufi motocin da ke fake a wajen, ko jira abude masa baiyi ba yabude yashiga.
Hankalinsu a tashe yake daganin yanayin boss in nasu, sunsan ba karami abune kesa ran boss ya baci haka ba.
Saida suka fita daga gidan suka hau kwalta kana suke tambayar ina suka nufa?.
Tamkar bazai tankaba sai kuma furta "airport" dake arms yana cikin dayar motarne ya sanya baima san abinda ake ba. Sai dayaga sun dauka hanyar airport din ne ya gane tafiyan nasu ashe na yanzu ne. Domin dama tunda yayi waya da zaid ya shirya tafiya amma sai washe gari.
Cike airpot din yake da tarin security na tashin hankali tamkar irin wanda suke gadin gidan mutuwar nan. Sanya yake cikin normal cashmere me tsananin taushi da laushi wanda tsadarsa yake a baiyane, kafafunsa sanye cikin wasu tsadaddun shoe cambot bleim.
Kasancewar yau babu komi a face nashi hakan ya bayyana hasalin kyakykywar fuskansa ga jama'a kai tsaye. Nan securityn suka shiga bashi wani irin tsaro na musamman.
★★★★
A hankali Maleek ya ɗago manyan idanunsa tare da kallon taswirar kasar sa da suka iso tsakiyarta.
Haka nan yake jin wani irin abu a cikin jinin jikinsa. Ji yake tamkar ya tafi yabar wani abu mai muhimmanci nashi ne a kasar ta 9j. Numfashin mai sanyi ya fesar tare da ƙkara ware manyan idanunsa yana jin yadda zuciyarsa ke hautsinawa bugunta na sake bugu.
Misalin karfe sha biyun dare Jirginsu yayi saukar angulu a cikin babban Airport din kasar kuwait. Din na Hammad international airport.
Da sauri arms ya kalleshi sai kuma yayi sauri ya mayar kallonshi gefen damanshi ganin har an buɗe ƙkofar jirgin.
A hankali ya fesar da sassayan numfashi dai-dai lokacin daya fara taka step na forko wanda ya fito da kanshi sararin garin kuwait yana shakar yancin iskar kasarsa.
“Yah Salam”
Ya furta Sabida wani irin ni'imtaccen iskar kasar sa mai dadi mai cike da salama da ke ratsashi yana shiga duk ta inda hudar gashin jikinsa yake.
Wani rin amintaccen numfashin mai cike da yanayin sauke ajiyar zuciya ya shaka like irin Wanda baya tare da natshwar nan yau kuma ya samj cikakkiyar nutsuwar.
A hankali yaci gaba da taka steps din yana sakkowa kasa.
Wani saurin runtse idanunsa yayi lokacin da ya dire tafin ƙkafarsa akan kasarsa. A take yaji naman jikinsa na wani irin tsuma tun daga can cikin jikinsa da zuciyarsa yakejiyo wani irin abu na kokarin fusgar numfashinsa. "Subhanallah!"
Ya furta a saman lips inshi yana karasawa ware eyes nashi sosae akan kasar sa. Bawai baya zuwa bane yana yawan zuwa kasar saidai zuwan yana kasancewa na sirru ne. Dan baya cikakken 5Months bai leko kuwait din ba.
Wasu shegun hadaddun dunkulallun luzury car's ne suka kutso kansu cikin airprt din. Wanda ko wacce bayan mota me makaon lamba dauke suke da sunan *GARGALION*. Ba'a taba ganin mitocin idan harba mamallakansu ne yaso a gane hakan ba. Duk wata shekarar da zata shude tana shudewane da duk samfurin sabuwar motar data fito na GARGALION din.
Wanda kai tsaye kowa yasan mamallakin sunan. Zaid ne da kansa yazo daukar biyuninsa airport din ba tare da sanin kowa ba a cikin masarautar.
Da yar sassarfa zaid ya karaso tare da hugging dan uwansa hana sumbatar shi a goshi. Tare da fadin
"Ur well come 2 u in my country twin"
Dan bubbugawa bayansa Ak yayi tare da furta "Well come back againt daya na"
Sake hugging nashi zaid yayi kana ya isa ga arms daya kasance amini a gareshi shima yayi hugging nashi.
Sake hugging Ak yayi kafin su nufi wurin dunkulallun motocin dake jiransum
Da sauri daya daga cikin tight security's din wanda ke gefen damar motar ya kai hannu jikin handle din ƙkofar ya bude Ak.
A nutse ya fada cikin motar kana sauran suka shishshiga, saida fadawan suka tabbatar da cewar ya rigada ya shiga kafin su shiga wani irin busa sarewar dake ma duk wani mahaluki cewar GAGALION ne a wurin. Domin busar da ake may ta daban ne irin me sanyin nance dake ratsa zuciya ya tsuma namomin jikin dan adam.
Wani irin lumshe ido yayi tare da budesu a firgice wata sabuwar izza da kasaita na zuwar masa.nan fa hankalin duk wani dake cikin airpot din yayo kansu duk da kasancewar tsakar dare na, amma sukam babu ruwansu wasun suma su yanzun shine rana a garesu.
Mandood dake daya daga cikin jama'ar airpot dim shima hankalinsa ba karamin tashi yayi ba. Su kuwa jama'ar sauran airpot din kowa kokarin gani yakai wurin tarin car's din, saidai security's sun hana hakan ta hanyar bashi garkuwa.
Mirza kan lafiyayyun motocin suka yi kyakykywan kwaltan airport din har zuwa EMAAR's MENTION.
Cikin tafiyar da bai wuce 50 minutes ba suka iso gaban katon get din masarautar, katon screen welpaper odysss na mention din na welcome nashi. Dauke da full name nashi shudaye da jajayen da blue din abubuwan ke zana sunan ak din. A get na farko, nu'urar dake tantance mutane ce ta tantance motar kana suka danna get na gana duk inda suka gilma sai kaga kowa a yanayi na kamewa da zuke numfashinsu na dan wani lokaci. Da wannan kaifaffan eyes din nashi yake bin ilahirin masarautar din da kallo.
Haka suka dunga shige get get ko wanne da kalan nashi tarban da sukema Ak din. Shi kuwa yana hakimce cikin tsumammiyar lafiyayyar kujerar motar ya nutse, sanyi da mayen kamshim sa na dada sanyi shi yin relax acikn kujerar mortar.
Gefe guda kuma daddadar kira'ar Afif muhd taj na tashi.
Nan din ma daya daga cikin bafadawan ne ya fito yana bude mai motar tamkar mai gudun tashin yaro a barci.A kalla saida aka kwashe sama da awanni goma ciff be fito ba, kana aka sake dibar wata gomar kafin almurin bakin takalmin shoe combat dinsa mai adon golden ya sauka saman maroon carpet din da aka shimfede masa ahankali. Sai da aka sake jan wasu sakannin kamar uku kana dayar kafar ma ta sauka sky blue din wandon cashmere nashi ya bayyana. Sannu a hankali sauran gangar jikin ma ta fito. Kaf wajen ya dauki wani irin tsitttt na bayyanuyar AK din tsaye akan diga digansa.
Tsaye yake kam akan tsahonsa na tsayayyen namiji da babu ko rankwafawa. Lallausan cashmere din jikinsa da ba sai an zauna bata lokacin lissafin kudin da suka lashe ba. sun masifar zauna masa da tabbatar da Ak din a matsayin jaruminsa mai gwara kan naira ta yanda duk yaso bisa damar da Allah ya bashi. Kamilalliyar fuskar san nan ma'abociyar kamewa da tsare gida kamar kullum a tsuke,
Saidai yau din ma dai akwai ring diamont barima manne da kunensa, hakama zanen tattoo dinsa mai fuskar lion na nan zaune daram.